Page 16
GABA KURA
AISHA HANWA
PAGE 16
Ganin da suka yi cewa a doke dai Inna Hauwa ta fi ƙarfin su haka a zage ma da bakinta; shi ya saka babu wacce ta tanka sai faman gyaɗa kai kawai da suke yi.
Yara ta saka suka kwashe kayan tsab dan shigar mata da su gida, ganin ba wacce ta kula a cikinsu ya saka suka yanki hanyar gida saboda direban na sauke kaya ta sallame shi; a cikin zuciyarta tana ta dariya ganin yadda suka tsaya tsirmai kamar wadanda aka tsare gulma.
[4/6, 8:48 PM] Aisha: Jamila ce ta fara sakin tsaki tana kinkimar ledar abincinta ta miƙi hanyar gida, ganin ta fara tafiya ya saka Guggonsu ta bi bayanta tana ƙudurawa a zuciyarta sai ta nuna wa matar nan yadda ake iko da mallaka.
Suka bar Munari a tsaye tana ƙokarin taya Inna Hauwa gyaran inda zata saka kayan.
Sun samu gida an cika ana ta aikin tsinkan alaiyahu da kayan miya gida ya ɗauki haramar biki.
Duk sannu da zuwa da ake ma su bai saka Jamila tsayawa ba;Ƙoƙari take ta samu shiga ɗaki ko ta samu ta koka ta ji sanyi.
Wuce su Innayo ta yi wanda suka baje a tsakiyar ɗakin suna dakon dawowar su ita da ƴan Uwanta. Da ido suka bita ganin ko kallo basu ishe ta ba, a zabure Innayo ta bita cikin uwar ɗakin.
A tsaye ta ganta tana faman Safa da marwa a cikin ɗakin "Ke lafiyar ki ko gamo kika yi a hanya da za ki shigo mana kamar mahaukaciya?", Ɗora hannu akai ta yi ta fara "Innayo ki barni na fitar da abinda ke raina ko na ji sanyi,ki barni na yi kuka ko abunda ya dunƙule mani a kirji zai sauka". Cikin faɗuwar gaba ta ce "Ke dan Ubanki ki mani dalla dalla mijin Aminan ɗan fashi ne ko ɗan damfara?".
Ta sharbe majina kafin ta ce "Allah na tuba kawai dan mijin Amina ya kasance ɗan damfara ne zan yi kuka? Ni na kawo mata shi? ana maganar mijin me kuɗi ne ke kina wata zance".
"Na shiga uku ni Innayo wani irin me kuɗi kuma?" Jamila ta ƙara rushewa da kuka tana faɗin "Wallahi Innayo ina cikin tashin hankali, idan kika ga gidan da Amina zata zauna sai hawan jini ya kashe ki; gida aljanna duniya duk faɗin garin nan babu irin gidanta wallahi" Ta faɗa cikin kuka.
"Shi kenan tawa ta ƙare. Ina zaune Saude za ta yi arziƙi ta barni jama'a" ta juya wurin ƙanninta da tun kuka farko suka cika uwar ɗakan nata domin jin ba'asi.
Wata ƙanwarta ne wacce halinsu kamar kwabo da kwabo ta ce "Idan kin so ba!, ai ba'a rigada an ɗaura ba ki shiga ki fita a fasa shege kawai, haba Yaya sai kace ba jininmu ba ke da kanki kinsan mu Bama bora kuma bama bari wata ta yi mowa a gabanmu.
Shiga ki fita ki san yadda za'ayi ki fatattaka auran kowa ya watse".
Jin haka ya sa Jamila ta share hawayenta ta na ƙara cewa "Inna kinsan har kayanta ba su amsa ba? Komai an saka a gidan yanzu haka mun dawo da rabin kayan?".
Dafe ƙirji Innayo ta yi kafin tace "Innalillahi yau ni Innayo naga baƙar rana! Yanzu ina kayan suke?".
"Suna gidan Innarsu Hauwa ta danke a ɗakinta bansan mene ne nufinta ba yau matar nan ba irin wulaƙancin da bata yi mana ba dan taga ƴarsu zata auri me kuɗi".