04
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
*04*
*9:43pm*
Har zuwa lokacin Habib bai dawo ba, Ummu ta kira shi sau uku bai ɗaga wayarta ba daga karshe ma sai ta ji ta daina samun shi kwata-kwata.
Zaune take a falo saman ɗaya daga cikin kujerun da suka yi ma falon ƙwanya, tun ɗazu ta gama girki ta yi wanka tana jiran dawowar Habib amma har zuwa wannan lokacin bai shigo ba, kuma bai saba yin dare a waje ba sai da dalili mai karfi.
Tunaninta da hasashenta bai taɓa kawo mata matsalan daga ita ba ne, tagumi ta yi ta ƙura ma talabijin ido a tashar tauraruwa an saka wakar Salin smart na Labarina. Amma hankalinta da nazarin ta ba ya wajen, idanuwanta na juyawa akan allon talabijin ɗin amma tunanin ta da dukkan zuciyarta yana kan Habib.
"Me aka yi masa?
Ta tambayi kanta sau shurun masaki a cikin zuciyarta ko daga ɗazu bayan dawowarsu daga asibiti ta yi ma Habib wani laifi ne? Ya iya hangen ta da tunanin ba ta hango wani laifin da ta yi masa ba, fuskar sa da ayyukansa sun sauya ne daga lokacin da ya samu tabbacin tana da shigar ciki, daga lokacin Habib ya sauya sauyawar da ta kasa gano dalilin shi, kuma zuciyarta ta aminta da shi, shi ya sa ba ta yarda ta kintsa mata wani mugun tunani a game da shi. Ƙarfafa kanta take yi da cewa watakila wani ne ya ɓata masa rai, amma Habib sai ya fi kowa murna da samun cikinta anan duniya.
Tun da ya sauketa a bakin get ta shigo gida take nazarin abin da ya faru amma ta kasa gano bakin zaren. Ko da daddaren nan sai da ta yi Amai bayan ta yini kwanciya saboda kasalan da ta rufe ta amma ba ta biye ma yanayin jikinta ba yamma na yi ta miƙe ta yi ma Habib girki, soyayyan taliya da Nama mai kayan lambu da ya ke ana gobe su Amma za su dawo ya ɗauke ta sun je kasuwa sun yo cefane mai yawa tana da komai na buƙata kayan miya ta ñika shi ta tafasa shi yana cikin Frezer ɗiɓa kawai take yi in ta tashi amfani da shi.
Wayarta ta sake jawowa yanzu kam har goma ta wuce amma babu alamun Habib, tunanin ta ya sake karkata kan ko dai yana fushi da ita ne ya ɗauka ta san tana da ciki ba ta faɗa masa ba? Tuna haka ya sa ta yi mirmishi ita kaɗai ta san ma saboda haka ne ya ke fushi yaƙi dawowa gida da wuri, in ya dawo za ta bashi haƙuri in dai Habib ne ba ya iya dogon fushi a kanta saboda yadda yake tsananin sonta da gudun duk wani abu da zai ɓata mata rai.
Gajiya ta yi ta zaman shuru sai ta yi tunanin bari ta kira Bestie sai dai wayar na ta ringing ba ta ɗaga ba, sai ta ma yar da akalan kiran ga Baɗɗo ita dai ta ɗauka sun yi mgana ga shi tana so ta sanar da ita tana da ciki amma kamar an matse bakinta ta kasa faɗa mata, ba su daɗe suna waya ba saboda ta ce mata tana karatu sun fara jarabawa a satin nan da ya shiga. Ta tambayi Habib sai Ummu ta yi mata ƙaryan ya biya ta gidan su bai riga ya ƙariso ba.
"Allah ya ba ki sa'a da nasara SisNa."
Ummu ta faɗa cikin mirmishi lokaci ɗaya tana shafa cikinta. Domin in ta tuna nan da wattani takwas ita ɗin uwa ce kuma mai uba irin Habib sai ta ji kamar ba macen da ta kai ta farinciki anan duniya.
Daga can bangaren Baɗɗo ta amsa ma ta da Amin, sannan suka yi sallama bayan Ummu ta ce a gaishe mata da Ummin ikki.
Bayan sun gama wayar Data ta buɗe ta shiga tiktok tana kallon girke-girke akan account ɗin Maryama Kitchen. Duk yadda ta ke son abin da ya shafi girki, in tana kallo ma wani nishaɗi take ji amma yau kwata-kwata ba wannan nishaɗin sai ta ji ma komai ya fita daga kanta kawai sai ta kashe datan, saboda kar ta zauna shuru ya sa ta fara duba contact ɗin ta. Lambobin da ba su da amfani take bi tana faman gogewa domin wasu lambobin ma sai su shekara ba su yi waya ba. Wasu ma duk sun daina amfani da layukan.
Lokacin da ta iso jerin sunayen Yayyenta da ko wanne ta yi masa saving da Hamma sannan da sunan mutum a gaba. Tsayawa ta yi tana kallo Hamma Mustapha ne suka ɗan jima ba su yi mgana ba. Kuma yana da ƙoƙarin kiranta lokaci bayan lokaci, ba za ta iya tuna last da suka yi waya da shi ba. Ita kuma ta sha'afa ganin bai kira ta ba, kuma ita ba ta kira shi ta gaishe shi. An ce ka gaida mai gaishe ka duk cikin yayyenta ta fi son Hamma Mustapha yana da sauƙin kai da sanyin hali ga haƙuri da kawaici hallayan Baffa kaɗan ne bai deɓo ba.
Yana da son ƴan'uwan shi sosai, saɓanin irin su Hamma Kabiru da bashi da kula kwata-kwata, duk a cikin su Hamma Mustpaha ne da Hamma Jibo suke ji da ita, to sai gwara ma Hamma Abdulrrahaman, shi Hamma Abdullahi in ya gan ka dai zai yi murnan ganin ka amma don bai gan ka baa zai damu da neman ka ba. Kar su Hamma Kabiru su ji labari, shi a motor ɗin shi cewa yake yi in ka ji shuru lafiya ne. Baya neman mutane in kuma ya gan ka ba zai yi murna ba in ma bai gan ka ba zai damu ba kuma ba zai tambaya ba. Shi ya sa Ummu ta sha faɗin cewa suna da kamanceceniyar halayya da Hamma Lamiɗo, wataƙila saboda tare suka yi wasan ƙasa suka kuma girma tare shi ya sa wasu hallayan na su marasa kyau suke kamanceceniya da juna.
Hamma Mustapha ta latsa ma kira, ringing ɗaya ana biyu ya danna mata busy, ta sani da man ba ya ɗaga kiranta. Shi zai kashe sannan ya kira ta. Cikin minti ɗaya sai ga shi ya biyo bayan kiran da sauri ta ɗauka cikin zumuɗi.
"Hamma ka manta da ni "
Ta faɗa cikin yar shagwaɓa kamar za ta yi masa kuka.
Daga can bangaren ya yi dariya har tana fidda sauti.
"Wane Hamma ya manta da Autan Ammah. Kina raina ayyuka ne suka yi mini waya a kwanaki nan. Kina lafiya?
Ya faɗa daga ƙarshe yana sirka mganar shi da yaren fillanci.
Ta amsa mishi itama cikin harshen fillancin, sun gaisa cikin fara'a da tambayan iyalan shi, da ya ke shi Gombe yake aiki can ya ke zaune da iyalansa.
"Ina Adda Aisha? Ina su Mahma da Baffan mu?
Duk ya ce sun yi barci saboda makaranta gobe Adda Aisha yanzu ta bar ɗakin sa.
"Ka gaishe mini da ita sosai."
"Zan faɗa mata Autan Ammah. Ya wajen megidan na ki?
Tana shafa cikinta cikin mirmishi ta ce" Duk muna nan lafiya Hamma. Yaushe za ka zo?
Sai da ya yi tunani kafin ya ce.
"Kin san ga aiki sannan yara suna makaranta itama Aisha tana makaranta ko?
"E na sani Hamma."
"To sai mun samu hutu za mu zo mu yi ko sati ɗaya ne in sha Allahu."
Cikin murna ta ce" Allah ya kawo ku lafiya Hamma."
Ya amsa da Amin.
"Ba dai wata matsala ko?
Ya tambaya sai ta amsa mishi da babu wata matsala ya ɗauka za ta yi masa sallama ne tun da dare ya yi sai ya ga ta fara zaro wata hiran.
"Auta dare ya yi, kar ki bar megidan na ki shi kaɗai."
Sai ta kasa mgana, jiki a sanyaye suka yi sallama in ta ce Habib bai dawo ba zai saka ayar tambaya, ko ba ma haka bai kamata ta faɗa mishi wani abu ba, yau dai zumumci take jin yi wayar Hamma Jibo ta kira shi, shi dai ba ta same shi ba Adda Nauwara ta ɗauka ta ce ya shiga wanka.
"Ummu yanzu da daren nan? Ko kewar mu kike ji ne?
Nauwara ta faɗa tana dariya, sai Ummu ta rufe fuska kamar tana ganinta itama tana dariyan, yara ta tambaya itama ta ce duk sun kwanta dare ya yi, suna ta hira da Nauwara har Hamma Jibon ya fito ya karɓa shima suna gaisawa sai da ya ce.
"Autan Baffa ko akwai damuwa ne?
"Ba komai Hamma kawai na kira ka ne na gaishe ka."
"To na gode. Ki kwanta kin ga dare ya yi, da safe za mu yi waya."
Da haka shima ya sallame ta, sai bayan sun gama wayar ne ta ga Hamma Mustapha ya tura mata 10k, duk da ya san ba ta buƙatar komai amma shi mai kyauta ne da alheri shi kafin ta yi kukan wani abu ya ba ta saƙon godiya ta tura masa da addu'an Allah ya sa ya gama da duniya lafiya.
lambar Hamma Abdulrahim ta gani shi da ya ke ba ya ƙasar sai dai in shi ya kira ka ko da yaushe wayarsa ba ta shiga. Amma suna mgana a chart sosai har Vadeo call suna yi wani lokaci in karatu ya yi musu sauƙi tana kewar shi ko bikinta bai samu zuwa ba ya fi shekara rabon shi da zuwa gida amman ya ce ya kusa kamallawa gabaɗaya shi ya sa zai jima a can kafin ya dawo gida.
Da har ta wuce lambar Hamma Kabiru, sai ta dawo bari dai ta kira shi, ko ba komai ɗan'uwanta ne kuma ba za ta biye ma halin shi ba, in ta duba ma ai akwai jininsa roba biyu a cikin jikinta. Sai ta latsa masa kira har ta katse bai ɗauka ba taɓe baki ta yi a cikin ranta ta ce ka huta.
Agogon wayarta ta sake kallo sha ɗaya har da mintina ta gota. Tagumi ta sake yi cikin bugawar zuciya sake kiran lambar Habib ta yi amma ba ta shiga ba.
Niyyarta ta kira ko ƙaninsa Maharazu acan gida ta ji ko yana gida ne tana cikin neman lambar ne kiran Hamma Kabiru ya shigo mata sai ta ɗauka.
A ginshiƙe ya yi mata sallama da muryan nan ta shi a cunkushe kamar mara lafiya ta amsa ita ta fara gaishe shi ya amsa da lafiya jin ya yi shuru itama sai ta yi shuru sai ta rasa ma abin da za ta ce masa, ba wani shaƙuwa sosai a tsakanin ta da shi ba kamar sauran yayyen nata.
"Mene ne haka, na zo na ga kiran ki ba na kusa. Na zo na gani na kira kuma kin yi shuru."
Tana so ta yi magana kamar an ɗinke mata baki ta kasa.
"Ke in ba ki da abin cewa zan kashe wayata. Kin san aikin da na katse ne na kira ki?
Ya faɗa cikin faɗa shi da man ko mganar arziƙi ce ta faɗa ce a wajen shi.
"Hamma."
Ta faɗa a sanyaye tana jin hawaye suna cika kwarmin idanuwanta.
"Me ya faru?
Ya faɗa a hankali jin muryanta ta yi sanyi alamun kamar za ta yi kuka, duk da ya san Ummu da shagwaɓan tsiya sai dai ganin dare ya yi yasa ya yi tunanin ba lafiya.
"Ki yi mgana mana."
Ya faɗa da karfi.
"Hamma."
Ta sake kiran shi a raunane lokaci ɗaya hawaye na zubo mata muryansa kawai da ta ji sai ta ji wani irin abu ya sauko mata mai kama da rauni, sai ta ke jin kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta a gaban shi kawai shi take son gani domin ta fi wata uku ba ta saka shi a idanuwanta ba, tunda shima a Jalingo ya ke aiki can ya ke zaune da iyalansa yana zuwa amma ita tana gidan ta in dai ba hutu suka zo shi da iyalansa ba ba ta samun ganin shi.
"Lafiya wai kike ta kiran sunana kuma ƙin ki mgana."
Hawayenta ta yi saurin sharewa.
"Mijin naki ne ya yi miki wani abu?
Ya faɗa kai tsaye domin shi abin da zuciyarshi ta kitsa masa kenan.
"Aa Hamma."
"To A'a me ye? Ke ba na son fa shanshanci in ba ki da abin faɗa zan kashe waya ta ina da abun yi."
Jin abin da ya ce ne ya sa cikin yar shagwaɓa ta ce" Hamma na kira ne fa na gaishe ka "
"Ƙarya ne"
Ya faɗa kai tsaye.
"Wallahi Hamma."
"Gaisuwan ne sai da daddare za ki kira ni Ummu?
Kanta ta sosa kafin ta ce" Ni ban ma lura da dare ya yi haka ba Hamma."
Kai ya jinjina kamar tana ganin shi kafin ya ce" Ko dai ba ki da kuɗi ne? Kin talauce ne?
"Kai Hamma."
Ta faɗa tana rufe bakinta.
"To ni dai ba saba kira na ki gaishe ni kika yi ba Ummu Salma."
Ya faɗa kai tsaye saboda haka ɗin ne suna daɗewa ba su yi mgana ta waya ba.
"Ina kiran ka mana Hamma."
"Ba na son ƙarya kina dai kiran su Mustapha amma ba ni ba. Ko da ya ke kin ce kin fi son su ni ina da mugun hali irin na Lamiɗo ko?
Ummu ta rasa in da za ta saka kanta saboda kunya da nauyi. Ashe ya ji wannan mganar? Amma abin mamaki wa ya faɗa masa?.
"Kin yi shuru ko ba haka na ji kina faɗa ma Baɗɗo ba."
Tabbas an yi haka tun kafin ta yi aure ne. Suka taɓa hiran a ɗakin Ammah ne su ba su taɓa sanin ya ji ba in ba za ta manta ba yana garin lokacin wataƙila ya zo shigowa ɗakin Ammah ne ya ji suna hiran
"Duk mugun hali na ina da kirki Ummu. Lamiɗo ma don ba ki zauna da shi ba ne he is a nice person."
Ta aminta da kirkin shi tun da shi uwa ɗaya ce ta haife su amma gwara shi akan wancan, ita dai ba ta yarda da cewa wai Hamma Lamiɗo is nice person ba.
"Ka yi haƙuri Hamma. Ba.."
Ya katse ta da sauri yana cigaba da faɗin" Hallaya ce Ummu. Wani haka Allah ya hallice shi ba ya son shiga rayuwar kowa. Kamar ni nan na fi son shuru fiye da komai, kamar Lamiɗo ya fi son rayuwa kamar yadda kika ga yana rayuwa, amma duka muna da kirki ba mugaye ba ne kamar yadda kika ɗauka ba."
Tana danne bakinta kar ta yi dariya ta ce" Na fahimta Hamma."
"So ko gobe ki daina yanke hukunci kan mutumin da zama mai tsawo bai haɗa ku ba."
Ta amsa masa da toh, suna ma cikin wayar ne ta ji ana taɓa kofa.
"Sai da Safe Hamma a gaida Adda Safina da su Yusra."
"Za su ji, da safe zan saka miki ko na kati ne domin na san dalilin kiran kenan."
Tana so ta ce ba haka ba ne sai har ya kashe wayarsa dai-dai lokacin da Habib ya shigo falon da sauri ta miƙe tana kallon shi cikin mirmishi, shi ko gogan kallo ɗaya ya yi mata bai sake ba, yana rataye da jakarsa ya fara takawa zai wuceta zuwa bedroom.
"Sannu da zuwa Noori."
Ta faɗa tana nufarsa, bai tsaya ba amma ya amsa da yauwa a ɗakune yadda ta bar fuskar shi a cunkushe ɗazu to a yanzu ma haka ya shigo
Tana ƙoƙarin karɓan jakar hannun shi ya wuce ta da sauri zuwa cikin bedroom tana jin ƙaran yadda ya rufe ƙofar da ƙarfi. Ummu salma ta yi sansarairai a tsaye ta kasa motsi saboda mamaki da al'ajabi a wattani takwas ɗin da suka yi da aure ita da Habib ba su taɓa riskan wannan matakin ba sai yau.
Ajiyar zuciya ta sauke, komawa ta yi ta zauna tana sake karfafa ma kanta gwiwan ba komai yana fushi ne ya ɗauka ta san tana da ciki ne ba ta faɗa masa ba. Tana nan zaune sama da mintina talatin sha biyu saura na dare sannan Habib ya fito daga cikin Bedroom, ya sauya kaya zuwa wani gajeron wando da farar singlete da alamu wanka ya yi ko kallon ta bai yi ba ya wuce kitchen ya ɗauko ruwan gora ya fito da shi a hannu ita kuma ganin haka ya sa ta miƙe jikinta har yana rawa.
"Noori."
Ta faɗa cikin sanyi da karyewan murya.
Sai da ya sha ruwan rabin goran sannan ya ɗago yana kallonta cikin wani irin kallo da ya sanyaya mata jiki.
"Ga abinci."
Ta faɗa tana nuna masa Dinner ɗin da ta gama shirya masa komai tun ɗazu.
"Na ƙoshi."
Haka kawai ya faɗa lokaci ɗaya yana sauke goran hannun shi a saman dinning ɗin ya wuce ta ya koma ciki, da sauri ta bi bayan shi ta ci sa'a bai rufe ƙofar ba.
Yana zaune a gefen gado yana duba wayarsa ta shigo gefensa ta zauna tana neman kwanciya a saman kafaɗan shi ya yi saurin matsawa gefe, Ummu ta saki baki tana kallon shi.
"Noori."
Ta kira shi da mamaki a muryanta bai amsa ba ya dai kalleta a tsaye da idanuwansa fuskar nan ba fara'a.
"Me ya faru ne?
Banza ya yi da ita sai ma ya cigaba da duba wayarsa.
Sai ta yi mirmishi kafin ta ce.
"Wai akan mganar ciki ne?
Ga mamakin ta sai ya amsa mata da cewa.
"E."
Ta ɗauka tunanin ta gaskiya ne yana fushi ne akan yana tunanin ta sani ba ta faɗa masa ba, ba ta san tunanin Habib a lokacin ba.
"To ka yi haƙuri Noori na, wallahi da gaske na ke yi nima ban san ina da ciki ba."
Har ta gama mgana bai ɗago ba, yana cigaba da latsa wayarsa.
"Ka ji Allah ban sani ba ka yarda da ni."
Matsowa ta sake yi kusa da shi tana mai riƙe hannun shi guda ɗaya tana sake marairaicewa da muryan tare da shagwaɓan da ta san yana kunna shi.
"Am sorry Noori na.
Baby ce fa? Za ka iya fushi da ni?
Ta faɗa tana mai kwantar da kanta a saman kafaɗan shi.
Sai ya sake matsawa da mamaki ta sake ɗagowa tana kallon shi kafin ta samu damar mgana ya miƙe tsaye.
"Ummu-Salma ina son na yi mgana da ke."
Ya faɗa lokaci ɗaya yana mai kallonta a mganar shi da yanayin shi babu wasa ko kaɗan.
"Magana kuma? Wata mgana?
Ta faɗa cikin mamaki gabanta na faɗi kaɗan-kaɗan.
Bai amsa mata ba sai ya koma can farko gado ya zauna sannan ya juyo yana kallon Ummu-Salma da ta daskare a zaune saboda ita fa ba ta gane ma yanayin Habib ba gaskiya
"Ki natsu ki fahimci umarnin da zan ba ki."
Kallonsa kawai take yi amma ta kasa mgana sai dai ta kasa haɗiye miyau a bakinta saboda faragaba da tarardadi
"Ina sauraran ka."
Ta faɗa dakyar cikin rauni har idanuwanta sun fara cikowa da ƙwallah tun kafin ma ya faɗi mganar.
"Ummu-Salma."
Ya kira sunan ta a kausashe, sunan da ba taɓa jin ya kira ta ba tun tana gida da Baby yake kiranta har bayan auran su bai sauya mata suna ba shi ya sa jin yau yana kiran ta da sunan ta cikin kaushi ba tausasawa jikinta ya fara rawa cikin tsoro ta amsa.
"Na'am. "
A muryan ta kamar saura ƙiris ta fashe da kuka.
"Umarni na ke so na ba ki, ta wani fanni kuma ba Umarni ba ne."
Ita dai ta ƙura masa ido, ta kasa cewa komai amma ta matsu ya faɗi abin da zai faɗa kafin zullumi ya ɗauke mata numfashinta.
"Ina son a zubar da cikin jikin ki Ummu-Salma."
Ya faɗa yana mai kallonta domin ganin yanayin ta.
Ita ta ko sai ta ji kamar ba ta ji da kyau ba ya sa ta sake tambaya.
"Naam me ka ce?
Ta faɗa tana mai ƙura masa ido, kamar ta ji Habib na maganar ciki, me ya ke cewa ne?
"Na ce ina so a zubar da cikin nan."
Ido ta zaro kafin ta ce" Wa ni ci ki.?
Ta faɗa a rarrabe cikin tashin hankali.
"Wanda ke jikin ki."
Ya faɗa ba tare da ɗar ba, kuma babu nadama a mganarsa.
Sai Ummu ta fara mirmishi kafin ta ce.
" Haba Noori ka bar irin wannan wasan don Allah ba na so."
Ta faɗa lokaci ɗaya tana girgiza kanta. Domin a tunanin ta wasa ya ke yi, ita kuma ba ta son irin wannan wasan, duk duniya a yanzu ba wanda ya isa ya raba ta da cikin jikinta sai wanda ya ba ta, amma ba dai wani mutum ba.
"Wasa ka ke yi ko Noori?
Ta sake faɗa tana kallon shi.
Amma sai Habib ya miƙe a fusace har yana nuna ta da hannu.
"Kin ga wasa a mgana ta! Ko kin ga fuskata da alamun wasa?
Ya faɗa a fusace, jikin Ummu na rawa ta miƙe, cikin mamaki da aljabi ta ce" Cikina zan zubar Noori?
"E haka na ce"
"To saboda mene? Cikin yana da wata matsala ne?
"Ba shi da wata matsala, amma ni ne zai iya kawo ma matsala a rayuwata nan gaba."
Ummu cikin rawan baki da na murya ta ce
"Ban ga ne ba?
"Ai ba za ki gane ba. Malama ni dai ga abin da na ce. Ciki za a zubar da shi."
"Aa"
Ummu ta faɗa hawaye na zubo mata cikin kuka ta ce" Me ya sa zan zubar da cikina? Cikin sunna ne ba na shege ba."
Ta faɗa cikin zubar hawaye
"Ni haka na ce za a zubar da shi."
"Ba zan iya ba. Ba zan iya zubar da cikin nan ba, haka kawai sai ka ce na zubar da ciki kuma ba da wani ƙwaƙwaran dalili ba"
Ta faɗa tana share ƙwalla kafin ta matsa kusa da shi tana cewa" Noori ni ce fa, ka tuna lokacin da ka shiga damuwa da na rasa cikina na farko me ya sa ba za ka yi murna da samun cikina a karo na biyu?
Me ya sa ka canza? Ciki fa ka ce na zubar? Zunubi fa kake so mu aikata."
Ta ƙarishe faɗa tana ƙoƙarin riko shi da sauri ya kauce yana faɗin
"Ni ba damuwa na shiga don cikin ki ya zuɓe ba, ko bai zube ba za ki zubar da shi. Murna na yi lokacin da ya fita ba baƙin ciki ba.".
Ya faɗa yana kallon ta, cikin ɗimuwa da firgici Ummu ta zare ido, kafin ta kifta idanuwanta amma ta kasa mgana domin sai ta ji wani abu ya tokare mata maƙogwaro
"Kin ji da kyau, saboda haka na ba ki kwana uku ki yi shawara. Duk da Umarni ne ba zan miki dole ba amma ki sani zubar da cikin nan kamar makullin auran ki ne, taurin kai kuma na ƙin zubarwa dai dai ya ke da rasa komai na ki, in na ce komai ina nufin komai. Kuma wallahi sai kin yi nadaman saɓa ma umarnina."
Yana gama faɗin haka ya fice ya bar mata bedroom ɗin. Ummu ta rasa wani tunani za ta yi, sai take ganin kamar a mafarki gaskiya ne abin da ke faruwa ko ƙarya, amma kuma kamar da gaske, ganin ta kawai ta yi tana tafiya a falo ta iske Habib zaune a saman kansa ta tsaya tana kallon shi cikin mamaki, so take yi ta ga shin Habib ɗin ta ne ko sauya mata shi aka yi amma ba ta gano wani abu da zai saka Habib ɗin ta ya sha bambam da wannan dake zaune a gabanta ba.
Tashi ya yi zai bar mata falon da sauri ta sha gaban shi tana faɗin" Noori an ya kasan me kake faɗa kuwa?
Ta faɗa muryanta na rawa kaɗan ya rage ta fashe da kuka
"Kwana uku na ba ki , ki yanke ma rayuwarki hukunci. Kwana uku kacal."
Ya faɗi haka sannan ya raɓa ta gefen ta ya bar falon, nan ƙasan cafet Ummu ta durƙushe tana mai fashewa da kuka, ji take yi kamar ba ita ba zuciyarta na zafi kirjinta wani abu ya tokare mata da ya kasa wucewa kuka ya sake kece mata, tunani take yi ko Habib ya fara shaye-shaye ne yau wata ƙila ya sha wacce ta fi karfin ƙwakwalwarshi shi ne ta faɗa masa ba daidai ba, amma ta ya ya zai ce ta zubar da cikin jikinta cikin sunna ba ta taɓa jin maganar da ta ruguza zuciyarta kamar wannan mganar ba, me mganganunsa suke nuna mata! Me ya sa ta ji zuciyarta na yi mata rawa akan Habib? Me ya sa yau ya sauya mata? Me ya sa zai yi haka?
Kuka take yi kamar ranta zai fita, tana kuma dafe cikinta da ta ji wani kaunar shi na ratsa jinin jikinta, tun tana gida ita mai sha'awar yara ce duk in da ta ga yaro sai ta ji da man na ta ne, ɓarin ta na farko kuka ta dinga yi sai da Ummin ikki ta yi ta lallashin ta. Ammah kuma faɗa ta dinga mata da cewa ba Allah ne ya ba ta ba, sai ta yi haƙuri shi zai sake ba ta wani, to ga Habib na faɗin da man ko cikin bai bare ba za a zubar da shi, an ya yana cikin hayyacinsa kuwa ita ce fa Ummu-Salma da ya ke so kamar ransa, ita ce matarsa da ya ke burin ta zama uwar ƴaƴan shi, me ya sa yanzu zai zo yana wasu mganganu?
Ta kasa gano dalili, ta fi tunanin wani abu Habib ya sha da ya birkita masa tunani amma a cikin hayyacinsa ba zai ce ta zubar da gudan jininsu ba. Wataƙila zuwa da safe zai dawo hayyacinsa ya ba ta haƙuri ya fahimci kuskuren da ya yi, ita kuma za ta yafe masa ta rufe mganar nan har duniya ta naɗe ba wanda zai ji
"Habib na shaye-shaye ne?
Wata zuciyar ta tamabaye ta, ko ba ya yi wataƙila dai jiya ya fara haka ta ba ma kanta amsam yunwa ta ke ji, amma ta kasa iya saka ma cikinta komai anan saman cafet ɗin ta kwana sai gabda asuba ta koma ɗaki, ta iske Habib na ta barci sai ta lallaɓa ta kwanta a gefen shi tana sauke ajiyar zuciya idanuwanta sun kumbura saboda kuka da man ita mai saurin kuka balle ta samu dalili, cikin lokaci barci ya kwashe ta duk da kanta na ciwo ba ta tashi ba sai da ta ji ƙaran ruwa a banɗaki sannan ta san asuba ta yi. Habib ne ya fito sanye da jallabiya ko kallonta bai yi ba ya saka hula ya fita zuwa masallaci.
Ita kuma daƙyar ta lallaɓa itama ta shiga tiolet ta ɗauro alwala ta zo ta ta da salla.
Ta idar kenan Habib ya shigo jallabiyan jikinsa ya cire daga shi sai ƙaramin wando ya koma ya kwanta. Ita kuma sai da ta gama addu'o'in ta sannan na nannaɗe darduman ta ijiye ta tare da hijabin nan saman side drower na gadon. Habib idanuwansa biyu yana latsa wayarsa yau asabar ba fita aiki.
"Ina kwana Noori."
Kamar bai ji ba sai da ta sake maimaitawa sannan ya amsa da lafiya kamar ba ya so har yana juya mata baya.
Ajiyar zuciya ta sauke ko a cikin Sujjadan ta sai da ta roƙi Allah ya dawo da hankalin Habib jikinsa ita fa a tunanin Habib ba ya cikin hayyacinsa ne.
Gefen sa ta koma ta kwanta tana cigaba da saƙe-saƙe.
Saboda rashin barcin da ba ta yi ba ya sa ta ji barci na shirin fizgan ta sai dai me? Kamar a mafarki ta ji Habib ya matso kusa da ita, yana shafa ta sai da ta yi mirmishi a fili a tunanin ta Habib ya dawo hayyacinsa ne tuni ta zage ta bashi dukkan halin kai, da a ce Ummu ta san manufar Habib a kanta da ko sama da ƙasa za su haɗe ba za ta sake ba shi jikinta ba.
Da safiyar ma da ta ɗumama musu taliyar ya ci sai ta dafa musu ruwan tea suka haɗa da shi, kuma a gida ya yini bai fita ba duk da bai sakar mata fuska ba amma in ta yi masa mgana zai amsa sai dai ba cikin walwala ba, sai dai yinin nan da ya yi a gida Ummu-Salma ta gane ba ta da wayau ita ya yi ta moruwa ita kuma jin daɗi take yi a tunanin ta ya bar wancan mganar ganin bai sake yi mata ba, har wani zumuɗin ba shi haɗin kai ta ke yi yana ta murzanta ko tausayi ba shi da shi a kanta alhalin a daran ranar ma ta ci abinci kenan ta amayar da shi duka kuma bai saka ya ɗaga mata ƙafa ba. Haka ma washegari a gida ya yini sai da yamma ya samu fita shima bayan duk ya gana sakar mata gajiya, Ummu ba ta damu ba tuni ta manta da mganar Habib a tunaninta ya dawo cikin hayyacin sa ya bar mganar, tun da kuma ta ga yana cin abincinta sannan yana neman ta a shimfiɗa sai ta yi tunanin addua'nta ce ta karɓu Habib ya dawo cikin hayyacinsa. Shi ya sa ma ba ta yi mganar da kowa ba hatta Bestie ko da ta kira ta a ranar lahadi suka daɗe suna magana tana ta tambayanta.
"Bestie kina dai lafiya ko?
Ita kuma ta ba ta tabbacin lafiyan ta ƙalau, a tunaninta ta rufe mganar ba wanda zai ji.
Sai dai abin da ba ta sani ba Habib zai yi silan tarihin auren ta da shi zai zama abin tunawa gare ta da ahalinta na har abada.
Abin da ba ta sani ba game Habib, ko ta manta ya ce lokaci ya ba ta. Wataƙila yana jiran cikar wa'adin kwanakin da ya ɗiba mata ne"
****
Monday.
Tun a daren jiya da zazzaɓi ta kwana da asuba ma sai da ta yi amai amma a haka Habib ya neme ta, ta fara jan jikinta da wannan rashin tausayin da Habib ke nuna mata. Za ta gama yin Amai amma sannu Habib ba zai ce mata ba.
Yadda ya ke son ta ta ɗauka tare za su yi wannan laulayin amma sai ta ga aka sin haka.
Ya ganta kwance cikin bargo tana rawan sanyi amma ya ce ta tashi ta sama masa abin karyawa, haka nan ta tashi tana makyarkyata ta fita zuwa kitchen buredi ta gasa masa a ovean ta dafa ruwan zafi ta so ko ƙwai ta soya masa amma ta kasa sai ta haɗa masa da sauran cake ɗin ta yi bai ida ƙarewa ba. Ba ta ma tsaya ba ta koma ta kwanta shi kuma sai da ya ci ya yi nak sannan ya fita ba tare da ma ya yi mata sallama ba.
Haka Ummu ta yini kwance da zazzaɓi sai can zuwa yamma ne ta ji sauƙi tun da ta sha paracetamol komai babu a cikinta ruwan lipton ta dafa ta sha sannan ta yi wanka ta ji ta ɗan samu sauƙi. Shi ne ta rarrafa ta yi ma Habib friederice mai nama tunda ba ta da hanta, abin ya ba ta mamaki ganin da wuri yau ya dawo tun kafin isha'i
Sai da ya ci abinci sannan ya fita sallar isha'i kafin ya dawo Ummu ta sake yin wanka duk da ta na jin kamar zazzaɓin zai dawo mata tana jin sanyi-sanyi.
Sai ta saka wata doguwar riga ta haɗa da rigan sanyi saboda ta fara rawan sanyi. Komawa ta yi ta kwanta ta rufa da bargo saboda har kanta sara mata yake yi, Habib na dawowa ya biyo ta har cikin ɗakin ganin ta a kwance bai sa ya yi tunanin ba ta da lafiya ba kawai sai ya saka hannu ya yaye bargon da ta rufa da shii.
A kasalance Ummu ta ɗago tana kallon shi.
"Ta shi mu yi mgana."
Ya faɗa a kausashe.
"Noori ba ni da lafiya zazzaɓi na ke ji."
Ta faɗa cikin rawan sanyi tana ƙoƙarin sake jan bargon ta rufa ya fizge cikin mamaki ta kalle shi kafin ta samu damar magana ya tare ta da cewa.
"Kin manta da maganar mu ne?
Gaban Ummu-Salma ya faɗi ras!. Cikin rawan baki da na jiki ta ce. "Wa ta maga na."?
Ta faɗa cikin mutuwar jiki, maganar cikin ne! Kar dai a ce Habib bai manta da mganar nan ba, kar dai a ce yana kan bakan shi.
"Kin manta ne? Mganar da muka yi da ke ranar. Da man kwana uku na ba ki ki yi tunani ki yanke shawara, yau kuma cikon kwana uku shi ya sa na ce ki ta shi ki faɗa mini matsayar ki "
Ummu ta ji kanta ya sake sarawa da ƙarfi da man kaɗan kaɗan yake ɗan sara mata. Maganar Habib ya sa ta ji kamar gefen kanta zai cire kallon Habib take yi cikin mamaki da gaske ya ke yi?
"Me kika yanke? Za ki zubar ko a'a?
Ya faɗa yana mai kallonta.
Ummu ta runtse ido kafin ta buɗe tana mai dafe kanta.
"Habib wai da man da gaske kake yi?
"Wasa na ke yi miki?
Ya katse ta a fusace.
"Na ɗauka ba ka cikin hayyacinka ne."
Ummu ta faɗa masa ido cikin ido saboda tana so ta samu tabbacin lafiyan Habib ƙalau.
"Au kin ɗauka na fara shaye-shaye ne?
Ya faɗa cikin riƙe haɓa, ita kuma Ummu sai ta ma yar da kanta a saman fito ta ma kasa magana mamaki take yi wai da gaske wannan abin da ke faruwa da gaske yake faruwa!
"Ummu-Salma."
Ya kira sunanta ta amsa ta na mai sake ɗagowa a lokacin ita gani take yi wasa ne ba gaskiya ba ne abin da ke faruwa.
"Kin ga wasa a magana ta ne?
Shuru ta yi masa ba ta yi mgana kawai sai ta ji ya daka mata wani matsanacin tsawa har sai da ta firgita
"Na ce kin ga wasa a magana ta ne Ummu-Salma."
Ya faɗa cikin ta da jijiyan wuya, Ummu ta firgita domin ba ta taɓa jin Habib ya yi mata tsawa irin na yau ba har ta fara hawaye.
"Ba wasa na ke yi ba. Mene ne matsayar ki?
Kanta dake girgizawa tana kwance amma ta kasa mgana saboda kuka ne ya taho mata zuciyarta na wani rawa rawa na ganin ko jin abin da ba ta taba tunanin gani ko ji daga bakin Habib ba.
"Amsa za ki ba ni da bakin ki ba kai za ki dinga kaɗa mini ba malama."
Ya sake faɗa lokaci ɗaya yana mai ɗora kafarsa a jikin gado ya ɗan duƙo yana mai kallon Ummu da ta fara rawan sanyi haƙoranta na haɗuwa gap! gap!.
Mirmishi ya yi, mirmishin da iyakarsa fatar bakinsa kafin ya ce" Ko mutuwa za ki yi sai kin faɗa mini matsayar ki."
Da ƙyar Ummu ta iya miƙewa zaune tana mai kallon Habib tana hawaye.
"Me kika yanke?
Ya sake tambayanta wannan karon ya ɗan ɗaga murya.
"Me ya sa kake son sai na zubar da ciki Habib?
Me ya sa? Lafiyata kalau, ba ni da wata damuwa cikin nan kuma na sunna ne to me zai saka ka ce sai na zubar da shi?
Kallonta yake yi amma bai yi mgana ba, ita kuma tana kallon shi hawaye na gudu bisa kumatun ta mamaki take yi? Mamakin Habib? Mamakin me ya sauya shi cikin lokaci ƙanƙani haka.
"Kawai ina so ki zubar da shi ne."
"Saboda mene?
Ummu ta katse shi da sauri cikin kuka.
Sai ya yi shuru bai yi mgana ba amma yana ta kaɗa kafa.
"Ba zan zubar da cikin ba, sai ka ba ni ƙwaƙwaran dalilin da zan gamsu da ya cancanta da na zubar ɗin sai na bi abin da kake so."
Kallonta ya ke yi cikin mamaki, bai ɗauka Ummu za ta ba shi matsala ba ya yi tunanin yadda take son shi komai ya ce ta yi, za ta yi ba tare da ta yi masa gaddama ba amma ya ga alamun sai ya fito mata a Habib ɗin sa sannan za ta fahimci ba da wasa yake yi ba.
"In kuma ban faɗa miki dalilin ba fa??
Ummu tana mai kallon shi hawaye na zuba ta ce" Ba zan bi Umarninka na saɓa ma Allah ba Habib. Ina son cikina kuma zan rene shi har ya fito Duniya. Ba zan yi ma Ubangiji butulci da kyautar da ya yi mini ba, ya tsamo ni a cikin dubu ya ba ni sai na yi masa butulci a wajen kashe rai?
"Ai bai za ma rai ba malama. Babu zunubi in an zubar da shi yanzu."
Ya katse ta a fusace, Ummu ba ta san tana da ƙarfi ba sai da ta gan ta a tsaye a kan kafafunta.
"Ai daga gudan jinin ne ake busa masa rai. Ka ga ko shima zunubi ne."
Ummu ta faɗa kai tsaye tana mai share hawayenta.
"Ban san dalilin ka ba, ko ma mene ne dalilin ka na tsayar da shawaran cewa ba zan zubar da cikin nan ba Habib."
"Ko da na ce ba yanzu na shirya zama uba ba.?
Habib ya katse Ummu lokaci ɗaya yana yi mata wani kallo.
Cikin mamaki ta ke kallon shi, amma ta kasa mgana saboda bakinta ya yi mata nauyi.
"Ko da na ce miki ba ke nake so ki zama uwar ƴa'ƴana ba?"
Ya faɗa yana mai kafe ta da idanuwansa sannan lokaci ɗaya yana takawa zuwa gaban Ummu-Salma da ta kasa mgana sai kallon Habib ta ke yi, domin sai ta ke ganin kamar a mafarki komai ke faruwa.
"Ko da na ce miki ban taɓa son ki ba, ba ke ba ce matar da na shirya ki zamo uwar ƴa'yana ba, a hakan za ki yarda ki haifi cikin da ni ba zan amsa sunan uban shi ba?
Ummu ta ji wani jiri ya kwashe ta, ba domin ta yi saurin jingina da wardrope ɗin da ke gefenta ba da sai ta faɗi saboda yadda kalaman Habib suka ruguza duka saurin kuzarinta. Kan ta ta ji ya sake sara mata har wani duhu-duhu take gani, jikinta na rawa kamar ana mata kiɗan mazari, kallon Habib ta ke yi kamar tana tunanin in ta buɗe ido za ta ga komai da ya ke faruwa ba gaskiya ba ne. Sai dai ta runtse ido ta sake budewa still Habib ta ke gani a gabanta yana sake jadadda mata bai taɓa son ta ba.
"Kin shirya ma hakan!?
Ta kasa mgana hawaye ne kawai ke yi mata ambaliya, duhu duhu ma take iya ganin Habib tsabar yadda ta ji kamar ba a duniya take ba.
"To ki sani in dai kin ƙi bin umarni na , kin yi taurin kai to ina so ki san wasu abubuwa guda uku."
Har wajen fuskarta ya kawo kansa sannan ya nuna ta yatsa kafin ya cigaba da faɗin.
"Ki sani wannan cikin ba ni da danganta da shi, tun da kika ƙi bin mganata to ki je na bar miki. Na biyu kuma da man na faɗa miki sai kin yi nadaman jayayya da ni Ummu-Salma. Na uku kuma ba zan ce miki komai ba amma zan sanar da ke daga yau kin fara bankwana da farinciki, kin ƙulla ƙawance da baƙin ciki da tashin hankali a rayuwarki, sannan kin fara rasa komai tun daga yau ɗin nan, kin rasa ni Ummu Salma. Watakila da kin bi umarnina da kin tsira da wani abun tun da kuma kika zaɓi taurin kai mu zuba mu gani."
Yana gama faɗin haka ya juya zai bar ɗakin cikin ƙaraji da ihu Ummu ta ce.
"To ka san ba ka sona me ya sa ka aure ni Habib?.
Ta faɗa tana wani irin kuka kamar ranta zai fita.
Kuka take yi da dukkan muryanta da iya ƙarfinta.
Juyowa ya yi ya kalleta kafin ya ɗan cije baki kafin ya yi mgana Ummu ta zuɓe a kasa a kan gwiwoyinta tana sake faɗin.
"Me ya sa Habib? Me ya sa haka? Me ya sa ka je ka nemi aurena a hannun iyayena in dai har ka san ba ka taɓa sona ba? Sannan ka san ba ka san haihuwa da ni me ya sa ka yi mini cikin?
Kuka take kamar ranta zai fita amma bai sa Habib ya ji tausayin Ummu ba, bala'in jin haushin ta ya ke ji, domin taurin kanta adadin ɓacin ran masoyiyar shi, shi kuma duk abin da zai ɓata mata rai yana gudun shi.
"Za ki san dalilin anan kusa."
Yana gama faɗin haka ya fice daga ɗakin har yana bango ƙofa yana jin ƙaran Ummu da sanda ta sake fashewa da kuka mai cike da sauti.
Falo ya fito ya kasa zaune ya kasa tsaye me ya sa Ummu za ta yi masa haka? Bai taɓa tunanin za ta ba shi matsala haka ba, ƙaran shigowan saƙo daga wayarsa ne ya dakatar da shi daga tunanin mafitan da ya ke yi.
"Ya ake ciki? Ta amince?
Wannan lambar dai da ya yi ma saving da M.S ita ne aka sake turo masa saƙo da ita.
Jikinsa na rawa shima ya ma yar da amsa.
"Ba ta amince ba."
Ya tura ba daɗewa sai ga shi an dawo masa da amsa.
"Duk da ka faɗa mata cewa ba ka taɓa son ta ba?
Shi ya sa ba za ka so haɗa zuru'a da ita ba?
"Na faɗa mata."
"Me ya kamata ka yi a yanzu?
"Na kasa samun mafita."
"Ka sake ta Habib."
Shuru ya yi kafin ya rubuta amsa.
"Zan sake ta. Amma sai na nuna mata kuskurenta sai na saka ta yi nadaman sanina a rayuwarta. Sai na saka ta ji dama ba ta yi mini gaddama ba tun fari. Sannan daga karshe na yi mata sakin wulaƙanci da ƙasƙancin da ba ma ita ba dangin ta ma ba za su taɓa mantawa da ni ba"
"Good Job.. Cikin jikin ta fa?
"Zai fita ko tana so ko ba ta so."
"Ka aiwatar da hakan da gaggawa domin ka san ba mu da lokaci"
"Ki yarda da ni."
"Na daɗe da Aminta da kai Masoyi na"
Saƙon ƙarshe ya saka shi farinciki har sai da ya murmusa, wayarsa ya ma yar cikin aljihun wandon jikin shi, ya fara safa da marwa yana tunanin yadda zai yi sanadiyar zubar cikin jikin Ummu Salma ko ta karfin tsiya, yana jiyo kukanta a cikin ɗaki amma ko a jikinsa tunanimsa kawai ta ina zai samar masa da kansa mafitar zubar da cikin nan? Domin bai shirya ba, kuma ba akan Ummu Salma ba.
Abin da bai sani ba, wannan gudun jinin sai an busa masa rai kuma sai ya shaƙi iskar duniya, duk abin da zai yi Ubangiji ya riga da ya gama na shi.
*Janafty*