Page 18
GABA KURA
Page 18
Last free page
Game buƙatar cigaban shi ya tura 500 kacal 8132283815 opay ya turo mini da shaidar biya ta whatsapp, kar ku sake a baku labari tafiyar akwai gwagwarmaya sannan akwai soyayya mai saka nishaɗi sai kunzo
AISHA HANWA
Murtuke fuska Baban ya yi ganin Hauwa na nemi zare mishi Zariya a filin idi, "Kinga Hauwa ki fita idanun na idan ba haka ba babu dole sai ki tarkata ki nufi gidanki ki ci tsiyarki a can, ni nan da kika ganni bana ƙaunar tashin hankali ko ƙankani".
"Yaushe Malam tashin hankali ya zama abun gudunka?, Ko dai ba zaka iya amsar ragowar kayan nan a wurin wannan me ido a tsakar ka ɗin bane?". Innayo ta katse shi cikin masifa ganin alamun shima kamar ba zai iya amsar kayan a gurin ta bane ya sake haukata ta ta yi.
A zabure ya juya kanta "E ba zan amsa ba ke ki amsa da kanki mana, yau ga maganar banza da wofi kawai ina namiji za ku saka ni a shirginku na mata" Ya juya ya koma waje dama kiran shi aka y.
Wata munafukar shewa Inna Hauwa ta yi ta wuce ɗakin Mama tana cewa "Dama baki shirya ba kika takali faɗan? Je ki shiryo ki dawo mu yi ta ruwa-ruwa domin ni nan da kika ganni babu mai nuna mani hannu ya maida shi lafiya wallahi gara ki kintsa kanki kafin ki ƙule ni na saita ki a hanya".
Takaici ne yayi kamar ya kashe Innayo ganin haƙarta bai samu ruwa ba.
Suna ji suna gani biki ya cigaba da wanzuwa, komai ya tafi daidai an ɗaura aure lafiya aka zo tafiya da Amarya nan ma aka ce Innayo ta je tace 'Allah Ya tsare ta taka gidan da aka gina da haramun ita ba kwaɗayayyiya ba ce' Haka nan aka ƙyaleta aka ɗauki Amarya Baba.
Anyi masu tarba ta musamman suka ci suka sha suka baro Amarya cikin ƙoshin lafiya.
Sai da Munari ta ƙara kwana a gida ita da Inna Hauwa tukuna ta fara shirye-shiryen komawa gida, gabaɗaya kuma yanzu hankalinta ya koma kan Mijinta.
Inna Hauwa tace "Za su yi shawarar yadda za'ayi da sauran kayan Amina, duk da akwai Habiba dake tasowa yanzu amma za'a ciran ma Munari abunda baza'a rasa ba acikin kayan.
Ta yi sallama da kowa ta ɗebi kayan biki da ragowar kayan gara da Mama ta ɗiban mata tace ta aikawa dangin Mijinta da shi, duk da ga baki ga hanci amma babu wanda ya leko mata.
Dama bata sa a ranta za su zo ɗinba shi ya saka ma bai dame ta ba. Da yamma liƙis ta nufi gida. Ganin kayan da yawa ga goyon Sani ya saka ta ɗauki ɗan mashi ya Kaita har gida.
Da saukarta a ƙofar gidan yara suka cika ana ta mata oyoyo. Jin haka ne ya saka maƙota suka fara leƙowa ana mata sannu da zuwa.
Yaran suka shigar mata da kayan cikin gida, ta kwance kayan duk ta bisu da dubulan, cikin farin ciki da tsalle suka fita daga gidan.
Wata makwaficiyarta ne ta shigo riƙe da hannun yaronta Khalifa yana ta cin dubulan ɗin da ta basu. "Sannu da dawowa Maman Sani,yanzu Khalifa ya shigo da dubulan ya ce ke ce kika basu,an wuce taro lafiya? Allah Ya sanya alkhairi".
Tana ƙoƙarin cirewa Sani wando zai yi fitsari ta ce "Yauwa Maman Khalifa ya gajiyanku Allah ya saka da alkhairi ya kuma bar zumunci, wallahi ƴan layin nan kun yi mini Kara sosai kuma na yaba Ubangiji ya ƙara haɗa kanmu.
"Amin sai kika ji abu ba daɗi Maman Sani?". Gabanta ne ya tattakura ya yanke ya faɗi ta saki kafar wando da zata maida wa sani ta miƙe tsaye "Maman Khalifa wani abu ya faru ne bayan zuwanku ban ji labari ba?.
Kama baki ta yi sannan ta ce "Wai dama baki san Baban Sani ya kuma ɓacewa ba? Tabɗi! To yau kwanan shi biyu ana cikin na uku ba'a ganshi ba;an dubu kaura da wanbai babu bawan Allah nan, sarakuwarki na nan a kwance ba lafiya hawan jininta ya tashi saboda damuwa.