Zuciya Da Ƙuna

Page 4

by @nanadiso10

ZUCIYA DA ƘUNA

By Billy S. Fari & Nana Hadiza

@nanadiso10 | Arewabook

PAGE 4.

Bayan kwanaki uku na jimami da addu’o’i, gidansu Haroon Kareem ya sake cika da mutane, amma wannan karon ba kuka ba ne ya mamaye shi gaba ɗaya akwai haɗuwar yanayi na tausayi da kuma wani sabon abu da ke neman bayyana, rana ce mai ɗan haske a Paris, iska mai sanyi tana shigowa ta cikin manyan tagogin gidan, lambun waje ya yi shiru kamar yana sauraron abin da ke faruwa a cikin gidan, a falon da aka kawata da kayan alfarma, iyalai da ‘yan uwa sun taru domin addu’ar uku, kowa ya zauna cikin nutsuwa, ana karanta addu’o’i cikin sanyin murya, ana ambaton sunan Allah, ana roƙon rahama ga mamatan, amma bayan kammala addu’ar ne komai ya sauya, saboda wannan shine lokacin da aka tabbatar da makomar jaririn, kalamai suka fara fitowa daga bangarori daban-daban, wasu cikin ladabi, wasu kuma cikin fushi mahaifiyar zeynab wato meme ta ɗaga murya tana cewa “Ya kamata a ba mu yaron nan… mu ne iyayensa” kalmarta ta fito da Zafi, Zeynab ta goyi bayanta cikin sauri “Exactly… it’s only right” mutane suka fara kallon juna, hayaniya ta fara tashi, wasu suna goyon bayan su, wasu kuma suna kallon Fatima da tausayi, Fatima na zaune a gefe tana riƙe da jaririn, zuciyarta na bugawa, hannunta ya ƙara matse shi kamar tana tsoron wani ya zo ya kwace shi, kafin rigimar ta ƙara tsananta, Haroon ya miƙe tsaye, muryarsa ta fito da ƙarfi amma cikin nutsuwa “Enough.” shiru ya sauka, ya kalli kowa ɗaya bayan ɗaya, sannan ya ce “Yaron nan zai zauna da mu… with my wife” ya jaddada kalmar my wife kamar yana son ya sa kowa ya fahimta, Uncle Usman ya ɗaga murya yana goyon baya “Haka ne… wannan shi ne mafi dacewa” wasu daga cikin dattawa suka girgiza kai suna amincewa, Meme ta yi ƙoƙarin sake magana amma Dada ta katse ta “An riga an yanke hukunci” kalmar ta tsaya a sarari, daga nan aka juya zuwa batun suna, Haroon ya ɗan sauke numfashi kafin ya ce “Sunansa Umar… sunan mahaifinsa” kalmar ta sauka da wani irin nauyi, wasu suka yi shiru suna jin zafin ambaton sunan, Fatima ta ɗago idanunta tana kallon jaririn, hawaye na sauka amma wannan karon ba kuka ba ne na baƙin ciki wani irin motsin zuciya ne mai haɗe da soyayya, ta ɗan murmusa a hankali “Amma… zan riƙa kiransa Rayyan…” kalmar ta fito da laushi kamar lullubi, wasu suka yi murmushi, wasu suka yi gulma a ƙasa ƙasa, “Rayyan kuma?” “Hmm…” amma Dada ta ce cikin nutsuwa “Suna ne mai kyau” daga nan hayaniyar ta ragu, iyayen Fatima da suka zo daga waje suka zo suka rungume ta, mahaifinta ya ce “Mun gode Allah…Allah ya baki lada” mahaifiyarta ta shafa kanta tana cewa “Allah ya sa albarka” Fatima ta ji zuciyarta ta cika da wani irin farin ciki da ba ta taɓa ji ba a rayuwarta, ta kalli jaririn Rayyan… ta faɗa a zuciyarta, kamar tana ɗaukar sabon numfashi na rayuwa, duk ranar suka yini cikin wannan yanayi, mutane suna zuwa suna gaisuwa, wasu suna ɗaukar yaron suna kallonsa, amma duk lokacin da aka ba shi wani, Fatima na jin kamar an cire wani ɓangare na zuciyarta, sai ta karɓe shi da sauri, tana murmushi tana cewa “He likes me better…” Dada ta dinga kallonta tana murmushi, tana cewa “Kin zama uwa kenan” Didi kuwa tana tsokanarta “See you… now you’re a full mom”. Fatima ta riga ta zama uwa, ba da haihuwa ba, amma da zuciya, da dare ya sauka, gidan ya yi shiru, mutane sun watse, fitilu sun ragu, sai ƙananan haske a gefuna, Haroon ya zo kusa da Fatima ya ce “Let’s go… we need to see the doctor” ta ɗago kai “Now?” ya ɗaga mata kai “Yes” ta miƙe da sauri, ta yi sallama da Dada, ta ɗauki Rayyan, suka fita cikin sanyi na daren Paris, motar ta ja cikin nutsuwa, tituna sun yi shiru, fitilun titi suna kyalli, suna isa asibitin, suka shiga, aka kai su wajen Dr. Sufyan, likita mai nutsuwa da professional attitude, ya kalle su da murmushi “Good evening… please have a seat” Fatima ta zauna tana riƙe da Rayyan kamar ba za ta sake shi ba, Haroon ya fara magana “Doctor… we want to ask about feeding… she wants to breastfeed him” Dr. Sufyan ya ɗan gyara zama, ya kalli Fatima cikin kulawa “That’s very good… it’s actually possible in some cases” Fatima ta ɗan matsa gaba “Really?” ya ɗaga kai “Yes… what we call induced lactation… with proper medication and stimulation, your body can start producing milk” ta kalli Haroon cikin farin ciki, ya ci gaba “I will prescribe some hormonal support medications… you also need to keep the baby close, skin-to-skin contact is very important… it helps bonding and stimulates the process” ya ɗan ɗauki takarda yana rubutu “Also… don’t stress yourself… stress can affect the response” ya ɗan yi murmushi “And if it doesn’t work immediately, don’t worry… we have formula options very high quality ones” ya nuna musu jerin sunaye “These brands are safe and recommended” Fatima ta girgiza kai cikin jin daɗi “Thank you so much doctor” suka tashi suka yi masa godiya, suna fita daga asibitin, sanyi ya bugi fuskarta amma ba ta ji shi ba saboda farin cikin da ke zuciyarta, a cikin mota ta juya ta rungume Haroon “Thank you… thank you so much…” ta maimaita kamar ƙaramar yarinya, ya ɗan yi dariya “It’s okay…” amma ya ji yadda wannan abu yake da muhimmanci a gare ta, daga asibitin, ya juya motar zuwa wani katafaren baby boutique store mai cike da kayan jarirai masu tsada, suna shiga, fitilu masu kyau suna haskaka shelves ɗin da ke cike da kayan alfarma, Fatima ta shiga wani irin yanayi na farin ciki, tana ta ɗaukar kaya “This one… oh and this… and this is so cute…” tana dariya, tana nuna masa, tana jin kamar duniya ta buɗe mata, Haroon na biye da ita yana kallonta da wani irin murmushi, sun sayi kaya masu yawa set na kaya, kayan wasa, baby crib mai kyau, blankets masu laushi, bottles, komai, siyayya ce mai tsada amma babu wanda ya damu, suna dawowa gida, ma’aikata suka shiga shigar da kayan cikin gida, Fatima ta zauna a kan gado tana riƙe da Rayyan, ta cire masa kaya a hankali, ta sa masa sabbi, tana magana da shi a hankali “My baby… my Rayyan…” ta sumbaci goshinsa, ta rungume shi sosai, kamar tana son haɗa rayuwarta da tasa gaba ɗaya, yaron ya yi ƙaramin motsi, ya yi ƙara kamar yana amsa mata, ta yi murmushi, hawaye na farin ciki na sauka a idonta.

Rayyan ya girma cikin irin soyayyar da ba kowa ke samu ba a rayuwa, irin soyayyar da idan ka kalla daga nesa zaka rantse cewa jini ne ya haɗa shi da Fatima, ba a taɓa ganin wani bambanci ba, duk motsinsa, duk dariyarsa, duk farin cikinsa Fatima ce a tsakiyar komai, ita ce farkon safe dinsa, ita ce ƙarshen darensa, idan ya farka daga bacci abu na farko da zai faɗa shi ne “Mom…” idan ya dawo daga school abu na farko da zai nema ita ce, ko da kuwa tana cikin kitchen ko a balcony tana kallon hasken birnin Paris, zai garzaya gare ta ya rungume ta “I missed you…” ita kuma zata riƙe shi da kulawa.

Gidan su ya zama wuri mai cike da dariya da walwala, musamman a Neuilly-sur-Seine, inda katafaren gidan su ke kallon wani sashi na birnin, lambu mai kyau cike da furanni da aka kawo daga ƙasashe daban-daban, a gefe kuma akwai ƙaramin play area da aka keɓe musamman don Rayyan motoci na yara masu tsada, kekuna kala-kala, electric mini cars, har ma da ƙaramin ATV bike da Haroon ya kawo masa daga wata tafiya zuwa Monaco, duk wannan ba don nuna arziki ba ne kawai, amma don farin cikin yaron da ya zama zuciyar gidan. Iyayen Fatima ma sun tsunduma cikin wannan soyayya, duk lokacin da suka zo daga wajen su, ba sa zuwa hannu wofi, ko dai kayan wasa ne, ko sabbin kaya daga Champs-Élysées, ko wasu custom gifts da aka keɓe masa, mahaifinta kan ce “This boy is special…” mahaifiyarta kuma ta kan rungume shi tana cewa “Allah ya raya mana kai” Rayyan kuwa ya saba da wannan kulawa, amma bai taɓa zama mai girman kai ba, yana da nutsuwa, yana da ladabi, yana girmama kowa, hakan yasa duk wanda ya haɗu da shi zai ji daɗinsa.

Amma rayuwa ba ta tsaya a wuri ɗaya ba.

A cikin wannan shekarar ne… Fatima ta rasa iyayenta. Labari ya zo kamar guguwa. Wani irin shiru ya mamaye zuciyarta. Duniya ta tsaya mata na ɗan lokaci. Fatima wacce ta saba zama mai ƙarfi, mai murmushi, mai kulawa da kowa… ta shiga wani irin yanayi na damuwa, tana zama shiru, tana kallon sarari, hawaye na sauka ba tare da izini ba, Rayyan ya lura da sauyin, ya kasa fahimtar abin da ke damunta gaba ɗaya, amma ya san abu ɗaya Mom is not okay. Dada ce ta tsaya mata.

Ta zama kamar mahaifiya a gare ta. Ta riƙe ta da kalmomi, da addu’a, da kulawa, tana cewa “Rayuwa haka take… amma kina da mu muma watarana haka zamu tafi.” Haroon ya lura da komai, ya ga yadda Fatima ke fama, hakan yasa ya ɗauki wani mataki ya siyawa dada gida a kusa da su, a cikin wani exclusive area na Boulogne-Billancourt, gidan da ke da duk wani abu na alfarma,yayi hakan saboda yadda dada ke son fatima duk da takasance uwa ga matar umar amma sunada alaka ta jini da’ita sosai, yadda take nunawa fatima kauna yasanya yayi mata hakan yawanci Fatima tana gidan Dada ne, saboda can ne take samun nutsuwa.

A cikin family ɗin Haroon kuwa… ba kowa ne ke farin ciki da wannan ba. Didi kakar Haroon tun farko bata son Fatima, tana yi mata kallon da bai dace ba, amma daga baya, ganin yadda Haroon ya tsaya tsayin daka a kanta, sai ta ja baya, ta rage tsangwama, amma hakan bai nufin ta amince ba. Meme kuwa… mahaifiyar Zeynab… bata ɓoye ra’ayinta.

A gare ta, Fatima black magic tayiwa haroon. Zeynab ma tana ci gaba da nuna ƙiyayya a ɓoye. Lokacin da aka yi aurenta ya mutu, ta so ta zauna a gidan Haroon, tana cewa “I’ll stay there…” amma Aslam ya katse ta “No… you stay with your mother” saboda ya san manufarta ta je ta ƙara musu damuwa.

A hankali, family ɗin ya rabu gida biyu waɗanda ke tare da Fatima da waɗanda ke kallonta da hassada Dalili kuwa guda ɗaya ne. Arzikin Haroon Duk inda aka je, sunansa yana ƙara ɗaukaka. Projects dinsa suna bunƙasa. Investments dinsa suna ninka.

Har ma a cikin estate ɗin da suke ciki, gidansa ya fi na kowa kyau, ya fi girma, ya fi tsari. Kowa yana son wani abu daga gare shi.

Amma… sai da yardar Fatima ake samu.

Hakan ya ƙara musu haushinta sosai Makiyanta suka ƙaru.Wasu har suna cewa suke a ɓoye “Ta yi masa black magic…”

Amma babu wanda ya isa ya faɗa a fili.

Rayyan kuwa…rayuwarsa tana tafiya cikin tsari. Fatima ce ke kai shi school. Fatima ce ke ɗaukar sa. Ko da akwai drivers, ko da akwai ma’aikata…ita ke son yin komai da kanta. Islamic school dinsa ma ta kula sosai da shi, ta sa ya shiga sosai cikin ilimi da tarbiyya, cikin ikon Allah, kwakwalwarsa ta buɗe, ya zama exceptional student, duk wani exam first position, duk wani competition shi ne a gaba. Teachers suna cewa “He’s brilliant”

Students suna girmama shi. Amma hakan ya ƙara tada ƙiyayya a cikin family. Har ma Uncle Usman…wanda a baya yana kusa da su…

ya fara canzawa. Saboda ganin irin nasarar da Haroon ya samu. Rayyan ya zama matashi mai hangen nesa. Wata rana ya zauna kusa da Fatima ya ce, “Mom… I want to join the army.” Ta ɗaga kai ta kalle shi.Idonta ya nuna tsoro. “No.” Kalma guda.Ya yi shiru. Bai ƙara magana ba. Saboda a wurinsa duk abin da Mom take so… shi yake so. Daga baya, ita ce ta zaɓa masa course Business Administration

“Zaka gaji Dad… you need to understand business.” Ya ɗaga kai. “I will.” Haroon ya yi alfahari da shi. Ya fara koya masa harkokin kasuwanci. Fatima kuma ta buɗe masa wata ƙaramar gonar da ta gada daga mahaifinta, a wani wuri mai kyau kusa da Île-de-France countryside, wuri mai cike da natsuwa da iska mai tsafta. Rayyan ya shiga cikin aikin. Da safe school. Da yamma farm. Cikin kankanin lokaci…ya nuna ƙwazo. Harvest na farko da suka yi… ya zama babba. Haroon ya ƙara musu kayan aiki, machines, support.“Good job,” ya faɗa yana kallon sa da alfahari.

Amma duk wannan nasara…ba ta kai girman soyayyar da yake yi wa Fatima ba.Idan ka gan shi a waje tare da ita yake. Idan ba school ba tare da ita yake. Idan ta yi tari kaɗan “Mom we need to go to the hospital.”

Idan ta yi shiru “Are you okay?” Wata rana ma ya ce, “I can’t lose you…” ta ɗan yi dariya. “Nothing will happen to me…” amma a zuciyarta… ta san wannan soyayya ba ƙarama ba ce

ZK2026

***

***.