8
*KUNDINA*
*SASAAL ****
8
Ba zan ce Sadiq yana cikin sahun Mazan da suka fi kyau ba, amma yana daga cikin Mazan da sutura ke yiwa jikinsu kyau da kwarjini.
Komai nasa yana yin sa ne cikin aji da nuna isa.
A makaranta muka haɗu da shi ya na 400 level ni da Farida mu na 100 level.
Lokacin da ya tare ni da zancen so na amsa masa. Daga nan muka fara yawo tare a makaranta.
Zuciyar ƴammata da yawa ta shiga ruɗani, har da Farida ƴar uwarta. Gaba ɗaya daina kulani ta yi, mu ka daina zuwa Makaranta tare, ko da lokacin lecture mu ya zo ɗaya daban take tafiyarta.
A ranar da Sadiq ya fara zuwa gaishe da su Mama da Baba, kasa ɓoye farin cikinsu su kayi, saboda farin sanin da suka yiwa kirkin Iyayensa.
Daga wannan rana Mama ta ƙara ƙaimi waje tara kayan kitchen.
Abinda ya ƙaramin zumuɗi akan auren Sadiq, shine yanda Mama take bin dangi, tana gaya musu na samu Mijin aure, kowa sai kira yake yana tayani murnar, da addu'ar Allah Ya kai mu lokaci.
A ɓangaren Sadik ma, Iyayensa, sun ba sa cikakken goyon baya, tare da nuna farin cikinsu.
Mahaifiyarsa har gida ta zo ita da ƙannensa Mata biyu, suka zo ganina da kyaututtukan kayan sawa da kayan kwalliya masu kyau da tsadar gaske a cikin akwati mai kyau.
Tun kafin su tafi na ji kaina ya fashe, saboda yadda Mommynsa take jaddada gaskiya bata taɓa ganin yariyar da Sadiq yake so kamar ni ba. Ta ce shiyasa ma ta kasa haƙuri ta ce dole ta zo ta ganni. Fatanta dai Allah Ya sa ayi da mu.
Sun jima suna hira da Mama har Baba ya dawo daga wajen aiki, suka gaisa Sannan suka fara shirin tafiya.
Kafin su tafi sai da ta kaisu suka gaisa da Hajiya Babba har da Aunty Amarya, sannan tayi musu rakiya har bakin Mota.
Bayan tafiyarsu Mama da farin cikinta tasa mai aiki tayi mata rakiya da akwatin da suka kawo, ta kaiwa Hajiya Babba da sam lamarin baya yi mata daɗi ta gani, ta kaiwa Aunty Amarya itama ta gani, suka sanya albarka.
Ranar da Sadiq zai tafi service ranar Iyayensa suka kawo kuɗin aurena.
Gaba ɗaya kaina sai ƙara ɗaukar zafi, ina jina kamar na fi kowa sa'a, musamman da Sadik ya kirani ya na rairamin waƙoƙin soyayya kala-kala, tare da zubomin godiya har da kukan daɗin na amince zan aure shi.
Bayan mun gama waya na kalli kaina a mudubi yafi sau biyar, kalaman Sadik da sautin kukan farin cikinsa su na ƙara tsumani.
"Gaskiya ni mai sa'ace, Sadiq ga kyau dai-dai misali, ga iya kwalliya, ga ilimi, ga kuɗi, Allah na gode maka ni Fatima"
Ranar saboda yawan Karaye-kirayen waya taya murna daga ƙawayena ƴan makarantarmu saboda na saka a Status da ƴan uwana kashe wayata nayi ina juya idanuwana.
Bayan wani lokaci;
Babbar illar da ya fara shigata ba tare da ita kanta Mama da take aikawa ta lura ba, shi ne zumuɗin siyayyan kayan amfanin da take yi yana ƙaramin ƙarfin gwiwar mallakar Sadik a matsayin Miji ko ta halin ƙaƙa.
Dalilin siyi waccen siyi wannan na Mama, da yadda ta gama gayawa dangi lungu da saƙo maganar auren, ya sa na dawo lallaɓa Sadik.
Ko faɗa mukayi akan abinda bai kai ya kawo ba, haka zai yi ta fushi ina bashi haƙuri.
A hankali soyayyarmu ta fara canza salo wata uku da kawo kuɗin auren Sadik gidanmu.
Ranar da Daddare ya turomin saƙon;
"Babe cikina ciwo, na kasa cin komai"
Cikin tausayin da ya bayyana a muryata na tura masa voice note;
"Subhanallah, menene yake damunka Yaya Sadik? Yanzu tun safe baka ci abinci?"
Shima sautin muryarsa da ya yi ƙasa-ƙasa sosai ya turomin;
"Wallahi ban ci ba Babe, gaba ɗaya yanayina ya canza kawai ji nake yi kamar zan mutu"
Ina gama saurara na ruɗe na tura masa;
"bari na kira Mommy na gayamata"
Ina tura masa haka sai ga kiran wayarsa ya shigo.
Hannuna ya na rawa na ɗaga..
Murya a tausashe kamar Maraya ya ce;
"Maiyasa baki da fahimta Fatima? Yanzu baki san me nake nufi ba? A haka zamuyi aure ba kisan me Mijinki yake so ba? Fatima ke nake buƙata ba magani ba, dan Allah ko iyakacin hoton jikinki ki ne rage kayan jikinki ki turomin ko ki cire gaba ɗaya na gani naji daɗi, a wajenki kawai zan iya samun wannan alfarmar don Allah"
Ɗif jina ya ɗauke, na yi maza na katse wayar nan ta ke, na kashe gaba ɗaya.
Daren ranar kwana nayi a zaune, ina tunani.
kuma na kasa fita na gayawa Mama halin da nake ciki, saboda zumuɗin da uban kayan da ta siya akan auren.
A wannan dare naji son Sadik ya fara raguwa a cikin zuciyata, har na fara tambayar kaina;
"Shin idan na turamai video da hoton tsaraicina wannan zai sa ya tsaya ya aure ni, ko kuma a'a ko ya samu zai tafi ya barni?"
Amsar;
"zai tsaya ya aureki"
Zuciyata ta bani, tunda abinda yake so kenan, zaki ƙara samun gurbi a cikin zuciyarsa.
A jikina nake jin shawarar da zuciyata ta bani ba daidai ba ne. Sai dai tsoron rasa Sadiq da tuna irin siyayyan kayan da Mama tayi, da dariyar da dangi zasu yi mana, idan ya ce ya fasa aurena yasa nayi watsi da komai, na yi na'am da shawarar da zuciyata ta ba ni.
Wannan shine mafarin kuskuren da na aikawatawa rayuwata.
★washe gari da kaina na kirashi bayan na karya.
Ga mamakina bai yi fushi ba kamar yadda ya saba.
Bugun farko ya ɗaga muryarsa ƙasa-ƙasa.
Ina cewa;
"ina kwana ya ya Sadik"
maimakon amsa ya fashe da kuka ya na cewa;
"Yanzu Fatima akan kawai na ce zanga jikinki na samu sauƙi, shine kika kashe wayarki, kin fi so na mutu kenan ko? Fatima ba fa lalata na ce zan yi dake ba, kawai ki nunamin jikinki na gani shine kike guduna? wacce irin soyayya kikemin, da babu sadaukarwa a ciki?
Wallahi da ni kika ce na nuna miki jikina, da gudu zan turo miki komai ki gani.
Amma babu komai ki riƙe jikinki, zan nemi wata ta nunamin, "
Ya na gama faɗa ya katse wayarsa.
Tashi hankalina ya yi, na fara kiransa babu ƙaƙƙautawa, bai ɗaga ba sai a wajen kira na goma.
Shima ya na ɗagawa ya ce;
"Maiyasa ki ke kirana eh? Bari na gayamiki maganar gaskiya Fatima wallahi bazan iya auren macen da take kokwanto akan irin son da nake mata ba, gani kike yi ni lalatacce ne ko? To shikenan ki je ki auri wanda ba lalatacce ba"
Kafin ya katse nayi sauri na ce;
"Don Allah kayi haƙuri, wallahi zan nunamaka, amma kayimin alƙawarin bazaka canza min ba, dan Allah ka ji"
Na ƙarasa faɗa ina runtse idona.
Marairaice muryarsa ya yi ya ce;
"Sauyi kuma Fatima? wallahi har abada ba zan sauya miki ba, kin san matsayinki a raina kuwa? Duk duniya bayan Mommy da Daddy ke ce ta ukun su, ke ce rayuwata, ke ce macen da nake kallo a matsayin farin cikina, sannan ki ce zan sauya miki, ai daga ranar na shiga uku na lalace, kar ma ki ƙara maganar rabuwar mu Fatima dan Allah na roƙe ki"
Ya ƙarasa faɗa yana sakin kuka....✍🏻
Rashin comment da like yasa ba na dogon pagi🤗