Chapter 6
(Past) Nasan mai karatu yashiga rudani matuqa,akan wacece aysha (dimple), sannan kuma meyafaru arayuwarta,kucigaba dabiyoni domin jin cikakken labarin AYSAM. Labari; Alh Abu jandal shaharran attajirin billionaire ne wanda akasansa aqasashen Africa daqetarensa,yana da tarin dukiya mai yawa wacca asali yagada daga mahaifiyarsa kasancewar sa da daya tilo data haifa wanda har tabar duniya batasake haihuwaba,mahaifiyarsa hjy Aishatu darma yar asalin jihar kano ce wacca take daya daga cikim dangin alasawan asali, yar kasuwace wacca take siye da siyarwa a jahohin nigeria harma daqeteren ta,Alh Abu jandal kuwa yayi arziqi shima sosai don dabashidashi iyayen ayshatu baxasu bashi aurentaba itace matar sa tafarko,wacce shekarar ta goma agidan aure bata taba koda bariba,hakan yasa dangin miji sukasata agaba har sukasa yaqaro aure ya auri yar uwarsa buzuwan agadas morem, aurensa da morem da shekara daya tahaifi santaleliyar yarta mace hauwa'u, nanfa alh abu jandal arziqinsa yafara qasa itakuma hjy ayshatu kmr ana qaramata fetir awutane sbd cigaban kasuwancinta,haka bata damuba take matuqar nuna soyayya ga yar abokiyar xamanta hauwa,hauwa nada shekaru biyu morem taqara samun ciki kuma lokacin gagarumar karayar arziqi tasamu alh Abu jandal,yaxamana ayshatu keciyar da gidan alh rashin abinyi yasashi kwanciya ciwo mai tsanani wanda yay dede da haihuwar morem tahaifi da namiji akarada masa suna sooraj, haihuwar sooraj dakadan Allah yabawa ayshatu ciki farinciki yakasa boyuwa gurin alh duk da bashida lfy yana fama hakan be hanashi nunawa ayshatu kulawa da soyayyar sa akan cikinba, nanfa dangin miji suka shiga tsakanin morem da ayshatu anacewa don taganta mekudi yar masu kudi yasa take ganin kowa daddai agidansu harta megidan tamaidashi bawanta balle kuma kishiya da yayanta anahaka Allah yakarbi ran alh cikin ayshatu nada wata 9 cif, adaren ranar tahaifi santala santalan yaranta maxa biyu taji mutuwar alh sosai amma haihuwarta tsata farinciki inta tina yaranta yanbiyu datake matuqar qauna, nanfa akafara gutsiri tsoman raban gado,watan alhassan da alhussain biyu Allah yakarba rana hussain, ayshatu tayi kuka sosai kmr ranta yafita kuma har lokacin ba'a raba sauran gadon da dan abinda alh yabari, jitai xaman garin gombe ya isheta tatattaro tadawo gidansu tareda alhassan dinta batareda tatsaya karbe karben gado ba,taraini alhassan cikin soyayya dakulawa irinta uwa da uba danginta bayajja basuyiba kan tasake aure tabasu riqon alhassan amma fafur taqi dasuka takuramata ma tattarawa tai tagudu abuja tasiyi gida daga ita sai alhassan dinta hakan yasa yan uwanta sukai fishi da ita don tanuna basu isa da itaba don iyayensu sunmutu shiyasa taxabi tabijire masu. tacigaba da harkokinta agarin abuja hartasaka alhassan amakaranta yatashi a abuja daga bayama tatattaro sa suka taho qasar England don tanason danta yay Karatu a best university dake duniya alokacin wato oxford,a Oxford city takama gida tun wancan xamanin tacigaba daharkokin ta lokaci daya alhassan na karatun jamia,ayshatu taji ita duk duniya tanason takoma gida dole alhassan yadakatar da karatunsa alokacin wanda yake,suka siya ticket xuwa naija dangin mahaifinsa suka fara nema inda suka tararda morem tarasu shekarar data wuce, yan uwan mahaifinsu sunguji su hauwa da sooraj sbd basuda abin duniya kuma daman sune nasu dangin uwa da uba, cikin kuka alhassan yaroqa mahaifiyarsa bayan yagane su hauwa yan uwansane shi mutum ne mekulaficin yan uwa da jama'a hakan yasa tadaukesu suka koma hannunta shaquwa meqarfi tashiga tsakanin hauwa da alhassan sooraj kam bewani shiga jikinsu ba don qarara xakaringa ganin hassada da baqinciki a idonsa kan dukkan abinda alhassan yakeda lokacin yakoma oxford inda yakammala karatunsa cikin yardar Allah bayan yadawone yatarar da mummunan labari namahaifiyarsa dake kwance asibiti wai tanada ciwon xuciya kullum mgnrta tanajiya cewa take alhassan Allah yasa naga aurenka kahaifamin jika mekama dakai dan albarka,inason kataramun jikoki masu tarun yawa kaji alhassaanuna Allah yabaka diya mace wacce xata qaunaceka takula dakai nibansamu nahaifa ba xakasamata sunana alhassanu, girgixa kai yakeyi yana furta umma baxaki mutuba kidena fadar haka. Bayan rasuwar hjy ayshatu badadewa kasancewar shine kadai magajinta ba uwa ba uba hakan yasa alhassan yakeda makudan dukiya metarin yawa turawa yagayyato musamman masu ilimin Kasuwanci duk da shima yanada nasa amma betinanin yasan abinda xeyi kuma yanxun harkokin da mahaifiyarsa keyi yanxun tayi sanyi sosai. Nanfa suka bashi shawarar fara haqar danyan manfetir yana siyarwa gwamnati tana siyarwa kasashen waje dahaka yafara har yabude companies masu tarin yawa na AJ group of companies. Yafara shahara datashen kudi yahadu da matarsa doctor bintu jafar itadin bayar kowa bace amma inkaga jinkanta xaka ce yar sarkin masr ce, macece mejidakanta,ha kyawu mairikitar da hankalin yaya maxa donko kemace kika kalla bintu saikin qara. A saudiyya suka hadu tana daya daga cikin yan sadakan yalla wacca iyayentane sukeyi suka taho da ita amma yar asalin jihar gombece tanada kyau nafitar hankali wanda imba kallon tsaf kamataba xakace balarabiyar ce, soyayya takeyi itada wani dan uwanta mesuna moddibo,qaunace tagaskiya wacca basirki xuwan alh alhassan yay daidai datarwatsa musu duk wani buri dasuka ci narayuwa tare,alh alhassan yasakarwa iyayenta yayan banki nandanan suka manta da alqawarin auren moddibo, shikuwa alhassan soyayya yarufe masa ido yakasa ganin tsantsar qiyayyar da bintu kemasa burin duniya yasaka iyayenta murje ido tagama tubure tuburenta akai auren. Shekara daya bata rufaba tasamu ciki kuma har lokacin sooraj da hauwa wacca ta aura wani attajirin yayan abokin alhassan din alh auwal ya aureta,kuma sunada yarinya guda daya maisuna zahra'u awancan lokacin,suna qarqashin kulawarsa duka subiyu baya kyashin kashemusu konawane hakan yasa suke fantamawa cikin masu kudi kaikace suma yayan wasune,kuma sooraj yaqi aure yanaxaune ataredasu alhassan hakan yake dada qonaran bintu duk da itama ba abinda bayamata amma tana baqincikin ganin abinda yakema yan uwansa musamman datasan yan ubane, kuma har lokaci tadau aniyar tana haife cikin jikinta wanda takira dana qaddara xata wawushi abinda xata wawusa takashe auren,haka xalika ko hauwa taxo gidan setafito taita cimata mutunci tanacemata kwadayayyyi itada yarta hartaji haushi tadena xuwa saidai shi alhassan din yaje yana matuqarson bintu, wanda mutane ke kallon hakan matsayin tsoro dayakema matarsa anace masa mijin tace, musamman abokanansa aminai,prof Noor abdulfatah saikuma qawarshi aminiya wacca tasoshi abaya kmr baxata kyalesa ba hjy maryam gidado, amma abin beyiwuba saidai abota sanadin bullowar bintu cikin rayuwar alhassan. Kokadan basa qaunar bintu kwata kwata sbd itadin fitsararriya ce tabugawa ajarida wanda duk wanda ketareda alhassan yasan haka. Haihuwarta tafari tahaifa twin's duka maxa wanda alh yaso diya mace tahaifa masa kodan yacika burin mahaifiyarsa hakan yasa hauwa taqara janjikinta daga gidan dan uwanta ganin iyalinsa naneman rabata da dan uwanta duka. Bintu tacigaba da Karatu gidan alhassan inda tana final year nagama MSC dinta Allah yabata wani cikin lokacin twins nada shekaru daya taso tacire amman alh alhassan yamata alqawarin maqudan kudade indai tabarshi sannan yaqara jaddada mata Allah yasa suhaifa mace yasaka sunan mahaifiyarsa, tsaki takeja duk lokacin dataji yana irin wnn burin nahaifar yamace ita haihuwarma dabadan buri da kwadayin abinda xatasamu daga garesaba bayajja xa'ai ta haihu da maqiyinta,don har lokacin xuciyarta natareda modibbo,bayan haihuwar Anwar dakadan taqarasa makarantarta wanda take karatun electrical electronic tun wancan xamanin aiko nan tanuna sha'awar cigaba da PhD, Alh Alhassan fafur yaqi amincewa acewarsa sunfara tara iyali mexatai dawani boko tunda Allah yamasa arziqin daxe iya daukar duk wata dawainiyarta data yaransu uku,hakan yatada masifa babba tsakaninsu hartakaiga tayi tinanin hauwa ke zugashi taje taxageta tas hargida, Alh yanajin labari kuwa yaxo yatura bintu gida domin gargadi karta sake nangaba hakan yay dede da rasuwar mahaifin bintu nanma kuma yay dede dajin labarin cewa moddibo tsohon saurayinta narugar bubayero yayi kudi natashin hankali sanadin shanu dayake kiwo yanafita dasu qasashen Europe da suke sarrafa madara kala kala,tayarda dahankalin tatai da alh yaxo daniyar kome yasameta agidansu dake gombe wanda shiya saya musu, nan tashiga yimasa tsiwa tace inyacika dan halak cikin uwa da uba yasaketa inshi bamaye bane tagama aurensa aikuwa cikin bacin rai alh yadanqara mata saki har uku itako dadi kmr yakasheta tashigo gidansu tana sanarda mahaifiyarta tana kukan gulma,ko wata daya ba'arufaba moddibo yaji labarin ansaketa aiko yadawo nemanta dukda danginsa basaso sun san bintu badan Allah xata aureshi ba kuma sunsan shedar san abin duniya da akaima dangin bintu amma dake ba uwa ba uba bawanda ya iya kwabar moddibo ya aureta kuwa cikin qanqanin lokaci auren bintu, fakadan qanwar moddibo maisuna walijam tadawo gurinsu daxama sbd mijinta dayatafi yawan fatauci kuma gata da qaramin ciki. suna xaman lpy matuqa kasancewar bintu nasamun kulawa takowana bangare gidan moddibo,tafarar daya gidan gonar moddibo yayi gobara yayi asarar dabbobi nagaske sannan wanda suka rage sunji rauni mai tarin yawa karayar arziqi tafarar daya tasamu moddibo shikuma alhassan yaransa uku suka koma hannun hauwa daxama inda yay danasanin biyewa zuciya yasaki bintu kobanxa dai ai itace tahaifa su muhsin ko darajarsu taci,hauwa bayajja bataiba kan alh yadaure yanema wata yasake aura amma fafur yaqi daga qarshema tattarawa yayi yakoma abuja daxama yasaka twins atsadaddiyar boarding school tamaza dake garin shikuma anwar be isa makarantaba akabarshi gun hauwa. Bintu tatashi hankalin ta ganin takoma talauci tsamo tsamo nanfa tagane abinda iyayenta kedorata kai kullum cewar kudi shine jin dadi a aure bawai soyayya ba bata taba kawo xataji rashin alh alhassan cikin rayuwarta ba seyanxun ita moddibon ma yanxun salla masa rashin mutunci take sbd baya bata kudi nayau daban nagobe daban qanwarsa walijam nakallon duk abinda takewa dan uwanta sbd qaddarar rashi data samesa bintu tasamu ciki gidan moddibon inda memakon tarage sai qaruwar rashin arziqi wanda yadasawa moddibon ciwon hawan jini mai tsanani dayay sanadiyyar rayuwarsa. Mutuwar moddibon arayuwar bintu kamar wani farincikine datake jira tuntuni tahaifa santaleliyar diyarta mace akasaka mata hudallah,walijam taso abata riqon hudallah tarena tareda danta data haifa sa'an hudallah mai suna SAMEER amma fafur bintu taqi tace yarta baxata gogo talauci cikin dangin uba ba xatasamo mata wani uban wanda xasuci arziqi sumore. Prof noor ne yakawowa alhassan labarin rasuwar mijin bintu atinanin sama AJ dinyasani yake cemasa kada yasake yace xaimaida ita, kunnan uwar shegu yamasa adaren rnr yadebo su muhsin daga makaranta yace xakai su gurin umminsu sugaisa wnn karon hannu bibbiyu bintu tanuna wa alh ta amince damaganar auren kuma tayi danasanin abinda tamai abaya baxata kumaba,kuma qaddarar haihuwar hudallah cema qila taja rabuwar auren cewarta,alh cikin tausaya wa yake furta mata duk abinda xefito daga jikinta yanaso kmr yajja yake tsanin sonta yakarba hudallah matsayin yarshi kuma xeriqeta amana kmr yajja xewa su muhsin insha Allah.sannan kuma ya amince data dora da PhD dinta intanaso baxe hanata ba.
AYSAM Love,passion,hatred,betrayals and power between two different worlds. By Fatoums passion