03
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
*03*
Daga Daura bayan an gama ɗaura aure Abuja aka sake dawo da Amarya tunda anan ne ƙayattace gidanta yake a cikin jerin gidajen masu kumbar susa da faɗa a aji a ƙasar gabaɗaya. A ranar aka yi buɗar kan Amarya a gidan iyayen ango, tab an yi ɓarin miloyoyi wajen buɗan kan Amarya kamar kuɗi ba matsala ba ne a wajen su, shi kan shi Ango dangin Amarya sun fanshe shi da miloyoyi, Matar Hamma Lamiɗo miliyan biyu ta fanshi kan Ango a madadin ita da Mijinta Yariman Daura, Muhammad Nasiru Muhammad Daura(Lamiɗo).
MC da aka gayyato domin gabatar da program ɗin ta kacame da guɗa tana yi ma Balkisu kirari.
"Takawarki lafiya Uwargida kuma Amarya a gidan Yariman Daura. Muhammad Lamiɗo ke ya zaɓa ke ma shi kika zaɓa, ɗiyar masu sarauta kike kuma Yariman daura ne mijin ki, sannu ƴar sarki matar ɗan sarki, uban ki sarki mijin ki ma zai yi sarki in sha Allahu, kuma za ki haifi Sarki da ikon Allah
Sannu likita bokan turai, uwar Sultan kike sannan ke ce kika haifi Beena. Na gaishe da sarauniya Balkisu, na gaishe da Matar Yariman Daura takwarki lafiya Gimbiya Balkisu Zinariya."
Sai dai kawai aka ga ta saƙa ma MC ɗin kuɗi a hannunta waje ya ɗau tafi Ummu ranar ba abin da ta yi sai faman bin shagulgulan bikin nan, matar nan ta Hamma Lamiɗo hadaɗɗiya ce ranar ma shigar lafaya ta yi, ta saka wani material gangariya daga ganin shi ya ba ma wasu nairori baya.
Tabbas ta cancanta domin zinariya ce.
Duk da Hamma Lamiɗo ba gwanin ta ba ne, ita ma matar tashi wata doguwar mu'amala ba ta taɓa haɗa su ba, amma dai ita a karan kanta tana yin matar saboda yar gayu ce mai kyau ce mai kama da model ce, ga ƴaƴan su farare gwanin ban shawa'a in ka ga rayuwar wasu sai ka yi tunanin wataƙila su suka zaɓa ma kansu, to komai na rayuwa na duniya sun same shi a hannu, suna yadda suka ga dama da shi.
Ita kanta irin mijinta ne ba ta samun zama, a ƙiyasin kirgin Ummu Salma sau biyu Dr Balkisu ta taɓa zuwa gidan su zuwa na musamman da ta kwana fiye da ɗaya.
Akwai zuwan da ta yi bayan auran su da Hamma Lamiɗo, to bayan shi ta yi biyu haihuwan matar Hamma Kabiru da yake wannan Aminin shi ne ta zo, sai wani zazzaɓi da Ammah ta yi mai zafi har ta fara sambatu hankula sun tashi, kowa ya ɗauka Ammah lokaci ya yi ashe zafin ciwo ne, suna Abuja lokacin kafin ta koma Lagos da zama ta zo duba Ammah, a lokacin Sultan na ƙarami to bayan shi
Yanzu daga baya tana biyo shi in ya zo hutun karshen shekara, tunda sai ya fara sauka a Jimeta ya gama kwanakin sa a nan suke wucewa Daura.
Daga ita har mijin nata suna yin wuyar gani, hutun na shi kuma a shekara sau ɗaya ne, in salla ne ma baya daɗewa za su fara sauka nan Jimeta su yi kwana biyu daga nan su wuce Daura saboda wasan hawan salla akwai ma sallolin da aka yi yana can bakin aiki bai ma samu zuwa ba.
Duk da itama tana da halin ɗagawa da ji da kai bai damu Ummu ba, ita dai bata ba ta haushi sannan tana burgeta ,hankalin ta bai kwanta ba sai da aka gama shagulgulan bikin nan sannan ta bari waya ta huta daga hannunta ta samu ta kira Ammah a waya ta gaisheta sama sama ma suka yi mgana tana cikin hayaniya ta ce za ta kirata ba kuma ba ta kira tan ba. Sai ta kudirta cewa in Ammah suka dawo za ta je har gida ta yi mata sannu da zuwa.
****
*NO. 224 NDC QUATERS. KADUNA NAGERIA.*
*9:47AM*
Da sassarfa take sauko wa daga kafar bene lokaci ɗaya hankalinta na kan agogon I.wacth ɗin dake maƙale a tsitsiyan hannun ta na hagu, lokaci take dubawa domin tana da aji ƙarfe goma da rabi na safiya yau ɗin nan
Falon ƙasa ta sauƙo da yake shuru ba ka jin motsin kowa, farar mace ce doguwa mai ɗan kaurin jiki, tana sanye da wata gold ɗin atamfa mai ruwan ganye shi yasa mayafin jikinta ma da takalminta haɗe da jakan dake hannunta masu kalan ruwan ganye ne.
Hannayenta da zobban gold guda biyu da a warwaro suna ƙyalli, haka wuyan ta wani ɗan kunnen gold ne da sarƙan shi mai kyau da yarari.
A ƙiyasin shekarunta ba za ta wuce 52 ba sannan ba za ta gaza ba, amma a kallon farko za ka fahimci mace ce mai ilimi da gayu.
Sake duba lokaci ta yi, kafin ta ɗago kanta tana sake nazarin ƙayattacen falon mai kama da aljanar duniya. Falon babba ne domin saitin kujeru ne sama da guda huɗu saboda tsabar girman falon.
Zama ta yi kan ɗaya daga cikin kujerun falon lokaci ɗaya tana sauke jakar hannunta daga gefenta.
"Baraka."
"Baraka."
Ta shiga kiran ta wacce aka kira da Baraka, da fito da sauri daga wani koridon dake yamma, matashiya ce domin ba za ta wuce 20's ba har gabanta ta ƙariso ta durkusa lokaci ɗaya tana faɗin.
"Barka da fitowa Mami."
"Kin tashi lafiya Baraka?
Ta amsa mata, muryanta da ɗan asset na fillanci, lokaci ɗaya tana ciro wayarta daga cikin jakar dake gefenta.
"Lafiya lau Mami."
Jinjina kai ta yi kafin ta ce" Kin gama gyara ko'ina ko?
"Na gama Mami, saura na kitchen ne kawai."
"Da kyau Baraka shi ya sa nake son ki saboda zafin naman ki."
Dariya ta yi kanta na ƙasa itama Mamin murmusawa ta yi kafin ta ce" Yau na ga mutumin naki bai yi rigiman tafiya makaranta ba"
"Bai yi ba Mami, na lallashe shi da cewa zan goya sa in ya dawo."
Mami ta yi dariya har haƙoranta suka bayyana farare, da haƙoran makka a bakinta.
"Baraka ina ta ya Faruk kewa ranar da Iya tace a maida ke gida."
Baraka sai ta dukar da kai ba ta yi mgana ba Mami na ta dariya kunya take ji domin an saka ranar auranta karshen shekara nan za su ma yar da ita gida, daga can garin megidanta suka ɗauko ta Ɗan marke, ta fi shekaru biyar tare tasu tun ba ta kai haka girma ba.
Miƙewa ta yi, kafin ta ɗau jakarta Baraka ta yi saurin riga ta ɗauka lokaci ɗaya tana faɗin" Mami ba ki karya ba za ki fita?
"Sai na dawo Baraka."
Sai ta jinjina mata kai, suna tafe har habaran gidan makeke mai cike da motoci ga su nan kala kala sun kai guda biyar, duka na kamfanin Toyota ita ma wata fara ta nufa camry da ita za ta fita yau, jakarta ta karɓa lokaci ɗaya tana cewa.
"Baraka ki kula da gidan sai na dawo."
Sai ta jinjina kai kafin ta ce" To Mami Allah ya dawo dake lafiya."
Lokaci ɗaya tana mai ɗan ramƙwafawa alamun ladabi, tana ƙoƙarin buɗe mota wani matashi ya rugo da gudu ya zo ya buɗe mata.
"Barka da Safiya Mami."
Sai da ta shiga cikin motar ta zauna sannan ta amsa masa.
"Ka tashi lafiya Hamisu?
Ya amsa cikin ladabi kafin ya ce" Lafiya lau Mami.. za a fita ne? Allah ya tsare ki ya sa ki dawo lafiya."
Mami na mirmishi ta amsa kafin ta ce" Ba wata matsala ko Hamisu?
Yana sosa kai ya ce"Hajiya Baraka ba ta ba ni abin karyawa ba goma ta kusa ta san ni mutumin kauye ne da wuri na ke karyawa amma Baraka sai sha biyu na rana take kawo mini abin karyawa fisabillahi fa Mami."
Kafin ya dire maganarsa ya fara sha harara wajen Baraka, Mami tana ta dariya diraman Hamisu da Baraka. Kuma duka daga gari ɗaya suke Abban islam ne ya ɗauko Hamisu yana kai yara makaranta sai ɗan aike-aike da kula da fulawoyin gida.
"In ka matsu sai ka shiga ka dafa."
Baraka ta faɗa sannan ta yi tsaki ta kama hanyar komawa cikin gida.
"Mami kina dai jin ta dai ko?
Mami na dariya haƙoranta a waje kafin ta ce" Na ji ta Hamisu ƙyale ta."
Jakarta dake kan kujeran mai zaman banza ta buɗe ta ɗauko masa 5k yan dubu dubu ta miƙa masa ya rankwafa ya karɓa.
"Ka siya wani abu ka ci, ka rabu da ita lokacin da ta kawo maka sai ka ƙara"
Washe baki ya yi kafin ya ce" Na gode Mami, Allah ya tsare gaban ki da bayan ki. Allah ya raya miki yaran ki cikin aminci, yadda kika ɗauke mu da mutumci kina saka mana da dukkan alheri ke ma Allah ya saka miki da alheri."
Mami ta amsa da Amin kafin ta ce" To sai na dawo Hamisu."
"A dawo lafiya Mami Allah ya tsare."
Ya rufe mata ƙofar motar ya ruga da gudu wajen Sunusi maigadi, itama sai ta kunna motar ta yi riverse ta dumfari get tana zuwa da man Sunusu ya buɗe mata sai ta tsaya ta ɗan sauke gilashi bangarenta suka gaisa cike da mumtatawa.
"Sunusi ina sane da mganar mu. Jibi Abban islam zai dawo za mu yi mgana da shi in sha Allahu."
Ya jinjina kai kafin ya amsa" Allah ya dawo da shi lafiya Hajiya. Na gode sosai da karamcin ki."
Kai ta gyaɗa masa kafin ta ce" Ba komai, sai na dawo"
"Allah ya tsare ki Hajiya."
Ta zuge gilashin sannan ta taka mota ta fice shi kuma ya rufe get ɗin ya koma saman farar kujeran da ya tashi kusa da Hamisu suka cigaba da hiran su, kuma duk na yabon kyawawan hallayan Mami ne na kirki.
Sannu sannu tana ta tafiya har zuwa cikin garin kaduna, daga nan ta ɗauke hanyar jami'ar ta Kaduna, Kaduna state University KASU. In da anan take koyarwa a Department ɗin Biology. Har cikin department ɗin su ta shiga da motar ta, ta yi parking ɗin ta in da aka tanada domin parking ɗin motoci, tana ƙoƙarin fitowa daga motar ne ta ji wayarta dake jikin jaka ta ɗan yi ƙara alamun an tura mata saƙo da kamar ba za ta duba ba, saboda ita saƙonni ma sun isheta a waya ba ta dubawa gwara mutum ya kirata da ya yi mata saƙo.
Jakarta ta jawo ta ɗauko wayar na ta iphone 14 ce, tana dannawa haske ya kawo sai ta ga saƙo ne daga My First Daughter, sai da ta murmusa ta manta yau Jumma'a da man ƙa'ida ne duk ranar irin ta yau Ummu Salma tana tura mata saƙon barka da Jumma'a kuma tana jin daɗi sosai.
"Barka da Jumma'a Mami na. Allah ya tsare ki da tsarewarsa. Allah ya ba ki abin da kike nema duniya da lahira. Ubangiji ya yi ma rayuwarki albarka. Happy Jumma'at mubarak."
Har ta gama karantawa da mirmishi a saman fuskarta, latsa lambar Ummu ta yi, jiya da daddare ta so kiranta sai ta sha'afa gwara ta kira ta yanzu kar ta sake mantawa.
Ringing ɗaya zuwa biyu Ummu-Salma daga can garin Jemeta ta ɗaga kiran.
"Mami na"
Ta faɗa daga can bangaren cikin murna da bayyana har a muryanta.
"Naam Daughter kuna lafiya?
Ummu ta amsa mata, suka gaisa daga can bangaren Ummu ta ce" Mami na ina su Islam?
"Suna makaranta."
"Yaushe za su zo?
"Sai sun samu hutu za mu taho gabaɗaya Daughter."
Daga can bangaren Ummu ta yi tsalle kafin ta ce" Mami na da man na yi kewar ki."
"Nima na yi kewar ɗiya ta."
Habib ta tambaye ta sai ta amsa mata da cewa ya tafi wajen aiki.
"Ki gaishe mini da shi."
"In sha Allahu Mami na."
"Daughter na siya miki kayan measurement ɗin fulawa, har spicess na kayan girki suna nan in zan taho zan taho miki da su in sha Allahu."
"Na gode Mami na. Allah ya saka miki da alheri."
Ta faɗa muryanta cike da murna, Mami ta amsa da Amin kafin ta ce" Take care na shigo cikin makaranta ne
"To Mami Allah ya ba ki sa'a."
Daga nan suka yi sallama.
Tana shirin mai da wayar cikin jaka ne, sai kuma ta fasa saboda wajen messages ɗin ta 99 ta gani alamun tana da saƙonni da yawa nufinta ta shiga ta yi delete all, duk MTN ne sai na bankun nan ta, amma sai me tana shiga sai ta bige da ɗan dubawa, tana ɗan jan ƙasa ta ga wata lamba ta turo mata saƙo, yanayin lambar ne ya sa dole ta shiga saƙon domin special number ce.
"Za a yi auran ɗiyarki Batula. Ko ba ki zo dan ni ba ki zo don Lamiɗo, in shi ma ba za ki zo domin shi ba to ki zo domin gudan jinin da Allah ya haɗa a tsakanina da ke. "
Na farko kenan na biyu kuma cewa aka yi.
"Tun da ba za ki samu zuwa ba Batula ba, ko yaran mu ki bar su su zo don Allah Batula."
Ko bai saka sunan shi ba, ko bai ambaci wata magana da za ta nuna shi ɗin ba ne, to shi ne domin nan duniya mutum ɗaya ne ke kiranta Batula ko Baffa Fatima ya ke kiranta, tuni fara'an dake saman fuskarta ya gushe cikin lokaci ƙalilan fuskarta ta sauya ta yi wani ja saboda bacin rai.
Hannunta na rawa ta goge saƙon gabaɗaya daga wayarta. Tana mamakin yadda aka yi ya same ta? Ita dai ta san ta rufe duka layukan da ya ke kiran ta da su, sai daga baya ta duba sai ta fahimci ya sauya wata lambar ne me ya rage tsakanin su? Ɗan shi ne kuma ba ya tare da ita, yana tare da shi me ya sa ita ba zai ƙyale ta ba? Ta ce ta yafe masa amma ba za ta bari mu'amalan wai Uba da uwa ta haɗa su ba. Tana da miji shima yana da matan shi, ɗan shi kuma ya san in da yake ba to bini-binin na mene ne? Ita fa har abada ba za ta yi wani aminci da su ba, babu sauran wani aminci har abada atsakanin su.
Sai yanzu ne ya san da gudun jinin da ya haɗa su? Sai yanzu? Ai lokaci ya kure musu, kurewan da ba za su iya gyara abin da suka lalata shi sama da shekaru talatin ba. Sai yanzu ne Fargar jaji ya kama su? Ba su da sauran abin da za su iya yi a yanzu, gabɗaya ta rasa natsuwarta in ta fita a haka ma ta je aji ɗalibai za su fahimci yanayin ta ba daɗi shi ya sa ta yi zamanta cikin mota tana faman sauke ajiyar zuciya.
Wai saboda Lamiɗo! Waye wani Lamiɗo! A lokacin da ya ke zanin goyo da jinin haihuwa a jikinshi da ba a samu damar wanke shi ba, mahaifiyar shi ba ta duba Lamiɗon a lokacin ba, ba ta duba shi ba ta saka ya yi ma rayuwarta mummuman taɓon da har ta koma ga Allah ba za ta taɓa mantawa ba. Shi kuma ya aiwatar da Umarnin mahaifiyarsa saboda kare martaban masarautar su me ta aika ta? Wani laifi ta aikata da za a sake ta a lokacin da zufan naguda bai gama safka daga jikinta ba? Saboda ita ba yar masu kuɗi ba ce, saboda ita ubanta ba sarki ba ne, tuna haka kawai in ta yi sai ta ji yanayin ta cikin kuka, yanzu ma hawaye ne suka kece mata, shi ya sa har abada ta tsani duk wani abu da ya shafi Sarauta daga kowani bangare ne, abin da ta sani su ɗin masu son kan su ne marasa adalci abin da suka yi mata ya munin da har abada ba ta fatan kafarta ta sake takawa Daura, tun bayan fitar ta ɗauke da jinin haihuwar dake jikinta ta yi alƙawarin ita da wannan garin har abada.
Duk da ko da har gobe akwai dangin mahaifiyarsu a garin ba ta taɓa jin marmarin sake saka kafarta a cikin sa ba, domin a cikin sa ta samu farinciki amma kuma ya gurɓata da baƙincikin rayuwarta duk farincikin da rayuwarta da ta ke ciki yanzu da ta tuna da rayuwarta ta baya sai ta ji komai na duniya ya yi mata ƙunci. In tana tuna wahalar da ta sha, deperession ne ya nemi kama ta, Allah ya saka ma Baffa da Ammah da alheri sune suka zama silar da ta zama Fatima a yau, in ta kalli rayuwarta yanzu sai ta ji ba za ta iya saka ma Baffa da Ammah ba domin sun yi mata komai anan duniya.
Ammah kuma ita ce ta sakar ma ɗan ta, ita ce ta yi wahala da shi, shi ya sa nan duniya kowa ya shaida Lamiɗo ba shi da wata uwa sama da Ammah itama ta shaida haka, yadda ta wahala da Kabiru haka ta wahala da Lamiɗo, kawai ita mahaifiyarsa ce a haihuwa, Ammah kuma uwa ce a gare shi da ta sadaukar da duka rayuwanta wajen kula da shi.
Hawayenta take sharewa, tana jin sanyi a cikin ranta tunda tun a duniya Fulani ta ga sakamakon ta, domin sai da ta zo ta roƙe ta gafara akan abin da ta yi mata sannan ɗan da ta guda tun yana cikin jinin haihuwa shine Sanyin idaniyar masauratar Dauran da suke taƙama da shi, ko a haka aka tsaya sun ga sakamako mai kyau, su ƴa'ƴan sarakunan da ta aura masa ba su iya ba ta abin da take so ba, dole dai sai ita ita ɗin da ba ƴar kowa ba ita ce ta sama mata abin da take muradi, to a haka aka tsaya ita Fatima ta yi nasara.
Tissue ta zaro daga cikin motarta ta goge fuskarta a fili ta furta" Allah ya jiƙan ka da Rahama Abba. Marigayi tsohon Sarkin Daura Muhammad Shitu Daura."
Tana tuna yadda ya ƙauna ce ta wata ƙila da yana raye da an yi mata adalci. Shi ne ya ce in ta haifi namiji sunan yaro Muhammad Lamiɗo in mace ce kuma Ummu-Kursum shi ya sa lokacin da ta iso Jimeta ta ce ma Baffa ya yi ma jaririn huɗuba da Muhammad Lamiɗo, ko ba ya raye za ta saka masa da ƙaunar da ya nuna mata wajen cika wasiyyarsa.
Ita ce za ta ba da labarin mutuwa mai tonon asiri domin mutuwa ce ta yi sanadiyar tonuwar asirinta, ta yi sillar gurbata rayuwar farincikinta zuwa baƙin ciki, ta wani bangaren kuma hakan ya yi sillar sauya rayuwarta daga wannan Fatimar yar mubi bafullatan ƙauye mara ilimi zuwa wata Fatima ta dabam da ta samu cigaban rayuwa ta ƙo'ina. Tabbas ta wannan bangaren za ta gode musu domin sun ma yar da rayuwarta yadda ba taɓa tunanin komawa ba.
Kimtsa kanta ta yi, gilashinta ta fiddo a cikin jaka ta saka saboda kauda idanuwan mutane a kanta bayan ta duba madubin motar ta ga idanuwanta sun yi jajir, sannan ta ɗau jakarta ta fito daga cikin motar ta yi amfani da key ɗin ta rufe motar. Tana fara takawa zuwa office ɗin ta daliɓan da take ɗauka yan level 1 suna ta gaishe ta ita kuma tana amsawa cikin sakewa daliɓai suna son ta saboda tana da sauƙin kai da taimako har malaman ma sun san Dr Fatima Baba wajen karamci da kyautatama duk wanda take tare da shi.
****
Su Ammah sai da suka yi kwana goma sha ɗaya sannan suka dawo, washegari Ummu-Salma ta je yi mata sannu da dawowa. Ta iske kayan biki niƙi-niƙi ga su nan a ɗakin Ammah har da bag da aka raba mai ƙaton hoton Amarya a ciki ake saka atamfa mai kyau da mayafi har da turaruka, ga kayan su fulawa tun da ta zo Ammah ke ba ta labarin abin da ya faru a wajen bikin nan, Hamma Sadam ma ba a bar shi a baya ba shima yana ɗorawa da na shi, su Ammah fa kaya suka dawo da shi niƙi niƙi ita da Ummin ikki, bayan kala ukun da aka yi musu Fulani ta ba su turame goma da dubu 200k Maimartaba Sarki ya ba su naira dubu 500k tukwaici Gimbiya Shahida ma da turamen zannuwa 20 da kuɗi har shaddodi aka ba da aka wo ma Baffa sun je ɗaurin auran amma tare da Hamma Abdullahi, Hamma Abdulrahaman bai samu zuwa ba, shi kan shi Hamma Sadam shaddoji sun fi kala biyar sabbi gezner masu tsada da takalma haɗe da hulana da ya dawo da su, cikin jin daɗi suke ba da labarin zuwan su Daura da man haka ne in dai Ammah ta je to haka za a rako ta da kayan arziƙi niƙi-niki Ammah kuma ta shiga rabo gidajen yan'uwa da Dangi, har can Mubi saƙon na iske musu. Ta ciccire ma su Umma Balki na su kason, da matan su Baffa Umaru.
Duk da ba ta samu zuwa ba tare da na Umma Salamatu da Umman A'i, Hamma Sadam ne zai je ya kai musu gobe, jibi zai koma makaranta.
Sannan ta ɗibar ma matan su Hamma Abdullahi, ita dai Adda Nauwara an ba ta na ta acan, amma na su Hamma Kabiru da Mustapha Amma ta ajiye musu abin biki, ita kanta Ummu da ta je an ba ta jaka da kayan fulawa sai turare. Sannan ta karɓan ma Baɗɗo itama.
"Amma na Bestie fa?
Amma ta ce za ta ijiye mata in ta zo da kanta sai ta ba ta.
Ummu tura baki ta yi kafin ta ce" Amma ni zan ci ne? Zan ajiye mata ne tana can makaranta sun kusa farawa jarabawa."
Amma ta ce Allah ya sa a yi cikin sa'a amma ba za ta ba yar ba.
"To na Noori na Ammah."
Ummu ta faɗa, Amma ta yi mata wani kallo kafin ta ce" Waye kuma haka?
Ummu na dariya ta ce" Kai Amma Habib ɗin ne ba ki san sunan shi Noori ba?
Ammah ta aika mata da daƙuwa kafin ta ce" ƙaniyar ki Ummu Salma."
Sai ta fara dariya ƙarshen ta dai sai da Amma ta ba da nashi shima tana cewa" Ya kira ni ina can ya gaishe ni, ya cancanci ya samu tsaraban Daura."
Saboda tana so ta tsokani Ammah ya sa ta sake cewa " Amma to ina na Mami na? Na ga ba ki cire mata ba ne"
Wannan karon sai da aka wurgeta da mafici sannan aka ce" Mamiyo, in tana son tsaraban me ya hana ta je da kanta? Uwar nan taki zuciyarta ba ta da kyau ko a waya ba ta kira ni ba, nima ko na ce ba zan kira ta ba ina nan za ta zo ta same ni."
Ummu ta gyara zama tana faɗin" Ammah to suma sauran da kika ba su ai ba su je ba."
Ta gama faɗa tana tura baki.
Amma ta miƙe ta fice tana faɗin" Ba zan ba yar ba, na ƙarfi ne ki ƙwatan mata mai uwa."
Ta fita ta bar Ummu na dariya da man ta san ba za ta ajiye mata ba amma ta yi son kai za ta aika da shi Mubi, ita Mami ko oho.
Ummu har dare tana gidan, labari kam sai da ta gaji da shi, Hamma Lamiɗo dai bai zo ba wai yana cikin aiki, matar shi ce dai ta samu zuwa da yaran shi itama Ammah ta ce ana gama biki daga Abuja ta hau jirgi ta koma Lagos saboda aikinta.
Da man Baffa baya nan ko da Ammah ta dawo ya je kwatano
Habib ya zo ya ɗauki Ummu da yamma, daga nan suka ƙarisa gidan iyayen shi dake anguwar Doubeli, Baban Habib ya tsufa yana zaune ma ba ya iya tafiya mahaifiyar Habib ce ta rasu, amma akwai sauran mata uku a cikin gida. Suna da yawa wasu duk sun yi aure mata da mazan wasu kuma yanzu suke tasowa. Da ya ke lokacin da aka yi ma Ummu buɗar kai(Fansa) akwai sunan da suka sanya mata bisa al'ada Tafisu da shi duka ahalin Habib suke kiranta da shi, shi ya sa in dai ta shiga cikin su ba sunan ta Ummu Salma ba, sunan ta Tafisu nan suka yi dare sai wajen tara na dare suka koma gida.
Duk kuma gajiyar nan da Ummu Salma ta kwaso bai saka Habib ya ɗaga mata ƙafa ba, har mamakin shi take yi ba ya gajiya, in har Habib bai kusanceta ba sai dai in tana jinin haila ne, shima ɗin saboda ba shi da yadda zai yi ne ammaa kafin ta samu tsarki duka gabban jikinta sai sun koma suna raɗaɗi saboda yadda suke shan yamutsa ba ya barin ta sukuni ko kaɗan shi ya sa har yau ta saka kumarin nan na masu aure ga shi sun kwarari wattani takwas da yin aure, ko lokacin da ta samu ciki da ga samanta ne kawai ta yi kiɓa amma ban da jikinta, irin yadda Habib ke matsa mata lamba ba lalle ta yi kumari ba, abu kamar cin tuwo ba ya gajiya.
Kuma har lokacin tana jin wannan sauye-sauyen a jikinta amma tun da ta yi gwaji ta ga ba haka ba ne sai ba ta saka ma kanta tunanin komai ba.
Ta fi danganta hakan da rashin hutun da Habib ba ya bari gangar jikinta ya samu shi ne dalili.
Abin da ba ta sani ba shi ne tana da shigar ciki. Dalilin wannan cikin rayuwarta za ta juye daga farinciki zuwa aƙasin hakan.
****
Jalingo street.
Tun jiya da daddare take fama da tashin zuciya amma ba ta damu ba, ta fi danganta hakan da soyayyen ƙwan da ta ci da safiyar ranar ne, can kuma da rana da ta sha zoɓo sai tashin zuciyar ya kwanta har dare da Habib ya dawo ba ta sake ji ba, da safe kuma da tashi sai kasala duk ya rufeta miyau na taruwa a bakinta sannan da zafin jiki ta kwana, Habib bai sani ba kuma bai hana da asuban ya sake nemanta ba, wani abu ke ba ta mamaki a group ɗin makarantan su na sakandiri mai suna Ahmadu ribaɗu Collage wanda suka buɗe na mata zalla akwai matan aure kuma tana gani suna hira, wata Aisha Iro ta taɓa tambayan cewa mijinta sai su yi kwana biyu bai neme ta ba, hakan ba matsala ba ce, nan fa aka yi ma tambayar caa, kowa na faɗin albarkacin bakinsa.
Mafi rinjaye sun ce ba wani abu ba ne, domin rayuwar aure ba domin saduwa ba ne, zamantakewar aure ibada ne. Wasu ma suna ta cewa sai su yi sati kuma ana zaune lafiya, sai dai a yi romance kawai a kwanta tun lokacin da ta ga maganganun su abin ya tsaya mata arai, ba ta taɓa tattauna wannan matsalan da kowa ba sai Baɗɗo ita kuma ba aure ta yi ba sai ta nuna mata wataƙila Habib na cikin maza mabuƙata, ko Bestie ba su taɓa maganar da ita ba amma lamarin na damun ta, ba ta nemi komai ta rasa ba, ba abin da Habib ba ya yi mata matsalanta da shi kawai wannan bangaren ne, kamar wata machine haka ya ɗauke ta kwata-kwata ba ya barin ta samu hutu, tana haɗa musu abin karyawa tana ta tunane-tunane a cikin ranta, ta taɓa yi masa mgana tun farkon auren su ya ce ta shirya mijinta mai yawan buƙata ne amma ita a ganin ta buƙatar ta shi ta yi yawa ne.
Indomie da ƙwai ta dafa ma Habib ba ta jin daɗin jikinta shi yasa ba ta yi dogon breakfast ɗin da zai ba ta wahala ba, sai ruwan tea da ta dafa masa sai da ta jera komai saman dinning sannan ta koma ciki ta tashe shi, wajen taimaka masa ya yi wanka ma sai da ya maimaita a tiolet, in Ummu ba ta furta ta gaji a baki ba gangar jikinta ya nuna gajiya da jarabar Habib, shi ya fara tsarkake jikinsa ya fito ya bar ta a cikin tiolet tana jin kirjinta da kanta sun yi mata nauyi.
Ko da ta fito har ya shirya kan shi cikin suit, ko yadda ya ganta ta yi wani suku-suku ba fara'a bai damu da ya tambayi dalili ba, faɗa mata yake yi ta yi sauri kar ya makara.
Wata riga mai gajeren hannu doguwa ta saka sai hula ta rufe gashin kanta dake jiƙe sai ta sallame shi ko za ta dawo ta busar da shi.
Tun da suka zauna saman Dinning karnin Dafaffen ƙwan nan ya dame ta, ba ta ma saka ma kanta shi ba, indomie ɗin kawai ta zuba wacce ta dafa tare da su carrot da greenbeans, tana kai cokali na ɗaya biyu, na ukun ne ya gagare ta haɗiyewa tuni ta ji kayan cikinta sun fara yamutsawa da gudu ta tashi ta faɗa tiolet kafin Habib ya samu damar mgana ya ji Ummu na ta sheƙa amai kamar za ta amayar da kayan cikinta.
Da sauri ya tashi daga zaman karyan da yake yi cikin mamaki ya bita tiolet ɗin amma daga baƙin kofa ya tsaya.
"Baby me ke faruwa? Wani abu kika ci?
Ya faɗa cikin bayyana damuwa a muryansa. Kuma damuwar har ya bayyana a saman fuskar shi.
Ba ta ma san yana yi ba, tana duƙe tana sheka amai sai da ta amayar da duk abin da ke cikinta sannan ta samu sukuni, ruwa ta buɗe a famfon sink ɗin ta wanke bakinta sannan ta kora Aman ta ɗago tana haki ta nufo hanyar fitowa jiri ya ɗebe ta za ta faɗi Habib ya yi saurin riƙo ta.
"Baby me ke damun ki ne?
Are you sick?
Ummu da saurin kuka tuni ta lafe a jikin shi ta fashe masa da kuka.
"Ni ma ban sani ba Noori amma ina jin jikina duk ba daɗi."
Ta faɗa cikin shagwaɓa, tarairayota ya yi suka dawo falo ya zaunar da ita akan kujera ya zauna a gefenta yana mai ƙura mata ido.
Gabansa ya faɗi kar dai a ce Ummu Salma wani cikin ta samu? Da ko ya shiga uku.
Da sauri ya tallabo fuskarta da duka tafukan hannayensa kafin ya ce" Baby yaushe rabon ki da ganin al'adan ki?
"Tun bayan ɓarin da na yi sau ɗaya na yi Noori."
Ta faɗa tana wani lumshe idanuwa har ga Allah jikinta ba ya yi mata daɗi so take yi ta kwanta.
"Ummu-Salma ko ciki ne da ke?
Ya faɗa cikin wata murya mai cike da fargaba.
"Ban sani ba, nima kwanaki na yi tunanin haka sai da na siyo PT na yi gwaji sai na ga babu komai."
Ta faɗa cikin sanyin murya tana mai ɗora kanta a saman kafaɗanta.
Duk da haka bai gamsu ba, sake ɗagota ya yi yana sake ƙare mata kallo.
"Noori ka bar ni na kwanta jiri nake gani."
Ta faɗa cikin shagwaɓa shi ba ma ta ita yake yi ba kirjinta yake kallo sai a lokacin ya lura kirjinta sun tasa bai taɓa lura da hakan ba.
"Wani yanayi kika ce kina ji a jikin ki?
Ya tambaya agaggauce.
Ita ko Ummu Salma ta ɗauka duk murna ce ya sa cikin sanyin murya ta amsa shin
"Noori ina ji fa ba ciki ba ne, na faɗa maka na gwada ba komai."
"Ki amsa mini tambaya ta."
Ya katse ta da sauri, numfashi ta fesar kafin ta shiga faɗa masa yanayin da take ciki ai tun kafin ta ƙarisa ya miƙe da sauri ya koma cikin bedroom ɗin su, da mamaki ta bi shi da kallo ganin ya fito da Hijabin ta a hannun shi da key ɗin motarsa lokaci ɗaya yana faɗin.
"Tashi mu je asibiti a yi gwaji."
Cikin mamaki take bin sa da kallo ba ta samu damar mgana ba har ya zura mata hijabi ya koma ciki ya ɗauko mata takalmi jikinsa sai rawa yake yi kamar mazari.
Tausayin shi ya kamata lokacin da ya duka yana zura mata takalmi kansa ta shafa lokaci ɗaya tana faɗin" Ka kwantar da hankalin ka Noori."
Miƙewa ya yi lokaci ɗaya yana kama hannunta ta miƙe tsaye ba tare da ya amsa mganar ta ba.
"Ka ji ?
Ta sake faɗa bayan ta riƙo hannunsa guda ɗaya kallonta ya yi duk ya firgice a cikin ƙanƙanin lokaci.
"Hankalina ba zai kwanta ba sai an yi gwajin nan."
Ya faɗa da sauri lokaci ɗaya ya ja jakarsa dake gefenta ya rataya, riƙe da key ɗin mota a ɗayan hannun na shi, ɗayan kuma ya jawo hannunta. Ita ce ma ta ce ya tsaya ta kashe kayan wuta sannan ta ɗauko key ɗin gidan suka fita tare ta rufe suka rankaya motarsa ƙirar Benz har suka ɗauki hanya bai sake yi mata mgana ba hankalinsa duk ya tashi sai faman gudu yake yi a titi
Ganin haka ya sa Ummu ta kama hannun shi dake saman sintari sai ya juyo yana mai kallon ta.
"Noori."
Da sauri ya katse ta da faɗin.
"Boshon clinic za mu je ko?
Sai ta gyaɗa masa kai kafin ta ce" E. Ai can na ke da fayel."
Daga nan bai sake magana ba hankalinsa na wajen tuƙi amma daga ganin shi ba ya cikin natsuwarsa.
"Noori ka kwantar da hankalin ka, in ba cikin ba ne ma in sha Allahu na kusa samu."
Wani irin kallo ya yi mata kallon da ba ta taɓa ganin ya yi mata irin shi ba za ta sake mgana ya ɗaga murya yana faɗin.
"Ki bar ni, ba ki ga ina driving ba ne."
Sai da ta kalle shi cikin mamaki shi kuma ba ya ma cikin natsuwarsa ballanta ya ji ba daɗi kan ɗaga mata muryan da ya yi.
Idanuwanta suka cika da kwalla, tausayin Habib ya kamata yanzu in suka je asibitin suka ce ba ciki ba ne fa? Wani hali zai shiga sai ta koma addu'an Allah ya sa ciki gare ta, ko domin hankalin Habib ya kwanta daga gani ya ƙwallafa rai akan samun cikin ta.
Abin da ba ta sani ba, tunanin da ke zuciyar Habib kishiyar tunanin da ke zuciyarta ne.
****
BOSHON CLINIC.
Suna isa asibitin sai da suka sake siyan kati saboda sauri sun manta da shi a gida. Bayan Ummu ta ga likita ta yi mishi bayanin duk abubuwan da ta ke ji a jikinta nan take ya saka aka ɗibi jininta zuwa lap, ya ce su ɗan jira sakamakon ya fita.
Da yake asbitin na kuɗi ne ba wani ɓata lokaci, suna waiting area suna jira Habib ya kasa zaune ya kasa tsaye, tana shirin ta ce masa ko zai bar ta ne ya tafi wajen aiki in ta karɓi result ɗin sai ta nemi Napep ɗin da zai kaita gida kafin ma ta yi mgana ta ji yana waya yana cewa ba zai shigo office da wuri ba shi ya sa sai ta yi shuru da bakinta.
Ita dai tana zaune saboda ba za ta iya tsayuwa ba, Habib kuma ko ya zauna sai ya tashi ya kasa zama a waje ɗaya tuni farar fuskan shi ta bayyana halin damuwar da yake ciki. Ummu na zaune tana bin shi da kallo tausayin shi take ji ta cikin hijabin ta, tana ta shafa cikinta a cikin zuciyarta take faɗin.
"Allah ya tabbatar da cikin nan."
Da ace Ummu-Salma ta san gaibu, da ace ta san fargan jajin da ke jiranta da ba ta yi ma kanta wannan addu'ar ba, da ta yi addu'an in ma cikin ne Allah ya sa ya bi rariya.
Zaman jiran mintina arba'in suka karɓi sakamakon gwajin. Bakin Ummu ya ƙi rufuwa tun bayan da likita ya ce tana da ciki na wata ɗaya da kwanaki, an rubuta mata magungunar karin jini da cin abinci, sai vitamin e, amma murnanta sai ya koma ciki na ganin fuskar Habib ta yi baƙiƙirin kamar an faɗa masa saƙon mutuwa, ita da ta yi tunanin yana jin tabbacin tana da ciki sai ya ɗaga ta sama ya yi juyi da ita, amma sai ta ga saɓanin tunanin ta, amma sai ta ƙarfafi kanta da cewa haka ya yi a cikin ta na farko lokacin da ya ji labari bai nuna murnansa ba amma lokacin da ya tabbatar da ta yi ɓarin shi ya fi kowa damuwa, ya yi jinyar ta har sai da ta warke da jikinsa da aljihunsa tunda ta kwanta asibiti wajen kwana uku aka ƙara mata jini, tun a lokacin likitan ya ce ta rasa jini da yawa. A lokacin ma jinin Hamma Kabiru aka saka mata tunda sun gwada na su Hamma Abdullahi bai yi mata ba, ita jininta O Negative. Na sauran kuma duk AB Negative ne.
Suna cikin mota a hanyar komawar su gida, kamar Habib zai ta shi sama. Ummu ta kasa yi masa mganar siyan mgani ganin fuskar shi tumu tumu ba annuri daga gani ba ya cikin natsuwarsa. A ƙofar get ɗin su ya sauke ta bai shiga ba tana kuma sauka bai ce mata komai ba ya fizgi mota a guje ya wuce ba domin ta yi saurin matsawa ba da ya take mata ƙafa.
Har ya ɓace ma ganinta bakin ta bai rufu ba saboda mamaki.
"Me ya samu Noori kuma?
Ta faɗa a fili saboda tunda suka yi aure bata taɓaa ganin shi cikin firgici da zafi haka ba.
Jiki a sanyaye ta shiga compound ɗin su har ta buɗe ɗakin ta shiga jikinta bai dawo daidai ba, mamakin yanayin yadda Habib ya yi mata yafi ba ta mamaki ta ɗauka cikin tattali da murna zai dawo da ita gida amma sai ta ga akasin abin da ta yi tunani, sai dai ta yi masa uziri da cewa watakila wani abu ne ke damun shi.
Takardan cikin ta ɗauko duk da ba gane yaren na likitoci take yi ba amma kallo kawai na saka ta farinciki, tana shafa cikinta tana jin murna da farinciki nan da watanni takwas za ta zama uwa.
****
Habib tun da ya fizgi motar nan a guje bai ci burki a ko'ina ba sai da ya isa haraban bankin su, a parking space ya faka motar shi amma bai fito ba kansa ya dafe da hannu biyu yana jujjuyawa.
Kafin lokaci ɗaya ya zaro wayarsa cikin aljihun wandon sa ya lalubo wata lamba da ya yi ma saving da M.S.
wajen saƙo ya shiga ya fara rubuta mai lambar saƙo.
"An sake samun matsala Ummu-Salma ma da ciki a karo na biyu."
Ya tura da mintina huɗu yana zaman jira riƙe da waya a hannun shi sannan mai lambar ya dawo masa da amsa.
"Again kuma? Habib wasa da hankalina kake yi? Da man ai ka san za ta iya samun ciki tun da mahaifarta lafiya lau. Sai da na ce ka yi mata planning ko a ɓoye ne amma ka ƙi amincewa. To na rantse da Allah ba zan amince ba, in farko ya zama kuskure wannan ganganci ne."
Jikinsa na rawa ya sake rubutawa ya tura.
"Ki yi haƙuri ki bar wannan mganar yanzu dai mene ne mafita?
Yana turawa da mintina biyu aka dawo masa da amsa.
"Ka fi ni sanin mafita. Ni dai ina so ka sani bayan ni babu wata macen da ta isa ta haihu da kai Habib. Ni ce uwar ƴa'yan ka nan duniya. Ka tuna da hakan"
Sai da ya share zufa duk da A.C ɗin dake cikin motar, daga ganin shi yana cikin tashin hankali.
Yana shirin sake rubuta wani sakon ne wani ya sake shigowa.
"Ka tuna da alƙawarin mu shekara ɗaya ka ce na baka za ka cire Ummu Salma daga rayuwarka na har abada. Yanzu kuna da wattani takwas da aure. Wattani huɗu suka rage maka Habib."
Sai ya dakata yana mai kallon saƙon zuciyarsa na bugawa da gudu fat! fat.
Ajiyar zuciya ya sauke a jere kafin ya ba da amsa.
"Ina sane da komai. Zan kuma ɗau matakin da ya dace."
Yana gama turawa, ya rufe wayar ya mai da ta cikin aljihun wandon shi, sai da ya ɗan natsa sannan ya ɗauki brief case ɗin sa ya fito daga motar bayan ya kulleta cikin Sassarfa ya nufi katafaren ginin ma'aikatan su na First bank.
*Janafty*