Chapter 5
*⚖️TUHUMA!⚖️*
🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️
PAGE 5️⃣
Ba zai taɓa manta ranar farko da ya fara ganin Hafsat ba. Yana wajen aiki ne, yana tsaka da gyaran wata mota, sai ogan shi ya kira shi.
Fitowa ya yi yana Karkaɗe jikin shi, cikin girmamawa ya tsaya a gaban ogan yace "Sir an ce kana kira na."
Makullin mota ogan ya miƙa masa yace "Ma za ka je kai da Sani ku gyara waccan motar, Clutch ne ya ƙone, sai birki da ya tsinke, in kun gama ka aje makullin a wajen ka, saboda Ni zan ɗan fita, in an zo ka bada makullin, kar ka bawa Sani fa."
Amsa ya yi ya juya suka fara gyaran motar, ya san abinda ya sa ogan yace kar a bawa Sani, dan duk faɗin garejin da Anwar kaɗai ogan ya aminta, yawancin abubuwa masu muhimmanci yafi sa Anwar, saboda riƙon gaskiya da amanar shi. Saɓanin sauran yaran da in an basu makullin suke fita da motocin mutane.
Ya yi mamakin ganin motar sabuwa dall, da ya duba sosai sai ya lura tsabar garaje da ganganci da ake da motar ne yasa hakan ta faru, tsaki ya ja lokacin da ya ciro kayan da suka lalace, yana takaicin hali irin na mai motar koma waye bai san ciwon kuɗi ba, ganin yadda ya lalata motar da ta lashe miliyoyin kuɗi haka.
Har suka gama gyaran lokacin tashin su ya yi, mai motar bai zo ɗauka ba ga shi magriba ta doso, dole ya zauna yana jira, har kowa ya tafi shi kaɗai ya rage a gare jin yana tsoron tafiya su zo babu kowa, saboda motar sabuwa ce duk da akwai masu gadi yana jin tsoron barin ta a wajen.
Har a ka yi isha'i babu wanda ya zo, bisa dole ya kira ogansu a waya ya faɗa masa, sai yace ya faɗawa masu gadin wajen a sa ido sosai, shi kuma ya kulle komai da kyau ya tafi da makullin.
Haka kuwa ya yi, da sassafe da ya ke yana da Lacture ƙarfe bakwai 7:am, dan daga makaranta ya ke zuwa wajen aikin, wani lokacin kuma in ba da safe zai yi ba, ya kan tafi wajen aiki daga can sai ya wuce makaranta.
Koda ya je ogan su bai zo ba, hakan yasa ya wuce makaranta da makullin motar, yana dawowa ya tambaya mai motar ya zo? Aka ce babu wanda ya zo.
Abin ya bashi mamaki, ogan su na zuwa ya sanar masa, sai yace ya ajiye makullin a wajen sa, duk sanda aka zo amsa ya ba da.
Ya koma kenan yana cikin aiki, sai ga kira ance ya zo ya kawo makullin mota mai motar ta zo ɗauka, haka ya taso yana laluba aljihun sa dan ciro makullin.
Ganin wadda ta ke tsaye a jikin motar sai abin ya bashi mamaki, ya yi zaton zai ga babbar mace mai hankali, sai ya ga yarinya budurwa ce wadda ba za ta haura shekara sha tara ba.
Takaici ne ya kama shi a zuciyar sa yana cewa Iyayen ta basu san ciwon kuɗi bane, shi yasa suka bata wannan babbar motar.
Ya bata makullin ya juya zai tafi kenan, ya ji tace "Ji mana."
Juyowa ya yi yace "Magana ki ke?."
Gyaɗa masa kai ta yi ta yafito shi da hannu kamar ƙaramin yaro tace "Eh zo nan."
Abin ya so bashi dariya yanayin yadda ta yi, sai kace irin uwar shi ɗin nan ko wadda ta girme shi.
Shi sai lokacin ma ya samu damar yi mata kallon tsaf, kyakykyawa ce ajin farko, sanye take cikin doguwar riga ta wani materia mai kyau, ta yi rolling ɗin ɗan ƙaramin mayafi a kanta.
Yana tsaye daga inda ya ke yace "Akwai matsala ne?."
Miƙo masa makullin motar ta yi tace "Ka zo ka amsa ka shiga ka kunna a gabana, na gani ko ta gyaru."
Ya so ya yi magana, tuna akan aikin sa ya ke ko mai tace tana da gaskiya, sai ya dawo kamar yadda ta ce ya amshi makullin ya shiga ya kunna.
Sai da ta ga ya zaga wajen, lafiya ƙalau sannan ta yarda ta amshi makullin tare da faɗin "Thank you."
Ta shige motar tana ƙoƙarin kunna ta, gani ya yi tana ta kiciniya da alama dai ƴar koyo ce.
Zira kan shi ya yi ta tagar motar yace "Anya kin iya motar ma kuwa?."
Da sauri ta ɗago ta kalle shi ta waro ido tace "Ai ina ga ko kai ba za ka nuna min yadda ake jan mota ba, ko za mu gwada ne?."
Girgiza kai ya yi yace "Allah ya kiyaye hanya."
Ya ja baya ya bata hanya ta wuce ganin ta tada motar.
Dan Anwar bai cika son magana mai tsayi a rayuwar shi ba.
Tana zuwa saitin inda ya ke tsaye, ta ɗaga masa hannu tare da sakin sassanyan murmushi.
Ya jima a tsaye yana mamakin halin yarinyar, yadda take yi kamar ta san shi dama can, ya kuma fuskanci akwai yarinta da rawar kai a lamarin ta.
Gaba ɗaya ya manta da wata aba wai ita Hafsat, sai watarana da ya je makaranta bayan ya fito daga Lacture, ji ya yi ana bin sa da gudu ana faɗin "Bawan Allah bawan Allah."
Tafiya ya cigaba da yi bai juyo ba, sai ganin ta ya yi ta sha gaban shi tare da sa hannu ta dafe ƙirjinta.
Cikin mamaki ya ke kallon ta yana ƙoƙarin tuna ina ya san ta?. Sai ta ɗago ta kalle shi tana sauke numfashi tace "Tun ɗazu nake kiran ka, ka yi kamar ba ka jini ba har ka sani gudu."
"Muryar da ta yi magana ita ta tuna masa wace ce.
Yana shirin yin magana ta riga shi tace "Me ka zo yi makarantar nan?."
Kallon gefen shi inda wasu ɗalibai ke zirga-zirga ya yi, ya juyo ya kalle ta yace "Ke me ki ka zo yi?."
Ware hannayen ta ta yi duka biyun tace "Karatu mana."
Sai da ya fara tafiya yace "To kin bawa kan ki amsa."
Tana ganin ya gota ta, sai ta ƙara take masa baya sai da ta jera da shi Sannan tace "Dama kuma kuna karatu?."
Tambayar ta bashi mamaki, da farko ya yi kamar ya share ta, dan gaba ki ɗaya surutun ta ya ishe shi, ba tare da ya tsaya ba ya bata amsa a gajarce yace "Muna yi."
Daga nan bai ƙara ce mata komai ba, ya cigaba da tafiya.
Tsayawa ta yi tana bin shi da kallo, har ya ɓacewa ganin ta, haka kawai tun ranar da ta fara ganin shi ya ke burge ta.
Washe gari yana fitowa daga Lacture kamar jiya, sai gata ta ƙara biyo shi, wannan karon sai da tasa ya biye mata har ta tambayi sunan shi ya faɗa mata. Ita ma ta faɗa masa sunan ta Hafsat Muhammad, bata daɗe da zuwa makarantar ba.
Tun daga ranar kuma sai ta ke shige masa, tun yana yakice ta har ya fara biye mata, saboda Hafsat akwai shiga rai ga ta da raha da neman magana.
Hakan da take yana matuƙar burge Anwar, kwata-kwata ba ta ɗauki kanta a Matsayin mai kuɗi ba.
A haka har sabo mai ƙarfi ya shiga tsakanin su, kusan ko yaushe in ya shigo makarantar sai ta zo inda ya ke, shima sai ya zama in bai ganta ba baya jin daɗi sai ya ne me ta.
Tana kiran shi Ya Anwar, shi yana kiran ta sa ƙanwar shi.
Har ta kai matsayin in an bata assignment shi ke duba mata, wani lokacin shi ke yi mata ma. Sannu sannu sabon da suka yi ya juye ya koma soyayya, duk da shi Anwar bai zafafa tashi soyayyar ba, yana ganin ba zai samu Hafsat ba tunda ba matsayin su ɗaya ba, kasancewar shi talaka ita kuma ƴar masu kuɗi.
Tasha yi masa kyautar kuɗi, wani lokacin ta siyo wani abu da ya danganci kayan sawa, ko tace ya zo su je su ci abinci. Amma bai taɓa amsar komai daga gare ta ba, ko amsa tayin ta na fita wani waje, tasha fama dashi akan ya amince ta dinga sauke shi gida nan ma ya nuna ya gode.
Anwar mutum ne mai gudun zuciya, ya san mutumcin kan shi sosai baya son abinda za'a wulaƙanta shi ko kaɗan.
Duk abinda ke faruwa bai taɓa zuwa gidan su ba, ita ce ma take damun shi akan ya zo amma yaƙi zuwa.
Ranar da ya san wace Hafsat, ita ce rana mafi zafi da ƙuna a rayuwar Anwar, a ɓangaren Hafsat kuwa tafi kowa wace rana muni a gare ta.
Motar ta ce ta lalace a hanyar zuwa makaranta, da ya ke ranar shi ba shi da Lacture sai ta kira shi a waya.
Nan yace yana wajen aiki, amma zai zo ya duba mata motar ya gani.
Koda ya je ya duba motar sai ya ga gyaran zai ɗauki lokaci, har sai ya kai motar garejin su, dan haka sai yace mata ta bashi makullin ta hau abin hawa ta tafi makaranta.
In yaso in ya gyara sai ta biyo ta ɗauka.
Nan ta wuce kamar yadda yace, shi kuma sai ya wuce da motar gareji. To har ta dawo gyaran bai kammala ba, kasancewar a injin motar matsalar ta ke.
Ganin yamma ta yi sai yace ta tafi gida, ta masa kwatancen gidan su yau dai zai zo da kan shi ya kawo mata motar, daga nan sa gaisa da iyayen ta.
Cikin murna Hafsat ta shiga masa kwatance, tunda ya ji ta ambaci sunan Alhaji Mamman Nera gaba ɗaya wutar kan shi ta ɗauke.
Tambayar kan shi ya ke yi _Dama Hafsat ƴar maƙocin su Alhaji Mamman Nera ce bai taɓa sani ba?. Ta ya ya ya kasa gane hakan?._
Ja baya ya shiga yi cikin tashin hankali, sai da Hafsat ta ji shiru sannan ta lura da halin da ya shiga, kafin ta yi magana sai gani ta yi kawai ya miƙa mata makullin motar ta fuskar shi cikin tashin hankali yace
"Amshi makullin motar ki." Ya haɗa hannayen sa biyu yace "Dan Allah Hafsat na roƙe ki ki fita rayuwata, Ni dake mun haramta ga juna, dan Allah ki fita a rayuwata."
Cikin kiɗimewa Hafsat ta fara magana "Ya Anwar lafiya? Me yasa ka ce haka? Dan Allah ka faɗa min kar kasa zuciyata ta buga, in ma da wasa ka ke dan Allah ka daina irin wannan wasan bana so."
Girgiza mata kai ya yi idanun shi sun kaɗa sun yi jawur, yana tuna irin cutarwar da mahaifin ta ya musu, cutarwar da ba zata taɓa gogewa a zukatan su ba, da tabon abin za su bar duniya."
Kafin ta ƙara magana ya yarda makullin ya juya ya fara tafiya, da sauri ta take masa baya ta na kiran shi, da ƙyar ya dakata yana jin zuciyar sa na masa ciwo yace "Hafsat abinda nake so ki sani, mahaifin ki shine mutum na farko da ya rusa kowacce irin alaƙa tsakanina dake, ki sawa ran ki ke ɗin ba ki halatta a gare ni ba."
Yana gama faɗin haka ya juya.
Duk yadda ta so ya saurareta yaƙi, haka ta shiga Mota tana bibiyar shi.
*Wannan shine abinda ya faru tsananin su.*
-------
*GIDAN ALHAJI BATURE.*
*KUBRA*
CIkin hanzari take tattara takardun dake zube akan tebur ɗin gaban ta, kai tsaye ta nufi ƙofar fita daga bedroom ɗin cikin shiga irin ta lauyoyi ta fito tsaf abinta, a farlo ta tarda Sayyada zaune kan Dining table ta na juya tea a kofin dake riƙe a hannun ta, kamar ba sha za tayi ba.
Ƙarasawa Kubra ta yi wajen taja kujera ta zauna ta fara ƙoƙarin haɗa tea, ɗagowa Sayyada tayi fuska a haɗe tace "Ina kwana Aunty Kubra."
Harara Kubra ta jefa mata tace "Da ban fito ba yau ba za ki gaishe ni ba kenan ko?."
Sunkuyar da kai Sayyada tayi ba tare da tayi magana ba, ita ma Kubra bata ƙara magana ba ta cigaba da haɗa shayin, ganin har ta fara sha Sayyada na juya nata, hakan yasa kalle ta taja tsaki tace "Kin san Allah in ki ka bari na kammala ba ki gama ba, yau sai dai ki jira Saminu direba ya kai ki, dan wallahi barin ki zanyi na tafi ba za ki sa nayi latti ba."
Turo baki Sayyada tayi cikin shagwaɓa tace "Ki yi haƙuri Aunty Kubra."
Banza Kubra tayi da ita ta cigaba da kurɓar shayin ta, shi kaɗai ta sha ba tare da ta taɓa komai dake wajen ba.
Bayan ta gaba tashi ta yi ta kalli Sayyada tana duba agogon hannun ta tace "Ina fatan Sayyid ya shirya?."
Miƙewa Sayyada tayi, ta fashe da dariya kamar ba ita ke kumbura fuska ba tace " To ai ina ga shine za mu bari a baya, dan tunda ya tafi motsa jiki bai dawo ba har yanzu bare ya shirya."
Tafiya Kubra ta fara ta nufi Bedroom ɗin Mamyn su tana faɗin "Aikam da alama shine zai tafi tare da direba."
Da sallama a bakin ta ta tura ƙofar bedroom ɗin, tsaye ta tarda Mamyn nata ta juya baya a gaban wadrobe da alamar shirin zuwa office take.
Nan ta amsa sallamar Kubra ba tare da ta juyo ba.
Ƙarasawa Kubra tayi cikin girmama ta gaida ta. juyowa Hajiya Bilki ta yi tace "Fatan kin tashi lafiya?."
"Lafiya ƙalau." Kubra ta amsa, tace "Kar dai har kin shirya?."
Cikin ladabi Kubra tace "Eh Mamy da yake yau akwai Shara'ar da za'a gabatar ƙarfe takwas da rabi (8:30am) kuma nice zan tsayawa wanda ake TUHUMA, kafin a shiga ina buƙatar ganawa dashi mu ɗan tattauna shi yasa nake so naje da wuri."
Gaban madubi Mamy ta nufa hannun ta riƙe da ɗankwalin atamfar jikinta, tana ƙoƙarin ɗaurawa tace "Ubangiji ya bada Sa'a da nasara ya tsare ya kare ki daga sharrin me sharri. Allah ya ƙara ɗora gaskiya a kan ƙarya."
Cikin jin daɗin addu'ar mahaifiyar ta ta, ta amsa da "Amen ya Allah Mamy."
Ta miƙe ta nufi ƙofa tana faɗin "Mamy sai mun dawo, ina ga ke za ki ɗauki Sayyid dan har yanzu bai dawo daga motsa jiki ba."
Ɗaukar mayafin ta da makullin mota Hajiya Bilkisu ta yi, ta bi bayan Kubra suka fita farlo tare tana faɗin "Sai dai ya bi direban dan na shirya nima"
Sun tarda Sayyada tsaye cikin shirin ta tsaf, suna shirin fita Hajiya Bilkisu ta kalli dining table sai lokacin ta tuna da Sa'id a gidan ya kwana.
Hannu tasa ta dafe goshin ta tace "Kubra dan Allah dawo tunda da sauran lokaci, ki shirya abinci ki kai sashin Yayanku, sam na sha'afa a gidannan ya kwana."
Wani irin faɗuwa gaban Kubra ya yi, a rayuwar ta in akwai abinda ta ƙi jini shine abinda zai haɗa ta da Sa'id, amma babu yadda ta iya umarnin Mamy ne.
Babu musu ta dawo ta nufi kitchen ta haɗa breakfast ɗin a ɗan ƙaramin basket, dan ta san zai yi wuya ya ci yanzu wataƙil ma yana can yana barcin da ya saba.
In ba Mamy ba wa zai sa ta shiga ɓangaren Ya Sa'id, saboda yadda take cin karo da abubuwan da basu dace ba, kama daga sigari giya kayan maye kaca-kaca haka take tarda su a can.
A rayuwar kubra babu abinda ta tsana irin shaye-shaye, ko warin taba ta shaƙa ji take kamar numfashi ta zai ɗauke.
Hannun ta riƙe da basket ɗin abincin, ta fita ta nufi sashin nasa dake ta can baya, zuciyar ta na wani irin bugu kamar za ta faso ƙirjinta ta fito.
Daidai kan kwanar sashin ta haɗu da Hajiya A'isha, da alama sashin Hajiya kaka za ta je.
Cikin girmamawa kubra ta gaida Hajiya A'isha, ba tare da ta damu da kallon banza da ta ke binta da shi ba. In da sabo ta riga da ta saba da wannan halin na matan ƙannen Dadyn su.
Har Hajiya A'isha za ta shiga sashin Hajiya Kaka, ganin hanyar da Kubra ta nufa yasa ta fasa, nan ta dinga binta a baya cikin sanɗa ba tare da Kubra ta san tana binta ba.
Ta daɗe a bakin ƙofar tana norking amma shiru babu wanda ya buɗe, duba agogon hannun ta ta yi taga har ƙarfe bakwai da rabi ta kusa, kamar ta juya ta koma sai kuma ta kama ƙofar ta tura sai ta ji ta a buɗe sai ta shiga kai tsaye.
Hajiya A'isha na ganin Kubra ta shige, ta kama haɓa cike da munafurci ta bi bayan Kubra tana faɗin "Ai kuwa sai na ga me za ki je yi, tsohuwar guzuma kawai.
Koda Kubra ta shiga ta tarda farlon shiru babu kowa sai dai ko ina kaca-kaca, ga kwalaben kayan maye akan tebur ɗin dake tsakiyar farlon, da alama wanda ya sha jiya ne, ga wasu tarkace ko ina a barbaje kamar ba jiya Mamy ta sa masu aiki suka gyara sashin ba.
Har ta ajiye basket ɗin tana shirin juyawa, sai ta ji kamar nishi-nishi na fitowa a bedroom ɗin Sa'id, kasa kunne ta yi a hankali zuciyar ta na bugawar tsoro, sai ta ji tabbas daga nan ne ya ke fitowa.
A hankali ta taka ta ƙarasa jikin ƙofar, ji ta yi nishin ya yawaita sosai kuma da alama ba na lafiya bane.
Ba ta san lokacin da ta tura ƙofar bedroom ɗin ba, duk da a cikin tsoro zuciyar ta take, sai ta ji ta kasa hana kanta shiga.
Gaba ɗaya ɗakin lulluɓe ya ke da duhu, ga wani wari-wari irin na giyar nan na tashi.
Da taimakon hasken safiya da ya shigo ta taga, ta hango Sa'id kwance a tsakiyar ɗakin, ya wani dunƙule hannun shi dafe da cikin shi yana wani irin nishi.
Hannu tasa ta lalubi makunnin fitilar ɗakin, tana kunnawa ta zaro ido ganin yadda ɗakin ya yi kaca-kaca da amai, ga wani irin mimmiƙewa da Sa'id ɗin ke yi, idanun shi a tsatstsaye yana kallon sama.
Wani irin ihu ta kurma ta nufe shi a rikice tana kiran sunan shi.
Hajiya A'isha tana ganin Kubra ta shige bedroom ɗin Sa'id, ta bi bayan ta a hankali, tana ganin abinda Kubra ta yi jinjina kai haɗe da cije baki.
A hankali ta zira hannu ta zare makullin ƙofar ta soke a rigar ta, ƙwafa ta yi ganin yadda Kubra ke jijjiga Sa'id, da alama hankalin sa sam baya jikin sa dan sai wani layi yake yana rirriƙe ta.
Fita ta yi tana ta bar ƙofar farlon a buɗe tana dariyar mugunta, ta gyara tsaiwar ta tare da faɗin "Yau zan ɗauki fansa akan ki Bilkisu, sai na sa kin zubar da hawaye kamar yadda ki ke ƙunsa mana baƙin ciki a gidan nan.
Kai tsaye ta nufi sashin Hajiya Habiba, a farlo ta tarda ita da Hajiya Larai, suna ganin ta suka yi shiru da alama wani tuggun suke shiryawa.
Taɓe baki ta yi dan in da sabo ta saba da wariyar da suke nuna mata, duk faɗin gidan ita kaɗai aka ware daban, ita Hajiya Bilkisu kansu a haɗe ya ke da Hajiya Asiya, a yanzu haka bata gidan sun je ganin likita ƙasar Egypt ita da mijinta, dan Allah bai basu haihuwa ba.
Sai ita kuma Hajiya Habiba da bata da wata abokiya sama da Hajiya Larai, hakan na matuƙar ƙona ran Hajiya A'isha.
Ganin ta tsaya ba ta ce komai ba, Hajiya Larai ta jefa mata harara tace "Ya za ki zo ki tsaya mana a ka, in wani abu ne ya kawo ki ki faɗa ki tafi, dan muna magana mai muhimmanci ne."
Tsaki Hajiya A'isha ta ja tace "Ba wajen ki na zo ba Malama." Ta kalli Hajiya Habiba da ta zabga tagumi tace "Ke kina nan zaune kin shanya baki, ga waccan guzumar can ta shige sashin Sa'id, akan idona kuma ta rufo ƙofar."
Kamar an yiwa Hajiya Habiba allura, ta zabura ta miƙe tace "Kina nufin Kubra?."
Zaro makullin da ta ɓoye a rigar ta ta yi, ta nuna muU ta juya ta fara tafiya tana faɗin "In kuna shakka ku biyo ni ku ganewa idon ku."
Ai sai suka miƙe dukan su, suka take mata baya hankali a tashe.
Kubra na ganin halin da Sa'id ke ciki, ta ruɗe cikin ihu tana faɗin "Me ya same ka Ya Sa'id? Me ka sha?."
Ina Sa'id bai ma san tana yi ba, numfashi sa sai ƙara sama yake yana wani irin abu kamar wanda ake zarewa rai, sai wani miƙewa ya ke a jikin ta yana wani irin abu.
Kuka Kubra ta fashe da shi cikin ruɗewa tace "Ka sake ni na je na kira Mamy dan Allah."
Ina Sa'id bai ma san tana yi ba, sai wani kakkamata ya ke yana wasu abubuwa, bai san abinda take cewa ba dan baya cikin hayyacin sa.
Hajiya A'isha suna zuwa bakin ƙofar bedroom ɗin, tace "Ku kasa kunne kun ji ko kun ji Muryarta tana kukan munafurci ko?."
Jikin Hajiya Habiba har rawa ya ke tace "Bani makullin A'isha."
Tana amsa ta buɗe ɗakin ta sa kai a haukace.
***
🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️