PAGE 61 - 65
by @swrites22
Dagowa yayi tare da sa idonsa cikin nata na yan dakiku sai kuma ya kalli najwa data zuba masu ido, idon sa ya maida Kan seenan uniform din yabi da kallo sky blue din shirt ce mai dogon hannu sai dark blue skirt wanda ko knee dinta bai karasa ba daga sama kuma ta kaishi har flat tommy dinta dake nan kamar bata cin abinci , sai black long pant da black socks da takalmi kallon sa ya maida sama ganin da dan karamin hijab din da take zuwa school wanda ko kirjinta Bai gama rufewa ba.
kasa² yake Mata kallon kurillla Wanda a tsawon zaman su bai taba Mata irinsa ba, haka kawai yaji wani abu ya darsu a ransa tare da jin kishin uniform din tafiya ya fara ba tare da yace komai ba najwa tace a dawo lpy ya amsa da Allah yasa .
Riko hannun seena najwa tayi sai a lokacin ta dawo daga duniyar tunanin data lula bayan sadam din tabi da kallo kafin ta sauke ajiyar zuciya suka shige ciki.
Suna shiga daki seena tayi jifa da scul bag dinta ta fara rage kayan jikin hade da jan karamin tsuka najwa ta kalleta tana yar dariya kasa ² , kallonta tayi tare da fadin "ke kuma me kikewa dariya ?
"baakomai fa ta fada tana sakin dariyar dake cinta, wani tsakin ta sake ja tana watsawa najwan hararar , tsagaita dariyar tayi tana fadin " kyaji dashi dai kina so kina kaiwa kasuwa har da wani lafewa sai kace wata mage ba saban ba anji.... hanata karasawa tayi ta hanyar fadin
" banza kefa whl najwa abun naki Kara gaba yake, to ni nace ma ya riqeni ne ya baini in fadin mana whl ki fita a idona bana san iskanci ki shiga hankali kafin mu haura yamma da kudu tana kaiwa nan ta shigewar ta toilet cikin borin kunya, daga murya najwa tayi yadda zata jita tace " Allah ya baki hakuri matar yaya .
Umma na shiga parlourn ta tarar da sajida (yar yayanta)da nafisa zaune suna hira sai Afnan dake cin abinci tana sanye da uniform da alama bata dade da dawowa daga makaranta ba.
A dage sajidar tayiwa umma sannu da dawowa itama sama² ta amsa Mata ta wuce sama ko sauraron nafisa dake Mata magana ba tayi ba domin duk yadda zaayi yau take so ta fara aikin ta tunda yau girkin tane dole tasan yadda zatayi sadam yaci wanna maganin .
seena na fitowa daga wanka tayi sallah ta shirya ba tare data Kula najwa ba ta dauki wayarta ta fice, saida ta leqa nina ta samu tana bacci sannan ta sauka kasa .
Abinci taci sannan ta fita wajen su inno ta zauna tana taya su hira tana dan danne² ta awaya amma duk rabin hankalin ta na wajen su tanajin hirar da suke tare da sauran masu aikin gidan Cox she had learned to listen while others speak ! The more she listen the more she learn and understand the concept of what's actually being brought to the table, understanding other peoples opinion enable her to come up with the great ideas and advice.
Mikewa tayi bayan ta gama jin yan hirarrakin nasu tace " inno barin shiga daga ciki .
" toh uwar dakina a fito lpy, Allah huta gajiya
Kamar zatayi part din nasu sai kuma tayi part din umma, clashing tayi da sajida ita tazo fitowa ita kuma tazo shiga idon ta akan wayar ta saisa bata lura da sajidan dake ta zabga uban sauri ba .
jakar sajidan ce tayi gefe abubuwan dake cikin ta suka watse a wajen , idon ta takai Kan yar karamar kwalbar turaren dake tarwate awajen turaran ya zube akasa
"Kan ubancan sadiqa ta fada tana ciza yatsa ke daga wani gidan mahaukatan kika fito da bakya ganin gabanki kin kuwa san tsadar kayan da kika fasa shegiya jaka dabba wadda bata ganin gabanta to ko ke aka siyar baza ki kawo kudin wanna turaren kadai ba bare wayoyina da sauran abubuwan ta fadi tana sunkuya wa da niyyar Kai hannu wurin turaren .
cike da haushin zagin data karemata seena ta tofa yawo kan turaren hadi da sa takalmin ta ta murje ruwan turaran a tiles din ganin ai itama bata sani bane shine zata kama zaginta cikin kunan rai da takaici sajida ta dago da niyyar kifawa seena Mari taji an rike hannun ta gam juyawa tayi dan ganin wani me karfin halin ne.
Adnan dake tsaye rike da hannun nata da alama ya dade awajen ya kalli seenah ba alamun Wasa tare dashi yace " wuce ciki , fasa shiga part din umman tayi ta juya ta koma bangaren su.
Wani kallo sajida ta watsa masa a wulakance tace Kai dalla Malam sakarmin hannu kai kuma awa Kare da gudun layya har zaka wani zo ka shirgar Mata Karan Kada miya , ba tare da yace Mata uffan ba yayi tsaki ya wuce dan yasan idan yace zai tsaya suyi musayar yawu da wanna marar kunyar zai iya illata ta , ni na rasa ma Mai wanna take zuwa yi gidan nan shima daddy ya zuba Ido Yana kallo wanna ai sai ta bata masa tarbiyyar ya'ya ma ya fada a zuciyar sa yana shigewa bangaren su.
Ko da ta jiyo tayi arba da turaran data sha wahala a kansa amma duka gashi bai amfane ta ba wata banza can tazo ta fasa shi "wallahi sai naci ubanta ko wace ita.
Duk dauriyar ta kasa tsaida kukan daya zo Mata tayi dan ita kadai tasan yadda takeji a kan turaren da aka fasa Mata ,wayoyin ta da Jakar ta dauka tabar sauran tarkacen zube a wajen ta juya ta koma side din umman da gudu tana kuka.
Da tunani iri² ta shiga dakin nasu , sosai ta sa ayar tambaya kan turaran da wanna matar ke masifa akai ganin turaren da baikai ya kawoba a yar kwalba take wanna masifar a kan sa, take nan wata zuciyar ta ayyano mata umma sai kuma ta karyata zuciyar ta da cewa to Amma ai ko umma za tayi hakan baza ta hada baki da yarinya kamar wanna ba saboda gudun tonon asirin ta , waje ta nema ta zauna tana ci gaba da nazari ko Kula najwa dake sake tsokanar ta ba tayi ba dan dama cike take da ita har malamin su yazo suka shirya su kayi waje .
Da kuka sajida ta koma parlourn Wanda hakan yasa nafisa tashi da sauri tana tambayar ta mai ya faru amma bata kulata ba , wucewa tayi ta shaidawa umma ita kuwa tace a rabu da ita kawai hakan yasa nafisa dawowa ta zauna hadi da zuba Mata Ido saida taci kukan ta sannan tace wacece ita ?
"Wa kenan ? Nafisa ta tambaya
"Wata kucakar yarinya na hadu da ita kofar part din nan ta bata min rai
"Seenah ? Nafisa ta tambaya dan ta san sajidar ta san Najwa so saidai in seenan ce
"Oho wacece ita a gidan nan
Tabe baki nafisa tayi tare da fadin yar uwar su daddy ce
Ba tare data sake cewa komai ba ta tashi ta zari jakar ta tayi waje .
Umma kuwa yamma nayi ta shiga kitchen ta yiwa sadam danbum nama tun a tukunya ta zuba maganinta tana ta farin ciki dan tasan sadam da masifar son dambun Nama.
Sai da suka gama cin abincin dare suka dawo parlour aka fara hira Nina ta kalli najwa da fadin "je ki kifitomin da seenah ita shikenan yanzu ta koyi wata sara kullum tana daki ta daina fitowa ayi breakfast ko dinner tare bare yar hirar da ake yi , bana son takura mata ne kawai saisa nayi shuru amma naga abin nata bana kare bane daddy yace nima yanzun nake shirin magana akai najwa jeki kirawo ta, da toh ta amsa tana tashi dan zuwa Kiran seenan.
A kwance ta same ta sanye da long pant white da armless t shirt onion colour wadda da kadan ta sauka lap dinta hannun ta riqe da wayar ta tana danne², sadaf² najwa ta karasa kusa da ita ta sunkuyo daidai kunnen ta ta saki ihu cikin firgici seena ta hantsilo daga Kan gadon dariya najwa tasa har tana rike ciki da sauri seena ta tashi ta ajje wayar ta ta nufo najwan ganin hakan ya sata ficewa da gudu itama seenah ta rufa Mata baya .
zagaye parlourn suka fara dakyar seenah ta rikota hade da gantsara Mata cizo a kumatu murza wajen najwa ta shiga yi kafin tace" kefa kinfiya wasan Yara whl, murguda Mata baki tayi tace
" eh anji din wayasa kizo ki tsora tani ina zaman zamana .
" toh ai mijin ki ne yake neman ki wai yayi missing dinki najwa ta fadi tana mai kashe Mata Ido daya .
"mtweee kinci kai whl ta fada tana yin hanyar dakin su , da sauri ta janyota ta tare da cewa "ke daddy da nina ne fa suke kiranki in kuma baza kije bane inje Ince masu kince baza kizo ba , kwafa tayi tare da nufar stairs tana fadin " ke dai whl baki da magana daya shikenan dai mutum ace ba shi da aiki sai ance kace nace biyo ta najwan tayi tana dariya tace "oho dai muje .
tunda suka shigo parlourn hankalin sadam ya koma kan seenah sosai yaga ta masa kyau kamar wata babyn roba ji yake kamar yaje ya daukota da kallo ya dinga binta har ta karasa gaban nina ta zauna tana fadin nina gani najwa tace kuna kira na ke da daddy , Nina tace wai Mai yake boye mana ke ne a daki kwata² kin canja kaman ba ke ba ko wani ya miki laifi ne ta karashe tana wurgawa sadam dake kallon su harara dauke Kai yayi Yana murmushi .
" a a whl nina ko daya kawai karatu ne kinsan mun kusa fara exam kuma a lokacin da kuke dinner ni kuma bana jin yunwa saisa.
" my dear wanna ba hujja bace kuma komai ai Yana da lokacin sa karatun ma in yayi yawa ai baya shiga kuma cin abinci cikin Yan uwa ai yafi dadi ko .
" in sha allah zan gyara Nina.
"yauwa to ko kefa tashi ki hau kujera ki zauna mikewa tayi ta koma kusa da najwa ta zauna ana hira jefi² wasu kuma na kallo, yayin da sadam hankalin sa gaba daya Yana Kanta da sun hada Ido zata dauke Kai tana murguda masa Baki .
umma dake lura dasu taja kwafa tana murmushin da ita kadai tasan fassarar sa ta kalli nafisa tare da fadin "tashi kije part dina kan centre table ki daukowa yayan ku dambun naman dana masa , zunburo baki tayi tana bubbuga kafa tace " Nikam umma ki aika Afnan mana ai itace karama sai ace ni zanje ke afnan tashi kije.
" au ban isa in aikeki kije ba Kenan ko ai nasan da Afnan din nace ke zaki dauko, tashi tayi ta nufi sashin nasu tana gunguni.
sadam yace hajiya yau danbu akai mana Kenan cikin fara'ar data bawa kowa mamaki abinda bata saba ba tace ai yau da kaina na shiga kitchen saboda nasan Kana sonshi sosai kuma tunda Ka dawo ban ma wani abu ba saisa dai yau nace barin ma favourite dinka.
cikin dan jin shakkun abun ganin ko daddy umma bata shiga kitchen ta masa girki bare kuma shi da har zata ce ta shiga ta masa abu yace hajiya kuma dan za amin danbu saikin shiga da kanki ai ko sawa kika yi za'ayi min, da murmushi tace to kuma laifine danna shiga da kaina na girkawa da'na abinda yake so.
Nina ce ta kalli daddy shima ya kalleta ba dai suce komai ba , Adnan yace to umma mu kuma daga bola aka dauko mune da banji ance damu ba dariya tayi tare da fadin
"karka damu kuma duk za'ai maku naku amma wanna nasa ne dan shi kadai nayi bashi ma da yawa amma tunda Ka fara korafi gobe za'ai maku kuma.
tuni seenah ta fara harhada maganganun umma tare da tuno abubuwan da taji tana fada shin maisa tace shi kadai ? Zuciyar ta ne ta shiga dukan tara ² mai ke shirin faruwa ne wai mai za tayi ta hana shi cin dambun nan gumi taji ya fara tsatsafo mata dukda AC da suke aiki har dan rawa jikin ta ya fara gani take idan har yaci kuma wani abu ya sameshi itama da tata gudummawar tunda tana sane amma ta kasa hana aukuwar hakan duk da bata da tabbas ko an sa wani abu a dambun.
Nafisa na shiga taga container a rufe Kan center table kamar yadda umman ta fadda dauka tayi ta bude tana gunguni
"kuma sai anci din haka kawai zanyi wahalar banza ai ba yar aikin su bace, zama tayi ta diba tana ci saida taga ta kusan rabi sannan ta goge bakinta ta rufe ta fice .
A gaban sadam ta ajje container din tana komawa wajen zaman ta zauna, addu a kawai seena take a ranta kar yaci , ganin bai dauka ba yasa umma cewa ha'a ka dauka kaci mana baka ji yadda yayi dadi ba dauka yayi ya bude da sauri seenah ta fara tarin karya dakata wa yayi daga kokarin diba yana jin yadda kamshin dambun ya bugi hancin sa murmushi yayi tare da rufewa Yana kallon seenah dake tari kamar gaske najwa na dan bubbuga bayan ta yace ruwa zaki bata kika tsaya kallon ta da sauri najwa ta mike ta nufi water dispenser
" bata wanna ya fada Yana Mika Mata robar faro Mai sanyi dake hannun sa , dawowa tayi ta karba hadi da karasawa ta mikawa seenah ruwan karba tayi ba tare data sha ba ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya , kallon sa tayi suka hada Ido girgiza masa Kai tayi hade da yi masa alama da Ido Kan kada yaci , tsayawa yayi Yana kallon ta ba tare daya fahimci Mai take nufi ba , ganin bai fahimce ta ba yasa ta murguda masa baki tare da banka masa hararar ta juya wajen su daddy dake Mata sannu.
Tsaki umma taja cike da haushin seenan tace ya ka rufe kuma , murmushin yake yayi dan ya tafi tunanin mai seenah take nufi yace hajiya barin bari saina shiga daki kar asamin wawa su hanani cin abin kirki Adnan yace aiko birnin sin Ka tafi tare zamu raba
"kuma haka fa da gaskiyar ka Kam gwara Ka boye duk da ba haka taso ba amma ba taso tayi insisting a fahimci wani abu.
Hira aka ci gaba dayi har 10:40 sannan kowa ya tashi amma seena ta kasa tashi har sai da najwa ta zungure ta tana fadin "tashi mu tafi mana .
"kije ina zuwa zata Kara magana ta tare da naj nace ina zuwa kije kawai wucewa tayi ta barta nan parlourn .
Kallon nafisan dake zaune tana danne² tayi kafin ta Mike kamar bata so ta nufi side din su sadam da harara nafeesah ta bita tana fadin "shegiya Munafuka yarinya har tasan ta fara bin miji daki hmmmmm Allah ya kyauta.
A zaune ta same shi Yana waya ga wasu takardu gaban sa ajiyar zuciya ta sauke tana karasawa cikin parlourn dagowa yayi ya sauke idon sa akanta da mamaki yake kallon ta, sallama tayi a Karo na biyu ganin kamar baiji wadda tayi a farko ba amsawa yayi a hankali still yana kollonta ba tare daya katse wayar ba duk sai taji ta takura kuma ganin ko dankwali bata dauko ba ga kayan jikin ta ba wasu na arziqi ba domin duk wata surar jikinta kayan sun bayyana .
daburcewa tayi ta rasa abinda za tace ganin hakan ya sashi katse wayar tare da fadin lpy ?
"umm dama daman nace kaci dambun da umma ta baka ? shuru yayi yana goga Kan pen din a lips dinsa kafin yace banci ba wani abu ne ?
"Yana ina ta sake tambaya ba tare data bashi tasa amsar ba .
" Gashi can ya nuna Mata Kan table din TV, wucewa tayi dan zuwa ta dauko .
ajiyar zuciya ya sauke tare da maida idon sa ga takardun dake gabansa amma yakasa gane abinda ke Kan paper sake dago kansa yayi daidai lokacin ta dawo dauke da container tace in baza Ka damu ba zanje dashi .
why ? ya tambaya Yana jifan ta da wani kallo wanda ya sata yin kasa da kanta .
murmushin karfin hali tayi tace" its my favourite snack please kabaimin , ganin yarinya karama nasan rikita masa lissafi yasa ba shiri yace jeki tho , har ta fara tafiya sai kuma ta juyo idon su ya shige cikin na juna kasa tayi da nata cikin baby voice dinta tace baka ci ba ko ?
girgiza mata Kai yayi tare da lumshe Ido ya jingina kansa jikin bangon kujerar, kallon sa tayi jin bai ce komai ba ta sake cewa baka ci ba? Bude Idon sa yayi yace yeah banci ba juyawa tayi da sauri ta fice har tana hada hanya.
Adnan ne ya fito daga dakinsa yace emir kaida waye ne naji kamar magana ko kunne na ne ba tare daya kalle shi ba yace 'seenah' jin sunan yayi wani bambarakwai kasancewar bai taba Kiran sunan haka ba.
"toh mai ya kawota? Ba tare daya dago ba yace yi maza Ka bita sai ka tambaye ta, dan tabe baki Adnan yayi ya karasa ya dauki system din sa dama abinda ya fito dauka Kenan ya wuce .
Ko da ta fito parlour bata sami nafeesah ba kamar yadda ta barta an kuma kashe komai sai dan haske kadan da aka bari dawurwuri ta tsaya yi na yadda zatayi da dambun sai kawai ta wuce kitchen leda ta samu ta juye a ciki kamar zata fita boys quarter ta bawa masu aikin gidan sai kuma wata zuciyar ta gargade ta da cewar Ka so wa dan uwanka abinda zaka so wa kanka, karka bawa wani abinda kasan Kai ba zaka iya ci ba ta hana sadam ci kuma itama tasan baza ta iya ci ba to mai sa zata Kai musu, dustbin ta bude ta jefa sannan ta wanke hannun ta ta wuce daki.
Washe gari kuwa umma da rigima ta tashi na cewa daddy yana nuna banbanci a tsakani mai sa zai siyawa su najwa waya bai siyawa Afnan ba, daddy ne ya gyara tsayuwar sa da fadin umaimah ki bar maganar nan saina dawo kinga yanzu office zan shiga ana jirana zan yi budget ne .
"gaskiya alhaji ba ai min adalci agidan nan kullum yayan nabila ne a sama komai su in ka tsanemu ai sai ka fada.
"yanzu ke umaimah akan waya kike irin wa annan maganganun kuma Naga ai Afnan din wanna shekarar zata shiga ss1 su kuma bakya ganin 2 zasu shiga bakya tunanin bata waya a yanzu zai shagaltata.
" toh su maisa bai shagal tasu ba ai suma bagamawa sukayi ba wato sai yayana ne shagalallu ko alhaji, cikin kosawa daddy yace shikenan zansa akawo Mata , ya juya ya fice dan yasan in zasu kwana umma bata taba ganewa a ko da yaushe a matsayin sa na mijinta bai isa yasa doka tabi ba saisa kullum yake Kara san Nina ko tsinke ya jefar in yace karsu tsallaka daga ita har yayan ta ba mai karasawa ko wajen balle aje ga tsallaka wa , alhaji nura ma (yayan umma)yayi fadan harya gaji sai dai kawai ya bashi hakuri in umman tayi wani abun
Umma ce zaune a main parlour su seenah suka shigo sun dawo daga makaranta da fara'a ta tarye su tana fadin "yan makarantar bokoko akwai karatu akwai sallah sannu Ku da zuwa cikin parlourn suka karasa suna mai zubewa a kujera seena tace hajiya ke kadaice Kenan .
"whl ni kadai ce zaman ne ya isheni nace barin zo nan na jira Ku najwa tace umma sannu da hutawa .
" yauwa najwa ya karatun ? " alhamdulillah whl.
Hira ta fara jansu dashi cike da raha yayin da seenah ta sake sosai har abin ya bawa najwa mamaki dan ita a darare take, kusan 30mins suka Mike domin shiga ciki Umma tace haseenah yarinyar kirki in kin huta kizo ki tayani gyaran wardrobe dina mana kinga Afnan sun fara lesson nafisa kuma bata nan , najwa zatayi magana seena ta kyafta Mata Ido sannan ta kalli umma tana fadin " karki damu barin watsa ruwa saina shigo.
cikin farin ciki umma tace to shikenan ina jiranki.
Suna shiga daki najwa ta rikota " wai mai sa kika amsa mata gsky kar kije nifa na kasa ganewa umma kawai suddenly mu ga ta canja ni dai ban baki goyon bayan zuwa ba, mai sa kuma za tace ke kadai in da gaske gyaran wardrobe dinne ai ke kadai baza ki iyaba da sai tace muje mu biyu gsky to be frank with you ban yarda da umma ba.
murmushi seenah tayi tare da fadin bakyau zato domin shi zato zunubi ne najwa Allah yace
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اجْتَنِبُوا كَثِيرًا مِنَ الظَّنِّ إِنَّ بَعْضَ الظَّنِّ إِثْمٌ ۖ وَلَا تَجَسَّسُوا وَلَا يَغْتَبْ بَعْضُكُمْ بَعْضًا ۚ أَيُحِبُّ أَحَدُكُمْ أَنْ يَأْكُلَ لَحْمَ أَخِيهِ مَيْتًا فَكَرِهْتُمُوهُ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۚ إِنَّ اللَّهَ تَوَّابٌ رَحِيمٌ
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nĩsanci abu mai yãwa na zato. Lalle sãshen zato laifi ne. Kuma kada ku yi rahõto, kuma kada sãshenku yã yi gulmar sãshe. Shin, ɗayanku na son yã ci naman ɗan'uwansa yanã matacce? To, kun ƙĩ shi (cin nãman). Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai karɓar tũba ne, Mai jin ƙai.
kika sani ko nutsuwace tazo Mata "nutsuwa najwa ta maimaita tunda shekara nawa nutsuwar bata zo ba sai yanzu girgiza Kai seenah tayi
"bazan iya maki ba naj bari in je in watsa ruwa .
Saida suka gama komai seena ta tashi tace bari kiga na amsa gayyatar umma.
" toh muje na rakaki da sauri tace " a a dear tunda tace ni kadai in mukaje tare zata ga kaman wani abu ne dan Allah kiyi hakuri ki zauna bazan dade ba , cikin jin haushi najwa ta dauki wayar ta ta wuce daki, kamar ta bita ta mata magana ganin kamar tayi fushi amma tasan ba lalle ta saurareta ba hakan ya sata tafiya dakin nina nan ta same ta ta fito daga wanka tana shiryawa .