Page 3
by @nanadiso10
ZUCIYA DA ƘUNA
By Billy S. Fari & Nana Hadiza
@nanadiso10 | Arewabook
PAGE 3.
Da kuka Zeynab ta nufi ɓangaren mahaifiyar dake can zaune ita da wasu mutan suna tayata amsar gaisuwa, Mémé dake zaune tana jan charbi ta ji sautin kukan ƴar tata tun daga can farkon shigowa ɓangaren nasu “Zainy” ta kira sunanta, da yake haka take kiranta saboda soyayyar da take yi mata tun lokacin data haifeta, Mémé tana da lalurar idanuwa bata gani tun shekaru uku da suka wuce, tana tsananin kaunar Zeynab saboda gaba ɗaya halinta ta ɗauko, saɓanin ƙanenta Aslam dake da wata irin zuciya mai sanyi tamkar Haroon, wanda hakan yasa ako yaushe cikin hantararsa take saboda sam baya yi mata biyayya ga duk wani abu daya san cutarwa ne ga mahaifinsu daya rasu ko kuma yan uwan nasa da Mahaifiyarsu daya ɗauka tamkar tasa mahaifiyar, ganin har lokacin Zeynab bata ƙaraso ba sai ƙarar sautin kukan nata da kunnuwanta ke jiyo mata yasa tafara lalubar sandarta da take amfani da ita tana kokarin miƙewa tsaye, wuɗan da ke cikin ɗakin ne ɗaya daga cikinsu ta taso ta riƙata sai ga Zeynab ɗin ta shigo ɗakin, tana zuwa ta faɗa mata a jiki, Mémé ta samu daƙyar ta koma ta zauna mazauninta tana laluben fuskar ta Zeynab “dama nasan wannan taron baza'a watsesa lafiya ba sai anyi ɗibar albarka, yi shiru Zainy ki faɗamun wane munafikin Allah ne ya taɓa ki, su ko zafin mutuwar nan bai ishesu zama aya ba? Waye ya taɓaki faɗamun baki” “Mémé Haroon ne, wai daga ɗai nace ina so a bani jaririn na riƙe shine Haroon da Dada suka zazzageni wai matarsa za'a bawa, shine don na faɗi gaskiya ya Haroon ya mareni.” Hankali a tashe Mémé tafara ƙoƙarin sake tashi a karo na biyu “Dama nasan zasu aikata, tunda su da akaiwa mutuwar bata dame su ba sukai haka ni bazan ki tafiya nabi miki haƙƙinki ba, da aurenki ace ya ɗaga hannu ya dakar min ke daga kin nuna masu kara wannan ɗibar albarka har inaa, to bazan lamunta ba ina zuwa." wannan karon har bakin ƙofa sai da Mémé ta kusa kaiwa sannan akayi nasarar dakatar da ita ana bata hakuri, ba tare data damu da yanayin jimamin da ake ciki ba tayita masifa har sai da sautin muryarta ya kai a can ta ɗaya ɓangaren, ita dai Dada bata san meke faruwa ba sai da yan tsirko suka zo suka sanar da ita, ta bi zancen da "Allah ya kyauta kawai". dama tasan sai hakan ta faru.
Sosai Mémé ta nuna ɓacin ranta tace Zeynab ta kyalesu kada ta sake komawa ɓangaren idan sunga dama sukai jaririn gidan marayu tunda sun fifita bare akan yar uwar ubansa ta jini, wato Fatima ce bare ba tare da sunyi la'akari da mijinta da shine mafi kusanci da Umar ba. Haka dai ranar Mémé tayita zabgar faɗa abunka da marar gani har dare yayi, ita ko Zeynab bata koma ɓangaren ba sai dai duk wanda ke son yimata gaisuwa ya sameta a can ɓangaren nasu, sosai hakan ya jawo ƙananun maganganu da yawa kasancewar family ɗin nasu babban family ne, wasu suna ganin ba'a kyautawa Zeynab ba musamman wuɗanda basu san yadda abun ya faruba, wasu kuma suna ganin koma meye abinda Mémé ɗin tayi ita da yarta basu kyauta ba,
Ganin abinda ya faru yasa da daddare Haroon ya kira Fatima yace tafito su wuce gida sai gobe su dawo tunda unguwa ɗaya ne, Fatima bata so hakan ba saboda jiya anan suka kwana taso sai anyi addu'a gobe sai su koma gidansu, Dada ce ta lallasheta saboda tayi magana da Haroon ɗin akan abinda ya faru, bata son bayan idonta yan uwan nasa su saje su yaɓawa Fatima magana kamar yadda shima Haroon ke gudun faruwar haka wanda shine dalilinsa nadin su koma gida, sai da Dada ta nunawa Fatima ai da jaririn zata tafi sannan ta samu natsuwar tafiya ɗin.
A cikin mota daga ita har Haroon Babu wanda yai magana har suka iso gidansu, kai tsaye sashenta ta wuce shima ya nufi nashi sashen, jaririn ta yiwa wanka ta yi masa shirin kwanciya sannan ta fito ta nufi sashen Haroon, ko data shiga ta samu yana wanka, bakin gadon Fatima ta zauna tayi shiru tana nazarin rayuwar duniya, tabbas ɗan adam ba abakin komai yake ba, babu abinda ya dawo mata a lokacin sai kalaman Yasmina wato mahaifiyar jaririn, shekaran jiya ranar data haihu da suka je dubata bayan an sallamosu daga asibitin tana cikin jin ɗan yanayin da kowace mai haihuwa ke tsintar kanta acikin bayan ta haihu, rungume take da jaririnta tace "Ukty na yimiki addu'a kema Allah ya nuna mana irin wannan ranar, duk da dai ina kallon wannan yaron kuma danku ne ba ɗanmu ba mu kadai, yaronku ne, zaku yi masa duk wata tarbiya ku kuma hukuntasa kamar yadda zamuyi masa, ina so ya zama ya taso ba tare daya iya banbanta tsakanin mu daku su waye iyayensa ba, ina fatar kema zaki saka hakan a ranki yar uwa ta yadda za mu taru gaba daya mu bashi kulawa?" Hawaye ne suka sake zubowa Fatima a fuska, kalaman sun tsaya mata a zuciya, sun dawo mata da wani zafi da raɗaɗi, Yasmina ta faɗi maganganu da dama a ranar kamar tasan tafiya zatayi tabar jaririnta, idanuwanka ta ɗaga sama tana sake ƙoƙarin shanye hawayen dake faman tsere akan fuskarta tare da rungume jaririn sosai a jikinta wani kukan na sake zo mata, a hankali ta ji saukar lausassun hannuwan Haroon ta bayanta ya zagayo dasu ta cikinta ya rungumeta tsam a jikinsa, ya azo fuskarsa ta jikin wuyanta shima idanuwansa na a rufe tare da sauke lallausar ajiyar zuciya da tayi daidai da lokacin da itama Fatima ta sauke tata ajiyar zuciyar, shi kaɗai yasan me yake ji a zuciyarsa na rashin ɗan uwan nasa mafi kusanci dashi da suka fito ciki ɗaya, yasan yanzu shi kenan baida wani abokin shawara daya rage masa aduniya da idan ya bashi shawara zai samu natsuwa da suka fito ciki ɗaya, dama-dama Aslam, duk da zamowarsa ƙarami da uba ɗaya suka haɗa yana da hankali sosai, saɓanin Zeynab da bai san me yake damunta ba, itace Yayar Aslam da suka fito ciki ɗaya dashi, sai dai ita sam bata ƙaunar abinda zai haifar da zaman lafiya a tsakaninsu, jinsa yake yi tamkar fanko tun ranar daya rasa Umar da matarsa, Ƙanƙame Fatima ya sake yi yana sake shigar da kansa cikin wuyanta alamun rauni, Fatima da idanuwanta ke rufe ta ɗaga hannunta ɗaya ta ɗora saman kan Haroon alamun calming ɗinsa tana sake ƙankame jaririn da daya hannun da take dauke dashi a jikinta, zuciyarta a karye take matuƙa tunawa da kalaman Yasmima, amma a yanzu tana buƙatar ƙwarin guiwa da karfafawa don cika burin mahaifiyar jaririn dake hannunta da sukai tsaftataccen zama da ita, Haroon shine ƙarfinta da komai ma, gashi shi kuma yana ƙoƙarin gazawa, ta sani rauninsa na ƙaruwa ne akoda yaushe idan tana cikin damuwa saboda haka dole zata yaƙi zuciyarta a daidai wannan gaɓar saboda Haroon, ajiyar zuciya ta sake yi sannan tayi kokarin furta kalaman dake cikin bakinta “Ta rayu tsakanin haihuwarsa har zuwa lokacin da ta Allah ta faru akansu cike da yaƙinin zamu bashi kulawa tamkar su, shin kana ganin anya zamu iya? Zamu bashi kulawa da soyayya tamkar su alhalin tun yanzu ina jin kamar mun fara gazawa musamman daga wajena dana kasa shayar dashi tun jiya da yake ta faman kuma sai dai aka bashi madara, ko dai haƙura zan yi abawa Zeynab ɗin shi kaga ita...” bata ƙarasa ba Haroon yai saurin sumbatar wuyanta don dakatar da ita daga faɗar abinda take son faɗa sannan yace “Wannan sam ba gazawa bace Fatima, idan har Umar da Yasmina suna jin cewa zamu ɗauki ɗansu da suka haifa tamkar namu ne mu bashi kulawa da tarbiyya tun suna da rai ba tare da sun san mutuwa zata raba su ba to mune muka fi cancanta da muji hakan a ranmu saboda mun fi su sanin kanmu, Saboda haka zamu kula dashi zamu kuma bashi tarbiya iya ƙarfinmu, amma kafin nan ina so kisa a ranki cewa a yanzu ke uwace da zata iya bawa ɗanta kulawa ta kowace irin fuska, wannan tunanin da ake dashi akanki na baza ki iya ba dole ki sauya shi izuwa zaki iya, wadannan kalaman da akayi amfani dasu dan raunana ki kina bukatar ki sarrafa su wajen bawa kanki ƙwarin guiwa, ba wannan jaririn kaɗai ba dake gabanmu hatta ni Haroon a yanzu kece karfina wajen tabbatarwa da duniya ni ɗin ko waye a wajensa, pls Fatima..” kasa ƙarasawa yai jin yadda ta juyo ta sumbaci fuskarsa, cikin wata murya mai sanyi tace “Zanyi hakan Haroon matukar baza ku raba ni dashi ba koda na gaza ta wani gun, zan cike masa duk wani giɓi a rayuwa na kuma tsaya a kowane tudu da gangare da rayuwa zata zo masa dashi, in sha Allah nayi alkawarin zai same ni agun domin bashi kariya.” Cikin jin daɗin kalamanta Haroon ya juyo da ita duka suna fuskantar juna "Na sani zakiyi fiye da abinda bakinki ya faɗa Fatima, burina kawai Allah ya raya mana shi cikin aminci." ya kamo fuskarta ya sumbata, cikin idanuwanta yake kallo yana ƙoƙarin tabbatar mata da abinda ya faɗa, Fatima ta sauke kanta kasa tana jin gaba-daya jikinta yai sanyi, amma a zuciyarta wani kwarin guiwa take ji tamkar kafaffen dutsin daya jima acikin ƙasa na tsawon shekaru, ta ɗauri aniyar fara sabuwar tafiyarta cike da karfin zuciya da kuma kyakkyawar manufa ba tare da gudu ko ja da baya ba, hakan da tayi yasa Haroon sakin murmushin da iya karsa fuska dan zuciyarsa cike take da mikin da baza ta bashi damar yin hakan ba acikinta, riƙo hannunta ɗaya yai, ɗaya hannun nasa ya ɗora akan jaririn dake cike da suma yana shafawa a hankali sai baccinsa yake yi abinsa "Uwa da ɗanta babu mai raba su sai Allah, in sha Allah gobe idan akai addu'ar uku zanyi magana da Dr. Sofiane (Sufyan) idan akwai magungunan daya kamata kisha ruwan mama su zo ko allurai duka sai abaki ki riƙa shayar dashi da kanki tunda bakya son madarar, ina hakan yayi miki ko?" Da “Eh” Fatima ta amsa tana jin wani farin ciki na lulluɓe mata zuciya, ta ɗago kanta tana kallonsa da idanuwanta masu nuna tsantsar farincikin da take ciki, irin annurin da fuskarta ke fitarwa yasa Haroon tana kokarin buɗe baki tayi masa godiya ya ɗora yatsansa akan laɓɓanta da akullum yake jinsu tamkar auduga saboda taushinsu yana ƙare mata kallo cikin idanuwa, tasan me yake nufi dan haka bata ce komai ba sai ɗan zamewa da tai a hankali ta sake matsowa kusa dashi sosai ta shige jikinsa haɗe da ɗora kanta a saman faffaɗan ƙirjinsa, Haroon tamkar jiraye yake da hakan yasa hannayensa biyu ya rungumeta tsam yana kallon jaririn da har lokacin take rungume da shi ta kasa ajewa tamkar wacce za'a kwacewa shi.
“A duk lokacin da nake tare da ke, duniya tana zama tamkar gida na lafiya da soyayya Fatima, nafaɗa maki gaskiya?” Fatima ta ɗaga masa kai ba tare data ce komai ba saboda yadda take sauraren bugun zuciyarsa da suka haɗe da kalaman dake fitowa daga bakinsa suka tashi wasu baituka tamkar waƙa suka saukar mata da natsuwa a zuciya, wata duniya take jinta ta daban gajimare na yawo da ita, ji tai ya ɗago fuskarta ya sumbaci bakinta “You're my comfort zone Princesse.” Murmushi ya ƙwace mata da sauri ta sake shigar da kanta cikin faffaɗan ƙirjin nasa cike da jin daɗi da farin ciki, mutsumutsun data soma jin jaririn nayi da ƙananun kuka ya sata saurin janye jikinta, ta sauka kan gadon ta miƙe ta ɗorasa a saman kafadarta tana ɗan bubbuga bayansa haɗe da kaiwa da komowa a tsakiyar ɗakin alamun lallashi, shi kuma Haroon ya ɗan yi baya kaɗan ya kwanta ya ɗora kansa a jikin pillow dake jikin kan gadon yana kallonta, sosai tayi masa kyau da zama uwa shi kan shi sai yake jinsa tamkar wani sabon mutum da aka sake halittawa a duniyar wuɗan dake amsa sunan iyaye.
Fatima tafi minti ashirin tana abu ɗaya kafin ta samu jaririn ya koma baccin da yai ta ƙananun kuka, tare suka sauke ajiyar zuciya ita da shi jin ya yi bacci, Haroon ya taso ya miƙa mata hannu alamun zai karɓi jaririn, tamkar ƙwai haka suka lallaɓa tare suka ajiye sa a tsakiyar gadon, Fatima takai hannu ta rage ƙarfin gudun A.C ɗakin sannan ta ɗan zame tana ƙokarin kwantawa, riƙota Haroon yai ta juyo tana kallon shi, lumshe ido yai ya buɗe su akanta, baki ya buɗe zai yi magana tai saurin rufe masa bakin tana zaro masa idanuwa mai mai jin tsoron wani abu dake shirin faruwa da ita, da ido yai mata alamar tambaya Meye? ta marairaice fuska tana kallon jaririn, ya fahimci me take nufi, tsakiyar tafin hannun nata data rufe bakinsa dashi ya ɗan ciza ba tare data ankare ba da sauri ta sake masa bakin tana yarfi da hannun, ta cikin kunnenta ya rada mata magana “Tunda kin gama da ɗanki kizo ki shimfiɗeni bacci nake ji nima ko na saka miki rigima." Harara ta maka masa da wasa tana ɗan haɗe fuska, ya langaɓe kai irin yadda yara keyi shima, Fatima ta buɗe masa hannayenta tamkar mai yi masa oyoyo a hankali Haroon yazo ya shige hukunta yana sauke ajiyar zuciya, a haka ta jashi suka kwanta Haroon na sake jinta cikin ransa tamkar jini da anta, jikinta ya sake shigewa ita kuma ta shiga tofa masa addu'a rabin tunaninta kuma ya tafi wata duniyar. A haka ta samu shima Haroon ɗin yai bacci ta miƙe da kyar tana sake gyarawa jaririn kwanciyarsa sannan ta shige toilet ta yo wanka ta ɗoro alwala ganin kusan karfe biyu har da wani abu na dare yayi, tana fitowa tayi yan abubuwan data saba yi na kula da jikinta don macece ita mai son gyaran jiki da kulawa da kanta yadda yakamata, shiyasa idan ka ganta baza ka taɓa yadda tayi shekarun da take dasu ba.
Kamar dai kullum Fatima sallah ta tayar tana miƙawa Allah kukanta, duk da yau adduoin nata sun sha banban dana kullum, a yanzu ba haihuwa kaɗai take buƙata ba ta fahimci har ƙwarin guiwar reno tana buƙata dan bawa maraɗa kunya.
Awwwn Haroon da alama fa kai da ɗan naka rasa wa Fatima zata kula dashi za’a yi, shin kuna ganin Haroon da Fatima zasu iya cika mafarkin Yasmina akan ɗanta kuwa?
ZK2026
***
***.