FARGAR JAJI

01

by @jamilaumarjanafty

*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

*To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"*

*"Littafin FARGAR JAJI goro ne zuwa ga Hajiya Zainab Inuwa Isah AUNTYSIS(My Anty) with your support na fara wannan labarin kuma da support ɗin ki na rufe shi. Thank you for always being there for me. It means the world"*

*Littafin FARGAR JAJI na musamman ne zuwa Yayana JAMILU UMAR wanda ya yi aure ranar 04 ga watan April tare da Amaryansa Mariya Iman. Ina fatan Allah ya ba ku zaman lafiya tare da zuru'a masu albarka Amin.*

*Tukwaicin Littafin FARGAR JAJI zuwa ga DR FADILA KABIR. Anty Fadila tana sona tana son cigaba na, yadda kike sona da kula da al'amurana Ubangiji ke ma ya so ki, ya tsare gaban ki da bayan ki ya albarkaci rayuwar su Maheer Amin*

*Yabon Littafin FARGAR JAJI zuwa Aminiyata AISHA ALTO, na yaba miki Tawan Ubangiji ya yaba miki Allah ya dauwamawar da farinciki a rayuwar auren ki, Allah ya raya mana Noor da Yumna Amin*

*Fatan alheri ga Ƙannena masu kula da ni tare da rubutuna. *AISHA UMAR*,
*MARIYA UMAR(Hajiya)*
*Allah ya taimake ku, ya ba ku sa'a akan karatun ku Amin.*

*Jinjinar littafin Fargar Jaji zuwa Surayya Dee. Kawata mutuniyar kirki mai zuciyar zinare, kina da karamci da dattako Janafty ta gode miki Ubangiji ya ba ki zuru'a masu albarka Allah ya jiƙan magabata Amin*

*Gaisuwar littafin Fargar jaji zuwa ga iyayen ɗakina*
*Khadija Salisu Yusuf*
*Haj Habiba Abubakar Imam (Yayata)*
*Haj Niima Bala Rabi'u (Anty Niima)*
*Haj Halima Ɗalha Shehu (Umma)*
*Haj Hadiza Mahe Muhammad*
*Haj Sadiya Abu.*
*Haj Samira Baffa*
*Haj Zainab Abdulwahab*
*Haj Aisha Ahmad Iya*
*Haj Lubabatu Musa(Mama)*
*Barrister Salamatu Doma(Mommy)*
*Haj Halima Wada Kura*

*Godiya ga ƙawayena*
*Halima Yusuf Gwarzo( Besty)*
*Maryam Jumare*
*Nana Halima(Masoyiya)*
*Jamila Umar(Namesake)*
*Aisha Umar Idris(Tawan)*
*Hafsat Mustpaha(Sahiba)*
*Sumayya Bashir Kugu*
*"Na gode sosai Allah ya saka muku da alheri ya Allah ya bar zumunci.*

*Gaisuwar sada zumunci ga Aminaina*
*Maryam Aminu Musa(Kitty)*
*Ummulkhairi Sani Panisau(Khairi)*
*Muhammad Sani Lawal(Sayyid Amanar Janafty)*
*Sadeeq Rufa'i Ɗanguguwa(Sadi namu)*
*Iyalan Fam ina son ku, Ubangiji ya so ku, Allaah ya ƙara haɗa kawunanmu tare da danƙon zumunci na har abada Amin.*

*Fatan alheri zuwa ga Maryam Saminu Sulaiman(Anty Maryam). Wannan gaisuwar ta musamman ce daga Janafty tare da Surayya Dee. Mun gaishe da shugabar masu sharhi Allah ya yi ma rayuwa albarka Amin*

*Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, Bismillah.*

*01*

*SHIMFIƊA*
*NIGERIA.*
*ADAMAWA:YOLA.*

Jahar Adamawa(Fula: Leydi Adamawa) jaha ce da ke shiyyar Arewa maso gabashin na shiyyar Nageria. Jihar Adamawa na daga cikin Jahohin mafi girma a Nageria, kuma ta mamaye kusan faɗin 36,917sqkm. Jahar ta haɗa iyaka da Barno daga arewa maso yamma. Gombe jaha daga yamma taraba daga kudu, maso yamma a yayin da ta haɗa iyaka da ƙasar kamaru daga gabas. Jahar ta samo asalin sunanta ne daga tarihinta daga Masarautar Adamawa, tare da tsohon babban birnin Masarautar watau YOLA wanda take a matsayin babban birnin Jahar Adamawa a yau.
Jahar ta kasance daga cikin mafi rabe-rabe tare da harsuna na asalin garin dabam-dabam fiye da guda 100. An kafa Jahar a shekaran 1991 a sa'anin da a ka raba tsohuwar Jahar gongola don samar da Jahar Adamawa da Taraba.

A cikin jihohi guda 36 na Nigeria. Jihar Adamawa ta fi kowacce girma ta fuskar faɗin ƙasa, amma ita ce ta 13 a jerin jihohi masu ƙarancin yawan jama'a tare da kimanin mutum milayan 4.25 dangane da ƙiyasin shekaran 2016. Dangane da yanayin kasa kuma jihar ta ƙunshi tsuddai da tsaunuka(kamar su Atlantika, mandara da kuma shebshi) da kuma tsaunin Adamawa pleateu tare da kogi zagaye da tsaunika.
Yanayin damshin zafi/Sanyi na Jihar Adamawa yana farawa ne, a watan nuwamba, garin na da zafi sosai musamman a lokacin zafi, sannan lokacin sanyi na farawa ne daga watan december zuwa watan fabarairu na kowacce shekara.

****
*YOLA:JIMETA*
*AREA:Jalingo street.*
*7:20PM*

JImeta birni ne, a garin Yola ta jihar Adamawa Nigeria. Yawan mutane garin ya kai 73,080 a shekaran 1991. Tsayin Jimeta yana da mita 135, kuma yana gefen kogin Benue.

Ta duba agogon wayarta sau shurun masaƙi ba tare da ta gaji ba, zaune take a saman kujera mai zaman mutum biyu da suka yi ma falonta ƙwanya. Ta yi kwanciyar rigingine tana kallon rufin POP ɗin da ke falon. Ƙaramar fankar dake saman ɗakin ke gudu idanuwanta na wajen kamar tana ƙirga adadin juyawar da fankar take yi a zahiri. A baɗini kuma hankalinta ba ya wajen zuciyarta da hankalinta sun tafi tunanin me ya hana Habib dawowa gida a lokacin da ya saba dawowa?

Ajiyar zuciya ta sauke lokaci ɗaya tana sake nisawa, sannan ta tashi daga kishigiɗan da ta yi ta samu nasaran zama sosai a zaman kujeran, wayar da ke gefenta ta miƙa dogon hannunta fari tas mai ɗauke da ƙunshi ja ta jawo wayar ta latsa gefe haske ya bayyana Idanuwanta na kan lokaci dai dai agogon wayarta na ƙara minti ɗaya daga cikin mintinan da ya ke ƙirgawa.
7:30Pm, iskar bakinta ta fesar kafin ta miƙe a kasalance, kasalan da ta fara jin tana muƙurƙusan jikinta a kwana biyu nan, bakin window ɗin dake falon ta isa ta yaye labulan tana mai kai duban ta zuwa haraban gidan da ba ka ji motsin komai sai ƙaran wucewar iska, sai kukan tsuntsaye, akwai haske tarwar a haraban gidan saboda akwai wutar nepa ta kai duban ta zuwa ga flat ɗin da gefen su, shima dai shuru amma akwai haske daga cikin gidan alamun masu gida suna ciki suna gudanar da rayuwar su kamar kullum, idanuwanta ya hango mata motar mai gidan a fake a bakin compoud, sai ita kaɗai ne mijinta bai dawo gida ba?

Gidan su gidan haya ne, sun kai kimanin su shidda a ciki. A jere flat ɗin suke amma suna sharing filin compound ɗaya, sai ka yi sati biyu ba ka haɗu da wani na kusa da kai ba wasu ma ana yin wata, wani lokacin ma in dai ba fita za ka yi ba, wataƙila wata ma ta fito za ta fita sai ku haɗe ku gaisa amma ba mai shiga bangaren kowa musamman da yake akwai ma'aikata da masu fita makaranta a gidan.

Ta yi wani luu da idanuwanta lokacin da iska ya taso sai ta kai kallon ta ga sararin samaniya, ashe haɗari ne ya haɗu sosai sannan ya ta so lokaci ɗaya da iska, suna cikin tsakiyar damuna ne, ana yawan samun ruwa musamman ma da daddare. Sanyi ne ta ji ya fara shigar ta har tsikar jikinta na tashi, saboda ƙaramar riga ce a jikinta. Sai ta yi saurin rufe window ɗin ta zuge labule ta ƙamƙame jikinta da gudu-gudu sauri-sauri ta koma kan kujeran da ta tashi ta zauna, wayarta ta sake jawowa a karo na uku ta sake kiran lambar Habib da ta yi ma Saving da NOORI, kamar sauran kiran wannan ma har ya katse bai ɗaga ba sannan bai biyo baya ba, ta fara jin ba daɗi saboda ba haka ya saba ba, duk in da ya ke yana dawowa gida kafin sallar isha'i, in kuma zai kai bayan isha'i a waje sai ya kira ta ya shaida mata. Amma yau ya makara kuma tana ta kiran shi bai ɗauka ba sai ta fara tunanin wataƙila ba lafiya ba ko wani abu ne mara daɗi ya same shi?

"Aa ba abin da zai faru da Noori na"

Ta faɗa a fili tana mai furzar iska daga bakinta, ƙokarin karfafa ma kanta gwiwa take yi na cewa ba abin da ya same shi, saboda ita ba ta iya shiga damuwa ba yanzu nan sai ta rasa hankalinta. Ta fi karfafa ma kanta gwiwa da cewa wata ƙila ya biya ta gidan su ne, wata ƙila can ya tsaya shi ya sa ya ɓata lokaci bai dawo ba, sannan watakila wayarsa na silent ko bata tare da shi, shi ya sa bai ji kiran ta ba.

"In sha Allahu yana lafiya. Ki natsu Ummu-Salma."

Ta faɗa a fili tana sake karfafa kanta, ajiyar zuciya ta riƙa saukewa a jere har sai da ta samu natsuwa sannan ta iya sauke numfashi a hankali. Jikinta ta bi da kallo a duk dare a irin wannan lokacin haka take yin ado domin tarban mijinta Habib, yau ma ɗin ba ta sauya zani ba ta yi adon ta cikin riga da wando, rigar ba ta ko rufe mata cibi ba, kuma sagalan hannayenta na vest ne shi ya sa take jin sanyi na shiga jikinta, sannan wandon jikinta iyakarsa ƙwarinta sannan ya ɗameta sosai ya bayyana suran jikinta. Kanta ba ɗankwali gashinta ta saka band ta ɗaure ta saki jelan daga tsakiya, fuskarta ba kwalliya ta yi sosai ba amma ta saka jan baki mai ƙyalli yana ɗaukan ido, daga ita har falon suna tashin ƙamshi mai sanyaya zuciyar ma'abocin son ƙamshi.

Ummu-Salma Hadi BaBa farar mace doguwa, Bafullatan hausa-fulani daga tsatson fulanin Mubi, haihuwan Jimeta, ba sai an faɗa maka ba kana ganin ta za ka shai da ita ɗin jinin fulani ce daga yanayin ta da komai na ta, sannan da yanayin mganarta da ba ta da hausa sosai, kyakyawa ce ajin farko ga fari ga hanci ga zati da zubi, komai na cikar ƙimar mace ubangiji ya riga ya bata. A ƙiyasin shekarunta ba za ta gaza shekaru 24 a duniya ba.

Lokaci bayan lokaci tana cigaba da duba agogon wayarta, har takwas ta kusa saura mintina goma, ga shi har an fara yayyafi. Ganin haka ya sa ta miƙe ta buɗe ƙofar tiolet ɗin dake tsakanin bedrooms ɗin ta guda biyu ta ɗauro alwala, bedroom ɗinta ta shiga mai ɗauke da makeken gado da wardrope, hijabin sallan ta na saman gado da ta yi sallar mangariba shi ta zura bayan ta shimfiɗa sallaya  ta da salla, bayan ta idar tana zaune tana ƙirga yatsunta lokaci ɗaya ta ƙura ma waje ɗaya ido tana tunani.

"Wai ina Noori ya tsaya ne?

Ta tambayi kanta a zucci da sarari, miƙewa ta yi da hijabin jikinta saboda ta na jin sanyi-sanyi, kwana biyun nan ta fara jin canje-canje a jikinta kamar samun kanta cikin kasala, ciwon jiki, ciwon kai ciwon mara da yanayi mara daɗi ta ji ba ta jin cin komai, ga yawan barci in za ta tashi da ƙyar jikinta ya yi ta ciwo kamar ta yi wani aikin wahala mai tsanani, tun tana jin yanayin kaɗan-kaɗan har yanzu yanayin na yin yawa, daman niyar ta yau in Habib ya dawo ta sanar da shi ba ta jin daɗi ya kamata ta je ta ga likita.

Falo ta koma ta zauna a saman kujeran da ta tashi, falon babba ne yana da faɗi da tsawo, daga can ta sama akwai bangaren Dinning amma ƙarami ne mai kujerun zama guda uku, sai falon da kujeru guda huɗu suka yi masa ƙwanya sai cafet da ya malale tsakar ɗakin mai ɗauke da santer table.

Daga gabas kuma ƙaton tibi ne akan tv stand, sai agogo dake sama babba yana ƙirga lokaci ɗit!ɗit. Kujerun falon black and milk ne, shi ya sa har labulayan suma colour ɗin su kenan, wayarta ta jawo saboda ta ɗauke mata hankali daga tunanin rashin dawowar Habib yau da wuri data ta buɗe ta shiga Tiktok tana ta kalle-kallen abubuwan girke-girken zamani, saboda in dai bangaren girkin ƴan gayu ne na zamanin nan za ka gan su a wajen Ummu-Salma kala-kala, tun tana gida in tana sarrafa wani abun sai ka ce in ta gama ba zai ciyu ba ne, amma in ta gama haka za a yi ta santi musamman ma Baffa da ke supporting ɗin ta a komai na rayuwarta.

Amma ce sarkin faɗa ta yi ta masifa tana cewa Ummu na yi mata ɓarna da shegen iyayin nan nata, saboda ita Amma yar gargajiya ce gani take yi duk abin da Ummu ke yi wahalar da kanta ne kawai da iyayi, a cewarta abincin gargajiya shi ne sahihin abinci ba kayan ƙwalama da Ummu-Salma ta ɗauka abin birgewa ba.

Amma ta sha ce mata in ta yi aure za ta gani in wannan ƙwalamar da ta fi ƙwarewa akai za ta riƙa girka ma mijin yana ci. A lokacin baki ta tura kafin ta amsa mata da cewa" Ammah ke fa ba ki gane ba, ko an yi abinci ana buƙatar irin haka saboda zamani ne ya zo mana da hakan"

Baffa ya sha kashe kuɗi akan online clasess da na training akan burin Ummu na ƙwarewa a girke-girken zamani da sarrafa fulawa ta kowacce hanya kuma ta yi nasara ta koya kuma ta iya kuma har gobe tana kan koya. Yanzu haka ma tana cikin wasu guda uku, kuma a wayarta girke-girke ne sun fi guda dubu, shi ya sa ko tiktok ta shiga abin da za ka yi ta gani kenan ta kalla ta yi like in kuma tana so sai ta yi saving Vedio ɗin, sannan tana da karambani, duk abin da ta gani sai ta gwada shi, shi ya sa a wajen Ummu-Salma fulawa ba ta bata tsoro za ta iya sarrafata fiye da nau'ika goma a lokaci ɗaya.

Daga Tiktok, WhatsApp ta koma charting bai wani dame ta ba tun da ba ta da yawan surutu a waya kafin ta duba chart sau goma ta lalace a wajen kallon status ɗin jama'a.  Ummu Salma sai ta yi watanni ba ta kira wayar mutum ko ta yi masa mgana ba amma kullum tana nan tana duba status ɗin ka sai dai in ba ka saka ba. Za ta duba kuma ta gani amma ba za ta yi mgana ba, ko da rashi aka yi ma mutum ko abin ƙaruwa a cewarta charting ba wajen jaje ba ne ko murna wajen nishaɗi ne, shi ya sa sau tari sai dai ta kira ka a waya ta yi maka jaje ko murna amma ba dai ta charting ba. In za ka jira ta yi maka mgana sai dai ku daumana a haka, yayyenta maza har sun saba da halinta in ka ga tana charting a waya mai tsawo da mutane uku ne. Mutum na farko Mami ce ta biyu kuma Bestie ta uku kuma Sisna, ban da mutanen nan guda uku Ummu Salma ba ta doguwar mgana da kowa, Habib ne lokacin tana gida suna yawan yin charting bayan sun yi aure suna yi amma ba sosai ba shi ya sa a saman chart ɗin ta ba ta kuskure ma waɗanan mutanen guda uku.
Bestie, Mami, Sisna.
Bestie da SisNa ƙawayenta ne Mami kuma wata mace ce mafi daraja a rayuwarta bayan Ammah.

Yanzu haka ma tana cikin duba status ɗin Hamma Abdulrrahaman ta ga ya saka wasu hotuna shi da abokan aikin sa sun sha Suit, da alama a wajen aikin shi ne aka yi wani abun tun da lauya ne, sai ta ga saƙon Sisna ya faɗo da sauri ta fita ta je ta duba.

"Sisna."

Ta turo mata da emojin kuka.

Wani farinciki ya kamata jiki na rawa ta ma yar mata da amsa itama.

"Naam Sisna ya aka yi ne? Wa ya taɓa mini ke yau na ta da garin Jimeta da kewayan ta?

Daga ƙarshen maganarta ta sirka da fullanci, ta tattara emojin wukaƙe da hannu zai kai naushi.
Vioce note ta turo mata na sakwan talatin tana buɗewa ta ji muryanta cikin shagwaɓa tana faɗin.

"Sisna, na gaji da karatun nan na yi matukar gajiya, ni dai kawai ki zo ki ce ma Umman ikki a yi mini aure kamar yadda aka yi miki."

Ummu-Salma ta kwashe da dariya kafin itama ta danna Vn ta fara mgana.

"Uhm ai ni da man na sani akwai abin da ya kai karatu wahala ne Sisna? Wallahi babu shi shi ya sa na ce na gama kuna ganin laifina. Yarinya ki zo ki yi aure a cikin aure akwai Nii'imaaa."

Ta ƙarishe faɗa tana jan maa ɗin da dariya.
Sannan ta tura.

"Wai ke me ya sa in dai mutun ya kawo miki damuwarsa akan karatu sai ki sake ƙarya masa gwiwa? Sisna ki ƙarfafa ni tun da na saka kaina kuma na fara ki karfafa ni, ki ce Sisna ki jure keep fighting za ki iya."

"SisNa Fight.!!!*

Ta tura mata tare da emojin ɗaga power hannu da jinjina.

"Yes Maa"!!

Itama ta sake dawo mata da amsa, har da emojin kai biyu da love a saman su.

"Ina Habib? 

"Bai dawo ba Sisna.".

Ta bata amsa da gayyar emojin kuka.

"Dilla ke kuma. To kin kira shi?

"Ba ya ɗagawa."

"Kar ki damu Sisna. Ƙila ya biya ta gidan su ne zai dawo yanzu kin ji ko?

"To"

"Smile my beautiful Baby."

Sai ta tura mata emojin heart, da na dariya sun fi goma.

"Good night. Ki yi mini addu'a kin san upper week za mu fara exams."

"Ubangiji Allah ya ba ma Sisna Sa'a. Allah ya sa Aisha(Baɗɗo) ta fi kowa maki da samun nasara."

"Amin Amin Sisna, sai mun yi waya."

"Bye"

Itama ta tura mata Bye ɗin amma bai yi marking sau biyu ba hakan ya ba ta tabbacin ta sauka daga online, numfashi ta fesar tana kallon window an fara ruwa duk da bai yi ƙarfi ba sosai, ta shi ta yi ta sake gyara labulen da kyau kar ruwan ya yi ƙarfi ya yi mata feshe duk da ta rufe window ɗin, kichen ta shiga da ya ke da ƙofa ta wajen dinning, kitchen ɗin shima Babba ne yana da space sosai ɗaya daga cikin drowers ɗin kitchen ɗin ta buɗe ta dauko wani ƙaramin mug, akwai ƙaramar buta a saman gas cike da ruwan tea da ya ji gayayyanki shi ta ɗaga ta tsiyaya bayan ta saka ƙaramar rariya ta tace, siga ta ɗan saka kaɗan sannan ta samu ƙaramin Bowl, ta buɗe wani kwali ta ɗebo doughnuts guda uku manya ta zuba a ciki sai da ta ma yar da komai a muhallin shi sannan ta ɗauki mug ɗin da Bowl ɗin ta koma falo ta jawo santer table ɗin dake tsakiyar falon ta ijiye saman ta isa gaban Tv ta kunna soket ɗin sai ta ɗauko remot ta dawo ta zauna ya kawo amma a tashar ƙwallo ne
Habib ke kallo in dai yana gida sai ta ma yar da ita tashar Arewa24 suna maimacin kwana chasa'in sai ta bar shi amma ta rage sautin duk da kallo bai dame ta amma tana yi jefi-jefi.

Kan kujera ta koma ta naɗe har da tankwashe kafa, ta ja mug ɗin tea din ta, tana kurɓa lokaci bayan lokaci tana gutsiran doughnuts ɗin dake saman cinyarta, har wani lumshe ido take yi saboda daɗi.

"Ashe ya fi ma daɗi in ya yi kwanaki."

Ta faɗa tana sake gutira a bakinta, Bowl ɗin ta sauke a saman kujera ta sake jawo wayarta chart ta shiga ta duba Habib tun 5.40pm ya sauka daga online, sai ta je ta duba Bestie itama tun safe ba ta damu ba sanin tun da suka kusa fara jarabawa Bestie za ta yi wuyar gani.
Sai ta rubuta mata.

"Bestie kina lafiya? Ya karatun? Da wahala ko. Ayya sannu Allah zai ba ki nasara Bestie na"

Ta tura mata kuma ya tafi amma ba ta online tun da bai yi marking sau biyu ba.
Sai ta koma ta duba Mami sai ta ga tana online da sauri ta tura mata.

"Mami na."

Ba daɗewa Mami ta dawo mata da amsa.

"My first Daughter me kike yi da waya da daren nan? Ina mijin ki?

"Mami bai dawo ba"

"Is he Ok?

Mami ta tambaya sai ta amsa mata da lafiya lau ya biya ta gida ne.

"Good, nima ina duba test ɗin ɗalibai ne, gobe zan kira ki. Good night."

"Good night Mami na."

Ta rubuta tana tura baki kamar tana ganin ta.

"Kowa sai ya ce mini wai Good night"

Ta faɗa tana sake tura bakin ta gaba, ajiyar zuciya ta sauke ta fita daga nan ta koma Tiktok tana ta kalle-kalle amma tana ta duba lokaci har tara ta kusa amma Habib bai dawo ba, kuma bai kira ta ba, ta fita daga wajen da niyar sake kiran shi sai kuma ta koma cikin chart ɗin ta bangaren status, kwatsam ta ga Hamma Sadam ya saka status 4m ago.

Da rawan jiki ta buɗe hotuna ne kuma hotunan ba baƙinta ba ne, duk wani ɗan Nageria dake mu'amala da social media ya san hotunan nan saboda yadda suke trending a duka kafafan sada zumunta tunda satin nan ya fara.

Amma abin da ya ba ta mamaki caption ɗin Hamma Sadam a ƙasan hoton

"Allah ya sanya alheri my Sis Badi'atu"

Baki ta buɗe sannan ta rufe tana sakin wata dariya.

"My Sis? Lalle ne ma to ko a yaushe ta zama sis ɗin ta shi ni ban sani ba?

Ta faɗa a fili tana sake yin dariya hotuna ne ya saka sun fi kala biyar na Amarya Badia'tu da angon ta wato Pre-wedding pictures ne da yan zamani ƴa'ƴan masu kuɗi ke yi in za su yi aure. Hotuna ne fitattu da suke tashe a yanzu bikin sai satin sama ne amma tuni hotuna da katin shagulgula sun watsu a duniya saboda bikin na masu kumbar susa ne da masu mulki da sarauta
Duk in da ka shiga hotunan Amarya da angon ne, sai katin bikin da na Program of events ke yawo a duka manya bloggers ɗin mu na arewa gabaɗaya.
Kallo take yi tana taɓe baki kafin ta ce a fili.

"Allah ya sa ta ma san kana yi Hamma Saddam"

Ta faɗa tana sake yin mirmishin gefen baki, sau ɗaya ta taɓa ganin ta lokacin da Ammah ta matsa mata suka je naɗin sarautan Hamma Lamiɗo a matsayin Yariman Daura. Tun a lokacin ta ga jin kai da isa a wajen wannan yarinyar, ta tabbata tusa kai ne kawai irin na Hamma Saddam ba ma a san yana yi ba. Wata ƙila Hamma Lamiɗo ya yi ma kara  shima kuma tana da tabbacin bai san ma yana yi ba. Abin da ya saka na karshe a status ɗin sa katin bikin ne da shagulgulan da za a yi tun satin bikin har zuwa ranar ɗaurin aure.
Ɗaurin aure ne kawai za a yi a masarautar Daura amma sauran shagulgulan duk a garin Abuja za a yi.

Ba ta san ta kwashe da dariya ba sai da ta ga caption ɗin Hamma Sadam a kasan katin

"Family and Friends bikin gidan mu ne fa ya zo.  Bikin gidanmu saboda haka ban ɗauke ma kowa ba."

Ummu-Salma tana dariya har sai da ta shaƙe, Hamma Sadam na da abin dariya wai bikin gidan su ne.! Yaushe bikin gidan masu Sarauta da masu mulki ya zama na gidan su? Bikin ɗiyar sarkin Daura ALHAJI Dr. NASIRU MUHAMMAD DAURA ne fa za a yi, za ta auri yaron mai ba ma shugaban ƙasa shawara akan yaɗa labarai, shi ne wai Hamma Sadam ke ta rawan jiki har yana faɗin wai bikin gidan su ne, gaskiya Hamma Sadam akwai tusa kai ba ƙwarjini da gayya ta masa reply akan status ɗin sa na ƙarshe.

"Ka ji Hamman nan, bikin gidanmu ma fa ka ce? Ko dai bikin gidan su Hamma Lamiɗo?

Kamar yana jiran ta sai ga shi ya turo mata da sticker na an ɗaga wani an tika da ƙasa sannan tare da emojin nan na ɓacin rai.
A ƙasa ya haɗo da cewa.
"Bikin gidammu ne Ummu ko ke ba na gidan ku ba ne?
Kai tsaye ta bashi amsa da cewa.
"A'a wallahi ba na gidanmu ba ne Hamma."

Emojin mamaki ya turo kafin ya ce" Ammah na gefe na nuna mata abin da kika ce?
Da sauri ta ce" Rufa mini asiri Hamma bikin gidan mu ne."
Ta rubuta sannan ta tura emojin heart har da na rawa.

"Yauwa yarinya."

Ya rubuto tare da sticker na dariya, saboda haushi ba ta amsa shi ba sai ma ta kashe data ta ajiye wayar, Hamma Sadam na so ya jawo mata masifan Ammah a daren nan ba ta shirya ba, ai tana jin yadda Amma take shirya ma wannan bikin ko ita uwar Amaryan albarka. Wanda take yin abin nan domin shi wataƙila ma ba zuwa zai yi ba, mutumin da an sha yin abubuwa na daɗi da aka sin su bai taɓa zuwa ba, shi bai ɗauki zumunci ma abakin komai ba, ba abin da ya sani sai tuƙin jirgi, kuɗi kawai alhalin ahalinsa suna da tarin dukiyar da har jokokinsa ma ba za su yi talauci ba, tana da tabbacin ko rantsuwa ta yi ba za ta yi kaffara ba, ba zai samu zuwa  ɗaurin auran ƙanwarsa ba shi ya sa da bai zo na ta ba, ba ta damu ba Ammah ce ta damu saboda sun yi mgana ya ce mata zai zo, a cewarsa ya ɗauka za su iso bakin gaba ne ana gobe ɗaurin aure sai kuma tafiyar ta su ta sauya tsari shi ya sa bai samu zuwa ba. Duk fa Ammah ce ke ta yawo da wannan mganar shi gogan ba wanda ya ji haka daga bakin shi. To wai wanda ko ɗaurin auran shi bai samu zuwa ba to na waye zai je? Shi ya sa ma wanda ya damu in bai gan shi a sha'aninsa ba, shi ke da kaico shi dai bai ma san kana yi ba, shi fa mutumin nan dabam yake, ɗauka yake kuɗi sune muhimmi a rayuwar nan daga naira ɗaya har miliyan goma zai iya tura maka amma kuma ba zai iya zuwa ya yi maka murna ko jaje ba shi ya sa har gobe bata taɓa saka Hamma Lamiɗo a jerin mutane masu karamci ba, ta fi saka shi a jerin mutane masu girman kai da ɗagawa.
  
Tana cigaba da cin doughnuts ɗin ta, tana kuma kurɓan tea a lokaci ɗaya amma sai taɓe baki take yi ita kaɗai daga gani hakan yana daga cikin ɗabi'arta.
Ita fa tun wancan satin da ta je gida Ammah ta dame ta da labarin bikin nan na Daura ta ji ba za ta sake komawa ba sai bayan an gama bikin nan, domin hankalin Ammah ba a kwance yake ba yanzu sai ta ga ta je Daura an gama biki lafiya ta dawo tukunna. Baffa dai ba ruwan shi ba lalle ne ma yaje ɗaurin auran ba Ammah kuma ba wanda ya isa ya ce ba za ta je ba ai sai ranar gidan ya kwana ba lafiya. Baffa ma yasan halin kayan shi, shi ya sa ba ya ma gigin shige mata na shi addu'a ne da fatan alheri, domin in dai akan sha'anin abin da ya shafi Hamma Lamiɗo ne ko Baffa bai da ta cewa, da jikinta da zuciyarta take hidimtama wannan bawan Allah da Ubangiji ne ya haɗa wannan ƙaunar da tana tunanin ko su ƴa'ƴan cikinta ba ta nuna musu ƙauna da kula da alamuransu da muhimmanci kamar yadda take kafa-kafa da duk wani al'amarin da ya shafi Hamma Lamiɗo.

  Shi ma kuma ba ya iya tsallake umarninta komai tsaurin shi a gare shi. Da Amma kaɗai yake iya doguwar hira cikin nishaɗi, ita ce kawai take iya ganin dariyan shi har da haƙora a waje. In ba za ta manta ba lokacin tana aji biyu a matakin babban sakandiri aka yi bikin Hamma Lamiɗo, auran da a farko cewa ya yi ba ya so tunda haɗin daga kakarsa ce Fulanin Daura, Mai martaba kuma ya ce ba zai matsa masa ba, Mami kuma ta ce ina ruwanta da sha'anin Lamiɗo? A nemi uwar sa Ammah ita ce za ta iya saka baki akan mganar,
Hamma Lamiɗo da bayan gaisuwa magana ta mintina biyar ba ta taɓa haɗa shi da Mami a matsayinta na mahaifiyarsa ba, ko da za su yini waje ɗaya su kwana. Ba ma ita ba, Hamma Lamiɗo zai yi rayuwa da mutum na tsawon kwanaki amma ban da gaisuwa magana ta fatar baki ba zai yarda ta haɗa su ba. In ko ka matsa ka yi hira da shi kai ne da haushi, domin a ginshiƙe zai din ga tafiyar da kai da har sai ka yi zuciya ka ƙyale shi.

Haka ko aka yi  tawagar Fulanin Daura har cikin falon Ammah, ta zauna ta roƙe ta da ta sanya baki Lamiɗo ya karɓi auran nan, da suka je suka karɓo masa ƙafa da ƙafa har wajen Mai martaba Sarkin Kano a lokacin Balkisu ba ta daɗe da dawowa daga ƙasar Spain ba, a can ta yi duka karatun ta na likitan ci. Ammah ta yi ma Fulanin Daura alƙawarin za'a yi auran nan kuma maganarta ya tabbata. Tana cema Hamma Lamiɗo in har ya ɗauke ta a matsayin uwa to ya karɓi wannan auran da cewarta da auran ko wata biyu ba a yi ba. Abin mamaki sun rufe shekara da wattani ne da aure matar Hamma Lamiɗo ta haihu,  har yau Ummu-Salma na mamakin wannan abu, ka ce ba ka son aure amma kuma ana yi sai shuru, kuma ko zuwa suka yi tare ba mai gane yanayin shi. Ba za ka ce yana son ta ba, ba kuma za ka ce baya son ta ko da wani lokaci yana nan a ginshiƙen sa. Shi fa ba ka iya gane ma yanayinsa kwata-kwata, fuskarsa ba ta bayyana farincikinsa ko bakincikinsa.

Ammah kuma al'amarin ƴa'yanta kuwa sai dai Ummi ikki ta yi gaba ita tana baya, amma in dai lamarin Hamma Lamiɗo ne ba ta jira ba ta kuma sakawa a yi mata, ita ce da kanta take yi masa komai, tun tana ƙarama ta shaida Ammah ta fi hidimtama Hamma Lamiɗo fiye da su ƴa'ƴanta na cikinta tun tana damuwa har ta saduda ta sare. Ta taɓa tambayan Baffa me ya sa Ammah ta fi son Hamma Lamiɗo akan kowa a gidan nan?

"Sabo da shima ɗan ta ne Ummu Salma. Nima ba ki ga ta fi son shi a kaina ba?

A lokacin dariya ta yi, kuma gaskiya ya faɗa ko Baffa bai isa ya ce wani abu akan Hamma Lamiɗo ba, ko yana nan ko baya nan Ammah mai tsaya ma yau ɗin sa ne har da jiyansa ma sannan za ta tsaya ma gobensa ma. Ba ta san Habib ya dawo ba domin ba ta ji motsin ko shigowar motarsa haraban gidan ba hankalin ta na kan Tv tana hakaito soyayyar Ammah ga Hamma Lamiɗo gefe ɗaya tana kallon drama ɗin Rayya da Avm Adnan, haka kurum take son film ɗin sabo da su, soyayyarsu na matukar birge ta Kamar ita da Noorin ta.
Su suka sanya ta mantawa da Komai ta ma yar da hankalinta kan kallon gabaɗaya.

Kamar daga sama ta ji ana murza ƙofa alamun an saka key za a buɗe, ƙurama ƙofar ido ta yi ba ta yi ko motsi ba. Ya saba ina tana dirin shigowar motarsa ta ke kamewa a tsakiyar falo yana shigowa za ta tafi da gudu ta naɗe a jikin shi, shi kuma kamar ko yaushe ya fara juyi da ita a tsakiyar falon cikin soyayya da muradi.
Amma yau sai ta ji kasala ya rufe ta ta kasa tashi, ko mararin ganin shi a lokacin ba ta ji ba wataƙila da ba ta gan shi ba ne ya sake ta ba ta dai sani ba. Tana nan zaune ya shigo falon ɗauke da karamar jakarsa ya ɗan jiƙe domin ga alamun yayyafi nan a jikin baƙaken suit ɗin da ke jikinsa.

Wataƙila ya ɗauka ba ta falon ne, shi ya sa ya tuɓe takalmansa ya ƙariso ciki sai dai me! Sai ya gan ta zaune tana mai kallon shi da manyan idanuwan ta.
Waro ido ya yi kafin ya ce.

"Baby da man kina jina?

Ya faɗa yana mai sauke jakar hannunsa a saman kujera mai zaman mutum ukun dake kusa da shi, ware ma ta hannuwa ya yi lokaci ɗaya yana sake faɗin.

"Baby na i miss you."

Ya faɗa yana yi mata murmishi, wannan murmishin na shi mai tsada da ya kan narkar ma ta da zuciya a lokuta da dama in ya kalle ta ya yi mata.

Maƙe kafaɗa ta yi, lokaci ɗaya tana tura baki , sannan ta kauda kanta alamun ta yi fushi, yana ganin haka ya yi saurin isowa kujeran da takwle zaune yana faɗin.

"Baby am sorry, kin ji ni shuru ko? 

Ta ƙi yarda ta kalle shi, ganin haka yasa ya ɗauke Bowl ɗin dakw gaban ta da mug ɗin tea ya ɗora bisa table ɗin gaban su da karfin sa ya saka hannu yana ƙokarin juyo da fuskarta ta ki ba shi damar haka.

"Baby ni ne fa? Noori ɗin ki ne yau ba ki son kallon fuskar shi?

Ya faɗa yana kawo mata hannu zai taɓa fuskarta da sauri ta bige hannun shi, cikin shagwaɓa ta ce.

"Noori ka san zan damu ko?

Ta faɗa tana mai kallonsa lokaci ɗaya hawaye suna cika kwarmin idanuwanta  ba ta da wuyar kuka abu kaɗan sai ya saka ta kuka ko kallo ta ke yi ɗan emotion kaɗan sai ta fara hawaye, yanzu ɗin ma ji kawai ta yi tana so ta yi kuka.

Jin muryar ta na rawa ga shi idanuwanta da jwalla ya sa ya ruɗe ya tarairayo ta da hijabin jikinta ya ɗora ta bisa cinyarsa yana tallabe da fuskarta da tafukan hannayensa duka biyu

"Ni ne ko? Sorry Baby Gwaggo ce t kira ni kuma na manta waya ta a mota na saka ta chaji, lokacin da na fito na ga kiran ki sai ban kira ba, tun da lokacin ina kan hanyar dawowa ne"

Ya faɗa yana mai kallon ta itama shi ta ƙura masa ido, tana sake runtse ido sai kawai hawaye suka zubo mata sharr a saman kumatun ta.

"Baby ki daina kuka mana. Bana so kin sani."

Ya sake faɗa bayan ya saka tafin hannunsa yana share mata hawaye.
Buɗe idanuwanta  ta yi  tana kallon shi, gashin idanuwan ta duka biyu ya sumbata kafin ya ɗago yana faɗin.

"Gudu na yi ta yi a mota fa Baby."

"Ba na hana ka ba."

Ta faɗa cikin wata irin shagwaɓaɓbiyar murya.

"Kin hana ni Baby."

Ya ba ta amsa shima cikin ƙaramar murya, lokaci ɗaya yana kwantar da kan shi a saman kirjin ta hannayensa kuma ya tusa su ta ƙasa hijabinta yana shafa mararta zuwa ƙirjin ta banƙarewa ta yi shi kuma sai ya ji daɗin haka zare mata hijabin jikin ta ya yi ya tsaya yana kallon kirjin ta.
Ganin haka ya sa kunya ya kamata sai ta faɗa kan kirjinsa tana masa kukan shagwaɓa.

"Noori ka bari."

"Me zan bari Baby? 

"Uhm"

Ya faɗa yana shinshinar wuyanta cikin lokaci ya fara birkicewa, yana bin sasaan jikinta da wasanni ta kasa mgana sannan ta kasa hana shi, duk da yau ɗin tana jin gajiya a jikinta amma Habib ya sabar mata da komai, ƙa'ida ne in ya dawo kafin ya yi wanka ya ci abinci sai ya riban ce ta, kuma a daran ma ba zai bar ta ba kafin asuba ya yi sau uku ko sui huɗu, haka ma bayan asuba, tun Ummu-Salma na ɗaukan hakan a matsayin amarci a farkon auran su har yanzu ta daina ɗauka haka. Sai ta bar shi a matsayin mijinta Habib na daga cikin mabukatan maza ma su yawan buƙata.

A farko-farkon auran su ta sha tambayan ta kanta da man wanne ne daɗin auran? Ba hutu sam, lokacin ba ta yi kiban amarci ba sai rama saboda kwazzaban Habib saboda ba ta cikin jinsin mata fitannanu, amma saboda Habib ta koya, har in bai neme ta ba sai ta ji ta a takure, da farko ta ɗauka illa ne hakan sai da ta ga wani rubutu a faceebook wanda ke nuni da cewa yawan mu'amalar aure ga mace nuna soyayya ce makura daga mijinta shike nan ta daina fargaba ta saki jikinta duk lokacin da Habib ya marabanceta za ta ba shi cikakken goyon baya, amma tunda ta yi ɓarin cikinta wattani biyu baya da suka wuce ta daina jin shauƙin abin, kwana biyu kamar lamarin ya yi sauƙi yanzu kuma ya dawo mata, sai ta rika jin ta gaji sannan ba ta son a sakar mata wata gajiyan bayan wacce take muƙurƙusan kashin ta a lokacin, sai dai ta kasa mgana ta na ji tana gani Habib ya ɗaga ta sama yana nishi zuwa bedroom ɗin su, kan gado suka faɗa ya cigaba da abin da ya fara.

Ta yi ƙokarin ta bashi dukkan haɗin kai har ya samu natsuwa, bayan ya shiga wanka ko ɗan yatsan ta ba ta iya motsawa tsabar yadda take jin jikinta a mace. Tana kwance ta rufe rabin jikinta da blanket saboda Habib ya yi fatali da kayan jikinta tun a farkon yaƙin. Tana kwance ya fito ɗaure da towel a ƙugun shi karamin kuma yana goge ruwan da ke gashin kansa.

Tana daga kwance take ƙare ma Habib kallo, in dai ana neman cikar zati da mazantaka Habib ya kai a namiji, fari ne tas shima sannan dogo amma ba shi da tsaho sosai yana da faɗin jiki daga sama kaɗan kyakyawa asalin bafullatanin Yola ne na uwa da na uba, hancinsa har baka sumar kansa tana nannaɗe irin ta fulani, ko ta ko'ina Habib ya kai za kuma a nuna shi daga nan har Saudiya a matsayin namijin da ya ƙera sa'a ga ilmi ga martaba ga sanin ya kamata ga iya soyayya, a kalla a shekarunsa ba zai gaza talatin da biyu ba 32. Shi ya sa yana cikin jerin layin matasa masu jini a jika, ma'aikacin banki ne shi ya sa ya zama ɗan gayu na karshe da kwatance.
Habib Idris Mai imani ya kai  ya haɗu ya gaji da haɗuwa da duk macen da ta mallake shi zai zama abin alfarinta.

"Baby ki tashi mana."

Ya faɗa bayan ya yarfa mata ruwan dake gashin kansa.
Mirmshi ta yi masa shima ya mayar mata da martanin mirmishin nata.

"Tashi ki yi wanka ki ba ni abinci yunwa na ke ji Baby."

Ya sake faɗa cikin yar shagwaɓa, hannunta guda ɗaya ta mika masa lokaci ɗaya tana faɗin" Noori ka ɗaga ni."
Ta faɗa tana mele masa baki.

"Baby me ke damun ki yau? Kin gaji ne da yawa?

Ya faɗa yana rike hannunta da taimakon shi ta miƙe zaune.

"Baby are you sick?

Ya faɗa yana kallonta ganin ta lamgwaɓe kai.

"Ban sani ba Noori amma jikina ya yi weak"

Da sauri ya matso gabanta ya dafa goshinta kafin ya ce" Kuma tempereture ɗin ki is Normal."
Shagwaɓa fuska ta yi kafin ta ce" Ni ma ban san meke damuna ba Noor."
Kallonta ya yi kafin ya kashe mata ido ɗaya yana sake faɗin.
"Ko ni ne Baby?
Ture shi na yi ina faɗin" Yau ne farkon mu?
"Baby to amma ai yau na kai farmaki na da kyau ko?

Sake ture shi ta yi sannan ta miƙe ya taimaka mata yana tura ta bakin tiolet.
"Baby yunwa."
Ya sake faɗa da karfi gwiwa ta tura ƙofar toilet ɗin ta shiga tana faɗin" 5 minutes."
Ta faɗa tana mai rufe ƙofar, da kallo ya bita kafin ya yi mirmishi. Wardrope ya buɗe ya ɗauko saukaƙkun kayan barci ya saka riga mai gajeren wando falo ya fita ya sauya tasha zuwa tashar ƙwallo mintina goma tsakani Ummu Salma ta fito itama cikin rigar barci mai shara-shara wacce ba ta wuce gwiwarta ba.

Abinci ta jera bisa dinning, yana daga can a falo ta kira shi.

"Noori Dinner is ready"

Da sauri ya taso, ita ta ja masa kujeran ya zauna yana faɗin" Thank you Baby."
"You are always welcome Noori na."
Mirmishi ya yi mata lokaci ɗaya yana kashe mata ido ɗaya, kau da kai ta yi tana yar dariya.

White rice ne da miyar allayahu, sai zoɓo da tea, tare suka ci abinci suna yi suna hiran su ta masoya.
Bayan sum gama suka shiga tiolet suka wanke bakin su, Ummu-Salma ta kwashe abin da suka ɓata zuwa kitchen sannan ta koma falo wajen Habib da ya rage hasken falon ta naɗe a jikin shi, suna kallo suna hira suna kuma soyayyar su.

****

Duk da yanayin Ummu-Salma da Habib ya gani bai saka ya ɗaga mata kafa ba, kafin su kwanta sai da ya maimaita. Can cikin dare ma sai da ya tashe ta tana so ta ce ya ƙyaleta ba ta jin daɗin jikinta amma ta kasa, yana dawowa daga sallar asuba ma sai da ya yi duk yadda ya ga jikin Ummu-Salma ya yi laushi a cewarsa jarumatarsa ce ta ƙaru, shi ya sa ta makara sai wajen bakwai saura ta iya ƙarfin halin tashi ta shiga kitchen, da ya ke girki Hobby ɗin ta ne garin fulawa ta iya sarrafa wa, cikin lokaci ta kwaɓa fulawa ta sarrafa shi zuwa Naan Bread.
Tun da tana da kayan lambu, nama ne babu sai ta yi amfani da ƙwai.

Ko kafin takwas ta yi ta jera komai a saman dinning. Ta koma bedroom ta tashi ta Habib ta taimaka masa ya yi wanka, ya tsuke cikin suit masu ruwan  baƙi da ruwan toka. Tare suka zauna zaman ƙaryawan Naan bread ɗin suke ci haɗe da tea Habib na gutsira yana yi mata santi.

"Baby ina son wannan abin. Ya ma sunan shi?

Tana dariya ta ce" Naan Bread Noori, amma wannan mai ƙwai ne ba nama ba."

Sai ya jinjina kai kafin ya ce" A online clases ɗin ku aka koya miki?
Bayansa ta dafa kafin ta ce" Noori na santi."
Sai da ya kurɓi tea kafin ya ce" Ba santi ba ne, Allah Baby yana da daɗi, in dai kika yi shi ai ina cewa yana da daɗi ko?

"Yes My Noori."

Hira suke yi, jefi-jefi ita tea ɗin ma kawai ta ke kurɓa saboda zuciyarta ta ji tana tashi tun da safe, shi ya sa ma ba ta ci ba naan bread ɗin ba.

Habib wayarsa ce a hannunsa yana ta dubawa. Lokaci ɗaya kuma yana cin abinci.

"Baby."

"Naam"

"Ashe kuna da biki ban sani ba?

Sai ta kalle shi cikin mamaki.

"Noori Biki kuma?

"Yes"

Ya faɗa yana karkata mata wayar ta leƙo da kanta sai ta yi arba da zafafan hotunan Badia'tu yar sarkin Daura.

"Ba bikin gidanku ba ne?

Ya faɗa  yana sake tura abin da ke hannunsa a baki lokaci ɗaya yana korawa da ruwan tea.

"Oh ai fa."

Ummu-Salma ta faɗa tana kauda kanta.

"Ammah za ta je?

"Za ta je mana. Kai ma ka sani"

"Mami fa? Itama za ta je?

Sai ta kalle shi kafin ta ce.

"Kai ma ka san Mami ba za ta je ba."

Sai ya jinjina kai yana cigaba da kallon wayarsa kafin ya ce" Baby da kin tambayeni da na bar ki, kin raka Ammah dagaa ganin bikin nan za a sha shagali."

"Uhm"

Ta faɗa ba tare da ta sake mgana ba.

Dariya Habib ya yi kafin ya ce" Am just joking. In kika tafi ni kuma ya za ki yi da ni?
Hararan shi ta yi, yana sake yin wata dariyan ya ce.

"I love you Baby."

Juya masa ido ta yi sannan ta yi masa fari, jinjina kai ya yi kafin ya ce" Ki bari kafin na ce mu shiga daga ciki."
Tana jin haka ta yi saurin gyara zama tana faɗin.

"Za ka makara fa Noori?.

"Ina sane da time fa Baby."

Sai ta jinjina kai, ba ta yi mgana saboda cikinta ne ta ji yana juya mata.

"Baby."

"Noori."

Sai da ya kalleta kafin ya ce.

"Hamma Lamiɗon to zai je can Daura ɗin ne?

"Ban sani ba Noori."

"Serous fa?

"Allah fa ban sani ba."

Ta faɗa tana mai kallon shi.

"Ko Ammah ba ta faɗa miki ba.?

"Ba ta faɗa mini ba Noori."

Ta faɗa cikin gajiya da tambayoyin.

"Noori yau kuma Hamma Lamiɗon kake son gani?

Ta  faɗa tana kallon shi mirmishi ya yi kafin ya ce" Ba laifi ba ne, kin manta sau ɗaya na taɓa ganin shi, shima daga nesa kafin na karisa ya shige cikin mota."

Baki ta taɓe kafin ta ce.

"Uhm"

"Baby ke dai kawai ki ce jininku bai haɗu ba, kuma saboda kin ƙi karatu ne "

Wani kallo ta yi masa da ya sa ya fara dariya kafin ya ce.
"Baby gaskiya na faɗa, nima fa ta shafe ni kamar baya sona saboda ke."

Kai Ummu-Salma ta girgiza kafin ta ce" Shi wannan yana neman dalilin tsanar mutum ne? in dai haka ne kowa ya tsana kenan."

"Me ya sa kika ce haka?

"To ban da Ammah wa ke ganin dariyan mutumin nan! Ko Baffa a ginshiƙe yake masa mgana. To bari ka ji ko su Hamma Jibril a takamance yake yi musu mgana, ballanta irin mu ƙananun ƙwari."

Habib ya kwashe da dariya ganin yadda matar tashi ta haɗe rai, tissue ya ɗauka yana goge bakin shi kafin ya ce.

"Kuma Ammah tafi son shi da ke ba Baby."

"Ta fi son shi da kowa ma Noori. Ni ai na bar masa ita na kama Mami na da Umman ikki."

Ta faɗa tana juya masa baki, miƙewa ya yi yana faɗin" Baby is time."
Itama sai ta mike, bedroom ta koma ta ɗauko masa briefcase ɗin sa ta dawo falon suka rumgume juna sai da ya sumbaci bakin ta kafin ya ce.

"Baby take care kin ji ko."

"In sha Allahu"

Ya hana ta masa rakiya a haraba shi ya sa iyakarta kofar falo ya fita tana ɗaga masa hannu har ta za ta rufe ƙofar sai ga shi ya dawo da sauri yana faɗin.

"Baby key ɗin mota ko a kafa kike son na je wajen aikin yau?

Sai ta juya da sarssarfa ta koma ciki ta ɗauko masa, bayan ta kawo masa sai da ya sumbaci hannun sannan ya wuce yana faɗin

"I love you Baby."

"Love you too Noori na."

Hannu ya ɗaga mata, itama ta daga masa sannan ta rufe ƙofar. Dinning ɗin ta koma ta zauna domin ba ta ƙoshi ba sauran Naan bread ɗin da Habib ya rage ta ɗauka ta ci guda ɗaya ta hada da ruwan tea, Allah ne ya sota da ta yi amai saboda zuciyarta ta yi ta tashi sai da ta sha ruwa sai ta ji zuciyarta ta kwanta 

Tunani take yi ko dai ciki gare ta? Sai ta fara tunanin yaushen da rabon da ta ga al'adanta? Tun bayan ɗaukewar jinin nan na ɓarin da ta yi ba ta sake wani jini ba, tsalle ta buga ita kaɗai a falo da gudu ta ruga ɗaki ta dauko wayarta Habib ta so kira sai kuma ta fasa kar ta ɗaga masa hankali.
Sai ta mai da alkalan kiran ga Sisna amma ba ta ɗauki wayar ba wata kila ta shiga cikin makaranta ne
Sai ta bar mata saƙo.

"Albishirin ki. Ina tunanin ina da wani cikin SisNa."

Ita kaɗai a gaban madubi tana shafa cikinta tana kallo, farincikinta ya kasa ɓoyuwa wani irin murna Habib zai yi in ya san tana da ciki? Ba ta da tabbaci amma alamominta na kwana biyun nan ya fi kama da na masu juna biyu, sai a lokacin ta kula da nonuwanta sun tasa, kuma da man cikinta na farko kafin ta yi ɓarin shi a Nono ya fara nuna kansa kenan wannan ma anan zai fara bayyana kan shi?

Wata zuciyar na faɗa mata kar ta faɗa ma Habib sai ta je asibiti an tabbatar mata sannan sai ta faɗa masa cikin mamakin da tasan murnan da zai yi ba ƙarama ba ce, saboda lokacin da ta yi ɓari ya shiga damuwa sosai har ta dinga mamakin haka yake son haihuwa? Ko da yake in ta yi duba da gidan da ya fito gidan yawa ne shi ya sa zai so shima ya tara yara kamar mahaifinsa.




*Janafty*
*Sat, 05. June 2025.*
5:53pm.
*Posting on 17/04/2026*