7
*KUNDINA*
*SASAAL* ***
7
Na fara rubuta tarihin rayuwata, da kuskuren da na aikata wa kaina, wanda har yau na nake nadamarsa a cikin *KUNDINA* kamar haka;
Sunana Fatima Umar Alƙali. An haifeni a garin Kano, Unguwar jan bulo.
Mahaifana ƴan asalin ƙauyen Gaya ne.
Neman ilimi ne ya shigo da Mahaifina cikin birni Kano ba tare ya san kowa ba.
Bayan gama karatunsa, ya samu aiki a kotun shari'ar Musulunci, sannan ya faɗa harkar kasuwanci.
Da ya tashi yin aure ƙayensu ya je ya auro ƴar uwarsa Saratu Hajiya Babba.
Haihuwarsu Ɗaya ƴa mace mai suna Zainab da suke yiwa alkunya da Ummi saboda sunan Mahaifiyarsa da ya saka, ya ƙara auro Maryam ƴar Abokin mahaifinsa, mahaifinyata kenan.
Bayan wani lokaci. Hajiya Babba da Mahaifiyata suka haihu a tare, dukkansu ƴaƴa mata.
ƴar Hajiya Babba aka raɗa mata Safiyya ita kuma ƴar Mahaifiyata aka raɗa mata Rahma.
Zaman haƙurin da babu fifiko Babanmu yake yi da su Mama. Su ma a tsakaninsu kowacce ta riƙe mutuncinta, ba sa faɗa, kuma basa hira, kowacce rayuwarta take yi a sashenta.
Daga haihuwar farko Mama bata ƙara haihuwa ba, sai Hajiya Baba da ta ƙara haifar Namiji ɗaya Usman da aka yiwa alkunya da Abba sai Fa'iza.
Sai bayan wasu shekaru, su Aunty Ummi da Aunty Rahma da Aunty Safiyya sun zama ƴammata Mama taƙara haihu ta samu Mace Baba ya saka sunan Mahaifiyarta Sa'adatu, suna kiranta Su'ad
Daga haihuwar Su'ad, zaman Mama da Hajiya Babba ya canza salo.
Faɗan da basa yi, Hajiya Babba ta ƙirƙiro a tsakaninsu, sai dai tsoro irin na Mama yasa faɗan bai yi tasiri ba, su koma kamar yadda su ke da.
A lokaci ɗaya Hajiya Babba da Mama suka ƙars samun ciki.
Tazarar haihuwarsu sati ɗaya ne kacal. Mama ce ta fara haifata kyakkyawa da ni, kamar yanda ta bani labari. Sannan Hajiya Babba itama ta haifi Farida.
A haka rayuwa tayi ta shuruwa, Ni da Farida mune ƙanana saɓanin yayyenmu da suka zama manyan ƴammata
Aunty Rahma ce ta fara yin aure, ta auri attajirin Matashin Ɗan kasuwa.
A tare Aunty Ummi, da Aunty Safiyya, suka samu Mazajen aure, masu kuɗine babu laifi, amma ba kamar Mijin Aunty Rahma ba.
Rashin samun Miji Attajiri kamar na Aunty Rahma baƙaramin sosawa Hajiya Babba rai ya yi ba.
Amma dole ta ja bakinta ta tsuke, tunda ga Fa'iza da Farida da take fatan su samu wanda ya fi na Aunty Rahma, ba ma irin nata ba.
Shekarar Aunty Rahma biyu da aure ta rame ta lalace, idan Mama ta tambayeta sai tace sabon cikin jikinta ne yake wahalar da ita.
Babu wanda Aunty Rahma ta gayawa halin da take ciki har ta zo haihuwa Allah Ya ɗauki ranta da Babyn.
Irin kukan da Mijinta yake yi ne, yasa Baba ya tausayamai ya ce ya bashi aure Su'ad.
Anan ma Hajiya Babba ƙiri-ƙiri ta fito da hassadar ta wai ga Fa'iza nan da ta girmi Su'ad ba ace ya aura ba, saboda an raina kyan nata ƴaƴan shine za'a ƙara maƙala masa Su'ad.
Ƙorafin Hajiya Babba bai tsaya a iya ita da Baba ba, sai da ta kai maganar har gaban Iyayensu.
Da yake Kakarmu tafi son ta akan Mama, a take tace a kira mata Mijin Marigayiya Aunty Rahma.
Har Gaya Mijin Marigayiya Aunty Rahma ya je, a gaban kowa ya shaida shi Su'ad yake so.
Babu yanda Hajiya Babba ta iya haka ta haƙura, aka ɗaura auren Aunty Su'ad da Mijin Marigayiya Aunty Rahma.
Kamar dai Aunty Rahma, itama Aunty Su'ad haka tayi ta ramewa, idan Mama ta tambayeta sai ta saka kuka, ta ce sam bata jin daɗin zama da Mijinta, dan Allah Mama ta taimaka tayiwa Baba magana a raba auren.
Duk lokacin da ta kawo irin wannan ƙorafin, Mama bata tsayawa saurararta take katseta da cewa;
"haba Mamana kowa fa haƙuri yake yi, ki yi haƙuri, In Sha Allahu wata rana zai zama labari"
Irin waɗannan kalaman Mama ne yasa Aunty Su'ad ta daina zuwa gida kwata-kwata.
Ranar da muka yanke shawarar zuwa dubata Ni da Mama, lokacin Shekaruna 15 ina aji biyar ɗin Sakandare, Mijin Aunty Su'ad ya zo gida yana kukan Allah Ya yi mata rasuwa.
Mutuwar Aunty Su'ad babu wanda bai girgiza ba, har Hajiya Babba da take kwaɗayin kudinsa sai da ta tsorata, aka fara zargin ko ɗan shan jini ne.
Sai dai kaf binciken da su Baba sukayi a ɓoye, ba su gano wani alama da ya nuna yana da wani ɓoyayyen abu da yake yi a ɓoye ba.
Su ma maƙota an tambayesu a sirrince sun ce basu san shi da wata matsala ba.
Bayan an gama zaman makokin Aunty Su'ad Baba ya roƙi alfarmar kar Mijinta ya ƙarar zuwar mai gida, ba wai don yana zarginsa ba, sai don ganinsa ya na tunamasa da ƴaƴansa biyun da ya rasa.
Daƙyar da addu'a Mama ta dawo hayyacinta, saboda ɗorawa kanta alhakin mutuwar Aunty Su'ad da tayi, a cewarta da ta saurareta ta ji matsalarta da yanzu bata mutu ba.
Bayan Shekaru biyu komai ya zama labari.
Aunty Fa'iza tayi aure, amma bata aure amma ba da irin hamshaƙin Mijin da Hajiya Babba take buri ba, ya na dai da kuɗi dai-dai gwargwado.
Yaya Abba shima ya zama Babban mutum ya yi aure yana zaune a Abuja da iyalinshi.
Ni da Farida mun kammala Sakandare har mun fara zuwa Jami'a.
A wannan lokacin Baba ya auro Hanifah Aunty Amarya, ƴar Attajiran da ya haɗu da ita a wajen Dinner ƙarin auren Abokinsa.
Dole Hajiya Babba ta ƙara kame kanta, saboda Aunty Amarya ba irin Mama ba ce mai haƙuri, tsoro da kawaici. Kai tsaye take komai na ta.
A ɓangaren Mama gaba ɗaya, burin duniya ta ɗora a kaina.
Bini-bini ta siyo kayan kitchen ta ce wannan naki ne Fatima, komai ta gani ya yi mata kyau sai ta siyo, ta ce nawa ne.
Wannan siyayyan na Mama shi yaƙara rura wutar son aure a raina.
Kyakkyawa ce ni, ƴar gata mai zafin kai, tsayina dai-dai misali, gashin kaina mai kyau da silɓin da yake ƙarbar gyaran irin wadatar da muke ciki
A wannan gaɓar Sadiq ɗan ƙwalisar matashi, Ɗan Aminin Baba ya shigo rayuwata.....✍🏻