ZEE ƳAR ƘARYA

2..

by @hussainyusuf

ZEE YAR KARYA

PART 02..

Halima, dan Allah ki taimake ni! Wannan mutumin, Khalid, yana son ya ganni gobe,” na fada cikin damuwa yayin da nake zaune kusa da ƙawata Halima a cikin kayataccen dakinta na alfarma.

​Halima ta dubeni, ta tabe baki. “Zainab wai yaushe zaki daina wannan ƙaryar? Idan mutum yana sonki da gaskiya, zai so ki ne a yadda kike.”

​“Ba zai taba so na ba idan ya san zahirina” Na katse ta. “Kalli gidansu, kalli motocin da yake hawa. Halima, ina bukatar ɗakin hotel na kwana daya, kuma ina buƙatar mota. Dan Allah ki tambayi yayanki ya bamu arar motarsa ta kwana daya.”

​Halima ta ja numfashi. “To, zan iya taimaka miki da motar, amma maganar hotel fa? Kudi ne fa da yawa.”

​Na kalli dan kunnen zinaren mahaifiyata wanda ta boye shi a matsayin kadara. Na sace shi ne dazu kafin na fito. “Zan sayar da wannan,” na fada muryata tana rawa....

​Washegari, na isa babban hotel din dake cikin gari, sanye da kaya na alfarma. Na dauki hoton kofar dakin na tura a matsayin “Home sweet home”. Bayan awa biyu, Khalid ya iso. Agogon hannunsa kadai ya isa ya biya kudin hayar gidanmu na shekara goma, ballanta motarsa.

​“Zainab, kin fi kyau a zahiri.,” Khalid ya fada yana murmushi, idanunsa suna yawo a jikina.

​“Nagode Khalid, barka da zuwa masoyina” na fada ina kokarin boye tsorona.

​Muna cikin hira, wayata ta fara ruri. Mahaifina ne. Na yi watsi da kiran. Ya sake kira. Na kashe wayar baki daya. Amma ban sani ba, ashe akwai babban dalilin da ya sa yake kirana a wannan lokacin.

​“Me ya faru? Kin ki daukar wayar,” Khalid ya tambaya yana dubana da alamar tambaya.

​“Kawai masu neman bashi ne na kamfanina, zan kira su daga baya, yanzu lokacinka ne my darling” na fada ina dariyar karya.

​Amma kwatsam, sai aka buga kofar dakin hotel din da karfi. Ma’aikacin hotel din ne tare da wasu ‘yan sanda. “Wace ce Zainab a nan?” daya daga cikin ‘yan sandan ya tambaya.

​Duk dakin ya yi tsit. Zuciyata ta hau bugawa da sauri, ko mahaifiyata ta gano na sace mata dan kunne...?

A zuba ruwan liking da comments don samun ci gaba...