HADIN KADDARA

Chapter 5

by @aishanalado88

🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

                    By 

        AyshaNalado



Page 5


Dai-dai wani tamfatsetsen get hause no 32, ya tsaya tare da danna horn, da sauri mai gadi ya wangale get, da alamar tsaye yake yana jiran isowar shi, koda yayi parking sai da ya kwashe kusan 2 minute kafin ya fito. Compound din gidan yalwace yake da hasken fitulun solar ta ko ina tar-tar kamar rana, hakan yasa ya kara jan P cap din shi gaba da kyau ya kare fuskar shi, kafin cikin takunsa mai cike da nutsuwa da kasaita ya nufi kofar shiga kayataccen ginin upstair ɗin da ke nan kalli ɗaya tal a cikin gidan. Danna doorbell yayi sau ɗaya yaja ya tsaya, kusan minti biyu ba'a buɗe ba, dan guntun tsaki yaja yana mai kallon agogon dake daure a tsintsiyar hannun shi, sake danna wa yayi a karo na biyu, wannan karon yana danna wa ana buɗe wa, dattijuwar macece wacce a kalla zata kai shekaru 40+ da haihuwa ba, ganin wanda ke tsaye bakin kofar yasa ta zaro manyan idanunta a tsorace, ba ta taba zaton shi ba ne, duk tunanin ta Suraj ne, da yace mata yana zuwa shiyasa ma ta buɗe kofar gabanta gaɗi, da sauri kamar wata mara gaskiya ta kamo hannayen shi ta janyo shi ciki, ta maida kofar ta rufe tare da murza key, koda ta juyo kan sofa ta ganshi yayi wata irin zama yayi balance ya cire P cap ɗin kanshi ya ajiye a hannu kujera, ƙarasawa ta yi gaban shi ba tare da ta ce ma shi komai ba ta saka hannu ta cire facemask ɗin dake fuskar shi tare da zare siririn glass din daya toshe kwayoyin idanun shi da shi.

Ajiye mai tayi kusa da P cap ɗin, ta juya zata bar falon still bata ce mai kala ba, da sauri ya riƙo hannun ta, tsayawa ta yi, ba ta tafin ba shi ma bai sake hannun ba, tasan me riƙo hannun ta da yayi yake nufi, haka zalika shima yasan me shirun ta yake nufi, ba tare da ta juyo ba tace, "Nasha gaya maka Bunayya, bana son kana fita kai kaɗai riski ne ga rayuwarka, balle ma a irin wannan lokaci na duhun dare. So kake su kashe mana kai? Idan kai baka son rayuwar ka mu muna son ka." Shiru yayi ba tare da iya cewa komai ba, dama ya shiryawa hakan don yasan dole za ta kasance.

Ganin bai da niyyar yin magana yasa ta fisge hannuta daga riƙon da yayi mata ta ci gaba da tafiyar ta, bata san tasowar shi ba sai dai Kawai ganin shi tayi a gabanta, dakatawa tayi ta daga kai kasancewar yafi ta tsawo sosai ta zuba mai idanu tana binshi da wani irin kallo mai cike da zallar madarar so dà kauna, hannu ya kai ya riƙe kunnuwanshi, tare da yin narai narai da idanu, a hankali cikin muryar shagwaba kamar ba wannan zankaɗeɗen murdadden saurayin mai cike da miskilanci ba ya ce " I am sorry mother ba zan sake ba in sha Allah " hararar shi tayi ta ce "sau nawa kake cewa haka kuma da anjima ka sake." Ya ce "kiyi hakuri Mother tsananin kewa da bagen son ganinki ne suka addabi ruhina, zuciyata ta dinga azalzalata a kan na zo na ga sanyin idaniyata." Hannunta ta daura a kumatunshi dake dauke da gewayyayyen saje mai taushi sassayayye da ya kara fito da kyawu da kamalar fuskar tasa ta shafa, tare da cewa Na hakura Bunayya, kasan ba zan iya dogon fishi da kai ba shi yasa ka ke yin abin da na haneka a duk sanda ka ga dama, saboda kasan lago da hanyoyin tankwara zuciyata, amma zan yi maganin ka soon." Tsadadden murmushin shi ya saki tare dà kamo hannunta dake kan kumatunshi, ya kai saitin bakin shi ya sumbata, tare da cewa "Thank you, mother like no other." Murmushi ta saki tana zame hannunta daga nashi, yace "Mother yunwa na ke ji tun safe ban ci komai ba." Zaro ido ta yi tace “Tun safe fa kace?" Ya langwaɓe mata kai yana taɓe baki kamar zai yi kuka, tace "Innalillahi Bunayya wai me yasa kake min wasa da rayuwarka ne haka for god sake." Bata jira jin amsar shi ba taja hannun shi zuwa dinning area, ta ja mishi kujera ya zauna kafin kace kwabo ta cika mishi gaban shi da abinci kusan kala uku, ta tsiyaya mai ruwa da zobo a cup, ta tura mai ta miƙe ta buɗe fridge ɗin dake angle ɗin wajen ta fito da dammammiyar fura mai sanyi a cikin wani dan bowl ta tura mai gaban shi, kasancewar tasan yana masifar son fura musamman ma wanna da take dama wa, wanda takanas take sanya makociyarta ta yi mata shi na musamman, so da yawa saboda shi take yawan ajiye damammiyar fura, duk wannan abubuwan da take yi tana yi tana mai faɗa akan wasa da rayuwar shi da yake yi, cikin faɗa faɗa amma a hankali kasancewar tasan shi mutum ne da baya son hayaniya take cewa “Yanzu menene amfanin ace mutum ya wuni bai ci komai ba, gaskiya kar ka sake maimaita irin wannan kuskuren, kai kenan baka da cikakken lokacin kanka kullum cikin aiki, kuma ma wannan abin harda laifin, Aunty Rukkayya itace bata kula da kai da cikin ka yadda ya kamata zan kai karar ta wurin Yaya, sannan mai babban laifin Kaine Bunayya na ce ka fitar da mata kayi aure kaƙi yanzu inda kana da mata ai ba za ta barka haka a gantale ba, cikin dubban yan matan da ke kara kaini kaunarka, ka fidda ɗaya dan Allah koda cikin Ahlin kangiwa ne ka zaɓa muna da ƴan mata birjit a zuri'ar mu. Ko huɗu kake so kana da halin, auren su a rana ɗaya, kana da inda zaka ajiye su kuma ka kula da bukatun ko wacce ba tare da ka takura ba, mahaifinka bashi da buri kamar yaga ka fitar da matar aure, kana tuananin idan haƙurin shi ya ƙare bazai aikata abin da ba zai maka daɗi ba kuwa? kasan fa mutum mai haƙuri kamar Yaya bai iya tunzura ba,muna saka ran nan da yan wasu watanni za ka taka babban matsayi a kasar nan, shin a haka kake so ka zama jagoran biliyoyin mutane, shi fa aure yana cika mutunci da kimar mutum ne, kai tsaye ma a addinance yana cike rabin addinin mutum, matashi mai shekaru kamar naka kamata yayi ace yana da mata har da albarkar ƴaƴa, ka duba abokinka Usman dan gidan Yaya dattijo tare a ka yi goyon ku, kama girme mishi a haihuwa amma yanzu ƴaƴan shi biyu matar shi nada cikin na uku kai kana nan har yanzu baka kama dahir ba."

 Duk wannan bambamin faɗan da mother ke yi yana jin ta bai tanka ba sai ma buɗe ciki da yayi yana ta kai lomar abinci, sai da ta yi mai isar ta, sannan kuma ta sausauta murya ta koma rarrashi, cikin raunin muryar ta ci gaba da cewa" shin me yasa ba za ka fitar da mace ka aura ba Bunayya? Idan ma ba za ka iya zaɓe ba ka bani dama ka faɗi irin wacce kake so wlh zan nemo maka ita a duk inda take. Idan kuma kace ka bani dama wlh na riga na tanadar maka mata nitsatsiya yar mutunci uwa uba kuma kyakkyawa ta karshe ga ilmi wacce zaka iya shiga ko ina da ita a faɗin duniya ba za ka ji kunya ba, ka yi tunani a kan maganata son dan Allah ka amince min kodan Yaya da damuwar da yake ci akan lamarin ka fitar da mace ka yi aure." 

Kadan yaci abincin ya dauki damammiyar furan data ajiye mai ya shiga shiga sha yana ji kunnen shi kamar zai tsinke dan santi sai da ya shanye tass, sannan ya ajiye spoon ɗin yana lashe baki, kallon shi mother ta yi tace "Baka ce komai akan magana ta ba Bunayya." Shiru yayi ya zuba mata idanu yana tunanin amsar da zai bata, can kuma ya buɗe baki dakyar yace "kiyi hakuri mother a kwai lokaci." “Wani irin lokacin ne wannan da  yaƙi zuwa har yau, kullum idan magana makamancin wannan ya haɗa ni da kai amsar da kake bani kenan, kiyi hakuri mother a kwai lokaci, to yau dai dan Allah ina bukatar jin wata amsar sabanin wannan, na gaji da jin wannan." Ta karshe maganar a ɗan kausashe da alamar abin yana cin ranta matuƙa, ta kuma tsare shi da idanu alamar tana jiran ji ta bakin shi, ƙasa ya yi da kai domin baya jure irin wannan kallon daga gareta.  Shiru ne ya ratsa wajen na mintuna har ta cire rai da jin amsa daga gare shi, ta tsinci muryar shi cikin sanyi yana cewa    “ Ki yi hakuri Mother,  zan yi aure in sha Allah, ku ci gaba da yi mini addu'a, i need to rest, zan dan kwanta." Yana gama faɗin haka ya miƙe idanunshi sun rine, da alama yayi babban fami a zuciyar shi, cikin sassarfa ya haura upstairs, ɗaya daga cikin ɗakunan dake saman ya buɗe ya shiga tare da maida ƙofar garam.

Da kallo Mother ta rakashi harya ƙulewa ganinta zazzafan numfashi ta sauke, a bayyane tace "A kwai ƙura, an ya ba aljanu ne suka auri Bunayya ba kuwa? Tabbas sune, idan ba haka ba ta yaya yaro daga an yi maganar aure sai ya birkice nan take, idan ba ita din ba ma wa ya isa ya yi mai wannan maganar ya sha lafiya, gaskiya da sake ba su ga ta zama ba kam, ya zama dole su tashi tsaye a kan shi, gobe dole ta kaima Yaya ziyara akan maganar nan." Ta dau tsawon lokaci tana saƙawa da kwancewa a zaune a dining  din ba tare da ta ankaraba.  Ƙarar doorbell da taji ne ya dawo da ita hankalin ta, ko ba'a faɗa ba tasan Suraj ne, tashi ta yi jiki a sanyaye ta bude mishi ƙofar, ya shigo, kallo agogo tayi tare da maida idanunta kanshi ta tsatstsare shi da su, ko bai tambaya ba yasan laifin shi, da sauri ya rike kunnuwanshi yace "Sorry Mother." Tace "Ina kaje." Cikin in ina yace "Gidan su Salman." Kunnensa ta kama ta Murda da karfi, “Ochhh!” Ya saki kara ya rike kunnen yana ja da baya,  “ Karya ka ke yi, yanzu na gama waya da Ammin  Salman ta ce min ba ku shigo gidan ba har shi Salman ɗin yawo ko?.”  Ya girgiza kai da sauri, ta yi kwata tare da mika masa hannu, musu ya saka mata makullin motar dake riƙe a hannun shi, tace "Punishment ɗinka shine ka shiga kitchen da kanka ka girka abin da zaka ci don na yi kyauta da abincin ka." Cikin ƙasa da murya yace "Father ya dawo ne naga kamar motar shi a parking lot, dan Allah ki rufa min asiri kice ke kika aikeni?" harara ta watsa mai tace "Bai dawo ba Bunayya, ne ya zo." Wani ɗan kayataccen rawa ya shiga takawa, cike da yarinta kasancewarsa gwanin iya juyi, matsayinsa na matashin mai jini a jika wanda yake kan ganiyar tashensa din zai gaza sheda ashirin zuwa da huɗu ba, ya tsagaita ya sake kallonta yace, “Mother yanzu haka kina nufin Yaya B na cikin gidan nan?" "Eh.” ta amsa masa a takaice, "Yeeeee!" ya faɗa tare da kwasa da gudu kamar wani dan 5 years ya nufi hanyar staircase, da sauri mother ta dakatar dashi , ta hanyar cewa "A kull! Ka bari da safe baya cikin good mood, kar kaje ka dame shi da surutu." Dawowa yayi yana taɓe fuska, ya nufi hanyar kitchen, har zai shige tace "Suraj ya juyo." "bani wayoyin ka." Ta faɗa tana mika mishi hannu, kamar ya kurma ihu amma ba yadda ya iya ganin yadda ta tsare gida ba damar wargi, dole yana ji yana gani ya ciro su a aljihu ya miƙa mata, ta amsa tace "idan za ka wuce school gobe ka tuna ka amsa" ya amsa mata da "To Mother." Kamar zai yi kuka, bai ji daɗin tunawa da tayi da batun karbar waya ba wlh, yaso kafin ya kwanta barci ko da bai yi komai da wayar ba, ya ji muryar Salmah, ka da  kuwa masifa za ta mai kamar yadda ta saba, amma ba komai gobe zasu haɗu a school ai. Ganin yayi shiru ya tsura mata idanu yasa tace "Da magana ne?" Da sauri ya girgiza mata kai, tace "oya goo." Ta faɗa tana nuna hanyar kitchen, jiki a sanyaye ya juya ya tafi, har ya shige ta daga murya tace "idan ka gama ka karkashe komai ka kulle ƙofa kafin ka kwanta." Daga ciki ya amsa da "OK Mother gud night." Bata tanka shi ba ta wuce nata dakin itama don ta kwanta ta huta...


Anya kuna biye kuwa? Bakwa comment ko labarin bai yi muku bane mu dakata?