Page 2
by @nanadiso10
ZUCIYA
DA ƘUNA
By Billy S. Fari & Nana Hadiza
@nanadiso10 | Arewabook
PAGE 2.
Washe garin safiyar Paris ta waye cikin wani yanayi mai ɗan sanyi da shiru mai nauyi a unguwar Neuilly-sur-Seine, gidan dangin Haroon Kareem ya cika fal da mutane masu zuwa gaisuwa, motoci suna jere a waje, ana shiga ana fita ba ƙaƙƙautawa, kowa da fuskarsa ɗauke da tausayi da jimami, kowa na magana da murya a ƙasa kamar ana tsoron a ƙara tada wani sabon ciwo, a tsakiyar wannan taron ne jaririn da bai wuce kwana biyu da haihuwa ba ya zama abin kallon kowa, mutane na kallonsa da tausayi, wasu na girgiza kai suna cewa “Subhanallah… yaro ƙarami haka ya rasa iyayensa” wasu kuma na share hawaye suna furta “Allah ya raya shi cikin alkhairi” amma duk da wannan taron da wannan hayaniya mai sanyi, akwai wani abu da ya fi ɗaukar hankali Fatima, wacce tun jiya bata samu nutsuwa ba ko da minti ɗaya, idanunta sun kumbura, kanta na mata ciwo, zuciyarta cike take da wani irin tsoro da ba ta iya bayyana shi ba, haroon ya yi ƙoƙarin janyo ta su koma gida domin ta huta amma cikin kuka ta ce “No… I’m not going anywhere… ni da baby zamu kwana anan” ya kalleta cikin natsuwa ya san hakan zai faru, tun daga daren jiya ya riga ya yanke shawara a ransa cewa wannan yaron nasa ne har abada, ba zai bari wani ya shiga tsakani ba, ba zai bari wani ya ɗauke shi ba, saboda haka bai ƙara mata gardama ba sai dai ya ɗan shafa kanta a hankali yana cewa “It’s okay… I understand” dare ya shige, aka siyo madarar jarirai domin a ba shi amma abin mamaki yaron ya ƙi karɓa, yana ta kuka, ihu yana ƙara, kamar yana neman wani abu da ya ɓace masa, hankalin kowa ya tashi, wasu na ƙoƙarin ɗaukar shi, wasu na girgiza kai, amma babu wanda ya iya kwantar da shi, Fatima kuwa ta rungume shi kamar zuciyarta zata fita, ta ƙi bacci, ta ƙi zama, tana tafiya da shi a hannu tana lallashinsa “please baby… please calm down… I’m here…” amma yaron bai daina ba, sai da safe ya waye cikin wannan hali, a cikin wannan taron ne Zeynab, ƙanwarsu Haroon amma ba uwa ɗaya ba, Mahaifin su ne ɗaya. ta tsaya tana kallon Fatima da yaron, sannan cikin ɗan ɗaga murya ta ce “Sis… banda abunki fa, ina ke ina raino? You’ve never had a baby before…” kalmarta ta fito da ɗan zafi, wanda ya sa wasu suka juya suna kallonta, kafin Fatima ta ce wani abu, kakarsu Haroon Dada tsohuwa mai hikima da nutsuwa ta ɗago kai daga inda take zaune tana cewa “Zeynab… ki kiyaye bakinki, idan ba za ki godewa Fatima ba, to kar ki ƙara mata ciwo” Zeynab ta yi murmushi mai ɗauke da raini tana cewa “Grandy… you know me now, ai ni zan kula da yaron nan, ko ba haka ba?” kalmar ta faɗi da sauƙi amma ta sauka da nauyi a zuciyar Fatima, gabanta ya faɗi, zuciyarta ta ɗan buga, amma ta yi shiru, ta ƙara rungume yaron kawai, ta miƙe ta nufi babban falon gidan inda mata ke zaune, mahaifiyar matar Umar ce ke zaune tana karɓar gaisuwa, tana kuka lokaci-lokaci, Fatima ta ƙarasa kusa da ita, ta zauna, matar ta ɗago ta kalleta cikin tausayi “Sannu Fatima… Allah ya saka miki da alkhairi” wasu matan suka fara magana a gefe “Allah mai iko… ashe ita ce zata raini yaron” wata ta ce “To ai ba ta taɓa haihuwa ba…” wata kuma ta ce “Dada ce ta fi dacewa da shi” kafin hayaniyar ta ƙaru, mahaifiyar matar Umar ta ɗaga murya cikin ƙarfi “Ku daina magana haka Babu wanda ya cancanci zama uwarsa sama da Fatima” shiru ya sauka na ɗan lokaci, amma wata tsohuwa a gefe ta sake cewa “Haba… yaro fa yana buƙatar wanda ya san raino…” kalmomin suna shiga kunnen Fatima kamar allura, amma bata ce komai ba, ta yi shiru kamar yadda take yi, sai ƙarar wayarta ya katse komai, ta duba, saƙo daga Haroon “Come upstairs… Aslam room” ta miƙe a hankali, jikinta ba ƙarfi, idanunta sun yi nauyi, zuciyarta cike take da damuwa, tana tafiya har ta isa matakala, kafin ta hau sai ga Zeynab ta biyo ta “Fatima… yakamata ki sauko da yaron nan, people want to see him… kin ɗauke shi kamar naki ne” kalmar ta sake soka mata zuciya, cikin ƙarfin hali ta ce “To…” ta miƙa yaron ba tare da ta kalle ta ba, ta juya ta haura sama, hawaye na zuba a idonta, zuciyarta na raɗaɗi, tana shiga ɗakin da aka nuna mata, ta tarar da Haroon zaune a kan kujera, jikin sa ɗan sanyi, fuskar sa ta nuna gajiya, bai faɗa mata ba cewa an yi masa allura saboda zazzabi, ya san idan ta sani hankalinta zai ƙara tashi, da ta gan shi, sai ta garzaya ta rungume shi, kuka ya ƙwace mata “Ils ne veulent pas me donner le bébé… Zeynab keeps talking… Haroon please… he’s my baby… I love him… I will take care of him… please…” ta riƙa magana cikin harshen Faransanci tana kuka kamar zata fadi, Haroon ya riƙe ta a hankali yana shafa bayanta “Fatima… please… calm down… kina son ki ƙara tashin hankali ne?” ya ɗan ɗaga kanta ya kalle ta cikin ido “Listen to me… yaron nan naki ne… nobody will take him from you… ke ce uwarsa… and you will even choose his name… he has no mother now… you are his mother… do you understand?” ta kalleshi cikin mamaki, idanunta cike da hawaye “Da gaske?” ya ɗaga mata kai “Yes… I promise” sai a lokacin ta ɗan sauke numfashi, zuciyarta ta ɗan samu natsuwa, daga nan ta lura da jikin sa “Are you sick?” ya yi murmushi mai laushi “I’m fine…” amma ba gaskiya ba ne, duk da haka farin cikin da ya shiga zuciyarta ya sa ta manta da komai, har ta yi sujudin godiya a gefen gadon “Alhamdulillah…” Haroon ya kalle ta da tausayi, yana jin yadda take jin wannan yaro kamar nata, a daidai lokacin Aslam ya shigo da abinci, ya ajiye yana cewa “You need to eat bro…” sannan wasu ‘yan uwa suka shigo suna masa gaisuwa “Ya jiki?” “How are you holding up?” Uncle Usman ya zauna kusa da shi yana cewa “Na san dole ka ji zafi… you were very close to Umar” Haroon ya sauke kai, kalmar ta taɓa masa zuciya, kafin yanayin ya koma kuka, Aslam ya yi sauri ya ce “Doctor said no stress please…” Fatima ta miƙe a hankali ta bar ɗakin, ta sauko ta koma kusa da Dada, wacce take son ta sosai, Dada ta ja ta kusa da ita “Zo nan…” ta zuba mata abinci da kanta “Sai kin ci…” Fatima tana cin abincin a hankali, Dada ta ɗago ta kalli Zeynab “Zeynab… ga uwarsa nan… ki kawo mata yaronta” Zeynab ta ji haushi sosai amma bata da wani zaɓi, ta miƙa yaron ba tare da so ba, Fatima ta karɓa da sauri kamar wanda aka ƙwace mata wani abu mai muhimmanci, ta rungume shi “My baby…” ta miƙe da shi ta nufi kitchen “Let me prepare his milk…” duk mutanen da ke wurin suna kallonta, wasu suna jin tausayinta, wasu suna jin mamakin yadda ta haɗu da yaron cikin sauri haka, ta shirya madarar cikin nutsuwa, ta dawo ta zauna, ta fara ba shi a hankali, abin mamaki… yaron ya fara sha, ya yi shiru, kamar ya gane hannun da ke riƙe da shi, kamar ya sami abin da yake nema tun jiya, Fatima ta kalle shi hawaye na sauka amma wannan karon na farin ciki ne “See… he knows me…” bayan ɗan lokaci, bacci ya ɗauke shi, bacci mai nauyi wanda bai samu jiya ba, ita ma ta jingina da kujera, jikinta ya yi sanyi, idonta ya lumshe, kamar karon farko tun jiya da ta samu natsuwa, Dada ta ɗan gyara mata mayafi, mutane suna ci gaba da shigowa suna gaisuwa har zuwa dare,
Washegari Fatima na zaune a gefen falon tana riƙe da jaririn da ya yi bacci a jikinta, fuskar ta ɗan samu natsuwa bayan dogon kuka da wahala, hannunta na shafa kansa a hankali kamar tana jin tsoron wani ya zo ya kwace shi, Dada na zaune kusa da ita tana kallonta cikin tausayi, amma daga ɗayan ɓangaren falon Zeynab na tsaye tana kallon su da wani irin ido mai cike da rashin jituwa, zuciyarta ba ta kwanta ba tun da aka ce Fatima ce zata riƙe yaron, duk da murmushin da take yi a gaban mutane, a cikin ranta akwai wata wuta mai zafi, tana jin kamar an ƙwace mata wani abu da ya kamata nata ne, sai ta juya ta nufi inda Fatima take zaune, mutane suka ɗan yi shiru suna kallon ta, saboda sun riga sun lura da yanayinta, ta tsaya a gabanta tana kallon jaririn sannan ta ce cikin murya mai ɗan sanyi amma mai tsini, “So… yanzu ke ce uwarsa kenan?” Fatima ta ɗago idanunta a hankali, ba ta amsa ba, sai ta ƙara rungume jaririn, hakan ya ƙara ɓata ran Zeynab, ta ɗan yi dariya kaɗan tana cewa, “Interesting… very interesting… mace da ba ta taɓa haihuwa ba suddenly ta zama mother overnight,” wasu daga cikin matan suka fara kallon juna, Dada ta ɗan motsa amma bata yi magana ba tukuna, Fatima ta sauke idanunta tana ƙoƙarin kaucewa rikici, amma Zeynab ba ta tsaya ba, ta ƙara matsowa kusa da ita, “You think it’s easy? Kina ganin raino wasa ne? Do you even know what you’re doing?” muryarta ta ƙara ƙarfi kaɗan, mutane suka fara jin abin da take faɗa, wasu suka fara girgiza kai, Fatima ta ji kalmomin suna shiga zuciyarta kamar wuka, amma ta yi shiru, sai hawaye suka fara taruwa a idonta, Zeynab ta ci gaba, “Wannan yaron yana buƙatar wanda ya san responsibility, ba wanda kawai yake emotional saboda ba shi da haihuwa,” kalmar ta fito da tsauri, wannan karon Fatima ta ɗago kai, idanunta sun cika da hawaye, “Please Zeynab…” ta faɗa a hankali, amma hakan bai sa Zeynab ta tsaya ba, sai ta ɗan sunkuya kusa da ita tana faɗin cikin harshen Turanci mai tsini, “Let’s be honest… you’re just trying to fill a void… right?” wannan kalma ta karya zuciyar Fatima gaba ɗaya, hawaye suka zubo da sauri, jikinta ya fara rawa, ta ƙara rungume jaririn kamar yana kare ta daga duniya, “Stop it…” ta faɗa cikin muryar kuka, amma Zeynab ta sake cewa, “You’re not his mother… and you will never be,” wannan kalmar ita ce ta ƙarshe da ta karya komai, Fatima ta fashe da kuka sosai, kuka mai ƙarfi wanda ya sa kowa a falon ya yi shiru, wasu mata suka fara cewa “Haba…” Dada ta ɗaga hannu tare da ɗaga murya cikin ƙarfi, “Zeynab” amma kafin wani abu ya faru, ƙofar falon ta buɗe da ƙarfi, Haroon ya shigo, idanunsa sun sauka kai tsaye a kan Fatima da ke kuka da kuma Zeynab da ke tsaye a gabanta, ya tsaya na ɗan lokaci yana kallon scene ɗin, zuciyarsa ta ɗan buga, sannan cikin murya mai ƙarfi ya ce, “What is going on here?” shiru ya sauka, babu wanda ya amsa, Fatima ta ci gaba da kuka, hakan ya ishe shi fahimta, ya juya ya kalli Zeynab, idanunsa sun canza, “Zeynab… what did you say to her?” ta ɗan ɗaga kai tana ƙoƙarin nuna ƙarfi, “I was just telling the truth” kafin ta gama magana, ya matsa kusa da ita cikin sauri, hannunsa ya ɗaga slap! sautin ya cika falon, mutane suka yi shiru gaba ɗaya, Zeynab ta dafe kunci cikin mamaki, ba ta taɓa tsammanin hakan ba, idonta ya cika da hawaye, amma ba saboda ciwo ba… saboda kunya, Haroon ya nuna mata hannu cikin fushi, “Don’t you ever… ever talk to my wife like that again!” muryarsa ta girgiza falon, “Do you hear me?” ta kasa magana, ta ɗaga kai kawai, hawaye na sauka, “You crossed the line, Zeynab… you went too far,” ya juya ya kalli mutane, “From today… you stay away from my wife and my son… do you understand?” kalmar my son ta fito da ƙarfi, ya jaddada ta da nufi, Dada ta ɗan lumshe idanu tana jin daɗin yadda ya tsaya tsayin daka, wasu daga cikin mutanen suka girgiza kai suna goyon baya, Zeynab ta juya da sauri ta fita daga falon cikin kuka, tana jin kamar duniya ta rushe mata, Haroon ya juya ya nufi Fatima, ya zauna kusa da ita, ya riƙe hannunta, “Hey… look at me…” amma ta kasa ɗaga kai, kuka ya rufe ta gaba ɗaya, ya ɗan matsa kusa da ita ya rungume ta, “I’m here… nobody will hurt you… not anymore,” ya ɗan ɗago fuskarta da hannunsa, hawaye sun ɓata mata fuska, “You are his mother… and nobody… nobody will take that from you,” ta kalle shi cikin rauni, “Really?” ya ɗaga mata kai, “Yes… I promise you,” ta ƙara rungume shi, kuka yana raguwa a hankali, jaririn a hannunta ya motsa kaɗan kamar yana jin yanayin, Dada ta matsa kusa da su tana cewa cikin nutsuwa, “Komai ya wuce… ki kwantar da hankalinki,” falon ya fara dawowa da hayaniya a hankali, amma wannan karon kowa ya san wani abu ya canza, wani layi ya ja… wanda ba za a sake ketarawa ba, kuma a cikin wannan dare, Fatima ta fahimci abu ɗaya ba kowa ne ke son farin cikinta ba… kuma ba kowa ne zai iya tausayinka acikin yanayin da kake ciki ba don haka dole tasan cewa ba kowa bane abun yarda...
_Sau da dama namiji kan taka rawar gani wajen shamakance iyalansa ga wata aibantawa daga wajen yan uwansa don gina mutuntakarsu a zuciyarsu, shin kuna ganin abinda HAROON yai yayi daidai kuwa?_
BZ2026
***
***.