Chapter 11
by @khairatup01
ADNAN (THE ARTIST)
Ummulkhair S Panisau
(Khairatup)
Vote@wattpad khairi_muhd
@arewabooks khairatup01
11
"A'a ba dai ka zama mawaƙi ba. Ga Yayan ka can soja yake marmari kai kuma wai waƙa ka ga ka kiyaye ni."
Bata ba shi damar yin magana ba ta fice daga ɗakin. Ya kalli ƙofar ya zumɓuri bakinsa gaba kamar zai yi tsini. Babban burinsa shi ne ya zama mawaƙi kawai wannan shi ne lissafin sa har kullum.
*
Zariya
Hawaye take sharewa da hannunta jikin ta sai rawa yake yi tsabar tashin hankalin da take ciki. Shiɗewa take tana ƙarawa. Cike da tausayi Alhaji Baba ya soma magana.
"An miki ba daidai ba Ummina,amma na ari bakinsa na ci masa albasa kiyi haƙurin ki yarda da kaddara haka Allah Ya tsara muku kaddara ce na san ki da haƙuri da biyayya kar ki bani kunya."
"Baba anyi wannan abin ne don a nunan iyakata,don kuma a ci mini fuska Baba dole sai ita?"
Baba ya gyara zamansa tsufa ya gama kama shi ba shi ma da lafiya dama. "Na san tarbiyyar da na baki. Kuma ko sun yi don su tozarta ki Allah Ya na kallon su kuma yana tare da ke babu abinda zai faru kiyi hakuri ya ci darajata ya ci ta yaran da ke tsakanin ku."
Ba zata iya yiwa Baba musu ba haka ya saka kawai ta gyaɗa masa kai ba don tana so ba sai don tayi wa mahaifin ta biyayya.
Inna tace "Banda ma abin ki Ummi menene a ciki shi namiji ai mai gane-gane ne sannan kuma zuciyarsa ba don mace ɗaya aka yi ta ba."
"Inna ya rasa wa zai gano sai Fatima? An min adalci kenan?"
"Babu komai Ummi addu'a tafi ƙarfin kowa da komai ke dai ki dage da addu'a ki cigaba da neman aljannar ki babu ruwan ki da su ko Sabgar su nauyin da Allah Ya ɗora miki da yake kan ki shi za ki sauke bana son inji ance ke ce kike tashin tashina."
Suna tsaka da magana Abubakar ya shigo da sallama hannunsa cikin na Adnan sun dawo daga ɗaurin auren kenan. Kallo ɗaya tayi masa ta ji ta tsane shi bata son ganin shi kwata-kwata haka ya sa ta ɗauke kanta gefe.
Abubakar ya tsugunna a ƙasa yayin da Adnan ya tafi kusa da Mami ya zauna yana share mata hawaye.
Ya yi wayo ya san kuma zafin hawayen uwa ya san Abba bai kyauta ba amma dukan su yana son su yana ƙaunar su shi yasa ko abu ake baya siding kowa sai dai ya yi ta basu haƙuri yana lallaɓa su don bai son abinda zai ɓata musu rai.
"Kiyi haƙuri Fatima ba da niyyar ɓata miki rai nayi auren nan ba haka Allah Ya tsara kaddara tace ta zo a haka ina mai baki haƙuri.
Bata kula shi ba ya gama shaciburutsun sa ya tashi ya fita Adnan ya bi bayansa. Aka yi aka yi su koma tare ta ƙi tace ba zata koma da su ba sai an kwana biyu ta basu fili ne suyi amarcinsu Baba ba shi da lafiya zata zauna ta ga yanayin jikin tukunna.
Ya so ya turza sai Baban ya yi masa magana ya je zai turo ta da kansa yanzu tana fushi ne ya bata space ta huta tukuna in ta sauko dan kanta zata taho abinda da ciwo ai an auri aminiyarta Fatima. Shi kanshi Baban yana jin zafin abin sosai amma ya zai yi ba zai hana abinda Allah Ya hallata ba kuma ba zai goyi bayan yar sa ba aure ne Allah Ya ba shi damar ya yi tunda ga kan ɗaya har huɗu.
Kwana ki biyu bayan komawarsu harda yara tana zaune a ɗakin Baba jikin ya tsananta baya ma iya buɗe ido sosai. Sun gama shirin za a maida shi babban asibitin dake Zariya.
Hawaye suke ita da Inna an rasa mai rarrashi wani a cikinsu. Idanunsa a rufe yaka magana a hankali cike da karaya da nasiha.
Daga waje Abdulsalamu ya shigo da sallama ya ce mota ta iso.
Baba yace "Kayya! Me yasa haka? Bana son a zo ana saka mini ƙarafuna ku bar ni na yi shahadata a ɗakin matata."
Inna ta fashe da kukan da take ta riƙewa.
Ya cigaba da magana "Ummina kiyi haƙuri ki ƙara haƙuri don Allah bana son ko bayan raina kiyi abinda za a ce ai wannan tarbiyyar gidan nan ce, ke kaɗai Allah Ya bani kuma Ya raya min ke ga shi kema kin haifa, komai nawa naku ne ki kula da mahaifiyar ki, bata da kowa sai ni da ke sai Allah ki kula da ita bana son kuyi ta koke-koke don bani. Komai da na mallaka a duniyar nan na ku ne Allah Ya yi muku albarka."
Tsabar kuka basu ma iya cewa komai ba sai shiɗewa kawai. Mutuwar mahaifi akwai ɗaci babu daɗi musanmman uba irin Baba mutum mai nagarta da son iyalinsa komai yana yi musu.
Inna ta kama hannun baba tace"Ka yafe min in na ɓata maka a iya zaman mu ka yafe min."
"Ba ki min komai ba, ai ke dai in dai ni ne zan ɗaga ƙafata ki wuce aljanna to babu shakka na ɗaga kin wuce Allah Ya yi miki albarka Ya raba ki da duniya lafiya."
Fatima ta dinga karanta masa kalmar shahada yana maimaitawa hannunsa cikin nata tana hawaye muryarta na karyewa tana karanta mai yana maimaitawa idanunsa a rufe baya iya buɗe su tun suna ji har suka ji shiru ta ji hannunsa ya saki nata a nan ta gane rai ya yi halinsa Alhaji Baba ya rasu ya riga mu gidan gaskiya.
Ta kalli Inna ita ma Inna ta kalle ta suka kalli Abdulsalamu a tare suka ce "Innallillhi wa inna illahi rajii'un." Suka dinga maimaitawa daga bisani ya fita ya gayawa mutane rasuwar.
Cikin ƙanƙanin lokaci gidansu ya cika da jama'a Alhaji Baba ya tara abokan arziƙi a garin Zariya aiki ne ya kawo shi amma Allah Ya kafa shi a garin har ya zama kamar ɗan asalin can kowa ya buɗe bakinsa alkairi da abin ƙwarai yake lissafawa na Alhaji Baba mutumin kirki da kyauta mara ƙyashi. Washegari Abubakar da yara suka iso harda amaryar sa Fatima.
Tayi wa Fatima gaisuwa tana kuka amma ba ta ita take ba.
Shamsudeen ya dinga kuka kamar wani ɗan shekara goma kowa ya san sabon sa da Baba Alhaji yana son kakansa saboda yana son shi. Da ya san rasuwa zai yi da ba zai koma da su Abba ba. Yanzu ma saura kwanaki bakwai su shiga training a Kaduna.
"Mami ya ƙarin haƙuri?"
"Alhamdu Lillahi Deeni Baba lokaci ya yi sai dai muyi masa fatan Allah Ya yi masa rahama."
"Amin-Amin Mami Amin."
Suka yi shiru a ɗakin jefi-jefi tana share hawayen ta da hannu tana jan carbi Deeni bai bar ɗakin ba yana nan gun Maminsa suna amsar gaisuwa tare daga baya ne Bayan anyi sallar la'asar Adnan ya shigo ɗakin shi ma ya zauna yana kallon Mamin cike da tausayawa da sanyin jiki.
"Mami kin ci abinci?" Ya tambaye ta. Ta yi masa murmushi kalar na yaƙe sannan tace "Na ci Babana."
"Ko na kawo miki hura?"
Ta gyaɗa masa kai "Zan sha Babana kawo min."
Ya tashi ya fita da sauri ta bi bayansa da kallo.
Bai jima da fita ba Abubakar ya shigo shi ma cikin babbar riga ta shadda ya zauna a kan laduma,Deeni da ke jin haushinsa ya tashi ya bar ɗakin shi ma matan da suke ciki suka fita suma daga ɗakin sai ɗakin ya rage daga ita sai shi. Ya rasa me zai ce mata kawai sai ya yi mata gaisuwa.
"Ya ƙarin haƙurin mu Fatima?"
"Alhamdu Lillahi."
"Allah Ya jiƙan Baba."
"Amin."
"Kiyi haƙuri Fati...." Kawai sai ta miƙe tsaye ta bar ɗakin ma gabaɗaya.
Ya bi bayanta da kallo ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi bai san tana da taurin kai ba bai taɓa ganin wannan halin nata ba saboda Fatima mace ce mai sanyin hali da tausayi bata taba yi masa haka ba shi kanshi bai san ya aka yi ba ya ji yana son auren Fatima Sale ba hakan nan lokaci guda ya ji yana son ta yana son ya kasance da ita ba shiru ya taho Zariya aka yi maganar komai a cikin ƙanƙanin lokaci dama su Fatima ƙiris suke jira su aurar da ita don baban nasu saboda girma baya komai yanzu sai abinda aka samo ake ba su ko da Abubakar ya zo ba su wani ja ba kuma basu wani duba sannaya ba suka yarda ayi auren dama Suwaiba da mahaifiyarta su ne suka tsara komai da gun malamin da aka je ya yi aiki akansa don ya aure ta kuma sun yi nasara.
Tashi ya yi ya fita daga ɗakin jiki a mace.
*
"Da gaske ba zaki yi haƙuri ki zo mu koma ba Fatima? Na yi miki laifi kuma na baki haƙuri yaya kike son sauya halin ki ne?"
"Hmm! Na haƙura ai, na haƙura kawai dai ina buƙatar space ne."
"Duk space ɗin da kika samu bai ishe ki ba tsawon watanni biyar fa kenann ya kike so nayi ne?"
"Babu ai ka ci amarci iya cin ka zan dawo amma ba yanzu ba."
Ya buɗe baki da mamaki ya kalle ta sai kuma yace "Wanne amarci zan ci? Ce miki nayi ina buƙtar na ci amarci?"
"Oo kawai ni na ga ya dace na baku lokaci ku ƙara sakewa."
Kamar ya maka mata mari haka ya ji amma sai ya danne yace "We need You ki dawo don Allah gidan babu daɗi."
Sai da tayi dariya sannan tace "Haba dai mutum mai sabuwar amarya gal a gida shi ne zai buƙaci tsohuwar fitila a'a wanann bai ba."
Ya gyara zamansa ya yi ƙoƙarin kamo hannunta sai ta yi baya dasu tace "Haba ai wanann karatun ya ƙare tunda ka zaɓi aminiyata Fatima Saleh to fa ka gama taɓa ni."
"Amma wannan wacce iriyar magana ce haka? Ban gane ba kamar yaya na gama taɓa ki haramci na aikata ne?"
"Ko ɗaya kawai ra'ayina ne a haka."
"Nufin ki ba za ki koma ba kenan?"
"Nayi wa Alhaji alƙawari zan zauna da kai zan koma amma ba yanzu ba kuma ban sani ba bani da tabbacin ko zan iya yi maka wata mu'amala ta aure. Na riga na barwa Fatima Sale." Ta ƙarasa faɗa tana murmushi.
Ya rasa me zai ce mata na kawai mamaki yake yi tambayar kansa yake anya kuwa ita ce Fatimar da ya sani?
Ya danne zuciyarsa ya danne yace "Yaushe za ki dawo to?"
"Ba zan iya barin Inna ita kaɗai ba."
"Mu tafi da ita mana gidanmu ai mahaifiyata ce ko ba ke."
"Ba zata yarda ba. Zan dai sai mata gida a kusa da mu zanje Rafin Gora na samo mai zama da ita."
"Zan sai gidan."
"A'a na gode Alhaji MD wanann hurumina ne ina da shi zan iya ni ta haifa ba kai ba."
Ya ji ciwon maganar amma da yake shi yake neman sulhu sai bai tanka mata ba suka yi shiru duk su biyun ba ka jin komai sai juyin fanka .
Dare.
Inna da Mami a tsakar gida kan tabarma suna cin tuwo a kwano ɗaya. Inna ta kalle ta ido cikin ido tace "Ki soma shiri Ummi za ki tafi da Mijin ki gobe idan Allah Ya kaimu."
Ta kasa haɗiye lomar bakinta ta zubawa Inna ido cike da tashin hankali tace "Inna kiyi haƙuri don Allah kar ki shiga maganar nan ya sani ba zan iya yi miki gardama ba shiyasa ya yi miki maganar da kan sa Inna don Allah ki cire ...."
"Saboda gani uwar banza ko?"
Mami tayi shiru ta kasa cewa komai tuni hawaye sun soma yi mata fareti a kan fuska ta rasa yadda zata yi da ranta taji sauƙi.
"Haƙuri ake yi Ummi, duniyar nawa take ne gabaɗaya,kansu suka yiwa ba wani ba ai baki da hakkinsu ki zuba musu ido ki kalle su kawai ai duniya makaranta ce. Ke dai ki kasance mai haƙuri da biyayya."
Ta saki kukan da take ƙoƙarin riƙewa gabaɗaya. Inna bata hana ta kukan ba jikinta ya yi sanyi ta sani akwai ciwo wai mutanen da ka yarda dasu du kware maka baya su ci amanar ka dole ne ta ji babu daɗi a ruhi da gangar jikinta.
"Kiyi haƙuri ni na san na haifi mai biyayya kuma kin haifu babu abinda zai faru ko a iya haka ai kin hora shi tunda ga shi ya kasa zaman lafiya ya kasa samun kwanciyar hankali ya zo yana bibiyar ki wani marar kunyar ma fuskewa yake yi."
"Inna ya ci darajar ki ya shiga rigar ki zan bi shi. Amma Inna zan dawo ba zan bar ki a nan ba za ki koma can Legas kusa da ni."
Inna tayi dariya tace "In kin ga na bar gidan nan na Alhaji nima gawata aka ɗauka ba zan bar nan ba duk wani farinciki ,faɗi tashi da darussa a nan muka yi tare da shi ya gina da gumin sa ina zani? A'a ba inda zan je."
"Haba Inna don Allah ki bi ni."
"A'a fa ba inda zani."
"Shikenan ba yadda zan yi amma zan nemo miki mai tayaki ayyuka."
"Na gamsu da wannan."
WASHEGARI
Cikin ƙananun kaya ya zo ɗaukarta ya ƙi yarda ya soma girma yaransa maza sun soma zama samari ko kunya wai ya nuna mata ya yi aure yana ji da samartaka. Fuskarta a ɗaure ta gaishe shi ya amsa yana murmushi a lallai sai ya nuna komai daidai yake a tsakanin su.
Ya ajiyewa Inna kayan abinci da kuɗi ya kuma ƙara bata haƙuri.Ta shi musu albarka ta yi musu rakiya suka ɗauki hanya.
A hanya da ya gaji da jin radiyo ya kashe ta kalle ta da gefen ido.
"Ki yafe min Fatima ki yarda dani babu wani abu da zai sauya a tsakanin mu ni da ke har yau ke ce a sama a kan gaba wadda nake so nake ƙauna ban yi don na naci amanar ki ba Allah ne Ya kawo za ayi."
"Hmm! Babu komai Allah Yana gani idan anyi don a ci amanata ne ko a ƙuntata min ne to Allah zai min sakkaya idan kuma don sunnar ma'aiki ne Allah Ya bamu haɗin kai zafin da naji da ka munafurce ni kai da ita babu wanda ya yi maganar da ni sai kawai na ji kun yi aure. Ka ga ai ka munafurce ni ko?"
"Na yi kuskure ni dai kiyi haƙuri don Allah ki daina fushi dani ,Wallahi na cutu na wahaltu, na yi kewar ki kar ƙi ƙara yi min irin wannan horon."
Bata dai ce mai komai ba ta koma kallon waje ta tagar motar. Da zasu wuce ya nuna mata makarantarsu Shamsudeen ta kalla ta ɗauke kai kawai amma ƙasan ranta cike da kewar yaron ta ko sallama basu yi ba ya dai kira ta a waya lokacin da zasu tafi.
*
Tana jin tsayuwar mota ta fita da sauri cikin shigar skirt da riga na ƙananun kaya. Sai dai tayi turus lokacin da ta ga Abubakar tare da Fatima.
Fatima da zata wuce ta tace "Fatima Sale amaryar Abubakar yaya gida?" Bakinta na rawa tace "Lafiya ƙalau ya ƙarin haƙurin mu?"
"Da godiya amarya na gode da kula da gida da kika yi Allah Ya saka miki da alkairi amfanin abiyar zaman kenan ai."
Fatima ta shaƙa ta ɗauka Fatima ta tafi kenan bata yi zaton zata dawo ba ganin har tsawon watanni biyar bata dawo ba. Da ƙyar ta haɗiyi yawu ta yi murmushin yaƙe.
Fatima kuma ta shiga ciki tana murmushin ganin ta guma mata ita ma.
Fatima ta kalli Abubakar tace "Dia dawo da ita kayi?"
Ya yi mata wani kalar kallo sanann yace "Da ba zata dawo ba?"
Sai tayi saurin waskewa "Na ji daɗin hakan ai na za ta wata tafiyar kayi ashe Zariya ka je ka ga ai da ka taho min da sautu a gun Umma."
"Ayya! Ban sani ba ai na gaji ne da zama babu Fatima shi yasa naje na dawo da ita duk gidan babu daɗi ya yi faɗi da yawa."
Kamar ya caka mata mashi a ƙirji haka ta ji. Ta bi bayansa da harara ta shiga ciki kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki. Duk wani karsashin ta an sauke mata shi haushin kowa ta soma ji.
Tana gani ya shiga ɓarin Fatima ta saki kuka ta shiga nata ɓarin da gudu.
"Me kike so na siyo miki?"
Hannun ta a kan handle ɗin ƙofar banɗaki ta tsaya bata kalle shi ba tace "Zan girka da kaina." Tana shiga ciki ta kulle ƙofar.
Ya bi ƙofar da kallo bai san tana da taurin kai ba sam. Fita ya yi daga ɗakin.
Ɗakin Adnan ya nufa ya shiga ciki ya same shi a kwance gabansa da takarda yana zana notes na waƙa. Ya wafce takardar yace "Kai ban hana ka wannan abin ba? Duk aikin duniya ka rasa me kake so sai waƙa bana son iskanci fa Baba."
Adnan ya tashi zaune ya ɓata rai ya sha mur dama miskili ne shi ya ƙi yin dariya yace "Ita nake so, zanyi kuma zan iya ku daina kushe min abinda nake so bana so."
"Kai na lura baka iya tauna magana ba wai kai sabgartatace ko?"
"Ka dawo min da Mamita." Ya faɗa yana tattare girarsa.
Abubakar ya kalle shi yace "Ba wanna maganar nake maka ba so nake ka ce min ka daina wannan haukan."
"Ba hauka bane Abba passion ɗina ne shi nake so."
"A'a ba zai yiwu ba in ma asiri aka maka don a tozarta ni zan maka, kai kana ɗana MD guda ɗan kasuwa kace wai shirme kake so a'a tun wuri ka shiga taitayinka ko kaima na tura ka Sojan."
Ya maƙe kafaɗar sa yace "Abba ko ka kai ni zan gudo na dawo gun Mami ta."
"Na daina mamakin taurin kan ka na lura halin uwarka ka kwaso."
"Abba zagin Mami fa kayi bana so Mami tace babu kyau zagi."
Abubakar ya rasa yadda zai yi dama a hasale yake in ya ci gaba da tsayawa zai masa duka ne ya zo kuma yana da na sani don baya son ɓacin ran Adnan sai dai shi Adnan ɗin ya yi hagu shi ya yi dama baya son wanna Sabgar waƙar amma shi ya nace sai ita. Ba tun yau ba ya lura yaron na da taurin kai ga miskilanci bai kai Shamsu magana ba ,ba shi da tsoron zare Ido ko faɗa ko a da can yana mamaki bare yanzu za yake ajin ƙarshe na Sakandire. Kawai sai ya tura ƙofar ɗakin ya fita ya bar shi.
"Me kika girka Fatima?"
"Ban yi girki ba."
"Me Adnan ya ci?"
"Ai ka sani baya cin abincina ban ma yi zaton za ka dawo yau ba ai."
"Ke me kika ci?"
"Cornflask na hada na sha."
"Yanzu ki je ki dafa mana abinci mu ci duka."
"Wa zan yiwa girki."
"Mu." Ya faɗa a dake.
Ta kuwa miƙe tsaye tace "A'a Wallahi babu ƙatuwar da zan yi wa girki mai jin yunwa ya girka da kan sa ya ci ba zan iya ba ah!"
Da mamaki yake kallon ta sai kuma ya yi tsaki ya fice daga ɗakin.
"Wallahi ba zan ba haka kawai ni za a mayar yar iska wai na mata girki ƙila ma ita ce ta aiko shi ni za a rainawa hankali ba zai saɓu ba a wayena na zo ni ya kamata na koya mata hankali ba ni za a koyawa ba."
Dole ya fita ya yo musu takeaway ya kai wa Adnan ya kai wa Mami sannan ya ci na shi ya kwanta a falon Mami yana kallon sama ya rasa ma kalar tunanin da zai yi ya ji daɗi a ransa. Yana son Fatima yana kewar ta sai dai akwai abinda yake danne masa zuciya akan ta kamar ana kwaɓar sa kar ya kula ta tashi ya yi zaune zuciyarsa na mai zafi.