Rayuwar Maraici

Chapter 03

by @teemerheart

Chapter 03 


Suna isa gida ba a dade ba sai ga su yaya Muhammad ma sun iso don Suna hanya ya bukar ya kira su ya sanar musu akan cewa an sallame su.Bayan sun gaisa ne Yaya Muhammad ya mai da hankalin sa ga Hajiya kaka yace 


“Nifa Hajiya zama kin anan hankalina baya kwanciya yanzu saboda yana yin jikin nafi so mu tafi tare dake can Kaduna mu sake ganin likita a can tunda akwae manya likitoci sosae”


Yaya Umar ne ya daura da fadi “Nima nayi Wannan tunani a raina kuma kaga zata samu Hutu sosae ba kamar tana nan gidan ba kasan hajiya da jama’a “


“Yanzu Haka daga dawowar mu ma mutum sun kai biyar suka shigo duba ta”Yaya bukar ya Fada 


Aunty ne ta daura da fadin “Haka ne kam yan dubiya ma kadai baza su barta ta huta bah”


Hajiya kaka ce tace “ Kun gama bayanan na ku,to ni ba inda zanje inan a mahaifa ta in na tafiya Ina kuke so ya Kai Zainabu”


“Hajiya a Wannan mai sauki ne sai ta dawo gida na tunda akwae dakin yara”yaya bukar ya fada 


“Aaa baza taje  gidan ka ba,Ni kan ma ba idan zanje Ina nan da ikon Allah”


“Muma bawai muna so kiyi nisa damu bane muna sone kije kika manyan likitoci a can dine”Maman Sadeeq ta fada 


“To naji sai nayi shawara tukun na”

Hajiya kaka ta fada tare da komawa ta kwanta 


Parlor suke fito gaba dayan su Maman Sadeeq ta wuce kitchen domin daura musu abinci,Su yaya Muhammad suka wuce gidan sa domin su samu suyi wanka su huta kafin su dawo gidan Hajiya kaka dake shi da yaya umar duka suna da gida a nan gombe.


“Jikin Hajiya nan yana daga min hankali wlh”Maman Haidar ta fada cikin damuwa 


“ abunne ya hadu da tsofa shekarun su ja sai dai muce Allah Ubangiji ya bata lafiya. Amma yanzu Haka karfi hali Hajiya take yi da kuma bata son tafi kaduna nan”Aunty ta fada 


Da Ameen ta amsa suna ciki Haka sai ga Asmira ta dawo daga Islamiyya da sallama ta shigo parlor ta gaishe su tare da tambayan jiki Hajiya kaka.


“Jikin ta da sauki Asmirah ya makarantan”maman Haidar ta bata amsa 


“Masha Allah,Allah ya bata lafiya”


“Ameen”


“Maza shiga kije ki canja Kayan ki ki wuce kitchen ki taya Umman ki aiki”Aunty  ta fada 


Da to Asmirah ta amsa sannan ta wuce daki.


Kwana biyu su yaya Muhammad sukayi a gombe suka kuma gurin aikin su a lokacin jikin Hajiya kaka da sauki ba laifi Alhamdulillah sai Dan abinda ba a rasa ba.Aunty Tana zuwa kullum duba Hajiya kaka idan ta taso daga gurin aiki kafin ta wuce gida.


*****

A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah yanzu haka Asmirah Sunyi registeration na Jamb.Ta mai da hankalin ta sosai wajen karatu saboda tana son ta samu result mai kyau tunda Medicine and surgery take so ya karanta.


Babbban burin Hajiya kaka a yanzu shine ta samu da aurar da Asmirah tunda dai ance saura kadan su gama makarantan to amma babban matsalan shine ita Asmirah bata kula samari ko kadan don akwae ni matashi a kan layin su yana masifar son ta amma ita bata san ma yana yi ba don kallon ida yake ma bata yin balle ma har ta kula shi.Shi ko biyyaya yake yiwa Hajiya kaka kusan kullum da yanma sae yazo ya gaishe ta abin ba karamı kona ran Asmirah yake ba.


Aunty ne tazo gaida Hajiya kaka ranan Saturday Asmirah tana gida ba school ai ko Hajiya kaka kamar jira take ta fara fada” yanzu Hafsatu haka zamu zuba ma yarinyan nan ido muna kallon ta ace har yanzu bata fito da miji ni wlh abin yana damu na”


“Haka ne kam Hajiya to amma ai har yanzu Asmirah yarinya ce duka duka shekaran ta 17 ne don dai an sata a makaranta ne da wuri”


“To daure ma kugu zakiye?to ni dai Auren ta zanyi da zaran ta kammala karatun nan na dai Fada miki”


“Allah ya kawo mijin nagari”


“Ameen ko kefa haka zaki fada ai.yanzu ga yaron nan Usmanu mai hankali amma bata kula shi “


“Jikar takı ne sai addua”Aunty ta fada Tana Dariya 


Asmirah tana daga daki tana jin su a ranta take cewa”ni yanzu mai na tare wa tsohowar nan ne take so ta aurar dani gwara ma ta kwantar da hankalin ta don sai na gama Karatuna duka kafin nayi aure.Tab so Aure manya to ni Ina naga saurayin ma da har take maganan Aure kwanan”


Bayan kwana biyu da tafiyan Aunty ne jiki hajiya ya tashe sosai don hankalin Asmirah yayi mumunan tashi cikin kuka ta kira yaya bukar da wayan kaka yazo da mota so kakai ta asibiti sannan ya Kira Aunty ya sanar ta ita. Ba a dade ba suka taho Ita da yan uwanta mata likita yazo ya yi mata allurai sannan yasa mata drip sannan ta samu bacci.bayan magariba ta farka jikin dai da sauki zamu ce suka tambaye ta ya take ji yanzu da sauki ta amsa musu a hankali Aunty ne tace to yanzu Asmirah tabi maman Sadeeq su tafi gida ita kuma da maman Haidar zasu kwana a nan. Da to suka amsa bayan sallan isha suka wuce gida.


Misalin Karfe biyu na dare Aunty ta fakar don sake duba jikin Hajiya sai dai tana taba ta bata ji alaman motsi ba cikin tashi hankali ta Kira likita, ba dade wa sai Gashi yazo ya duba ta yayi gwaje gwaje maman Haidar banda kuka ba abinda take yi Aunty ma Kawae dauriya take yi hakuri ya basu tare da jan mayafin da ke jikin Hajiya kaka ya rufe mata fuskan ta yana fadin sai dai muyi hakuri fa Allah Ubangiji ya karbi abin sah.