Gaba Kura

Page 17

by @aishayusufhanwa

GABA KURA


AISHA HANWA


PAGE 17


 Wani busasshen murmushi ta yi kafin tace "Ƙarya take wallahi, ko me ta taka yau wannan kayan ya bar kwana a gidanta; wasa take dani" daga faɗin haka ta juya ta fice a ɗakin.

Shigowar Munari ya dakatar da Mama daga fitowa ta yi ma su Jamila sannu da zuwa.

Ana ta musu barka da dawowa Habiba na dafe da Munarin tana son ta ji kanun labarai. "Ina Hauwan?, tun ɗazu su Jamila suka shigo ina ta ware idon ganin ta inda zaku shigo amma shiru".

Murmushi Munari ke ta faman saki kafin ta ɗauki Sani dake ta faman riƙo mata hijabi yana kuka, "Mama daga dukkan alamu addu'arki ta fara aiki, gidan Aminanki tamkar gidan Gwamna, komai Ma sha Allah, a takaice kayanma daga muka je da su ba duka suka shiga ba mun dawo da ragowa suna gidan Inna Hauwa shi ya saka ma kika ga jinkirin mu saboda sai da na taya ta muka kimtsa su a cikin ɗaki".

"A kimtsa a ɗaki mana tunda daga gidan tsoho da tsohuwa aka siyo ba?" Innayo ta katse musu murnan da su Habiba suka fara yi.


 "Me ya kawo wannan maganar kuma Innayo?" .

"Komai ma anyi munafukan banza da wofi kawai to da kuka ɓoye mana mijin da kuka nemo da asiri sai me? Nace sai me?. Ta faɗa cikin faɗa idanuwanta sun kaɗa sun yi jawur tsabar bala'.

Ana cikin haka Inna Hauwa ta Kunno Kai cikin gidan, cirko-cirko ta ga mutanen gidan sun yi kowa ya dagata da aikin da yake yi ana sauraren su masu gulmar Innayo na yi suna dariya daga gefe.

"Lafiya?" Ta ambata ganin yadda ita ma suka zubo mata na mujiya.

Jin muryarta ya saka Innayo ta yo tsakar gida ta bar Mama a tsakar ɗakin ikon Allah Ya hanata magana.

Kakabin yadda Innayo bata jin tsoron Allah bata jin tsoron fito da hassadarta kowa ya gani, ba tun yau ba ta fuskanci idan har wani abu ya faru da yaranta daɗi ne ke mata yawa a ranar za ka ga farinciki da walwalarta tafi ta kullum amma akasin hakan ta dunga shiga tana fita har sai ta lalata abun.
 
  Ajiyar zuciyar ta sauke tana ƙudurawa a zuciyarta wannan karan ta yi kaɗan, za su yi fito na fito da duk wanda ya nemi kawo cikashi a wannan auren.

Hayaniyar da ta kaure ne a tsakanin Innayo da Inna Hauwa ya sakata jan kafafuwarta da suka yi mata sanyi ta nufi tsakar gidan.

Kusan a tare suka iso gurin ita da me gidan nasu. Faɗa ce na sosai ake yi wanda ya haɗa har da dangin Baban suna faɗin sai ta fito da ragowar kayan da aka dawo da shi, ita kuma ta ce babu uban da ya isa.


 Tsawa Baban ya daka masu sannan kowa ya yi shiru, ya tambayi ba'asi Guggonsu Munari ce aka ce ta yi bayani ta koro duk yadda ya faru ta ƙarkare da cewa "Ni a ganina ai sauƙi ne aka nema ma Yayan tunda akwai sauran yara mata a gidan ba sai a ajiye ba da sun kawo sai dai a ƙara da wanda babu ba?". "Hakane" cewar mutanen wurin.

Murmushin takaici Inna Hauwa ta yi kafin tace "Idan shi ya yi kayan ko?,ga shi nan ku tambaye shi idan kaf kayan zai ce shi ya bada kuɗin su, ko ko ba gudummawa ya bamu ba?.

***