PAGE 66 - 70
by @swrites22
A hannu kujera ta zauna tana fadin " nina sannu da gida ."
" Baby ashe kun dawo ya karatun yanzu nake cewa naji shuru ko har yanzu baku dawo bane ".
"a a mun dawo muna daki har ma mun ci abinci."
" toh hakan ma yayi ina najwan ?"
" tana daki ".
" ai fa shikenan tunda ta samu wayar nan mun bani, dan dariya tayi tace "nina barin shiga wajen umma, kallonta tayi ta mirror. "mai za kiyi wajen umman ?"
" itace tace nazo na tayata gyara wardrobe dinta shuru nina tayi kamar za tace a a sai kuma taga in tayi hakan yanzu sai ya zama abun magana ace tana nuna iko hakan ya sata cewa a dawo lpy."
*********************
A parlourn ta sami umman tsaye tana jiran ta , kallon ta tayi na yan dakiku sannan ta karasa shiga cikin parlourn ta nemi waje ta zauna tana fadin
" hajiya gani na cika alqawari murmushi tayi
" gsky Kam yarinyar kirki barin dauko maki madarar shanun da aka kawomin dazu daga kauye kinsan amarya da sauri tace a a ki barta kawai I'm okay muje in tayaki gyaran da kikace a fakaice umma ta galla mata harara sannan tayi gaba tashi tayi ta bita a baya tana sake sake.
Kallon kayan dake kan gadon tayi tare da kallon umma ganin ba wasu kayan azo a gani bane amma har take fadin azo a tayata tabe baki tayi ta karasa tana fadin " wa annan ne kayan ?
" Eh sune ai ganin zasu maki yawa yasa na rage maki aiki na linke wasu , bata ce komai ba ta fara linke kayan da sauri da sauri tana sawa a wardrobe dan dama a linke suke kawai hargitsasu akayi tana daga rigar karshe wani turare ya fado kallon umma tayi tace " hajiya ga turaranki .
" wani turare kuma ? dauko shi tayi tare da miko mata
"laaa wanna ai turaran dana dade ina nema ne ashe cikin rigar nan ya shige ina son turaran saboda kamshin sa amma dauki kawai nabar maki kya ringa amfani dashi idan mijinki na gidan, ita dariya ma abun ya bata amma ta danne tace hajiya yanzu fa kika gama cewa kina son kamshin sa kuma kice zaki bani inaga kin fini bukatar sa a halin yanzu ko ta karashe tana dasa alamar tambaya ?
" Eyyerh ai dane dana neme shima bangan shi ba saina sayi wani wanda ya fishi kamshi dan haka kije dashi kawai idan kinga mijinki na gida kiyi kwalliya ki shafa abinki dan sai kina dagewa kinga sadam ga arziki ga ilimi ga kyau idan kika tsaya Wasa saidai kiji ana ayyiriri yiriri ya auro daidai dashi tunda kinga ke ba auran soyayya kukayi ba su alhaji ne suka makala masa ke shi kuma saboda biyayya baiyi musu ba.
Ba karamin zafin maganar seenah taji ba amma ko a fuskar ta bata bari hakan ya bayyana ba sai murmushi da tayi tace "shikenan hajiyar mu nagode sosai kuma zanyi amfani da shawarar ki, cikin farin cikin hakarta ta kusa cimma ruwa tace yauwa ko kefe yar gari ai saida gyara kinga jeki abinki nagode kinji Allah yayi Albarka , juyawa tayi ta fita ba tare data Kara magana ba ita kuma umma ta bita da hararar tana fadin
" na dai kusa maganin ku munafukar yarinya tazo ta wani mike kafa sai kace gidan uban ta an kusa komawa kauye aje a ci gaba dacin koriyar miya taja tsaki tana tashi ta shige toilet .
Tana fita garden ta wuce nemi waje ta zauna sosai zuciyar ta ke kuna akan maganganun umma dukda tasan da biyu ta gaya mata amma kuma a wani bangare tana da gaskiya dan tun ranar da daddy ya fada masa zancen auren ta fuskanci haka " to maisa daddy zaiyi hakan maganar daya fadawa nina ranar ta shiga dawo mata, in kuwa hakane to gsky ba'a Mata adalci ba mutumin da bai dauke ta a bakin komai ba kawai a tashi a aura masa ita kamar wata marar galihu , ya daketa ya zageta kuma wai tana a sunan matar sa , itafa duniya takan zama kurkuku ga matan da ba suyi dacan Mazan kwarai ba masu san su da gaskiya domin samun miji nagarih Mai tsananin kaunar Ka na daya daga cikin abinda kesa mace rayuwa cikin kwanciyar hankali da jin dadi .
saisa yana da kyau mu tsaya da addu a akan Allah ya hadamu da abokan rayuwa nagarih tare da neman zabin Allah Akan duk wani lamuran mu, kar soyayya ta rufe maki Ido daga waje kije ki auri wanda bana kwarai ba .
to balle kuma ni da inada yakinin ko takalmin kafar sa ya fini daraja wani abun ma kawai yana ragewa ne saboda tsoron daddy , kwalbar turaran da umma ta bata ta daga ta rotsa a bango tana mai fashewa da kuka ta hada kai da guiwa saida taji kanta ya fara ciwo sannan ta tashi ta wanko fuskar ta ta nufi cikin gidan a parlour ta samu nina da najwa suna kallo nina na ganin ta tace "yauwa dama yanzu nake cewa najwa ta tashi taje ta kirawoki naga kin dade murmushin yake tayi hadi da fadin
" Ai kuwa sai gani ba , barin shiga daki kafin Malam yazo , har tayi gaba nina ta sake kiranta
" zo nan baby meya saki kuka ? " laa kuka kuma nina ah ah ba kuka nayi ba nazo shigowa ne wani abu ya fada min a Ido barin shiga in Kara wankewa ta karashe tana barin parlourn da sauri gudun Nina ta sake koro Mata wata tambayar .
Tana shiga daki ta jingina da kofar tana share kwallar da suka zubo Mata ta daga hannu sama tana fadin ya Allah kadubi lamuran na Ka kawomin mafita kamin zabin alheri a rayuwata اللهُمَّ لاَ سَهْلَ إِلَا مَا جَعَلْتَهَ سَهْلاً، وَأَنْتَ تَجْعَلُ الْحَزْنَ إِذَا شِئْتَ سَهْلاً
Ta shiga maimaitawa tare da wucewa Kan gadon ta kwanta.
Najwa ce tace "nifa nina nake ga kamar karya seena take akwai abinda ke damun ta ko umma ce ta mata wani abu kuma whl nina komai ma ta mata ai ita taja saida nace kar taje tace sai taje kuma nace zan rakata tace bata so dan nasan halin umma saisa ni kwata² ban wani sake da ita ba, dan jijjiga Kai ninan tayi tana fadada tunanin ta akan maganar najwan ba tare data ce mata komai ba.
1 WEEK LATER
seena ta rage yawan walwala irin nada ta zama wata so silent dukda kuwa zata zauna cikin su in ana hira amma har a tashi ba lalle tayi kwararan magana sau uku ba , idan daddy ko nina suka tambaye ta kuwa sai tace stress ne na karatu saboda exams .
Ba karama damuwa najwa ta shiga ba ganin wanna sauyin daga seenah Wanda ba haka suke ba ada ayi Wasa ayi dariya su tsokani juna suyi fada amma yanzu duk babu Ko daya ko tsokanar ta tayi saidai ta kalleta tayi murmushi kawai taci gaba da abinda takeyi.
Hakan ce ta kasance da sadam domin shima samun kansa yayi da rashin walwala domin alamu sun nuna masa seenah na da damuwa amma shi dai bazai iya zuwa ya tambaye ta damuwar ta ba bare ya tambayi Najwa ko Nina meke damunta , Amma duk lokacin da suke zaune waje daya to hankalin sa na Kanta.
ita kuwa umma ganin canjin nan yasa ta zaci cewa aikin tane yaci saisa ta dauki layar ma taje ta adana kamar yadda malamin nasu yace da ita.
sai dai kuma wata sabuwar matsala da ta fara fuskanta daga nafisa wadda ta kasa ganewa wato na yawan fitar da take, idan tasa kafa awaje to sai dare.
ko da daddy ya nemi yi Mata fada akan hakan Kiri² tace itafa ba yarinya bace dan haka kar ya takura mata Wanda daddy ya taalaqa hakan da umma ganin itace me goyon bayan duk wani abun da suke .
Ita kanta umma data Mata magana saida ta kusan kai mata duka sosai abun ya fara bawa umma tsoro kuma da sata a tsaka me wuya dan sosai nafisa ta tubure ta zama wata tsagerar karfi da yaji.
Tabbas sihiri gaskiya ne domin Allah ya fada a alqur'ani me girma .....
ﻭﺍﺗﺒﻌﻮﺍ ﻣﺎ ﺗﺘﻠﻮ ﺍﻟﺸﻴﺎﻃﻴﻦ ﻋﻠﻰ ﻣﻠﻚ ﺳﻠﻴﻤﺎﻥ ﻭﻣﺎ ﻛﻔﺮ ﺳﻠﻴﻤﺎﻥ ﻭﻟﻜﻦ ﺍﻟﺸﻴﺎﻃﻴﻦ ﻛﻔﺮﻭﺍ ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺍﻟﺴﺤﺮ وما ﺃﻧﺰﻝ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﻠﻜﻴﻦ ﺑﺒﺎﺑﻞ ﻫﺎﺭﻭﺕ ﻭﻣﺎﺭﻭﺕ ﻭﻣﺎ ﻳﻌﻠﻤﺎﻥ ﻣﻦ ﺃﺣﺪ ﺣﺘﻰ ﻳﻘﻮﻻ ﺇﻧﻤﺎ ﻧﺤﻦ ﻓﺘﻨﺔ ﻓﻼ ﺗﻜﻔﺮ ﻓﻴﺘﻌﻞﻣﻮﻥ ﻣﻨﻬﻤﺎ ﻣﺎ ﻳﻔﺮﻗﻮﻥ ﺑﻪ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻤﺮﺀ ﻭﺯﻭﺟﻪ ﻭﻣﺎ ﻫﻢ ﺑﻀﺎﺭﻳﻦ ﺑﻪ ﻣﻦ ﺃﺣﺪ ﺇﻻ ﺑﺈﺫﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻳﺘﻌﻠﻤﻮﻥﻣﺎ ﻳﻀﺮهم ﻭﻻ ﻳﻨﻔﻌﻬﻢ ﻭﻟﻘﺪ ﻋﻠﻤﻮﺍ ﻟﻤﻦ ﺍﺷﺘﺮﺍﻩ ﻣﺎ ﻟﻪ ﻓﻲ ﺍﻵﺧﺮﺓ ﻣﻦ ﺧﻼﻕ ﻭﻟﺒﺌﺲ ﻣﺎ ﺷﺮﻭﺍ ﺑﻪ ﺃﻧﻔﺴﻬﻢ ﻟﻮ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ.
Wannan ayar ta nuna cewa sihiri gaskiya ne, kuma sihiri yana cutar da mutane amma duk saida izinin Allah.
To hakance ta kasance domin duk sauran aikin sun lalace amma Layar nan takama, hakan yasa su nina suka fara rage kula da seena instead ma sai suka fara hantarar ta haka ta bangaren sadam ma in dai yana waje yaga tazo giftawa to zai daka Mata tsawa ko ya korata har sai tabar wajen.
sosai seenah ta sake fadawa wani tashin hankali amma ta rasa Wanda zata fadawa damuwar ta, mahaifiyar ta ba wani shakuwa mai karfi a tsakanin su bare ta iya fada Mata, hajjo ma kuma ta kasa fada Mata ta bar abunta ita kadai ta dai ci gaba da addu ar neman mafita .
TOH MASU KARATU MAI KUKE GANIN ZAI FARU
MUJE ZUWA