ADNAN (The Artist)

Chapter 12

by @khairatup01

ADNAN (THE ARTIST)
Ummulkhair Sani Panisau 
(Khairatup)
Vote@wattpadkhairi_muhd
Vote@arewapen @khairatup01

                     12
*

Da farko dai komai na tafiya ya da ya dace saboda Fatima ba ta kula ƙawarta Fatima hasalima da lokaci ya ja sai ta manta da cin amanar ta zuba musu ido kawai ta zauna da su biyun da amana. Har aka shekara lafiya lau ba wata haya-haya a tsakanin su. Arziƙin Abubakar kuwa sai wanda ya yi gaba dai-dai ruwa dai-dai ƙurji suna zaune cikin wadata da godiyar Allah. Shamsu ya gama training ɗinsa ya dawo gida hutu kafin ya kama aiki yadda ya dace.
Fatima Sale kuwa an samu abinda ake so babban gida ,mota ga Ac ga kwanciyar hankali amma fa ita duk da haka Fatima Sani ta tsone mata ido bata son ta tashi ta buɗi ido ta ganta a gidan ta fi son ace ita kaɗai ke da wannan ragamar don kuwa komai aka kawo ko Abubakar ya aiko sai Fatima ta fara ɗauka ko ta raba hakan na sosa mata rai sosai ga shi bata haihu ba tun zuwan ta shekara ɗaya ta wuce an shiga ta biyu hakan yana damunta. Ta ɗauka zuwanta zai rage daraja ta Fatima Sani a gidan a tunanin ta ita zata koma mai authority da capacity sai ta ga fa ina maigirma uwargida na baza rayuwa yadda take so idanta ya ma rufe ta manta cewa Fatima Sani na da gado,gadon mahaifinta da ta samu kasancewarta tilo ga mahaifinta kuma ba laifi ya tara na shi arziƙin daidai aljihun shi. Ga shagon ta da ta ƙara buɗi wani reshe daban akwai gidan da take ginawa wanda shi kan shi Abubakar bai san tana yi ba wannnan sirrinta ne gida ne babba ta kashe kuɗaɗen ta wurin gina shi a cikin victoria island ɗin. 
Zaune suke kan kujerar dinning suna cin abincin dare da Mami da Sahib da Abban sai Adnan da Mami ta fito da shi ta dole yau ya zo don su ci abinci like a happy family.
Sai yamutsa fuska yake yi don shi baya son mutane.
Abba ya ajiye cokalin hannunsa da ya kai kankana bakinsa fruit Salad yake ci daman.
"Babana ya batun jarabawar bata fito bane ko baka duba bane?"
Ya kalle shi ƙasa-ƙasa ya juya ya kalli Sahib yace "Abba...ta fito kuma na ci ba wata matsala."
"Ma sha Allah! Haka nake son ji dama, yanzu in fara proceccing tafiyar ka Turai kenan."
"Abba na gaya maka ni bana son naje ko ina na fi son ƙasata kusa da Mami ta kuma ni ko nayi karatun ni waƙa zan yi ina son na yi suna ina son na shahara ina son duniya ta san ni a matsayin ADNAN THE BLAZE...."
Abba ya sa hannu ya daki tsakiyar teburin da ƙarfi gefen kumatunsa don faɗa har rawa yake yi. Shi da Adnan ko a jikinsa.
Mami tace "Ka kwantar da hankalin ka zan mai magana yaro ne."
"Yaro kamar Adnan ki ce mai yaro ai kin san son rai kika bi kalle shi fa baligi kuma yana raina mahaifinsa a'a kar ma ki sa mai wanann tunanin gaskiya ba wani yaro." Fatima Sale ta faɗa tana kallon Mami a tsakiyar ido.
Mamin bata kula ta ba ta kalli mijinta shi ma ya kalle su yace "Magana ta za a bi dole,ni ne dai man of the House ni na isa na ce kuma dole ayi bana son wanann haukan ka ma cire wata waƙa a ran ka matsayin ka ya wuce waƙa i want to see you a wuri mai muhimmanci babba wanda ya fi wannan status."
Adnan ya tashi tsaye yace "Waƙa zan yi."
Abba ya tashi tsaye yace "Baka isa ba."
"Kai wai baka da kunya" Fatima ta faɗa da zafi-zafi.
Ya juya a fusace ya kalle ta yace "Wai wace ke ne ina magana da mahaifina kina magana bana so ki yi abinda yake gaban ki bana son ana shigar min magana babu ruwan ki a ciki."
"Rashin kunya za ka yi min?" Ta faɗa tana sosa ido zata soma kuka.
Abba ya tashi ya sa hannu ya kwaɗawa Adnan mari yace "Baka da hankali? Ba uwarka bace wannan? Bata haƙuri."
Adnan jikinsa na rawa ya kasa cewa komai tuni kanshi ya fara mai ciwo. Ya matse bakinsa ya ƙi yin magana.
Ta kalle shi tace "Aa ka ƙyale shi na san ba laifi sa bane saka shi aka yi koya masa aka yi don ban haihu ba ni ba mai tare min." Ta faɗa tana kallon Mami da ko kanzil bata ce ba amma ta ji marin har a tsakar kanta.
Adnan ya kuma fusata yace "Na gaya miki babu ruwan ki da mu wannan rayuwata ce tsakanina da iyayena ne ban sa ki a ciki ba."
A tsawace Abba yace "Adnan bata haƙuri nace."
"Abba kayi haƙuri ba zan bata haƙuri ba." Yana kaiwa nan ya juya ya bar dinning area ɗin Sahib ya bi bayan shi da gudu Abba ya bi bayansa da kallo har ya ɓacewa ganin sa.
Ya juya ya kalli Fatima yace "Hajiya Fatima kina jin abinda ɗan ki yake cewa ko? Kina kallo amma ki ka kasa taka masa burki da gaske dai kina so ki sauya min tarbiyar ɗa saboda banzan kishin ki?" 
Bata ba shi amsa ba kuma bata daina cin abincin ba. A kan ɗa ba za a ji bakin ta ba kuma a kan Fatima Sale ba za ayi sa'insa da ita ba ta wuce wannan wurin. Amma tabbas zata ja wa Adnan kunne kan abinda ya yi yau amma ba a gabansu ba.
Tashi tayi ta bar musu gun.Tana jin Fatima na cewa "Ka gani ko ai na sha gaya maka ita ke koyawa Adnan raini ita ta saka ya rainaka nima ya raina ni wataran ma ƙila ya sa hannu ya dake ni ko kai yadda yake ji da zafin kan nan..."
Bata ƙarasa ji ba ta bar falon gabaɗaya.
Kaitsaye ɗakin Adnan ta shiga ta same shi a kan gadonsa ,Sahib na gefen shi yana lallaɓa shi. 
Ta kame a wuri guda bayan ta kulle ɗakin ta kalle shi tace "Me kayi a falo?"
Ya sunkuyar da kan shi ƙasa yi kasa haɗa ido da ita.
Ta kuma yin magana tace "Ina tambayar ka kayi min shiru, wacce sabuwar tarbiya ka tsinto?"
"Mami kiyi haƙuri. Ban san nayi ba kin san bana son ana shiga harkata,bana son ana min magana ana shiga na tsane ta, ta shigo gidanmu tana haɗa masifa."
"Shut up! Waye kai da ba za ayi magana ba yaushe ka girma?"
Bai ƙara cewa ƙala ba amma idanuwansa sun yi jajir saboda raɗaɗi.
"Kar ka sake,kar ka kuma ,kar na kuma gani ba sa'ar ka bace matar baban ka ce she is my friend?"
"Mami.... Ta daina min magana bana so."
"Adnan...da ni kake?"
Bai kuma cewa ƙala ba ya yi gum yana kallon ƙasa ƙiris yake jira ya fashe da kuka.
Ta juya ta bar ɗakin.
Ya kalli Sahib yace "Tashi mu fita mu sha iska."
"Ina zamu je?"
"Koma ina ne, kai mu tafi gidanku kawai."
"To muje ka gayawa Mami."
"A'a mu tafi."
Ya san halin shi sarai haka ya sa ya ja shi suka tafi. Mami na kallon fitarsu ta tagar ɗakin ta.
*
Hayaniya ce ta farkar da shi daga baccin da ya ɗauke shi. Hasken rana ya ratsa ta cikin labulen ɗakin ya shigo ya sauka a kan fuskar sa.
Ya sa hannu ya saka ya kare fuskarsa da shi. Ya zuro ƙafafunsa daga cikin duvet ɗinsa,slippers ɗinsa ya saka ya fita daga ɗakin nasa.
Hannun Mami ya fara cin karo da shi da akwati a hannunta. Sai Abba a tsaye, Amarya a tsaye daga nesa ya hango Shamsudeen cikin kakin sojoji ya yi masa kyau a lokacin sai ya ji dum ya rasa ma farinciki zai yi ko bakin ciki duk da bai san ainihin abinda ya faru ba.
Mami ta kalle shi idanuwanta cike da hawaye suna ƙoƙarin saukowa. Shamsudeen ya ji ya ce "Mami ki zo mu tafi."
Sai a lokacin ƙwaƙwalwarsa ta harba masa saƙon Mami za ta bar gidan ne.
Abba yace "Idan yau kika bar gidan nan ki sani kin bar shi har abada kar ki kuma dawowa kuma ba zan sake ki ba."
"A'a Alhaji sakinta zaka yi ai wane irin ba zaka sake ta ba so kake ta kashe ni kana gani fa me ta min so tayi na mutu abin cikina ya mutu amma za ka ce ba za ka sake ta ba?"
Adnan ya matsa sosai cikinsu yace "Mani what is happening?"
"Adnan koma ciki." Abban ya faɗa.
Adnan yace "In koma ina? Mami ina za ki je?"
A hankali ta buɗe bakinta tace "Adnan babu komai ka koma ciki and be a good boy."
Kansa ya ɗaure ya rasa wane tunani zai yi wa zai bi bai san me ya faru ba.
Yaya Deen yace "Adnan ka ji abinda Mami ta faɗa ka koma ciki zan na zuwa ganin ka."
"Babu inda zaka je don uban ka. Kana nan kai ɗana ne."
"Abba akan wannan matar ka ce Mami ta bar maka gida? Za ka zo kana neman Mami a lokacin kuma komai ya lalace.Ke kuma Allah Yana kallon ki za ki gurbi abinda kika shuka zaki yi kuka akwai ranar da na sani. Ba zan taɓa zabar ka akan Mami ba."
"Haka kace Shamsu?"
"Haka na ce." Ya faɗa ya amshi akwatin Mami ya fita ya ja hannunta suka fice.
Adnan yana kallo suka tafi suka bar shi a gidan har yau bai san dalilin barin Mami gidan ba amma ya san cewa dalilin matarsa ne amma ya rasa gane me na yasa shi ta bar shi a gidan a wancan lokacin. 
Mami ta koma gidanta a lokacin bata ma gama gidan ba akwai dai inda aka ƙarsa. Takanas Shamsu ya ɗauko Inna da ta tsufa ba sosai ma take iya tafiya ba ya kawo ta suka ci kukansu suka gama. Inna ta dinga bata baki tana tuna mijinta ta kwantar mata da hankali.
Abubakar so ya yi ta tozarta amma sai Allah Ya nuna masa ikonsa Ya nuna masa ya fi shi,shi ne mai yi shi ne mai iko da kowa da komai.
Wannan fushi da Adnan ya ɗauka ya sa baya zuwa ko ina ƙarshe ma ya yarda ya koma Turai Oxford University karatu don ya nesanta kanshi da kowa amma ya sa Abba ya biya wa Sahib suka tafi tare.
Fatima ta haifi yara mata uku tana da burin ta samu namiji amma Allah bai bata ba wannan shi ne burinta da bai samu cika ba.
A maimakon ta ga Fatima ta tozarta sai ta ga ta ci gaba ba da Abubakar take taƙama ba kuma ba abinda ta rasa tana da labarin komai a kanta.
Ta samu Abubakar kuma sai yadda tayi da shi.
Adnan ya tuna kalmar da Amaryar Abbansu ta faɗa a lokacin da Mami zasu bar gidan.
_Sai gida an harbi kare a ka._ kalmar nan ta tsaya masa a rai kuma duk sanda zai shigo gidan sai ya tuna. Bayan dawowarsa daga karatu ne ya tattara ya koma gun Mami duk da baya hira da ita sosai baya kuma sakar mata fuska amma ya koma can sai dai bai bar Abba ba yana zuwa can ma ya yi kwanaki ba shi da tsayayyen gida.
Cikin shiga mai cika ido ya fito daga cikin motar tabarau a kan fuskar sa,ya soma tafiya cike da izza. Gidansu Adnan ya ginu da tubalin kuɗi da iko. 
Falon ya shiga ya soma cin karo da tsofaffin hotunan su wanda a ciki harda na Mami da na su suna yara.Ammi ma tayi ta cire su ta kasa saboda Abba ya hana duk da kuwa bala'in da suke yi a tsakaninsu.
Abba ya hango zaune a ka kujera cikin jallabiya fara kar ,fuskar sa cike da nutsuwa da iko. 
"Adnan." Abba ya kira shi. Ya samu wuri ya zauna ya ɗan zame kaɗan yace "Abba."
"Tashi zauna da kyau na zaci ai uwar taka ta hana ka zuwa."
Ya yi murmushi yace "Mami bata taɓa hanani zuwa wurin ka ba."
"Kana dai kare ta. Kamar yadda ka ji na gaya maka na maka mata ,sunanta Bilkisu yar yayar Fatima ce kuma ina son kai da Sahib ku je ka gan ta kuyi magana ba wai dogon lokaci za a ɗauka ba ka san dai bana son shirme."
Bai yi mamaki ba amma tabbas abin bai masa daɗi ba kawai dai ya sa a ransa ita Bilkisun da ta yarda zata aure shi sai ta gane cewa shi ɗin ba sa'an yin ta bane kuma Ammi tayi ne don ta ɓata masa rai.Amma duk zai yi maganinsu.
Can Amarya ta fito daga ɗaki cikin shiga mai kyau ta yi kwalliya fuskantar ta ɗauke da murmushi. Tana ganin shi ta ɗan saki dariya ƙasa-ƙasa.
Ya kalli Abban yace "Abba ,ba matsala tunda wanann shi ne ra'ayin ka hakan za ayi ba zan ƙi yin yadda kake so ba in sha Allahu, na amince ko ma wace zan aure ta."
"Allah Ya maka albarka Adnan, Allah Ya sa ya'yanka suyi maka biyayya yadda kayi min."
"Amin." Abba ya faɗa a ƙasan maƙoshi. Inda Abban ya gane muryarsa zai gane cewa babu wani sha'awa ko amincewa daga zuciya sai dai ya amsa ne don girmamawa kawai.
Abba ya tashi ya bar falon.
Ammi ta tashi tsaye ganin Adnan ya tashi tace "Dole ka auri yar yar'uwata. Wannan ba zaɓi bane dole ne umarni ne."
Ya juya a hankali ya kalle ta. Idanunsa sun sauya kaɗan kamar ba shi ba ,daga wanda ya gana yiwa mahaifinsa ladabi yanzu zuwa mutumin da ya saba ba da umarni ga wasu.
Ya yi dariya, ba dariyar farinciki ba sai dai dariya mai cike da gargaɗi da rainin hankali.
"Kina son ki san me yasa na amince?"
Ta girgiza kai. Ya ci gaba da magana.
"Ba don kin isa ba ne,na amince don Abba ne kaɗai ,girmansa ya kai ƙololuwar da zai iya cewa yi na yi ,zai iya cewa haka zaka yi na yi ba musu amma ba don ke ba kuma ba don maganar ki ba."
Ammi ta ɓata fuska,amma sai ta yi ƙoƙarin sakin murmushi tace "Ai Abban naka umarni na yake bi...."
"Gara da kika gane hakan ke ce zai bi umarnin ki ba ni ba, ni kuma yar taki za ta bi nawa umarnin." Ya gyara agogonsa ya cigaba da magana yace "Idan kuma za ki cika baki ne,to ina son ki ɗauki hakan a matsayin nasarar ki..." Ya ɗan matsa kusa da ita sosai ya yi ƙasa da muryarsa yace "Zan iya baki mamaki. Zan iya fasa komai." Ya faɗa idanunsa cikin nata.
"Ni Adnan ba abin wasa bane shi yasa ake kirana sa Blaze (wuta) kenan na ce eh saboda shi ne idan kuma nace a'a ,babu wanda zai iya tilasta ni na yi babu fa kin san babu."
Ammi ta gane wanann ba Adnan bane wanda a baya za a iya juya shi ba, wannan ba ƙaramin yaron da za a iya juyawa kamar igiya bane." 
Abba da ya dawo ɗaukar glass ɗinsa ya ce "Adnan."
Ya juyo yace "Abba , sanyi abin da ka ce. Amma a san cewa ni zan zaɓi yadda rayuwata zata tafi." Yana kaiwa nan ya fita daga cikin falon. Ammi ta kalli bayansa ta matse haƙoranta cike da taƙaici da ɓacin rai ta tsani yaron sosai ta tsane shi fiye da ƙima.
*

"Wallahi ni ba kalar shi bace kai ba ma sa'ar shi bace ai abin kunya ne ma na fita na tsaya da wannan yaron a matsayin saurayi ya zo wurina a'a Wallahi matar manya ce ni a gaya masa ruwa ba sa'an Kwando bane." Ta faɗa cike da tsiwa tana fari da ido.
Usai tace "Amma baki da mutunci me aibun wannan mutumin kin gan shi ne da kika ƙaƙaba mai yaro?"
"Ke ba kin gan shi ba ? To ki aure shi mana."
Usai tace "Ai da ni yace yana so zan aure shin amma ke yace yana so."
"To bana so ki gaya mai na bar miki."
Usai ta rasa me zata ce mata ma tsabar baƙinciki kawai sai ta fita daga gidan. Lamrat ta bi bayan ta da harara ta ja tsaki ta koma cikin gidan.
Kallon sama da ƙasa ta bi yan takarar gidan da shi Lamrat ba dai tsokana ba. Bata bar su a haka ba sai da ta saki waƙar habaici sannan ta shiga ciki bata jima ba ta fito cikin hijabi ta fita daga gidan gabaɗaya. 
Tana fita ta tari adaidaita sahu ta saka niƙabi.
Wayar ta ta zaro daga cikin hijabin ta yi dialing wata number.
Bugu biyu aka ɗaga kiran.
"Ina hanya an shirya komai?" Ta ajiye waya.
*

Wani ɗan ƙaramin ɗaki ne mai duhu a tsakiyar ɗakin akwai wani teburi mai faɗi zagaye da kujeru guda shidda kowanne da akwai mutum a kai. Hasken majigin ne kawai yake haska cikin ɗakin banda shi babu wani hasken.
A jikin majigin hotuna matasa ne sun kai sun bakwai a jere wanda sanannu ne.
"Sune target ɗin mu. Aiki ya biyo ta kan su kuma manyan ƙusoshi ne da dole sai mun yi taka tsan-tsan mun saka ido mun bi komai a hankali lamari ne na iko da dukiya idan muka yi kuskure tabbas zamu yi kuka da idanuwan mu babban mission ne shi yasa na zaɓe ku a tawagata don na san kuna da ƙoƙari da ƙwazo." Ya faɗa yana sauke baƙin gilashin fuskar sa. Kallo ɗaya ya yi mata yace "Me update daga wurin ki?"
"Ban samu shiga ba har yanzu amma ina kan tattara dukkanin wasu bayanai da tsara hanyar da zan bi na shiga jikin shi."
"Ya kamata ki hanzarta wata biyar kacal ne a gabanmu saboda muna zargin akwai wani babban al'amari da zai faru a kwana kusa shi yasa na shigo don na ankarar da ku. Na yaba da ƙwazon ku duka ,kuma ba yaba da ƙoƙarin ku sai dai ina son ku sani dole ne ku sake ɗaura ɗamara ku Zage dantse."
"Yes sir!" Suka amsa duka.
Ya kuma haska wani hoto yace "Wannan shi ne mukullin ƙofar da muke buƙatar mu buɗe dole sai da shi komai zai wakana so nake a shiga jikinsa da gaske duk wata shaida tana gidansa duk da na samu labarin ana ta Kai masa hari a ɓoye."
"Yallaɓai kar ka damu zamu yi aiki yadda ya dace." Ɗaya daga cikinsu ya faɗa.
Basu bar wurin ba sai da suka gama meeting ɗin su tsab tukunna sannan suka tashi.
Ta tattara kayanta zata fita yace "Agent."
Ta dakata ta juya tace "Yallaɓai."
"Kowanne ido yana kan ki saboda ke ce a gaɓar da ta fi kowacce muhimmanci da ƙwari ya kamata ki zage ki dage kuyi abinda ya dace."
"Yallaɓai! Ina iya bakin ƙoƙarina wurin ganin na kai wurin amma zan sake bada ƙaimi."
"Kar ki manta nan da wata biyar komai zai zo ƙarshe ki shiga aiki ƙa'in sa na'in wasan ya isa haka."
"An gama Yallaɓai."
Daga haka suka rabu da juna.
*