ADNAN (The Artist)

Chapter 10

by @khairatup01



                   10

Fatima Sale bata tabbatar da za ayi auren Fatima da Mr.Abu ba sai yau da ake ta hada-hadar ɗaurin aure baƙinciki a cikin ranta kamar ana babaka mata wuta. Kuka kuwa tunda aka fara bikin take kuka idanunta sun soye saboda kuka sun yi jajir.
Fatima ta kalle ta kamar ba zata ce komai ba sai kuma tace "Ke, wai na gan ki jikin ki duk ya yi sanyi kamar ba ke ba me ke faruwa ne?"
"Hmm!babu komai kukan rabuwa da ke nake yi."
"Kai! Fatima abinda babu nisa duk sanda kika yi niyya za ki iya zuwa ki gan ni?" 
"Uhm ba za ki gane ba."
Bata kuma jan zancen ba. Da yamma aka kai amarya ɗakin ta da rakiyar iyaye da yan'uwa. 
Ɗakuna biyu ne a gidan da banɗaki a tsakar gidan da madafi ɗan matsakaici daidai rufin asiri.
Fatima taƙaicin gidan ya ishe ta yadda ta ga komai ya yi kyau ya fita fes sai ƙamshin sabon fenti da siminti ko ina mul-mul cikin tsari da ado mai ƙayatarwa ga samiru an jera mata su dama fa Fatima Sani yar gata ce ya ɗaya tilo gun iyayenta dole su yi mata komai na bajinta da burgewa. Ta jima tana ciwon ran wannan abu tuƙiƙi a cikin ranta har ba ta iya cewa komai dai da aka yi wata kafin ta iya taka ƙafarta gidan Fatima.
Ranar da ta zo kuwa Fatima ta cika da mamakin ta tace "Idon ki kenan Fati? Ai nayi fushi."
Ta taɓe baki tace "Ba za ki gane ba ƙawata bani da lafiya ne ga alhinin rabuwa da ke."
Fatima ta kawo mata ruwa da wainar gero da ƙuli a cikin kwano ta ajiye mata ta zauna tana kallon ta tace "Allah sarki! Ban sani ba bani da labarin hakan. Yaya jikin naki?"
"Da sauki Wallahi."
"Ma sha Allah!"
"Na ga kin rame kamar ba amarya ba. Wani abin ke damun ki ne duk kin lalace."
Fatima ta kalle ta da mamaki baki a sake ,ta rasa me zata ce mata wani zubin bata gane hallayen Fatima sai ta rasa ina ta dosa ma gabaɗaya tun da ta gano za ayi aurenta da Mr.Abu ta ga sauyi a tare da ita.
"Ba fa wani abu bane na ga kin yi kasake kina kallona kamar nayi miki wani abu raina an faɗa kin san dai bana ɓoye abinda yake raina."
Fatima ta gyara zama tace "Allah sarki! Babu komai Wallahi lafiya ƙalau muke zaune da shi ba ki ga yadda yake kula da ni ba ya ce ma za mu je Lagos nan da sati biyu."
Fatima Sale ta miƙe a bazata ta zauna tana kallonta tace "Da gaske can za ki koma?"
"A'a amarci za mu je zan raka shi ne zai je kasuwanci kuma zai jima."
"To wai aikin bankin fa?"
"Eh to yana dai son....." Bata ƙarasa faɗa ba ta ji sallamar Abubakar a baƙin ƙofa bai san da baƙuwa ba a ciki.
"Salamu alaikum Noorita."
Fatima ta amsa sallamar haɗe da tashi tsaye ta isa gaba shi ta masa sannu da zuwa yana ƙoƙarin rungume ta ne ta sa hannunta ta tare shi tace "Muna da baƙuwa fa."
"Wacce?" Ya faɗa yana leƙa cikin falon sosai.
Sai a lokacin ya ga Fatima Sale ya ɗan yi jim kamar dai bai ji daɗin ganin ta ba sai ya waske yace "Ƙawar mu ce ashe sannu da zuwa ya ya hanya kin zo lafiya?"
"Lafiya lau malam Abubakar ya amarci?"
Ya ji tambayar banbarakwai ya yi yaƙe ya kalli matarsa yace "Hajiya zo na gaya miki me ya dawo da ni."
Suka shige ɗaki tare.
Wani abu ya tsaya mata a maƙogwaron ta ya ki ya wuce ya tsaya mata ,wani kalar tuƙuƙi ta ji a maƙoshinta bata san lokacin da hawaye suka soma zubo mata sai jin gishiri-gishiri ta yi a bakin ta da sauri ta sa hannu ta share hawayen ta don kar su fito su gan ta shiru-shiru ma har kusan minti goma basu fito ba sai ta ji ta kasa zaman ma ji take kamar zuciyarta zata fashe in ta ci gaba da zaman kawai sai ta suri mayafinta tayi waje da gudu.
Tana tafe tana haɗa hanya tana kuka sai kallonta ake yi bata san tana son Abubakar ba sai yau da suka yi mata wannan wulaƙacin.
A can kuwa Fatima ta samu ta fito da ƙyar don wasu takardu ne ya ajiye ya manta inda ya ajiye su take neman masa shi yasa ma suka jima tana fitowa ta ga wayam babu kowa a falo ta juya ta kalle shi tace "Ka gani ko na gaya maka za ta zaci wani abun ne."
"A'a ni da matata kuma ko da wani abin ne ai matata ce ke kunyar wa zan ji?"
"Gaskiya ban ji daɗi ba Wallahi."
"Sai kiyi ai ki dama min hura don Allah ina dawowa da ita zan soma."
"Shi kenan sai ka dawo Allah Ya bada sa'a."
"Amin."
Ya fita ya bar ta, Fatima ta koma kan kujera tayi zugum tana jin babu daɗi a cikin ranta bata son Fatima tayi zaton wai don mijinta ne ta sosa mata rai da shi ba.
*

Kwance take a kan tabarma a tsakar gidan ta ,laulayi ne ya saka ta a gaba gefenta da goro da ɗata tana maida numfashi a hankali a hankali.
Fatima ta shigo ta same ta sai da ta fara taɓe bakinta sannan tace "Wai duk laulayin ne Ummi?"
"Uhm Fati ba za ki gane yadda nake ji ba."
"Eh ya zan gane abin ma'aurata."
Ba haka nake nufi ba amma in kin ji haushi kiyi haƙuri. Ya kike ya gida ya su Anti Suwaiba?"
"Suna lafiya lau. Wucewa zan yi nace bari na shigo mu gaisa."
"Na ji daɗi kuwa Wallahi. Ga shi ban yi girki ba saboda bani da ƙwari."
"Ai da yake ma ba girkin na zo ci ba. Ke na zo gani."
Ta ji ba daɗi amma bata nuna komai ba ta yi murmushi kawai.
"Amma kina sa ido akan mijin ki kuwa Ummi?"
Tayi mata kallon me kike nufi. Ita kuwa ta ci gaba da magana.
"A'a kawai dai wai na gaya miki ki sa ido da kyau kin san yanzu mazan nan ba amana gare su ba musanmman ma da yanzu kike laulayin nan ƙila ba kya ba shi lokacin ki."
"Me yasa kika ce haka Fatima?"
"A'a kar kice gulma na kawo miki ko zuga ki zan yi jiya ne na gan shi a ƙofar gidansu Hansai suna hira."
Fatima ta buɗe baki da mamaki amma tana ƙoƙarin hana zuciyarta karbar zancen sai tayi shiru kawai. Fatima ta kalleta ta gefen ido tana son ta ga yanayin ta sai taga ko a jikinta ta ciji leɓenta a ranta kuwa cewa tayi "Shegiya ba a gane zuciyar ta." Ta tashi tace "Na gan ki na tafi."
"To shi kennan ki gaida gida na gode."
Haka Fatima ta wuni tana wasi-wasi da tunanin maganganun Fatima sun tsaya mata a rai kam sai dai ba ta son ta soma zargin Abubakar dama ai shi namiji mijin mace hudu ne wannan kalmar ta tsaya mata a rai don Inna na yawan gaya mata bata son kishin hauka kuma kar ta saka a ranta wai mijinta na ta ne ita kaɗai watarana zai iya hango wata yace yana so kuma Allah ne ya bada damar suyi saboda haka ta kula ta kuma shiga hankalinta. Wannan ya sa ta manta da batun Fatima.
Kullum da abinda Fatima Sale zata zo da shi amma daidai da rana ɗaya bata taɓa ganin tashin hankali a kan fuskar Fatima ba wannan abu yana ƙular da ita matuƙa gaya wani bin zai ta ji kamar ta yi mata dukan mutuwa kowa ma ya huta. Haka dai watan haihuwar Fatima ya tsaya ta koma gidan Inna a can ta haihu ta haifi namiji ranar suna Abubakar ya saka masa Shamsudeeni an yi komai yadda ya dace daidai da ƙarfin sa ya yi bajinta anyi alibudi gida-gida aka kai kunun kanwa da farfesun naman rago haka suke yi a lokacin. Kowa ya sa albarka suna dai ya yi kayan Barka ba a magana Jariri ya yi goshi.
Suna zaunen su lafiya ba wata matsala sai fahimta. Har lokacin Fatima bata samu mai sonta ba duk sa'anin su sun yi aure da masu ya'ya hakan na baƙanta mata rai ƙwarai da gaske. 
Lokacin kuwa likkafa ta ci gaba wa Abubakar arziƙi ya shigo mai. A shekarar su ta biyar ne mahaifin Abubakar ya rasu mutuwar ta girgiza ahalinsu sosai da ma yan'unguwa don Alhaji. Muhammadu mutumin kirki ne mai kishin al'umma ne. A lokacin Fatima na da ciki ne ba a sani ba amma saboda bai zo mata da laulayi ba.

1993

Shekarar da aka haifi Adnan kenan inda ya ci suna biyu wato sunan Baban Abubakar da sunan Baban Fatima. Fatima da kanta ta sa masa sunan Adnan don ta jima tana son sunan. Fari ne tas mai kama da mahaifinsa har ya fi shi kyau gashin sa a cukurkuɗe kamar na larabawa(Curly hair) tun yana yaro yake da rigima da kuka amma ba shi da hayaniya ko son mutane yana son Fatima sosai ko ina ta sa ƙafa ta cire sai ya saka. A lokacin kuma buɗi sai abinda ya yi gaba don har Abba ya samu aiki tare da wani babban banki a can Legas ya tattara iyalinsa ya koma can dama harkokin kasuwancin sa a can suka fi ƙarfi saboda Alhajinsu yake zaune bayan an yi musu rabon gado ya haɗa da na shi ya koma suka bar Inna da Baba cikin kewa. 
A can suka saka yara a makaranta rayuwar Legas daban da ta Zariya. Kafin Fatima ta saba ta sha wuya don komai a gaggauce ake yin sa ga area boys da suka yi yawa in baka yi da gaske ba ma sai a yanke maka kunne in ka saka ɗan kunnen gwal ko satar sarƙa ko kuɗi. 
Ya mai da ita makaranta ta ci gaba da karatu hakan kuwa ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba da farko dai komai lafiya rayuwarsu gwanin sha'awa da burgewa ba a taɓa jin kan su ba ko da sun yi yar hayaniyar su babu mai ji tare suke kashewa suke birnewa. Ba ƙaramin so yake yiwa Fatima ba sai dai aka ce kaddara ba yadda bata juyawa bawa ,a sauyin kaddarar ne kuma Fatima da Abubakar suka soma fuskantar rashin jituwa.
Yan ƙananan matsaltsalu suka dinga kunnowa ciki harda zuwan Fatima Sale Legas ziyara ,ziyarar da ta zame musu ta annoba ziyarar da ba zasu taɓa mantawa ba don kamar guguwa ta shigo cikin rayuwarsu ta kuma tafi kamar guguwa. Fatima ta kuma gogewa idanuwanta sun kuma buɗewa ta zama wata sisi
Yau ma da yamma bayan ya dawo daga aiki yana zaune a falo Fatima Sale ta fito cikin doguwar riga ta zauna a kan kujera yana kannoon NTA. Fatima Sale ta zauna a ɗaya daga cikin kujerar falon tana murmushi ta kalle shi tace "Barka da war haka Mr.Abu ya gajiya?" Ta faɗa tana yi masa wani irin kallo. 
Yana kallonta ya ji kansa ya sara zuciyarsa ta buga a maimakon haushin ta da yake ji sai ya ji ya kasa yi mata musu ya maida mata martanin murmushin da tayi masa yace "Barka dai Fatima na ga kin saki jiki da Legas har kin saba."
Sai da tayi fari sannan tace da shi "Wallahi garin akwai daɗi."
Suka dinga hira harda dariya irin wadda ya jima be yi ta ba tun zuwan su Legas su zauna ma su yi hira mai tsayi ba ta samu amma yau sai baɓaka dariya yake yi da Fatima Sale taba bakin kitchen tana kallon su a karo na farko  ta ji babu daɗi ta ji wani sashi na zuciyarta na sukar wannan hirar ba su ma lura tana wurin ba amma da yake Fatima zuciyarta mai kyau ce sai ta gayawa kanta "Mutunci ne kawai ,babu wani abu  bayan hakan Fatima Sale yar'uwa ta ce kuma aminiyata."
Bayan kwana biyu da daddare aka ɗauke wutar Nepa ,Masu generatorn maƙota na ta amsa amo a iska. Fatima ta shiga ɗaki ta kwanta da wuri saboda ta wuni da ciwon kai. Bata ma san ya dawo ba ta dai kunna kyandir a falon guda ɗaya don sai ya dawo zai kunna musu generator.
Fatima Sale na jin shigowar shi tayi wuf ta fito daga ɗakin da ta sauka ga duhu ba wadatacen iska sosai suka yi karo a falo jikinsu ya haɗe da na juna. 
Ya kama hannunta saboda tana ƙoƙarin faɗuwa ƙasa ne.
"Yi hankali Fatima."
"Hah! Legas ta koya min jarumta fa."
"Ko kuma ta koya miki ɓoye sirri ba?"
Ta saki murmushi ta karɓi jakar hannunsa suna kallon juna ido cikin ido idanuwansu suka sarƙe da na juna suka koma kallon-kallon yayin da yara suke kiran shi da kallon ƙuda. A lokacin wata soyayya ta harba zuciyoyin mutane biyun nan ba tare da sun furta kalaman kai tsaye ga juna ba.
Fatima da ta fito daga ɗaki hannunta a goshi sai ta ga kusancinsu ya yi yawa da juna tayi gyaran murya suka matsa da sauri cikin inda-inda sai taji wani banbarakwai. Abubakar ya matsa kusa da ita don ya wanke kansa ya sumbaci gosin ta yace "Masoyiyata."
Da ƙyar bakinta ya iya buɗewa tace"Sannu da dawowa."
"Yauwa sannunmu."
Kawai sai ta juya ta koma ciki. Ya juya ya kalli Fatima Sale sai kuma ta bi bayansa ta shiga cikin ɗakin.
"Na gan ka da Fatima a falo?"
Ya juyo yana cire rigarsa yace "Ban gane ba."
"Ka gane abinda nake nufi."
Ajiye rigar ya yi ya juya da kyau yana kallon ta yace "Ban fa fahimce ki ba, me kike son ki ce?"
"Ni dai ba wani abu nake nufi ba kawai ka ji tsoron Allah."
Tana kaiwa nan ta bar ɗakin shi kuma ya bi bayan ta da kallo cike da mamakin wannan yanayin da ya gani a tare da ita.
Ya zauna a gefen gadon yana kallon ƙofa ya soma tunanin ko wani abun ya yi da Fatiman ne bai sani ba amma babu amsa haka ya haƙura ya shiga banɗaki ya yi wanka yau saboda kishi ba a haɗa masa ruwan wankan ba ma.
Fatima na fita daga cikin ɗakin falo ta koma kaitsaye ta isa gun Fatima tace "Fatima yaushe za ki koma ne?"
Fatima tayi mata kallon mamaki tace "Korata kike yi Fatima?"
"A'a tambayar ki dai nake ji zamu yi tafiya ne da Abubakar."
Tayi mata wani irin kallon sheƙeƙe kamar zata yi magana kuma sai ta fasa ta kame bakinta tayi shiru ta saki murmushin da bai kai zuci ba tace "Ba komai gobe in sha Allah sai hanyar Zariya dama nayi niyyar tafiya."
"Ba komai na gode da kika fahimta." Daga nan ta koma ciki zuciyarta na mata tururi.
Fatima kuwa ta bi bayanta da kallo ta ciji leɓɓen ta na ƙasa a ranta tace "Zan tafi amma zan dawo zan dawo a matsayin guguwar da zata ɗauke ki ta kai ki wani wurin, zan ɗauke miki dukanin wani walwala da kwanciyar hankali Fatima Sani na gaji da ganin ci gaban ki a rayuwa baki fi ni da komai ba Abubakar dai sai na raba ki da shi ta yadda tsakanin ki da shi sai kallo kawai daga nesa ba dai a kusa ba."
Bata kula shi ba ya yi yan lalauben sa ya gama bata ce mar ci kan ka ba. 
Washegari Fatima ta haɗa kayan ta tas ta fito zata tafi. Abubakar ya fito daga ɗaki shi da Fatima suna dariya. Abu ya tokare mata kirji.
"Ba dai tafiya za ki yi ba?"
"Tafiya zan yi Abban Deen."
"Haba na zata za ki yi sati ne tafiyar fa da tsayi."
Ta kalli Fatima tace "Ai tace zaku yi tafiya ne."
Ya yi shiru ya kalli Fatima sai kuma ya gane nufin ta bai ce komai ba ya zaro kuɗi daga aljihunsa ya bata wai ta ƙara kuɗin mota tayi masa addu'a ya fice. Suka yi sallama da Fatima ta saka dereba ya kai ta park ta hau mota ta tafi amma da kudirin sake dawowa irin dawowar da ake kira no going back.
*

Kallo take yi a tv. Kwanaki biyu kenan da dawowarsu sabon gidan su wanda ya gina gida iya gida daidai da arziƙinsa. A lokacin ya zama babba a banki yana matsayin MD ne kowa ya san MD Abubakar Muhammad ya zama wani babban Mutum girma ya hau kanshi. Yaran ma sun yi hankali a lokacin Adnan na aji uku a Sakandire yayin da Shamsudeeni yake shekarar sa ta ƙarshe a sakandire daga Adnan bata kuma haihuwa ba har yau ta gama makaranta har ta juya masters ma.Ta zama wata babbar mace a lokacin zamani ya juya sai take kai wa Innar ta kayan Legas na mata musanmman Lagos lace da atampopi kuma ana siyen su Baba ya bata jari ya kuma ce ta buɗe shago ta zuba kaya a nan Legas ɗin ma yana siyarwa wanann shawara ita ce tayi amfani da ita kuma ta samu albarka don shagon ya karɓu.

Tv take kalla amma hankalinta baya wurin,tana can wani tunanin na daban.
Shamsudeen da Adnan suka shigo a gajiye daga makaranta.
Suna ta sallama bata amsa ba kanta na kallon wuri guda.
Adnan ya matsa kusa da ita ya kama hannun ta yace "Mami muna ta sallama."
Tayi firgit ta dawo cikin hayyacin ta kallonsa tayi tace "Babana yaushe kuka dawo?"
"Mami baki da lafiya ne?" Ya faɗa yana taɓa goshin ta.
Tayi murmushi tace "A'a me ka gani Baba?"
"Na ga sai tunani kike yi ba kya kallona."
"A'a kallo nake." Ta juya ta kalli Deen tace "Sannu Deeni manya."
Yana dariya ya ce "Mami ta mu."
"Soja marmari daga nesa."
Ya yi dariya ya gyara tsayuwar sa yace "Mami an kusa ma fa soma ɗauka duk na.ƙagu ma Wallahi na gama makarantar nan na tafi training."
"In sha Allahu za ka yi kamar yau ne ai."
"Amin Mami. Mami don Allah yaushe zamu je Rafin Garo?"
"Wai ai ka san Abba baya ƙasar in ya dawo sai mu tambaye shi."
"Haba Mami kin san ba yanzu zai dawo ba Abba ina son na ga Baba tsoho."
Ta yi masa daƙuwa "Baban nawa ne tsoho?"
"Ba shi bane Mami ya yi white hair fa."Adnan ya faɗa a shagwaɓe.
"Duk ba wanann ba ku je kuyi wanka kuyi Sallah ku zo ku ci abinci kawai."
Suka amsa mata suka nufi ciki. Sune take kalla ta ji sanyi a ranta watannin biyun nan kawai tana haƙuri ne tana fama da kanta abubuwa ne suka dame ta musamman alaƙarta da Abubakar ta soma sauya jiha duk ta gaji. Tana ma zargin kamar yana so ya yi aure ne shi yasa ya dawo dasu nan kuma ya hana a buɗe wancan ɓarin a kulle yake hakan nan zuciyarta ke raya mata akawai abinda yake faruwa wanda bata sani ba. 
Dole ta tashi ta warware saboda yara sun dawo suna buƙtar kulawar ta,musamman Adnan.
Tana shiga ɗakin ta ga ko sun shirya ta sami Adnan na sana'ar sa ta waƙa tun yana yi yana shirme har ya ƙware ya gaya musu shi fa ba abinda yake so sama da waƙa so yake ya zama mawaƙi tana ɗaukar hakan a matsayin shirme ne ɗakin ta shiga sosai ta buɗe baki ganin yadda ya ɓata bangon ɗakin na sa da zanen sunaye.
*The Blaze.*
*The Artist.*
*The Adnan The singer.* 
Hadda zanen Radio da zanen shi da kuma ta microphone.
Ta kama baki tace "Adnan...." 
Ya dakata daga murɗa jita da yake yi yace "Mami."
"Me haka ka mayar da ɗakin nan haka?"
"Mami kin san fa ina so don Allah kar ki ce na goge."
"Yaushe aka yi wanann abin?"
"Wancan satin ni da Sahib muka zana."
"Shi ma zai zo ya same ni. Amma ne wani Blaze?"
"Mami stage name ɗina ne in na fara waƙa haka zan na sawa saboda ina ji a jikina zan shiga harkar da zafi kuma zan haska sosai, zan zaga ko ina kamar wuta."
"Innallillhi wa inna illahir rajii'un wai ka fara hauka ne? Stage name,kuma wai ma da gaske kake waƙa zaka yi duk aikin duniya Babana."
"Mami addu'a kawai za ki min."