9
*KUNDINA*
*NAFISAT ALIYU SASAAL*
***
9
SADIQ; marairaice muryarsa ya yi ya ce;
"Sauyi kuma Fatima? Wallahi har abada ba zan sauya miki ba, kin san matsayinki a raina kuwa? Duk duniya bayan Mommy da Daddy, ke ce Macen da nake kallo a matsayin farin cikina, sannan ki ce zan sauya miki, ai daga ranar na shiga uku na lalace, kar ma ki ƙara maganar rabuwar mu Fatima dan Allah na roƙe ki"
Ya ƙarasa faɗa yana sakin kuka.
Sanyi jikina ya yi nima na fashe da kuka, ina ji a raina zan iya yin komai don farin cikinsa.
Ban tsagaita ba, har sai da ya fara lallashina ya na cewa;
"Haba Babe, ki daina kuka kin ji? Ni naki ne kema tawa ce, zamu rayu har abada, ina so zuwa dare, zan kiraki Video call, ki nunamin komai kin ji, kuma bana son wannan kunyar, saboda zai ragemin sonki a raina. Baby Ko ki naso na rage sonki?"
Ya tambaya da wani irin yaudararren murya ƙasa-ƙasa.
Da sauri na ce; "a'a"
"To promise me zaki yi duk abinda na ce, kuma zaki riƙemin sirrina bazaki faɗawa kowa ba, har da ƙawayenki"
Ba tare da wani tunani ba, na ce;
"I promise"
Murmushi ya yi yace; "yanzu ki kwanta ki huta, anjima ki shirya kin ji da kayan barci mai kyau, kuma make sure kin kulle ƙofa da key, saboda ba na so Mama ta fahimci komai, kar ta ce iskanci muke yi, tasa a fasa auramin ke, da kuwa na shiga uku"
Murmushi nayi ina sauke ajiyar zuciya.
Da haka muka yi sallama, babu tunanin komai a raina, sai yarda duk da abinda ya faɗa.
Barcin da ban samu yi a daren jiya ba ne ya ɗauke ni.
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
Dare na yi, na shige ɗaki tsabar zullumi ko abincin dare ban tsaya na ci na arziƙi ba, nayiwa Mama sallama.
Kayan barci mai kyau na ɗauko na saka hannuna yana rawa, zuciyata tana tsananta bugu.
Bayan na kimtsa na zauna a bakin gado, na kunna Data ina jiran kiransa.
Sai wajen ƙarfe goma da rabi ya kirani..
Hannuna har tsuma yake yi wajen ɗagawa.
Ina ɗagawa Sadiq ya bayyana, sanye cikin guntayen kayan da suka yi masa kyau, yana kwance.
A hankali na ce; "Barka da dare Yaya Sadik ya ya jiki?"
Bai amsa ba ya ce;
"Wowww Baby kinyi kyau, Baby In Sha Allahu tare zamu rayu, tare zamu mutu, ba zan iya rayuwa babu ke ba"
Ya ƙarasa faɗa kamar zai yi kuka.
Ido na lumshe, kalamansa suna ƙara samun gurbi a cikin zuciyata tare da ƙaramin ƙarfin gwiwar son na faranta masa ko ta halin yaya.
Katsemin tunani ya yi da cewa;
"Baby, cikina har yanzu bai daina ciwo ba, ki kiyimin abinda na ce don Allah"
Jim nayi, ina tunanin ta yanda zan fara, gashi bana so nayi kuskure ya ce ya fasa Aurena.
Ganin kamar da kwakwanto a raina sai ya fashe da kuka, yana sambatun irin son da yake min da alƙawari ba zai iya rayuwa idan babu ni ba.
A wannan dare sai da Sadik yasan yanda ya yi yaga jikina, ai kuwa ya yi ta zuzuta ni, da jinjina tun da yake a rayuwarsa bai taɓa ganin macen da ta fini kyan sura ba, har da cewa kar na ƙara fita ko nan da ƙofar gida babu liƙab.
Bayan kwana biyu, Sadik ya ninka kalaman soyayyarsa a gare ni, kamar zai cinyeni.
Tun ina jin kunyar yi masa abinda yake so, har ya zama na daina ji, gaba ɗaya na watsar da lamarin karatu, sai dai kawai na je Makaranta, amma ƙwaƙwalwata tuni ta toshe da kalaman Sadik, gani nake yi ma kamar ilimin ba shi da amfani a gare ni.
Bai fasa kirana duk dare ya kalli jikina ba, ya cemin na taɓa masa can, na shafa can, kullum aikinsa kenan.
Idan nayi ƙorafi sai ya ce babu abinda yake ƙaramin ƙima a idonsa irin yadda nake bin umarninsa...
Nasha ji ana cewa duk Namijin da yake yiwa mace irin abinda Sadik yake min, ba Sonta yake yi ba. Ire-iren waɗannan kalaman a Matsayin shirme na ke jinsu, saboda ina kallon Sadik a matsayin Namiji da ya banbanta da sauran Maza.
Duk abubuwan da suke faruwa tsakanina da Sadik, da rashin mayar da hankali kan karatuna, duk Mama bata da sani akai, saboda gaba ɗaya hankalinta yana kan tara kayan kitchen, da sauran tarkacen kayan ƙyale-ƙyalen da zan tafi gidan Sadik da su...
Ku yimin afuwa bana jin daɗi ne, amma In sha Allahu, zamu dawo posting kullum🙏🏻