Zuciya Da Ƙuna

Page 6

by @nanadiso10

ZUCIYA DA ƘUNA

By Billy S. Fari & Nana Hadiza

@nanadiso10 | Arewabook

PAGE 6.

A hankali ya ƙara kusantar ta, yana kallon idanunta kamar yana neman wani abu a ciki, hannunsa ya zagayo bayanta ya jawo ta jikinsa, numfashinsu ya gauraya, zuciyarsa ta fara bugawa da sauri, ba da tashin hankali ba… amma da wani irin so mai nauyi, ya saukar da kansa ya sumbaci leɓenta cikin laushi, kissing ɗin ba na gaggawa ba ne, na nutsuwa ne, yana ɗauke da tausayi da kulawa, kamar yana tabbatar da cewa tana jin shi sosai, Fatima ta ɗan riƙe rigarsa a hankali, jikinta ya amsa wannan kusancin cikin sanyi, ya ƙara rungumeta da ƙarfi amma cikin kulawa, yana shafa bayanta a hankali kamar yana lallashinta, kissing ɗin ya ɗan tsawaita, har sai da numfashinsu ya rikice kaɗan, a hankali ya ɗan janye kansa, amma har yanzu hannunsa na jikinta, idanunsa sun ɗan rufe kamar yana ƙoƙarin dawo da nutsuwarsa, ya sauke numfashi mai nauyi, sannan ya buɗe idanunsa ya kalle ta, tana kallonsa da murmushi mai ɗauke da wasa, “Baka girma kai…” ta faɗa tana ɗan dariya, ya ɗan yi murmushi kaɗan yana jan hancinta a hankali, “Ana girma da soyayya ne?” ya tambaya cikin muryar da ke ɗauke da ɗan wasa da ɗan gaskiya a ciki, ta ɗan turo baki, “Eh mana…” ta amsa, ya ƙara matsowa kusa da ita yana kallon ta da wani irin ido mai cike da so, “Then I don’t want to grow up…” ya faɗa a hankali, ta buɗe ido kaɗan cikin mamaki, kafin ta yi murmushi ta jingina da shi, shi kuma ya ƙara rungumeta yana rufe ta da jikinsa, kamar yana kare ta daga komai, a wannan lokacin… soyayya ta yi shiru, amma zuciyarsu suna magana da juna…

*****

Shekaru sun ja sosai… kuma yanzu Rayyan ba ƙaramin yaro bane, cikakken matashi ne mai kamala, a cikin ɗakinsa mai faɗi da aka kawata da modern luxury design a saman bene na gidan su a Neuilly-sur-Seine, yana kwance a kan makeken gadonsa mai laushi amma bacci ya gagara, yana juyi daga gefe zuwa gefe, numfashinsa yana fita da ɗan nauyi, zuciyarsa cike da tunani da kuma wani sabon yanayi na girma da yake fara fahimta a hankali, ya lumshe idanunsa yana furta addu’a a hankali “Ya Allah ka shiryar da ni…” kafin ya miƙe tsaye, jikinsa ya nuna cikakken ƙarfi, tsayin da ya ƙara, muscle da ya fito a jikinsa, yana kallon kansa a madubi na ɗan lokaci kamar yana nazarin sabon kansa, sannan ya juya ya nufi bathroom, ruwan shower mai sanyi ya sauka a jikinsa yana kawar da duk wani nauyi da ya taso masa a zuciya, ya tsaya ƙarƙashin ruwan na ɗan lokaci yana shiru, kamar yana ƙoƙarin dawo da nutsuwarsa, daga ƙarshe ya kashe ruwan ya fito, yana tsane jikinsa da towel cikin nutsuwa amma fuskar sa na ɗauke da ɗan gajiya da tunani, wayarsa ta yi kara, ya ɗauka ya kalli screen, “I will be there in 30 minutes.” ya faɗa cikin nutsuwa ya katse, a daidai lokacin ƙofar ɗakin ta buɗe a hankali, Fatima ta shigo kyakkyawar mace mai nutsuwa, kamanninta sun ƙara haske da shekaru amma har yanzu tana da wannan soft elegance ɗin nata, ta yi murmushi tana cewa “My love, good morning…” Rayyan ya ɗan sauke fuskar damuwa ya maye gurbinsa da murmushi mai ɗumi, ya ajiye turarensa ya matsa gare ta ya rungume ta, ya sumbaci kanta cikin girmamawa “Good morning Mom…” ta shafa bayansa cikin kulawa kamar yadda ta saba tun yana ƙarami, “Open your mouth…” ta faɗa cikin wasa, ya ɗan yi dariya ya buɗe baki, ta ciyar da shi kamar ƙaramin yaro, duk da cewa yanzu ya fi ta tsawo sosai, amma a gare ta… har yanzu yaron ta ne, ta juya tana fita tana cewa “Two minutes… ka fito” ya ɗan murmusa “Coming…” Yana saukowa ƙasa cikin full dressing simple but expensive outfit, wristwatch ɗinsa mai kyau, kamanninsa sun cika da confidence ya tarar da dining area an shirya breakfast a kan babban table mai sheƙi, Suhayla wacce yake kira Baby sis ta zo da gudu ta rungume shi “Yaya..” Yace “yau sai kin makara ko?” ya faɗa yana dariya, ta turo baki “Wallahi assignment ne…” ya ɗan ɗaga gira “And Nayla?” Suhayla ta yi dariya “Har yanzu bacci take… I told her she has lecture by 9 ” Fatima da ke zaune a gefe ta girgiza kai tana cewa “I don’t know what to do with that girl… jiya ma lecturer ya korota” Rayyan ya ɗan yi shiru na ɗan lokaci sannan ya miƙe “I’ll handle it.” Ya nufi saman bene, ya tura ƙofar ɗakin Nayla a hankali, ɗakin ya cika da wani irin soft feminine luxury light colors, scented candles, dressing table mai kyau Nayla na kwance a kan gadonta, gashinta ya bazu a pillow, tana cikin bacci mai nauyi kamar ba ta da damuwa a duniya, ya tsaya yana kallonta na ɗan lokaci, yana girgiza kai kaɗan, sannan ya matsa kusa ya danna gefen hannunta kaɗan, ta yi motsi cikin bacci tana furta addu’a, ta buɗe idanunta da sauri ganin sa tsaye, ta miƙe a firgice “Yaya I’m very sorry… please…” bai ce komai ba, kallon ta kawai yake yi da seriousness ɗin da ta saba, sai ya ce “Five minutes. I will drop you myself.” kalmar ta isa ta sa ta miƙe da gudu zuwa toilet, tana cewa “Coming..” shi kuma ya juya ya sauko ƙasa, Fatima na dariya tana kallon yadda yake sarrafa Nayla, saboda shi kaɗai ne take ji, duk wani rawar kanta, idan yana nan… sai ta nutsu, soyayyarsu ta ‘yan’uwa tana da ƙarfi sosai, amma yana da tsauri akan karatu.

Fatima ta kalle shi tana gyara masa agogonsa “My love… you’re getting late, you have a meeting by 8:30” ya ɗan yi murmushi “If I don’t do this… she’ll be late again.” ta girgiza kai tana murmushi, a zuciyarta tana jin alfahari da yadda ya zama, Suhayla ta riga ta fita school, gidan ya ɗan yi shiru, Rayyan ya ɗan juya ya kalli Fatima “Mom…” ya kira da ɗan nauyi a murya, ta san me yake son faɗa, ta yi saurin katse shi cikin laushi “Please… kar ka fara yanzu…” ya yi shiru nan take, saboda ya san batason wannan magana, ya girmama hakan.

A daidai lokacin Nayla ta sauko daga stairs cikin sauri tana gyara hijab ɗinta “Mom Mom I’m going…” ta tsaya cak ganin Rayyan a zaune, ta rufe baki da sauri, Fatima ta fashe da dariya, Rayyan ya kalleta kawai ba tare da ya ce komai ba, hakan ya isa ya sa ta nutsu, ta ɗauki bag ɗinta, “Let’s go…” ya faɗa yana miƙewa, suka fita tare, a waje motar luxury tana jiran su, ya buɗe mata ƙofa ta shiga, sannan ya zagaya ya shiga, Motar ta na tafiya cikin nutsuwa a titunan Paris, fitilun safe suna haskakawa a jikin gilashin motar, Nayla na zaune a gefensa tana ta hira babu ƙaƙƙautawa, hannunta na motsi yayin magana kamar kullum, “Yaya honestly I’m tired… this school is too much, wallahi I can’t wait to graduate…” ta faɗa tana ɗan turo baki, “assignments, lectures, presentations… it’s too much…” ta ƙara da ɗan shagwaɓa, Rayyan bai amsa ba, ya ɗan kalle ta kawai sannan ya mayar da hankalinsa kan tuƙi, ba don bai ji ta ba… amma zuciyarsa na wani wuri daban, jikinsa na ɗan ba shi wani irin yanayi da bai gama fahimta ba, shiyasa ya zaɓi shiru, hakan bai dame ta ba domin ta saba da shi, ta ci gaba da magana “And you know what? If I fail this course ehn… I’m done…” ta ƙarasa tana dariya kaɗan, daga ƙarshe ya tsaya a gaban Sorbonne University, ɗaya daga cikin manyan jami’o’i a Paris, ya ajiye motar a hankali, kafin ta fita ya ɗauko wallet ɗinsa ya miƙa mata kuɗi, ta kalle shi da murmushi mai faɗi “Thank you Yaya…” ta faɗa cikin farin ciki, ta jingina kaɗan “You’re the best…” ya ɗan yi murmushi kawai, ba tare da ya ce komai ba, ta buɗe ƙofa ta fita cikin sauri, tana daga masa hannu “Bye!” ya ɗan ɗaga mata hannu sannan ya ja motar ya tafi.

A hankali Nayla ta juya tana takawa zuwa cikin campus ɗin, cike da nutsuwa da confidence, takunta mai tsari yana ɗaukar hankali, gashinta ya ɓoye a ƙarƙashin hijab ɗinta mai kyau, kayan jikinta sun dace da ita cikin salo mai tsabta amma classy, shekaru 21 kacal amma kamanninta sun nuna cikakkiyar mace, akwai diri a jikinta masha Allah, ba raini gare ta ba amma akwai tsiwa mai kyau, irin wacce take jan hankali ba tare da ƙoƙari ba, students da ke wucewa suna kallonta, wasu suna gaishe ta “Hey Nayla…” tana amsawa da ɗan murmushi, wasu ma suna juyawa suna kallonta daga baya.

A gefen parking lot, kawarta Amina ta hangota, ta daga hannu tana cewa “Naylaaa!” Nayla ta juya tana murmushi, ta ƙarasa gare ta, suka haɗa hannu cikin farin ciki “You’re late!” Amina ta faɗa tana dariya, Nayla ta turo baki “Don’t start please… you know how it is…” suka shiga cikin building tare, corridor ɗin ya cika da students, hayaniya mai laushi na fita, ƙarar takalma, dariya, hira… rayuwar university na tafiya yadda aka saba.

Suka isa lecture hall ɗin su, Nayla ta zauna tana sauke numfashi “I’m tired already…” ta faɗa tana jingina da kujera, Amina ta girgiza kai “You complain too much…” kafin su ƙara magana, wasu students suka fara fitowa suna cewa “The lecturer is not coming…” Nayla ta ɗaga kai cikin mamaki “Seriously?” Amina ta ce “Yes… class is cancelled” a nan Nayla ta fashe da dariya mai daɗi “Oh my God I love this school sometimes!” ta faɗa tana ɗaga hannu sama, zuciyarta ta cika da farin ciki, duk gajiyar da take ji ta ɓace a lokaci guda, ta jingina da kujera tana murmushi, ba tare da ta sani ba

A cikin harabar Sorbonne University, rayuwa na tafiya cikin sauri kamar yadda aka saba, students suna zirga-zirga, wasu suna dariya, wasu suna cikin damuwa, amma a tsakiyar wannan cunkoso akwai wata presence da take jan hankali ba tare da ƙoƙari ba Nayla Haroon, a hankali take tafiya a cikin corridor, takunta na fita da nutsuwa da confidence, ba gaggawa, ba tsoro, kamar wacce ta saba da kallo da kulawa daga mutane, hijab ɗinta mai tsabta ya zauna da kyau a kanta, kayan jikinta simple ne amma suna da class mai nauyi, duk wanda ya san quality zai gane cewa ba kayan kasuwa bane kawai, akwai tsari, akwai style, akwai ɗan alfarma a ciki, fuskar ta tana da wani irin haske, ba wai kwalliya mai yawa ba, amma natural beauty da ke fitowa da kanta, idanuwanta masu zurfi suna ɗauke da wani irin ɗan tsiwa da confidence, lips ɗinta suna ɗan motsi kamar tana riƙe da murmushi a ɓoye, ba raini gare ta ba, amma akwai wani irin girman kai mai kyau irin wanda ba ya cutarwa, amma yana nuna cewa ta san darajar kanta. “Hey Nayla…” wasu students suka kira suna wucewa, ta ɗan juya kai tana murmushi kaɗan “Hi…” ba ta tsaya hira mai tsawo ba, domin ba ta daga cikin masu son hayaniya, tana da nata circle, kuma ba ta yarda da kowa cikin sauƙi ba, Amina na biye da ita tana ta magana “Honestly you’re too calm… if it was me I would be shouting that lecturer didn’t come!” Nayla ta ɗan yi murmushi tana girgiza kai “You talk too much…” ta faɗa cikin wasa, suka zauna a bench kusa da glass wall da ke kallon harabar makarantar, rana na haskawa a waje, hasken ya sauka a fuskar Nayla yana ƙara fito da kyawunta cikin nutsuwa. Ta ɗan ja numfashi ta jingina baya, idonta ya ɗan lumshe, kamar tana tunani, Amina ta lura da hakan “What’s wrong?” Nayla ta buɗe idanunta a hankali “Nothing… just tired…” amma a zahiri akwai wani abu da ke cikin zuciyarta, wani irin yanayi da ba ta iya bayyana shi ba, kamar tana neman wani abu… ko wata rayuwa da ba ta samu ba tukuna. A cikin wannan lokaci, wayarta ta yi ƙara, ta ɗauka, screen ya nuna Yaya, ta ɗan murmusa kafin ta ɗaga “Yes…” ta faɗa cikin laushi, daga can ya tambaye ta ko ta isa, ta amsa “Yes I’m in school…” ya ce mata ta kula da kanta, ta ɗan yi dariya “I’m not a kid…” ya katse ta “Behave yourself…” ta ɗan turo baki “Okay…” ta katse, ta sauke wayar tana murmushi kaɗan. Amina ta kalleta da ɗan mamaki “Your brother is too serious…” Nayla ta ɗan ɗaga gira “You don’t know him…” ta faɗa cikin wata murya mai nuna cewa akwai wani abu daban a tsakanin su, ba wai kawai yaya ba… akwai wani irin kusanci da fahimta, amma kuma akwai wani layi da ba ya wucewa. Ta miƙe tsaye a hankali “Let’s go… since lecture is cancelled, I’m not wasting my day here.” suka fara tafiya, yayin da take tafiya, wasu idanu suna binta, wasu suna kallonta.

ZK2026

***

***.