02
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
*02*
_JIMETA: Zone 3_
*10:30pm.*
Alhaji Hadi Baba na zaune a gefen gadon dake cikin turakan shi, wasu takardu ne a hannun shi yake dubawa sanye yake da jallabiya mai ruwan madara, kansa da tsilintsilin furfura wani siririn farin gilashin ne a idanuwansa wanda in zai karanta wani abu yake amfani da shi saboda raunin ganin sa.
Sallaman matarsa ne ya katse masa nazarin takardun dake hannunsa, ya ɗago kansa lokaci ɗaya yana mai amsa mata cikakkiyar sallaman kamar yadda ta yi.
Dattijo ne mai cikar kamala da haiba, fari ne amma ba shi da haske sosai wataƙila ya yi sirki shekarunsa na haihuwa za su kai 66 amma hutu da jin daɗi sun saka fatarsa da yanayin jikinsa suna ƙaryata shekarunsa
mai ɗakin sa yake kallo dai-dai lokacin da ta ƙariso gaban shi.
"Baffa ba ka kwanta ba?
Ta faɗa da muryanta da ta cakuɗe irin na fulani lokaci ɗaya kuma tana nufar can ƙurar ɗakin in da ta ijiye mganin sauron da ta kunno a hannunta a saman wata kwalba lokaci ɗaya tana sake faɗin" Na manta yau ban yi maka feshin magani ba Baffa."
"Sannu da ƙoƙari. Na gode."
Ya faɗa da cikin harshen fillanci, dawowa ta yi zuwa gefen shi ta zauna tana kallon shi, itama ita ya kalla amma bai yi mgana ba sai ta fara dariya tana faɗin" Baffa me kuma na yi ni Jamila?
Kai ya girgiza kafin ya ce" Ba ki yi komai ba."
Agogon da ke sama ta ɗaga kai tana kallo sha ɗaya saura daga nan ta gano laifinta.
"Baffa ka san ina da tafiya a gaba na ina can ina ta ƴ'an kimtse-kimtse ne "
Ta sake faɗa tana yi masa mirmishi, takardun hannun shi ya adana a cikin dirowan gefen sa, sannan ya mai da hankalin shi a kanta, ba ta damu da jiran amsar shi ba har ta miƙe, farantin kwanukan abincin da ta kawo masa tun bayan dawowarsa ta sumguma tana faɗin" Bari na kai wannan kitchen na dawo Baffa."
Daga haka ta sake ficewa shi dai kawai ya bita da kallo yana mai girgiza kai, lokaci ɗaya yana sakin mirmishi.
Mintina huɗu sai ga ta ta sake shigowa da sallama wannan karon har sai da ta tura ƙofar daƙin lokaci ɗaya tana cewa" Baffa ko za ka sake fita ne?
Sai da ya amsa mata da kai kafin ya amsa mata da baki.
"A'a"
Ta fara tahowa zuwa gare shi, shi kuma yana kallonta, Jamila (Ammah) ko da shekaru suka tura kyanta da dirin ta bai samu wani tawaya ba, ko yanzu da yake kallonta yana ganin kyawunta na shekaru sama da talatin da auran su, ita ce dai Jamilar da ya aura yarinya yar shekaru sha shidda a lokacin, ita ce wacce Gwaggo ta yi masa auran gata da ita(Allah ya gafarta mata) ita ce kuma a yau uwar zaratan maza ginannu har guda bakwai, uwa kuma ga Muhammad Lamiɗo, kuma uwar Auta Ummu-Salma, har yau hasken fatarta ba ta dishe ba, da ya ke fara ce sosai mahaifiyarta kafin rasuwarta Nenne tsada ake kiranta saboda tsabar jan ta, sannnan kaf ya'yan su jan fatan ta suka ɗauko a kammani ma ta rinjaye shi, duk da mutane da dama sun sha cewa shi da Jamila suna ɗiban kama, tun da su ɗin jini ɗaya ne, wani lokacin Amma ba uwa ce kaɗai a wajen ƴa'ƴan shi ba hatta shi kan shi uwa ce gare shi, in ta rufe shi da faɗa kamar Gwaggo, shi ya sa ya sha cewa Ammah mata ce, ƙawa ce Aminiya ce sannan uwa ce a gare shi da ƴa'ƴan su gabaɗaya. Da yake kuma ya aure ta da ƙananun shekarun a wancan lokaci yanzu ma take cikin shekarunta na hamsin da shidda, babban yaron su Jibo ya zo duniya tana da shekaru goma sha bakwai, sau tari in suka jera da Jibril kamar ƙaninta yake ba ɗanta ba, yadda tserensu yake kamar a jere da juna. Sannan ta mori jikinta ba da ta kiba kuma ba ta da tsawo, gajera ce tsawon da yaran suke ɗaukowa tsawon uban su ne shi Alhaji Hadi Baaba.
Sai da ta zauna kusa da shi sannan ya sauke ajiyar zuciya.
Ya juyo yana kallonta ita kuma sai ta saka hannu ta zare masa gilashin fuskar shi lokaci ɗaya tana faɗin" Baffa a cire gilashin hakan nan, ko nima sai da shi kake iya ganina tarwai?
Dariya ya yi har sai da haƙoran shi suka bayyana a waje.
"Ahto Baffa ba amana a ce ba ka gane ni sai ka sanya gilashin ƙara karfin gani."
"Ammah ba ki da dama."
Ya faɗa da sautin muryan shi ya saba da kiranta Ammah kamar yadda yaran su, suke kiran ta ba ma shi ba kowa yanzu Ammah ne yara da manya. Shi kuma da man ita ce take ce masa Baffa kafin yaran su su tashi da sunan a bakinta.
Akwai wata rana da ya shuɗe Saddam na zolayanta da cewa.
"Amma wai kema Baffa Baffan ki ne?
Dakuwa ta yi masa kafin ta ce. "A'a naka ne mai uba, to ni ce mai Baffan gabaɗaya ku duk yan cikon banci ne."
Suna falo ne suna karyawa a wata safiya shi kan shi sai da ya yi dariya da kalamanta
Ammah ce, ba ta da dama mace ce mai jajircewa kan mijinta da ƴa'ƴanta mai son zumunci da yaƙana ce, amma kuma ba ta da haƙuri Amma mace ce da ba ta ɗaukan Nonsense tana da faɗa da zafi, zafin namanta har a jikinta da kazar-kazar ita ce mata ɗaya cal da Alhaji Hadi Baba ya mallaka a matsayin mata anan duniya amma ko yanzu da shekaru suka tura ba ta taɓa jin ta gaza daga hidimta masa ba.
Yanzu ɗin ma cewa ta yi ya kwantar da kansa saman filo, ta jawo kafafunsa a saman cinyarta tana matsa masa a hankali cikin kulawa tana faɗin.
" Baffa ya kamata ka huta. Kwana biyun nan ba ka samun zama sosai."
Sai da ya dan muskuta kafin ya ce" In na zauna gida na huta sauran harkokin nawa wa zai yi mini?
"Ka bar ma Baba"
"Ban da abin ki ai ko a yanzu shi ke yin harkokin, shima abin a tausaya masa ne ba ya cikakken sati tare da iyalansa."
Amma ta jinjina kai kafin ta ce" To shi yanzu jininsa yake Baffa kai kuma jiya ba yau ba, ni dai ka dinga hutawa kar wata rana aga tsoho na ya faɗi."
Ta ƙarishe faɗa tana masa dariya da man in tana jin nishaɗi ɗan tsohona take kiran shi, kai ya jinjina kafin ya ce.
"Tun da haka kike bukata ai haka za a yi uwar Lamiɗo "
Ta sake faɗaɗa mirmishinta ba ta dai ce komai ba tana cigaba da matsa masa kafafuwansa.
Idanuwan Baffa na lumshewa domin akwai gajiya a jikinsa Ammah dai sai dai Allah ya yi mata albarka ta san shi fiye da yadda shi ya karance ta. Mubi ya je shi da Abdullahi duk da ba shi ya yi driving ba doguwar tafiya yanzu na bashi wahala ko don shekaru sun tura ne? Shi da a shekaran baya a jihohin Nageria ba in da kafarsa ba ta ka da sunan kasuwanci ba. Kasuwanci ma irin na shi na siyan injinan manyan motoci ƙananu da manya da kuma wasu part-part na jikin mota ya daɗe yana wannan harkan kafin daga baya ya fara sirkawa da harkokin siyar da motoci sanadin haɗuwar shi da Alhaji Isa Ɗanmarke.
amma yanzu saboda girma da shekaru in ya yi doguwar tafiya a mota sai ya ji duk ya gaji sauƙi sauƙin ta ma in a jirgi ne.
"Saddam ya dawo gidan nan kuwa?
Ya tambaya cikin sanyin murya.
"Tun ɗazu fa ya dawo muna tare da shi, ya so ma ya jira ka har ka shigo sai ya ce mini kansa na ciwo zai shiga ya sha mgani, wataƙila lokacin da ka shigo ya kwanta ne."
"Me ya sa yake jira na?
Ya tambaya har lokacin idanuwansa na lumshe.
"Gobe ya ce yake so ya koma makaranta."
Sai a lokacin ya buɗe idanuwansa kafin ya ce" Gobe kuma? Ya fasa raka ki Dauran ne kuma?.
"Aa bai fasa ba ya ce akwai abin da zai yi ne a can, satin da za mu tafi zai dawo."
Ɗan miƙar da kansa ya yi yana gyara kwanciyarsa kafin ya ce" Allah ya ba da sa'a."
Ta amsa masa da Amin Amin.
"Bayan Umman ikki, sai kuma suwa kika shirya tafiyar da su?
Ya tambayeta yana kallonta, kai tsaye ta ce" Umma A'i tunda na fara yi ma mgana sai ta ce ba ta nan ɗiyar mijinta ta haihu a kano za su tafi, Umma salamatu kuma kasan ba ta son doguwar tafiya. Yanzu daga ni sai Umma Balki, sai Saddam da Ummin ikki."
Kai ya jinjina kafin ya ce"Kun isa ma, Allah ya nuna mana ya sa a yi biki lafiya a gama lafiya."
Ta amsa masa da Amin tana cigaba da faɗa masa sun yi waya da Lamiɗo ya ce Abdulrahaman zai siya musu tiket jirgi za su bi zuwa katsina daga nan motocin gidan Mai martaba sarkin Daura suna jiran su za su ɗauke su zuwa masarauta.
"Allah ya sa albarka."
Ta amsa da Amin kafin ta ce" Baffa ba za ka je ko ɗaurin auran ba?
Kai tsaye ya ce" Zai yi wahala. Ban dai sani ba, bari mu gani."
Tana jin ya ce haka ta san bai yi niyyar zuwa ba.
"Kai Baffa ban san ka da riƙo ba fa. Ai komai ya wuce yanzu mun zama ɗaya silan Lamiɗon mu."
Shuru ya yi na wani lokaci ba tare da ya yi mgana ba. Ya manta sannan ya yafe, kara yake yi ma Fatima, shi ya sa bai cika tusa kansa a wannan bangaren ba.
Janye kafafunsa ya yi daga cinyar Amma ya sauke a ƙasan cafet ɗin da ke ɗakin.
Sannan lokaci ɗaya ya yunƙura ya miƙe zaune yana mai kallon Amma.
"Na san zuwan ba zai gagare ka ba, sai dai in Fatima ce ta ce maka kar ka je ko?
Baffa Mai martaba fa da kansa ya kira ka ya sanar da kai bikin ɗiyarsa me ya sa ba zaka yi masa kara ba! Sannan Gimbiya Shahida ba ka ga yadda ta ke yawan kirana tana tambayana yaushe za mu taho ba, a ƙalla dai sun nuna mana ƙauna hatta Fulani ta kira ni, ta ce ba ta ɗauke mini zuwa wannan bikin ba."
Mirmishin gefen baki ya yi, a cikin ran shi yana faɗin sai yanzu? Da ma ace za su iya mayar da hannun agogo baya wataƙila da sun gyara kuskuren su na baya da Fargar jaji bai kama su a yanzu ba amma a sarari sai ya kalli Amma kafin ya ce" Ni wallahi ban taɓa rike su a raina ba Ammah kin sanni kin san halina. Kawai dai."
"Kawai dai me?
Ta katse shi tana kallon shi sai ya kasa amsa mata, domin ai ta san amsar tambayar nata.
"Fatima ce! Saboda Fatima ce ya sa kake yin wannan baya bayan ko Baffa?
Tafaɗa tana sake matsawa gare shi lokaci ɗaya ta tsare shi da kaifaffun idanuwanta masu sanya shi ya yi laushi bai shirya ba.
"Baffa don Allah kar ka biye ma wannan ƙanwar taka mai zuciyar rashin yafiya, yadda na sanka mai yi ma zumumci hidima ne. Ko saboda Lamiɗon mu ko sabo da shi, kar ka manta har abada Lamiɗo ɗan mu ne."
Ta gama faɗa tana mai riƙo duka hannayensa a cikin nata, ta kuma kafe shi da idanuwanta da ba ya iya mata gaddama in dai ta kafe shi da su.
"Za ka je ko Baffa?
Ta faɗa har tana kasa-ƙasa da murya.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Za mu je, zan yi ma Abdullahi(Baba) mgana."
"Baffa ka yi ma Abdurrahaman mgana ku zo tare da shi."
Sai ya jinjina mata kai kafin ya ce" Shike nan. Da ma kin sani kin yi ma Abdullahi(Baba) mgana ko da matarsa sai ku tafi."
Baki ta riƙe bakin ta ce" Na sha'afa wallahi bari zan yi masa mgana na ji."
"To Amman Lamiɗo."
Tana dariya ta ce"Kai kuma Baffan Lamiɗo ba."
Yana y'ar dariya ya ce" Na bar miki, duka matsayin tuntuni. Wannan Lamiɗon naki ai sai ke. Ni fa cikin satin nan da ya doka mini kira cikin dare sai da ya sa jinina ya hau na ɗauka ba lafiya ba ina ɗaukan kiran cikin damuwa na ce" Lamiɗo lafiya cikin daren nan?
Buɗar bakinsa sai ce mini ya yi" Baffa me ya sa kake tambaya? Ai da man wannan ne lokacin da na ke kiran ku a waya"
Ja'irin yaron nan ko a jikinsa bai ma damu da ɗaga mini hankalin da ya yi ba, muna gama gaisawa ya kashe wayarsa shi ya sa ma ko zan je ba saboda Lamiɗo ba ne sai saboda zumunci da girman mahaifinsa , amma shi Lamiɗo da na samu zuwa da kar na samu zuwa duka ɗaya ne a wajen sa."
Amma na dariya Baffa na taya ta, ya ci gaba da faɗin" Ta bakin Fatima ta ce ba zan iya da ɗan Ammah ba shegen faɗin rai. Ta manta jinin dake gudana a jikinshi."
Amma na gimtse dariyanta lokaci ɗaya tana faɗin" Ni fa bana ganin duk abin da ake faɗa akan Lamiɗo, a wajena yafi kowa sauƙin kai."
"Uhm da yake ɗan gaban goshin ki ne ai ba kya ganin laifinsa. Gaskiya Fatima ne ke kika bata Lamiɗo ya saba da komai ya yi dai-dai ne a wajen ki."
Amma ta dariya ta ce" to ba ta bar mini ɗan ba, babu kuma ruwanta da ni balle rayuwar ɗa na."
"Allah ya ba da sa'a."
Baffa ya faɗa Amma ta amsa da Amin..
"To iyalan na Lamiɗon za su taho bikin dai ko? Domin shi gogan na san ba zai samu zuwa ba."
Amma ta ce" Gaskiya ya ce mini da wuya ya zo suna can ko wata ƙasa ne ma, sunan da wuyar faɗa Baffa, amma ita Balkisu ya ce za su taho tare da yaran gabaɗaya tun da sun samu hutun makaranta."
Baffa ya jinjina kai kafin ya ce" Hakan ma ya wadatar. Allah ya nuna mana lokacin."
Ta amsa da Amin suna cigaba da tattaunawa har sha biyu saura na dare sannnan suka yi shirin kwanciya sai bayan sun kwanta ne Amma ta ce.
"Baffa ka yi mgana da Ummu ne a kwanaki nan?
Baffa na daga kwance ya ce" Jiya ta kira ni da safe mun gaisa. Tana lafiya ita da mijinta, shima yau da safe sai da ya kira ni muka gaisa."
Amma ta yi kyafci kafin ta ce" Habibu dai ya kira ni da safe amma Ummu ba ta kira ni ba."
"To ai kin yi mata faɗa zuwan ta na karshe shi ya sa ba ta kira ki ba."
Baffa ya faɗa yana dariya Amma ta kalle shi tana cigaba da faɗin" Au har ta faɗa maka? Munasiran yarinya."
"Ki rage yi ma uwata faɗa, kar ki manta ta girma yanzu matar aure ce."
"Ai ko duniya ta haifa sai na ci mata in ta yi mini ba dai-dai ba."
'"To me ta yi miki kuma?
Ammah ta miƙe daga kwancen da take tana faɗin" Zuwa fa ta yi ina mata hiran bikin nan na Daura ta yi banza da ni, shi ne na danƙwashe ta yarinyar nan ta fara mini kukan shagwaɓa wai ita ina ruwanta da bikin da zan ce sai ta saka baki a hiran? Ka ji fa shi ne na fattatake ta na ce kar ta dawo mini gida ta ce wai gidan ai na Baffa ne, na ce ta ci ubanta Baffan ma a ƙarƙashina yake ballanta ita "
Kafin ta gama bashi labarin ya fara dariya, Ammah dai ba za ta sauya ba, in tana faɗa da yara sai ka ce ba ita ta haife su ba musamman ma ita da Autar ta Ummi, ba sa zama a inuwa ɗaya yanzu nan lafiya anjuma za a ji su suna tafka tsiya ta fattateketa a gidan tun kafin ta yi aure gidan Ummin ikki take zuwa ta yi ma Amman ya ji sai in ta gaji da kanta take dawowa, ita fa Ammah ba ga ya'yanta ba ko na yan'uwa ne ba ta da sauƙi, jikoki kan sun san sauran in ƴa'yan su Jibo suka zo hutu sun ma san hali ba ruwanta da wasan jika da kaka yanzu sai ta ji ƙaniyar mutum, ba a yi mata wargi in aka dame ta ta kira uban ko uwar ta ce su zo su tattara ƴayan su ta gaji, ita da gidan Baffa ba za a bar ta sake ba. Babar ɗiyar Jibo Sauda wancan hutun da suka zo kafin su koma ta ci dundun Ammah, saboda ba ta jin mgana ga son jiki ita kuma Ammah ba ta shiri da yaro mara kunya da son jiki yanzu za ku samu matsala, ba su gama cinye hutun ba ta kira Jibo ta ce ya zo ɗauki sangartatun ya'yan shi ba za ta iya ba sun dame ta. Da yake shi ne babba kuma yana aiki ne Airport na Abuja can yake zaune da iyalansa.
Baffa ne mai wasa da jikokinsa da ƴa'ƴan sa amma ban da Ammah kana yi mata wasan za ta ma yar da shi na faɗa, ƴaƴan lamido ne kawai jokokin gata a wajenta in suka zo ta rasa ina za ta saka su kamar yadda take yi ma ubansu hidima suma haka take yi musu.
Hatta matar Lamiɗo hidima Ammah ke yi mata, ita kuma sanin Amma ce komai na mijin nata sai ta riƙe ta gam, domin yadda take yi ma Amma hidima da kuɗinta ko Mami da ta kawo Hamma Lamiɗo duniya ba ta yi mata haka, to ina ma ta ga fuska Mami ko a fili ko a sarari ba ta taɓa nuna Lamiɗo ɗan ta ba ne, Islam da Faruk sune duniya ta shaida ƴa'ƴanta. Shima bai taɓa nuna wata a matsayin uwa ba bayan Ammah ba
Sannan matar Hamma Lamiɗo ita ɗin yar masu kuɗi ce ɗiyar sarauta ce domin babanta shi ne Sarkin Kano na yanzu, ita kuma likitar mata ne mai zaman kanta, shi ya sa ko su matan Yaya Jibo ba su isa su haɗa kan su da Balkisu ba, ita ɗin ta musamman ce a wajen Ammah kamar yadda mijin nata yake gangariyan na musamman a wajen Amma.
"Ummu ta raina ni Baffa."
"Ba ruwana ina shiga zan ji kunya ke da Autar ki."
Da sauri Amma ta ce" Ba Auta ta ba ce, Autar Umman ikki ne."
Baffa ya sake yin wata dariyan kafin ya ce" Har da ke me, ni na ɗauka har da ita za ki tafi bikin. Na tabbata Habibu ba zai hana ta zuwa ba."
Da sauri Amma ta ce" Wallahi ba zan je da ita ba, kawai ta kunya ta ni, ka manta zuwan da na yi da ita naɗin Sarautan Lamiɗo nan fa na faɗa maka abin da ta yi mini sai da na yi nadamar zuwa da ita, tana ta taɓe taben fuska suna jan ta da mgana sai ta ga dama take amsawa, sannan ta maƙale mini ta ƙi zuwa ko'ina sai na yi mgana sai ta tura baki ta ce ba ta san kowa ba, wallahi ban ji daɗin zuwan da na yi da ita da man na ce har abada sai dai in ita ta kai kanta ba dai ni ba."
Baffa dai na ta dariya bai yi mgana ba.
"Ka san ta da shegen iyayin tsiya, ba ta da wayewa a wajen shiga mutane. In da Baɗɗo ta fita kenan da ba domin makarantar ta ba da tare da Baɗɗo zan tafi"
Baffa ya gyaɗa kai amma bai yi mgana ba.
"Ka dinga yi mata faɗa Baffa in kana so mu shirya da Auta nan ta ka."
"Zan yi mata"
Ya faɗa yana riƙo hannun Ammah, sai ta kalle shi, shima ita yake kallo waiwayi ya fara mata sai ta fara dariya tana kiran sunan shi.
"Baffa..!!!
*****
Jalingo Street.
Taa ƙasa faɗa ma Habib canje-canjen da ta ke ji a jikin ta. Tsoron ta kar ta sanya masa rai akan cikin kuma su je a yi gwaji a ga ba shi ba ne, kuma sun yi mgana da Sisna da ta nemi shawaranta sai ta ce kar ta faɗa masa amma ga shawara mai zai hana ta yi gwajin da PT ta fara gani in tabbas akwai cikin?
Sai ta aminta da shawaran Baɗɗo, ita ta bar ma alhakin siyo mata PT ɗin da alƙawarin in za ta zo gidan sai ta taho mata da shi, haka kuma aka yi ranar wata Jumma'a daga makarantar da take karatu wato State polytechnic Yola(SPY JIMETA) ta hayo abin hawa zuwa gidan Ummu.
Tare suka yi gwajin har tsinke biyu amma sai ya nuna babu cikin shike nan murnan Ummu ya koma ciki.
"SisNa kar ki wani damu, soon in sha Allahu za mu samu wani Baby kin ji ko?
Baɗɗo ta faɗa cikin sigan lallashi ganin Ummu ta ɗaga hankalinta.
"To amma yanayin da na ke ji a jikina fa SisNa?
Baɗɗo ta ce" Wata ƙila gajiya ce kawai ba wani abu ba."
Ummu dai duk da ba haka ta so ba amma hakan nan ta haƙura ta cigaba da karɓan lallashi daga wajen yaruwata Aisha(Baɗɗo) wata ƙawarta kwara ɗaya da dangatakar jini bai haɗa su ba amma amincin Amma da Ummi ikki shi ya haifar da wannan kyakyawan dangantar dake tsakaninta da Baɗɗo a yau.
Ba sa iya ɓoye ma juna komai, tun suna yara tare suka taso, duk da Ummu ta ɗan girme ma Baɗɗon da shekara ɗaya, amma yadda suka taso suka ga aminci mai ƙarfi a tsakanin iyayensu suma haka suka samar da na su misalin aminci a tsakanin su, duk da ita Ummu tana da wata ƙawar da suke kusanci sosai Shamsiya(Bestie) ita makaranta ce ta haɗa su tun da ga primary har gama babban sakandiri, a yayin da ita Baɗɗo ba ta da wata ƙawa Aminiya kamar Ummu Salma
Tare suka yi girkin dare, don Ummu ta hana Baɗɗo tafiya da ta matsa ma sai ta kira Habib a waya ta kai masa ƙaran ta shi kuma ya ce a ba ma Baɗɗo wayar ya yi mata magana da cewa ta tsaya har ya dawo su ci abiinci sai ya ma yar da ita gida tun da itama duk suna cikin garin Jimeta ne a wata anguwa mai suna Nasarawo.
Baɗɗo ba ta da yadda za ta yi dole ta zauna da man in dai ta zo gidan Habib da Ummu ke ma yar da ita gida wata rana kuma shi kaɗai, ta daɗe tana yi ma Ummu murna da farincikin samun gwarzo irin Habib, ta daɗe tana sha'awar irama ta yi aure ta tafiyar da mijinta da gidanta kamar da Ummu ke tafiyar da na ta gidan abin sha'awa abin birgewa, sannan abin da ke ƙara sa take ganin girman Habib girmama duk wani ahalin Ummu, son duk wanda take so shi ya sa ita da Shamsiya Habib ke yi musu hidima da jikinsa da aljihunsa saboda kawai sune makusantan Ummu na sosai ɗin da ba wanda ya san tsakanin su.
Bayan sun gama girkin Baɗɗo ta gyara gidan tas ta goge ta saka turaren wuta yana tashin ƙamshi, Ummu ta matsa mata sai da ta yi wanka kaya ma ta dage sai ta saka nata taƙi, a cewarta na ta ba su yi datti ba tun da ta ƙwabe su da za su fara girki ta saka wata doguwar rigar Ummu sauƙaƙƙa ta zaman gida. Bayan sun yi sallar mangriba ne Ummu ta yi wanka ta ci ado suka zauna a falo suna kallo suna hira a cikin hiran ne Baɗɗo ke faɗa ma Ummu ranar litini su Ummin ikki da Amma za su wuce Daura.
"Au da man tare da Ummin ikki Ammah za ta tafi?
Ummu ta tambaya Baɗɗo ta gyaɗa kai mata kafin ta ce" Ke ma ai kin sani, suna nan suna shiri."
Baɗɗo da Ummu suka kwashe da dariya har suna tafawa.
"To su Daura za su je ko Abuja? Tun da na ga duka events ɗin na su a Abuja za su yi ɗaurin aure ne kawai a garin Daura fa."
Ummu ta tambaya tana kallon Baɗɗo da dariya a bakin ta.
"To ni ina zan sani, kullum dai dai sai Ammah ta kira Ummi a shige ciki a daɗe ana tattaunawa."
A tare ma wannan karon suka kwashe da dariya kafin Ummu ta ce" Wa ya ga su Ammah a tawagan uwar Amarya."
"Sai ki iya ganin su."
Suka sake yin dariya nan Ummu ta fara ba ma Baɗɗo labarin karon su da Amma zuwanta gida na karshe.
"Sisna haka fa Ammah ta fitike ta in da take shiga ba ta nan take fita ba wai kawai saboda tana labarin bikin Daura ban tanka ba, shike nan fa ta fara faɗa daga ƙarshe ta ce na bar mata gida tun da ba gidana ba ne, ki ji ƙarfin hali."
Ummu ta ƙarishe faɗa tana, riƙe haba da sigar mamaki.
"Amma hoo. Ammah drama Queen."
Baɗɗo ta faɗa tana dariya.
"Ba wanda Amma ta ƙyale. Hamma Lamiɗo ne kawai ban taɓa ganin ta yi ma faɗa ba."
"Ke ko wannan ai ɗan gaban goshi ne."
Ummu ta taɓe baki kafin ta ce" Ai ni tun da gabda bikina ya taɓa kiran wayar Amma na ɗauka ya ji ni ce, ina fa mgana ya yi banza da ni daga karshe sai ce mini ya yi wai shi ba ya mgana da mara son makaranta .
Ummu ta karishe faɗa hawaye na cika ƙwarmin idanuwanta in ta tuna da cin mutumcin da Hamma Lamiɗo ya yi mata sai ta yi hawaye.
"To ke me ya kai ki ɗaga kiran sa? Mutumin da sai ya gan ka ya nuna bai san ka ba, ka gaishe shi yana ji sai ya ga dama zai amsa sai ka ce jinin sarauta hauka ne."
Baɗɗo ta faɗa cikin jin takaici domin itama ya taɓa yi mata wulakanci zuwan farko da ya kawo ma Amma matarsa, sai ya kawo ta wajen Ummin ikki, ta shigo falon tana gaishe shi ya yi kamar bai ji ba sai da Ummi ta ce Baɗɗo na gaishe ka sannan hankalinsa na kan wayarsa ya amsa a ɗakune kamar mai ciwon baki da " lafiya" Wannan abin ya yi mata ciwo tana uwar ɗakin Ummin ta ji yana cewa bai gane ta ba lamarin Hamma Lamiɗo bayan jinin sarauta har da wulakanci da ɗagawa ma a cikin shi.
"Ban san shi ba ne, saboda lambar ba suna, kuma ni na san sai dare ko asuba yake kiran Amma, in da na san shi ne ai ba zan ɗauka ba, ni da lokacin da maganar aurena da Habib ya taso ya kira Amma a waya yana faɗa wai ya za su biye mini na ƙi karatu na ce aure zan yi ina yarinya da ni ban san komai ba? Da shi da Hamma Kabiru da yake shima irin halin su ɗaya ya zo yana ma Baffa kumfar bakin cewa na yi ƙankanta da aure."
Baɗɗo ta kalli Ummu ganin har ta fara hawaye.
"Ni yaushe na ce aure na ke so? Ni dai ba na ce ba ne a ƙyale ni bana son cigaba da karatu abin da na san kawai na ce kenan."
Sai kawai Ummu ta fashe kuka Baɗɗo da ya ke ta san hali sai ta dafa kafaɗanta tana faɗin" To ke ma ban da abin ki duk wanda ya ji ba ki son karatu ai zai fassara ki da cewa aure kike so ne SisNa"
Kafaɗan Baɗɗo ta kai ma duka ita kuma sai ta goje tana dariya .
"In kowa bai fahimci halin da na ke ciki ai ke na san za ki fahimce ni. Karatu na daga cikin abin da ke wahalar da ni, tun da ya ke ba ni wahala na yi kuma iya yina na riƙa ganewa na kasa ba gwara na hakura ba, domin ina tsoron na shiga jami'a domin faranta ma su Hamma Kabiru rai kafin na yi nisa a kore ni."
Baɗɗo ta kwashe da dariya Ummi na ta ya ta da guntun hawayenta.
"Hamma Saddam ya ce sai ya ga wanda zai aure ni ina low class ban ji turanci mai zurfi, sai ko ga shi ya sha mamaki. Ya ga Noori na, wanda kyau dai na fuska da zati bai isa ya nuna masa ba."
"Bai isa ba."
Baɗɗo ta faɗa tana dariya.
"Bestie ta ce tana roƙon Allah ya ba ta miji kamar Habib. Ya so ta kamar yadda yake sona."
"Amin."
Baɗɗo ta amsa kafin ta ce" Ai Habib miji goma ne, kin gama dacewa SisNa muma Allah ya sa mu da ce irin na ki."
"In sha Allahu za ku samu fiye da wanda ya fi Habib ma."
"Allah ya sa hakan."
Baɗɗo ta sake amsa mata, sannan suka cigaba da hiran su, ana haka sai ga Shamsiya ta kira wayar Ummu sai ta saka ta speaker suna fara mgana Baɗɗo ta kira sunanta.
"Bestien SisNa."
Tana jin haka ta san Baɗɗo ce domin haka take kiran ta, ita kuma sai ta ce mata Sisna Bestie na.
"Wayau kika yi mini Sisna bestie na? Kika taho duba Bestie ba tare da ni ba?
Shamsiya ta faɗa daga cikin wayar, Baɗɗo ta ce mata itama fa ta kwana biyu ban leƙo ta ba sai yau fa kin san saboda makaranta mun kusa fara jarabawa.
Shamsiya ta ce suma sun kusa farawa shi ya sa amfani da wayar ma sai a hankali.
Shamsiya irin yaran nan ne masu ƙoƙari da nacin karatu, kaf gidansu yan boko ne sai kin gama jami'a ko kin kusa gamawa kike da damar fidda mijin aure, ko ba ka son karatu su a gidan su wajibi ne sun ɗauki boko kamar wani zunubi ne in ba ka yi ba. Ita kanta Shamsiyar ɗaliba ce a jami'ar Modibbo Adama University Yola a garin girai can ta ke zama a hostel sai sun samu hutu take zuwa ganin gida.
Sun daɗe suna waya suna ta hira, har sai da dawowar Habib ya katse su. Baɗɗo sai da ta kauda idanuwanta, saboda rumgumar da ta gudana tsakanin Habib da Ummu in da a ce ana sabo da tuni ta saba da ganin haka tun bayan auran Ummun da Habib.
"Baɗɗon mu."
Habib ya faɗa yana yi mata murmishi bayan sun gama oyoyon shi da Ummu.
"Noorin mu."
Dariya ya yi, domin Habib akwai harka ko yau kuka taɓa haɗuwa da shi sai ka ji kamar ka yi shekara da sanin shi, yana da magana da harka sosai.
"Na sa ka ki jirana ko?
Bari na yi wanka mu ci abinci sai mu je mu kai Baɗɗon mu gida ko Baby?
Ummu ta gyaɗa masa kanta lokaci ɗaya tana mai saukar da kanta a saman kafaɗan sa.
A falo suka bar Baɗɗo suka shiga ciki mintina talatin sai ga su sun fito Habib ya yi wanka ya sanya kaya zuwa jallabiya baƙa a dinning suka zauna Ummu ta yi serving ɗin su jalop rice mai salat, sai zoɓo sauran na jiya ne da ta saka a frizer suna ci jefi-jefi suna hira, hiran kuma tsakanin Habib da Baɗɗo ne yawanci kuma akan karatun ta ne.
Sai can ne Ummu ta kan sako musu baki ko kuma in ya juya ya sako ta a ciki.
Sai wajen tara na dare Habib da Ummu suka tafi kai Baɗɗo gida, da suka isa ƙofar gidan Habib ya ce su shiga ciki su gaisa da Ummu ikki, Ummu ta ce aa suna shiga za ta yi musu faɗa ne.
"Mu shiga Baby, ba fa Ammah ba ce."
Ya faɗa yana dariya Ummu ta girgiza kai kafin ta ce" Ba ka san su ba ne, daga ita har Amma halin su ɗaya."
Ya dage sai da suka shiga cikin gida, matan baban su Baɗɗo Biyu Ummin ikki ce uwargida sai Anty Saratu, suna tsakar gida ne suna hira lokacin da suka shigo Baɗɗo da Ummu Habib kuma ya tsaya a sauro kafin su yi masa iso.
"Ke yanzu Ummu kin kyauta ma kan ki kenan?
Da tsohon daren nan?
Ummin ikki ta fara faɗan ta, itama kamar Amma ne ba su gani su ƙyale.
"Ummi Baɗɗo ce ta yi dare Habib ya ce ta jira mu kawo ta gida."
"Habib ya ce ko ku kuka ce?
Umma ikki ta faɗa tana hararan su, Baɗdo ta kwaso rantsuwa tana faɗin" Wallahi Ummi shi ya ce na jira shi."
Wata uwar harara ta maka musu, atare Ummu da Baɗɗo suka saka dariya suna kumshe bakin su.
"Ja'iran yara kawai, to ina shi Habibun? Waje ku ka baro shi?
Jin haka yasa Ummu ta miƙe tana faɗin" Bari na ce ya shigo."
Ummin Ikki ta yi ƙaramin tsaki kafin ta ce" Ba ni hijabi na"
Hijabin Baɗɗo ta ɗauko mata a cikin ɗaki ta saka ita kuma Anty Saratu da man ta shiga ciki tun bayan da suka gaisa da Ummu da farko.
Habib har ƙasa ya duka ya gaishe da Ummin ikki kamar yadda ya saba ta amsa mishi cikin sakewa, ba su daɗe ba suka yi musu Baɗɗo ta raka su har bakin gida nan suka ci karo da Baban su Baɗɗo ya dawo shima faɗan ya fara yi da ya gan su.
"Kai Habibu ba za ka daina biye ma shirmanmun yaran nan kuna yawan dare ba ko?
Ya faɗa ba wasa a muryan shi Habib a ka bari da kare su Ummu.
"To ku yi sauri ku isa gida garin da kamar hadari. Allah ya yi muku albarka."
Suka amsa da Amin ya shiga gida, su kuma suka shige motar Habib ta kamfanin Toyata, Baɗɗo na ɗaga musu hannu har suka ɓace daga layin.
*****
Ammah da tawagarta ranar litini da safe jirginsu ya ɗaga zuwa katsina. Ummu ma ba ta san tafiyarsu ba sai da ta ga Hamma Sadam na posting ɗin hotunan shi a status a cikin jirgi a first class, shi ne ta tambaye shi ya ce tun safe suna Daura.
"Eyye Baffa ne ya biya muku kuɗin jirgin?
"Wani Baffa, ai wani kaya sai amale Hamma Lamiɗo ne, na ke faɗa miki a rukunin masu kuɗi muka je katsina. A VIP muka kame, muna sauka kuma ga motocin masarauta da dogarai da yan sanda suna jiran saukan mu, suka kwashe mu da jerin convoy motoci hadaɗɗu, sai ga mu dai a cikin Masarautan Daura."
Duk Hamma Saddam ne ya zayyano mata wannan labarin, da man shi nan ya fi ƙwarewa.
"Ba shakka. To ina su Ammah yanzu?
"Suna can cikin gida ni ina bangaren Hamma Lamiɗo ne nan ake sauke ni, Ummu kin ga masarautar Daura? Kin ga shashen Hamma Lamiɗo? Na rantse da girman Allah ban taɓa ganin tsaruwa da kyau na masarauta kamar yadda na ga tsaruwa irin ta masarautar Daura ba"
"Uhm. Na gani."
Ta tura masa ganin yana neman ya manta itama fa ta je ta ga komai ba sai ya sake zayyana mata ba.
"Yanzu muna tare da Saleem ne ƙanin Hamma Lamiɗo, anjuma za mu je gaida Mai mairtaba Sarki"
Ba ta tambaye shi ba amma sai zuba mata labarai yake yi, gajiya ta yi ta katse shi da cewa." kai ma har can Abuja za ka je?
Ya dawo mata da amsa da cewa sosai ma a gobe za su tafi tare da tawagar matayen Sarki amarya da tawaganta suna can tun shekaranjiya.
"Allah ya ba da sa'a."
Ta rubuta mai daga nan ta kashe data, amma bayan awa ɗaya da ta sake kunnawa sai da ta ga saƙon sa
"Kin san Mai martaba Sarki na da wani ƙaton gida a garin Abuja acan za mu sauka. Har sai an gama shagulgula sai ranar ɗaurin daure da safe za mu koma Daura."
Emojin mirmishi kawai Ummu ta tura masa, ita fa shi yasa ba ta yi mamaki da ta ga Hamma Saddam ya je Jamia yana karantar aikin jarida daman ya fi dacewa da shi, shi fa duk in da ya je sai kowa ya sani posting ne kan posting har da karin bayanai, ranar ya saka status sun fi goma na ƙarshe shi ne wanda ya ɗauka tare da Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Dr. Nasiru Muhammad Daura a cikin fadar shi yana zaune kan ƙaraga idanuwansa ne kawai ake iya gani saboda yana cikin naɗi. Caption ɗin da ya saka ne ya sa Ummu kwashewa da dariya.
"Allah ya ja zamanin ka ubanmu uban ƙasa, Allah ya ƙara maka lafiya Mai mairtaba Sarkin Daura."
Hamma Saddam na da abin ban mamaki, sawa yake yi har bargar dawakai da ya shiga sai da ya yi hoto ya saka, Ummu ta tabbatar da ba za ta yi missing komai na shagalin bikin nan ba, tun da dai Hamma Saddam ya na can ai kamar suna can ne suma.
Sai ranar Jumma'a Habib ya sauke ta gida da safe kafin ya tafi wajen aiki, duk da Ammah ba ta nan amma Baffa na gida bai je ko'ina ba tare suka yi ta hira sai da ya fita zuwa sallar jumma'a, yana fita ba daɗewa matar Hamma Abdurrahaman ta zo ita da yara, Adda Ummu Sulain tare suka yini a gidan har dare, Ummu ta yi ma Baffa tuwo miyar yauƙi, da man da Amma ba ta nan daga gidajen su Hamma Abdullahi ake kawo masa abinci sai misalin tara na dare Habib ya zo ya ɗauki Ummu suka koma gida bayan ta yi guzirin tuwo saboda ɗumamen safe.
Lalle ko an sha shagali a garin Abuja, ashe su Ammah duk uwar Amarya ta yi musu anko da man shi ya sa take ta tambayan mutanen da za su zo daga bangaren Ammah. An yi mothers Day su Amma an sha kamfala da mayafi ita da Ummin ikki, Hamma Saddam ya ɗora su a status a ƙasa ya saka
"Hamma Lamiɗo mai uwaye biyu."
Hoton ya yi kyau, sai da Ummi ta ɗauka itama ta yi status, da wanda aka yi ma Ammah ita kaɗai ta yi shar da ita, ita da ta tashi saka hoton sai ta yi zolaya.
"Amman Baffa"
Ta saka emojin love da rawa.
Baffa kuma ya gani dariya kawai ya yi bai yi mgana ba.
Da man Hamman Saddam ya faɗa ma Ummu Amma na ta masa faɗan wai ya yi ya tura ma tsohon ta hotunan ta. Ummu ta yi dariya sosai rayuwar auran Ammah da Baffa rayuwa ce abar burgewa da tsari, ita tana da zafi shi kuma Baffa mai sanyi ne da haƙuri shi ya sa aka zauna lafiya.
An yi Dinner na gani na faɗa abu ne masu mulki da sarauta, matan sarakuna sun zo ma uwar Amarya biki, a matsayinta na uwargidan Mai mairtaba Sarkin Daura Gimbiya Shahida, itama ɗiya take ga tsohon wazirin na garin Daura. Sai ga su Ammah a tawagan uwar Amarya suna jera kafaɗa da matan gwamnoni da sarakuna da matan ƴ'an majilisu har da matar mataimakin shugaban ƙasa, ga matar Gwamnan Jihar Katsina sannan ga bangaren uwar ango itama da na ta tawagan, matan ministoci da masu faɗa aji a fadar gwammatin tarayya.
Ammah sun yi hotuna da uwar Amarya sannan ta yi da Amaryan da ango sai kuma wanda ta yi ita da matar Hamma Lamiɗo Dr. Balkisu Usman Bayero"
Su Hamma Saddam an saje cikin ƴaƴan sarakuna da ƴaƴan ministoci shima cikin ɗanyar gezner irin ta masu bikin, sai da Ummu ta yi da gaske ta iya ma gane shi, lalle su Hamma Saddam an samu duniya.
Matar Hamma Lamiɗo Ummu ta shagala da kallo, matar nan akwai gayu, yar gayu ce ta bugawa a jarida ga kyau ga ilimi ga gayu, ƴa'ƴan su Biyu mai sunan Maimartaba Nasiru(Sultan) sai mai sunan Amma, Jamila(Beena) wani arnen leshi ne a jikinta da ga gan shi ka ga kuɗi, ankon Dinner ɗin ne amma na ta kalan peach ne na su Amma kuma maroon ne kalan ya yi kyau sannan da mayafin su kalan head ɗin su, Amma da Ummin ikki fa har da makeup aka sha irin light ɗin nan sun fa ba za kafacity.
Baɗɗo ta saka su a status ta rubuta.
"Capacity iya capacity Amma da Ummin ikki."
Babu wanda bai saka su a status ba, har Hamma Jibo, Hamma Kabiru ne ya saka hoton Amma ita kaɗai ya yi caption da cewa.
"Ammah uwar Amini Lamiɗo"
Ummu na gani sai da ta taɓe baki, duk wannan bidirin da ake yi shi gogan bai san ma ana yi ba.
Ba ta da lambarsa , yadda bai taɓa nuna damuwarsa akan rayuwarta ba, itama ba ta damu dashi ba duk da ko uwa ɗaya ce ta yi musu tarbiya.
Har Adda Nauwara matar Hamma Jibo ta je Dinner ɗin ita da su Saudat, tun da suna garin suma sun yi kyau da ya ke Hamma Jibo shima ba daga nan ba ɗan gayu ne sosai, matarsa ma yar gayu ce haka ma ƴaƴan su. In suka zo hutu Jimeta ba sa yin hausa wa junan su yaran su yi ta turanci wata rana da Saudat ta yi ma Ammah mgana da turanci yini ta yi faɗa tana cewa ita za a nuna ma iskanci to ko uban ta nan ya girma ita da Baffa hausa da fillanci suka koya masa ba ta son tsirfa da iyayi, kar a sake yi mata turanci a gida gargaɗi aka yi ma Hamma Jibo da Adda Nauwara, da cewa ba su ko ya ma yara fillanci ba sai wani turanci yaren da ba na su ba. Ammah fa Ƴa'ƴan Hamma Lamiɗo ba su jin hausa daga uwar har uban da turanci suke yi musu mgana gwara ma Hamma Lamiɗo shi yana yi musu hausa da fillanci wani lokacin amma uwar sai turanci amma har yau ba a ji Amma ta yi faɗa akan haka ba tun da Hamma Lamiɗo ne, shi kuma Hamma Lamiɗo shalele ne a wajen Ammaj ba ya laifi.
Ranar da aka yi Dinner sai wajen ɗaya na dare Ummu ta kwanta Habib ya gaji da jiranta ya kwanta ta kafa ta tsare tana kallon abin da ke kwana a garin Abuja a wani ƙayattacen hall, an sha Dinner sai wanda ya je ya gani su ɗin ma dake gida sun gamsu da Dinner ɗin ta masu mulki da sarauta ne. Maƙawan arewa sun hallarta kowanne mawaƙi ya baje na shi kolin, irin su Ali jita, Naziru sarkin waƙa, Nazifi Asnanic, Auta MgBoy, Auta waziri, Salim smart, Ɗan musa da sauran su ko wanne da irin karin waƙar shi ga amarya da ango sun kuma sha kuɗi, domin miliyoyi ne ke tashi da dollars, wannan daren dai Dinner ɗin ce ta dinga trending a kafafen sada zumunta ita dai ko alama bata nuna ma tana da alaqa da masu bikin ba.
Sai washegarin ranar asabar aka ɗaura aure a masarautar Daura, Hamma Kabiru ya saka hoton Hamma Lamiɗo.
Sai da Ummu ta kau da wayar daga fuskarta saboda tsoratar da ta yi, sanye yake da uniform ɗin su na matuƙan jirgin ruwa
Farar riga da baƙin wando fuskar shi ce ta ba ta tsoro, ta yi gargasa gemunsa ya yi kamu uku, kansa gashi ya cika ya yi yawa babu kyan gani.
"Amini a bakin aiki."
Haka Hamma Kabiru ya saka, sai da ta je hoton gaba sai ta ga ya saka wanda ya yi gyaran fuska ya rage gashin fuskar da na sumar kan amma ba sosai ba.
"Amini ya yi gyaran fuska."
Wataƙila Hamma Kabiru ne ke wahalar posting ɗin Hamma lamiɗo, shi ko ba ta da tabbacin yana saka shi, duk dai kowa ya shaida akwai aminci a tsakaninsu fiye da kowa ma, Hamma Lamiɗo mutum ne da bai cika bayyana ƙarfin alaqar sa da ko ma waye a zahiri ba, fuskar shi ba ta fallasa sirrin zuciyarsa.
Kullum a ginshiƙe za ka gan shi, fuskar nan kamar yana cikin wani damuwa a kame in ma ka samu ganin shi kenan, mutumin da a shekara bai wuce sau ɗaya
yake zuwa ganin gida ba. Duk da yana da tamƙamemen gida anan garin Jimeta, sai ya yi rabin shekara a rufe wani lokacin a shekara sau ɗaya yake zuwa in an yi wani abu ne sau biyu sai dai yana yin sama da wata a Jimeta in ya samu hutun karshen shekara wani lokacin shi kaɗai ya ke tahowa matar tashi sai aiki ya yi mata sauƙi sai ta biyo shi ita da yara, daga nan ne suka wucewa Daura can ma wani alkarya guda ne da sunan bangaren Hamma Lamiɗo.
Aikin su na yana da tsauri, Captain ne shi ma'ana matuƙin jirgin ruwa ne. CAPTAIN M.N. MUHAMMAD.
Yana aiki da kamfanin Nigerian port Authority jiragen dake jigilan mutane da kayan masarufi shi ya sa suke daɗewa a saman ruwa
Babu ƙasar da ba sa zuwa ta kogi sai su yi wattani sama da shidda a saman ruwa ba su shigo gari ba, sun fi ma saurin dawowa gida in sun ɗauko kayan masarufi.
Shi ya sa suma kan cika fuskar shi wani lokacin sai sun zo bakin gabar wani garin ne suke samun damar yin wani abu, hutu ko bai wuce na awanni huɗu ba ka ci abinci ka kwanta kana tashi ka koma bakin aiki, sau tari shi ya sa ba ya kiran waya da rana sai cikin dare ko asuba, wani lokacin ma sai a yi kwanaki ba a samu wayar sa ba.
*Janafty*