AYSAM

Chapter 19

by @fatoumspassion

(Swimming comp) Dalibai ne suka fara fitowa daya bayan daya daga auditorium din gurin se hayaniya wasu students nata faman clicking pictures saboda kasancewar yau taxamo ranar dasuka gama jarrabawarsu generally tashekarar bayan mid term's da mid year's dasuka yiyyi wanda gaba daya ake hadasu guri daya gurin fitarda sakamakon jarrabawar, kowa kagani cikin farinciki wasu kuma tini sukai saman last floor na babban ginin makarantar domin kidane yake tashi tako ina alamun seniors suma sun kammala tasu jarrabawar zasuyi signing out,kowa yana cikin farincikin gama jarrabawar da yayi sai kuma dorawa da jarrabawar games dazasu yi cikin sati maizuwa haka takasance gurin qawayen guda hudu sune talk of IMPERIAL fitowarsu daga jarrabawar suka wuce hostel batareda kowa ya ankareba suka shiryo cikin wasu qananun kaya riga da wando na company din KC tsadaddu wanda guda hudun kacal akai shipping africa cikin shekarar saboda latest designer ne da american celebrities ke yayi, deep margenta kimono suka daura akai ba tareda sun daureba inda duk wani shape najikinsu yafita kamar susuka zana kansu,handbag's din channel kowacce tarataya iri daya seka rantse uwa daya tahaifesu daman meenah da meemee hakan take saidai mutane dayawa nawa dimple da lilly kallon siblings sbd fixge dasukeyi harta da bronze skin dinsu iri dayane lokacin dasuka qaraso theater din makarantar kusan kowa yashiga donjin orientation daza ayi na interhouse sport din domin IMPERIAL abuja bata fiya shiga interschool competition ba gani suke yi kaf naija bakalar makarantar datai sa'a datasu saidai makarantun south Africa dasu suke karawa inzasuyi. "Wow,hot babes,amazing,wonderful" kakeji anafada shikansa qamshinsu nadaban ne wanda dimple tai tai kada sufesa turaren suka mata kunnan uwar shegu shikansa director sai murmushi yake yana yaba kyawu da ajin yarannasu sameer nacan qarshen corner din theater din daga baya,shishi kadai domin shidin ba mutum bane meson taran jama'a dayawa Musamman yanxun dayake general assembly ne na junior class sukenan da sophomore year sai yan manyan aji dasukai grad ayau duk da makaranta bata sallamesu ba amma za'ace yauce ranarsu taqarshe narubutu da biro datakarda a IMPERIAL, dimple wurga ido kawai takeyi tanaso tahango sameer din amma takasa harseda Meenah talura taja tsaki tana furta "malama kinfa isheni da waige waige" harara tagalla mata domin tunda ranar datai befriending sameer meenah kebata wannan attitude din itakuma dede take da ita daya yakasa jan daya anagama orientation din head prefect yafito saitafi domin TA din mutum ne nakowa amatsayinshi na president din IMPERIAL gaba daya bayada girman kai ko jiji dakai kowa nasane bayanin bankwana yafarayi wanda jama'a dayawa saida sukai kwalla domin qila insun tafi ba lallaine asake ganin junaba,ciki kwa harda su dimple akwallar domin TA nadaya daga cikin sirrin nasarorin ta a IMPERIAL,shine personal tutor dinta wanda popsy dakansa yahadata dashi sbd yawan fashin school datakeyi duk abinda tai missing har gida yake biyota yakoya mata lallai zatai missing dinsa gashi daman shidin dan port Harcourt ne kuma yace mata can xe koma bayan grad dinnasu, harbata ankareba director nafita seniors suka saki DJ aiko ansha rawa,su Samar inaga kida sune kan gaba miqewa tai su Lilly ma suka shiga aiko charaf tana musu video tahango sameer can ya lumshe ido tunsafe dasuka hadu before exam se yanxun take ganinsa tini takashe video tatako ahankali zuwa inda yake,tace "hey SAM," dagowa yayi yana kallonta fuskarsa bayabo bafallasa yabi yakayan jikinta dakallo wani irin abune yatokare masa qirji ganin abunda yaci karo dashi yalumshe ido kansa nasara masa atake anan mehakan kenufi yatambayi kansa,qara matsowa daf dashitai zata kai hannunta jikin wuyansa wai taji temperature dinsa dasauri yadago yana watsa mata idanuwansa dasuka sanja color yace "don't touch me" yana miqewa yaraba gefenta yawuce binsa tai tana kiran sunansa bawanda yalura sbd kidan dake gurin se xahra wacca hankalinta kekan sameer din tundaxu domin itama taje tanai masa kanainayenta ya yarfata tadawo ganin za'a yarfa dimple itama yasa tai saurin binsu tana kunna wayarta daniyar video domin idan kana neman gulma a IMPERIAL xahra ce lamba daya a munafunci tana sunkuyi dakai bawanda besan halinta ba, Aqofar hall din dimple tai nasarar fizgo hannun sameer da iya qarfinta yatsaya domin baxa iyayin sauri tabishi inda yakeson zuwaba da takalmin qafarta me shegen tsini,juyowa yay zemata magana idonsa yaqara sauka kan zanan niyar qirar jikinta wacca tahargitsasa tun shigowarsu gurin, "SAM what" tafada cikin fada fada "mekuma namaka dazaka min haka" tafada tana kicin kicin da ido,hannunsa yajanye anata qala bece mata ba yafara matsowa daf da ita, "SAM what are you......." kasa qarasa tambayar data dakko tai sakamakon jin yariqo waist dinta zuwa jikinsa hannunsa nayawo abayanta igiyar dataiwa tufkar ribom abaya ta kimono dinta yakeson kwancewa,numfashinsa nasama daqasa awiyanta sakamakon bugun zuciyarsa dake wani tsere kamar zata faso qirjinsa tafito itakuwa qamewa tai tama kasa katabus zuciyarta nahar bawa amma ba irin harbawan ciwo data saba jiba wannan yana tafene dawani shauqi da kadaicin irin wannan kusancin da aduk rayuwarta bata tabayi dawani wanda yayi affecting dinta kamarsa, ahankali taji yajanyo igiyar xuwa gaba yarufe mata qirjinta darigar ciki tadame tabayyana harshatin bra dinta ana gani yadaure mata tayajja ba inda yafito ajikin ta p cap dindake kansayacire sakamakon ko dankwali babu akanta sewata tsadaddiyar baby bandana dasuka saka su duka gashinta dake baje awayanta yadaure yatura cikin hular yadago yana kallonta ido cikin ido kafin yace " the beauty of Moon does not change when covered by clouds,just as the beauty of woman remains covered, muslimah check list before leaving home No perfume No make up No tight clothing No high heels No ornaments Proper hijab Aysh fadamin shiganki dame yayi kama,kinyi kama da abunda sunnah ta lissafo gameda diya mace yafada yana dage mata gira,girgixa kai tai yace "kisani Aysh duk wani abu maitsada da daraja boyeshi akeyi amma kekina revealing wa kowama yaga sirrin kyawu wanda aka umarci kikallace kowama yakalla bakiji memaxa kecewaba akanki,hot,sexy,and......" kasa qarasawa yay yana juyawa yana dan yarfar da hannunsa,yaqara facing dinta yana furta "this is not right bawayewa baceba abinda kuka aykata suma friends dinnaki ki sanardasu imbasu saniba," juyawa yayi xetafi ahankali tafurta " SAM" yajuyo yana kallonta tace "thanks for telling me the truth,kuma in sha Allah zangyara nidasu Lilly gaba daya," smiling yay yana furta "you're most welcome," sannan yace "xanje garden nasha iska banason kidan wanna join me?", ta daga kaida sauri tana qarasawa inda yake suka fara jerawa zahra datai suman tsaye agurin kasa motsi tai tana zazzare ido sameer nakishin Aysha mehakan kenufi duk abinda takeso arayuwar ta dimple ce kesamu lallai yanxun taqara gasgata abinda hudallah kefada mata koyaushe akan dimple din cewwar itadin threat ce mafi girma arayuwar duk wanda kekusa da ita xatai duk yajja tai tamallake duk abinda taga kanaso itadin snatcher ce thief na farincikinsu, kwafa tai tanafurta "ya kuma isa haka inkin kwace kowa a family nabarki sbd babanki nada kudi banda sameer" takalli video din data dauka dayay looking like dimple da SAM na having romantic moments tace "bari muga inna nunama ubannaki me goyamiki baya wannan abin inxe cigaba da biye maki kiqarasa lalacewa" tawuce abinta tana murmushi. Kwanciya sameer yayi qasan tsaftataccen grass carpet din dake garden din yasha gyara kansa asama yanajin dadin iskar yammacin dake kadawa,dimple ma kwantawa tai adannesa dashi gefensa tana kallon sararin samaniyar kafin tadan juyo gefensa tana kallonsa shima gefen yajja xeringa kallonta yajuyi ba abinda suke yi sai sauke Zazzafan numfashi suna aikama dajuna murmushi,ahankali taji yace "I'm sorry" dan far tai da ido abinda yasashi lumshe ido kenan wanda ita har ga Allah bada wata manufa tai ba illa hakan yaxamo kamar dabi arta in akabata mamaki, tace "sorry for what?" yace " i was a little bit harsh on you earlier," smiling tai kafin ta kalli p cap dinsa dake kanta ayanxu tace "shikenan sena riqe wannan" tana nuna hular "amatsayin token of apology " dariya yayi for the first time dataga qerarrun fararan haqoransa awaje har wata qaramar wushirya gareshi asaman haqoransa wanda bata taba lurada itaba sai yau din,yace "shikenan inna baki p cap din kin haqura", "Uhm" tabashi answer tana smiling yace "you own it now." Dimple taji anfurta kamar daga sama wazata gani leo ne atsaye shida gang dinsu kowanne sanye da wasu tsaddaddun qananan kaya sunyi wata shegiyar aski daman ba yayan musulmai ba, dasauri tatashi zaune tana kallonsa adan firgice shima kallonnata yayi cikeda takaici yake furta "daman abinda akefadamin akanki gaskiyane keda wannan matsiyacin wanda tsiya tamai katutu," zabura tai tana furta "how dare you?are you stalking me" yace " I'm doing more than that sbd kedin tawace Miss Aj,i own you kaikuma" yafada yana juyawa ga sameer bakaji dukan dana makaba wancan lokacin kaqara shiga gonata ko, "toh yau zankasheka inga ubanka waye dazai tsayamaka inkasheka inkashe banxa bame taba ni banza mara tinani kawai kekuma zanhada dake don yaxama gargadi ga duk me sha'awar hada inuwa dake amatsayin sa nada namiji bawai zanbar IMPERIAL Kiyi tinanin kinsamu yancin kankiba,zankoyamaki hankali" gadan gadan yayi kanta aiko sameer yashiga tsakani yana furta " karka soma," Cikin gadara yake furta "kaika isa kahanani abinda nai niyya matsa a way dina kona illata ka," "what's going on here ?" suka tsinkayi muryar TA dinsu wanda yasa leo shiga hayyacinsa domin bawanda baya ganin mutunci da girman TA din sbd shidin mutum ne mekame wa dasanin yakamata,kallon dimple yay yana furta "Miss AJ meke faruwa inatambaya?" dasauri tafurta "Its leo senior, he's harassing me and SAM" kallon leo yay yana furta " kai har abada bazaka ringa riqe girmanka ba ko dimple kuje kunji I'll take care of this," tace "TA pls make sure beqara xuwa inda nakeba inba haka ba I'll tell everything to popsy kuma kasan abinda zebiyo baya ko," yace "nasani dimple xe Iya affecting duka IMPERIAL gaba daya," tace "good" tanajan hannun sameer leo naji yana gani suka bar gurin aqofar hall suka tarar dasu Lilly senemanta suke yi kuma wayanta najaka,Lilly kefada "kinga dimple popsy yata kirana yana tambayar ina kike yana kiranki bakiyi picking up ba se qarya kikasa ka namasa" yace "kije gida dawuri imba hakaba xezo dakansa " tace "what inje gida kuma is everything OK" Meenah ce cikin bacin rai take furta "wakike tambaya sanda kika tafi wani kikafadawa," wani kallon banza da Aysha tawatsa mata yasatai saurin furta "Miss Gabby fa najiranki kitafi gida karya sake kira," xuwa tai gabanta tace " meenah avoid me the next time kika ganni sbd I'll be harsh on you." Juyawa tai tanawa sameer bye tatafi.

bangaren popsy tafara xuwa guard dinsa suka sanar mata ai yana gefen hjy takoma mota sukayi bangaren ummin a qaramin parlor tatarar dashi canciki yana xaune shida Mr bunyamin yana duba file's din sameer da aka kawo masa jiya,gefe guda yaya hauwa taxuba tagumi tana kallon qofa da alamar jiran shigowarta take aiko tana shigowa tahauta da nasiha wai ashe makarantar datake zuwa kenan shiwannan video din da'aka turo musu a group din family meye hadinta da naciki, kallon mamaki tabita dashi kafin taxauna tana furta "wana video" miqa mata wayarta mama hauwa tai tana furta "gashi gani kiga,meye hakan dakukeyi keda wannan din kuma waye shi," straight ko dar tace "his my friend popsy sameer nefa nafada maka wayeshi ince" ko se asannan yadago cikin tausasa murya yake furta "mamana waye sameer acikin zuciyar ki?" tace "popsy you too," yace "pls dimple let's not argue nayarda da abinda meenah takirani tafadamin randa nadawo cewar you are in love sbd abinda video dinnan yanuna kenan," tace " popsy wai wana anna mimin ne yaturo video dinnan ma group," Yaya hauwa tace "xahra'un gidan babanku surajo ce taturo seta goge nikuma daman kudrat tasaita min wani wasup waishi GB shinefa nawa begogu ba," tace "mama dams zahra fa daman munafuka ce so tana bibiyatane daman amakaranta ko," yaya hauwa cikin jimami take furta nima dai haka nagani uwar muminai mesunan nana aishatu tana janyota jikinta cikin salon makirci natsaffin duniya, AJ smiling yay yanajin dadin kulawar datake samu daga gurin sister din tashi,yace "wato yaya hauwa kareta kike ko" cikin nuna kara daya koya nunawa akan ayshan in yayarta tananan, tace "toh immadai masoyinne meye aciki ko uwata kamata yayi kikawoshi musheda," daure fuska Aj yayi katamau yana furta "yaya pls banda wannan dimple din har nawa take," dimple miqewa tai daga jikin yaya hauwar taqarasa gefen popsy din nata,taleqa fuskarsa tana furta "popsy kishi yakeyi karnaso wani dayawa" itada yaya hauwa suka sheqe da dariya kafin yaya hauwar tamiqe tace " tatafi girkama uwarta abincin larabawan data fiso" tawuce sashenta,Mr bunyamin ma sallama yayi da Alh yawuce yarage saura su biyu,kallonta popsy yayi yanafurta "meye genotype dinsa" yana basarwa zaro ido tai tana furta "popsy kaima,"tana dariya,shima dariyar yake, file din sameer din yamiqo mata yace "nasan komai gameda shi harta da earnings dinsa monthly nasani yanada part time Jobs both kano danan shine first born in family dinsa,shidin native din bubayero ne kinsan me hakan kenufi" tace " a ah " yace shidin kusan family dinsa nada alaqa da mahaifiyarki,cikin mamaki take furta tayaya yace "moddibo gidado bubayero da mahaifiyar sameer wali jam............" meke faruwa anan sukaji anfurta daga ciki,ummi ce tafito tana kallonsu,dasauri yake furta "nothing" yana daukar file din dan yasan dawiya umminta ma yarda tasaurari shirmansu shida diyarsa,karbar file din dimple tai tana murmushi tace " popsy zanjiraka asashenka we have alot to discuss" yace " OK ganinan" Wucewarta tai tafice itakuma ummi tatsaya tana yiwa Alh kallon tuhuma tace " gani bare ko baza'ai tattaunawar agabana ba ko Alh," smiling yay yana miqewa yace " waye yamaida kannasa bare" yadora dacewa " nixan wuce saida safe kuma in kinsamu lokaci ran Monday dimple xasuyi competition dinsu na swimming,sun aikomin da invitation naduka family din inzakije," zamatai tana furta "nima inada meeting a asokoro dawasu yan ghana zasu siya kayanmu" girgiza kai yay yana furta "Allah yakiyaye hanya bint tunda meeting yafi farincikin diyarki" yaficewarsa sarai tasan yaji haushi amma ko aqasan silifanta. Asashensa yasamu dimple tanata qara karanta profile din sameer din,dasallama yashigo ta answer yazauna gefenta yana furta " toh fadamun daga niseke ne anan bamejinmu se Allah,do you like him?" yaqarasa yana smiling,rufe fuska tai tana furta "ni Allah popsy kana sani jin kunyafa", Yace "kunyar me I thought nidin friend dinkine,kokuma kinfison nakira yayanki Arsal nafada masa" dasauri tagirgiza kai tana furta " Nidai karka kirashi jiyama fa saida mukai arguing da shi akan SAM din da dare," Yace what?why? Tace " bashine yake cewa wai infita harkar kowana namiji ba kullum haka yake his over protective popsy," nutsuwa yayi tayajja xata fuskanceshi sosai yakamo hannunta yana furta, "Mamana Arsal ma mutumin kirkine and he love's you more than yajja yakeson kansa kinsani," dagowa tai tana gyada kai alamar eh, yace "mamana kinason Early marriage ne,senakirashi yadawo" Dasauri tazaro ido tana furta "popsy nifa ba soyayya mukeyi da yah Arsal bafa,shidin kawai yayana ne kumafa ma his too old for me,sa'ansu yah muhsin ne fah,kuma shima betaba cemin yana sonada aureba," yace " maamana,Arsal is my choice kije kiyi tinani kitsayar da matsayin sameer azuciyarki shida Arsal wanne kike ganin zaki iya rayuwa da,you have all the time you need kinji dimple dina," dariya tai tana sumbatar yatsunsa tace "ni popsy zan aura kawai banason kowa, sameer is not my boyfriend kakwantar da hankalinka kaji abun alfaharina," yace " my princess come here" yajawota jikinsa yarungume qaunarta naratsa dukkan sassan jikinsa,yanaji kmr yan kwanaki suka rage masa da ita sosai yakeji ajikinsa kmr baxe rayu da ita nahar abada ba. Monday morning abubuwa dayawa sunfaru cikin weekend din ga both Aysha da Sameer adaddafe sukai sbd kewar juna dasukai gashi kowanne nada number dan uwansa daya dauka a group amman kowa naji dakansa cewar kar yakira dayan yaji wani abu musamman ma ga Aysha saida qyar Lilly tahanata kiransa cikin weekend din suna tahfiz amma hankalinta baya kan karatun se latsa waya takeyi wai taga ko Miss call dinsa ne xata gani,Lilly kam se nasiha da lallabi take mata kan dimple din taringa jannata ajin domin tacigaba da mannewa sameer din haka ze iyaji ta takura masa koma yatsaneta lokacinda Lilly kefada mata hakan zaro ido tai tana girgiza kai "ah'ah bazan kirashiba toh,baxe tsaneni ba Lilly ko,zanke jan ajin nadena nuna masa komai," haka taringa lissafawa Lilly irin azabtuwa dakewarsa kasancewa batareda shi, Lilly kam murmushi kawai takeyi domin tasan aminiyar tata tariga tafada tarko mewiyar warwarewa tarkon soyayyar S Fulani wanda tafaraddaya yamata dauri mewiyar kwancewa,sannan da fata fatan dasukai da meenah shima cikin weekend din kan kai qaranta datai gurin popsy akai baran baran amman dare nayi Meenah takira dimple tabata haquri kan tadena itakuma dake batada da ja'inja nanfa tayafe, hannunta saqale dana popsy suka shigo swimming pool stadium din ga professor agefen hagunta su Lilly natake musu baya for the first time dazasuyi competition tashigo sanye dawani babban hijab design din oman ne kana gani kasan ba ordinary hijab bane shikansa yadin da akai amfani gurin dinka hijab din abin kallone tanada iri iran hijaban dayawa agida kala kala wanda bakowa kesiya mata suba se yayanta anwar donshima yaqi jinin yawan fidda tsiraicin da takeyi amma duk dahaka inyabata xata karba tajibgesu a closet sedai tai sallah dasu kawai,kota bayar dasu,yau kam tadau dammarar farantawa sameer tahanyar rufe jikinta ruf ko swimming suit dinta yau dogaye tasaka wanda suka rufe mata Ko'ina da ina najikinta, VIP resort su popsy din suka zauna can sama susu kadai tana iya hangosa inta daga kanta, Student kam kowa sanye yake da different swimming suit na house dinsa wasu harda ganguna wasu kuma zanan sunan gidajen nasu akai masu temporary tattoo ajikinsu,two minutes to start abunda commentator din yafada kenan duka representatives na house's dim suka yo gaba, "Miss AJ Alhassan Aysha Miss AJ sooraj xahra Miss laika..........." hakadai akaita kiran sunayensu suna taking position dinsu,sameer tahango yana facing dinta,murmushi yasakar mata itama tamaida masa yana tafa mata cikin dan daga murya tayadda xata jishi yace "AYSH make us proud tiger house up" yana daga mata hannu dariya tai domin yajja yake maganar kana gani kasan besaba hayaniya ba yayine kawai don yafaranta mata whistle din akabusa aiko seqarar fadawarsu shiga ruwa ake ba abunda kakeji sai sunayen participants dinkowana house nakiran nasa, "dimple dimple dimple," "laika laika " haka dai suka ringa cheering nasu cikin sa'a dakwarewa dimple ce mutum nafarko data fara juyowa harta kai Saura qiris zahra tawuceta tafara gani sama sama tajiyo muryar sameer yanafurta "you can do it Aysh,you can common," dawani irin mugun speed dabatasan tana dashi a swimming ba taqara sa tana fitowa aruwan aiko se ihu masu murna nayi masu barinciki nayi,squad dinta kam dako tsalle sukai akazo aka rungumeta basu damu da jiqewar dajikinta yayi ba aiko se sunanta ake kira kamar kowacce shekara yauma bata sauya zaniba dimple Aj ce tai nasarar lashe gasar swimming ta IMPERIAL SCHOOLS, Samar kam qarasowa yayi yana miqamata towel medan girma don tagoge gashinta har zata warware seta juya takalli sameer wanda shidinma ita yake kallo yaqaraso da ido taimasa alama kan cewa tawarware kallonta yay kana yajuya yana ganin jama'ar dake gurin tabbas baxe bari suga gashin taba ana haka professor yafito aka kirata ita datai tadaya da laika datai nabiyu se xahra datai nasarar xuwa ta uku, bathrub Lilly tasanya mata tana yafa nata towel din akanta,aka gaiyaci babban soja Marine general Ahmad mammada don yafito yakarramata yaqaraso kana ganinsa kaga Meenah da meemee saidai farar fatar da zasu nuna masa shitasa ta kode ayawan yaqe yaqe dakashe kashe, yarataya mata gold medal din yana miqamata trophy dinta na gold shi ma me shape din kifi, smiling take tayi tadaga sama tana murna,microphone akabata kotana da wani abun cewa karba tai tana magana cikin harshen turanci, "wannan nasarar batawa bace nikadai baxan taba kaiwa inda nakeba batareda support dinkuba gaba daya Cheer's to tiger house duka,I'm so proud of you guy's thank you" tana qarasa fadin haka tasakko da gudu gudu sauri sauri tai sama,allon talabijin nabinta kobaka hangota xaka ganta ta TVs din dake gurin gaban popsy din nata tatsaya wanda se alokacin talura da ya muhsin da alama shima bedade dazuwa ba trophy din tadamqa masa tana furta, "this is for you popsy" tafada ajikinsa tarungumeshi shima hugging nata yay yana furta "I'm so proud of you my princess," gurin se ihu nandanan videos din suka fara yawo a social media, AJ dake wiyar gani sekai wata da watanni kake iya samun appointment dashi anganshi ataron makarantarsu diyarsa abin yabaxa ko ina kowa na admiring tsananin son dayake yiwa diyar tasa, abin yanata trending comment kala kala, Bayan tashiga tasauyo kaya xuwa wata deep red Turkish gown tadan saqalo mayafin gown din asaman kanta sai murmushi take kowa burinsa yadau hoto da ita, xahra nazaune gefen pool tana kallon silver trophy din da akabata tana zubda hawaye,dafata taji anyi tadago adan firgice tana kallon kamillalliyar fuskar uncle din nata tace " uncle," yace " xahra na lafia kike zaune anan kinyi shiru ina family dinnaki," kasa riqe kanta tai tafashe dakuka tana furta "uncle ban gayyaci kowaba sbd nasan baxan taba ciba akullum dimple ke nasara akaina,shiyasa ban gayyaci abbana ba sbd inyaxoma zagina zeyi, yace nabar ta sbd sakarci tayi nasara nina fadi," Alh AJ har zuciyarsa maganganun yarinyar sun tabashi amman yasan balefinta bane sooraj ke daurata akomai akan tsanar daya yiwa diyarsa dimple tunda yakyalla ido yaganta aduniya taxama mafi soyuwa agurin dan uwansa yake nuna qiyayyarsa ga yarinyar afili amma yanxun meye amfanin saka xahra cikin wannan kudirin nasa,Alh nisawa yayi yana furta "you never failed xahra wayace miki kedin kinfadi kiduba kiga tarin daliban dakika bige kikai na uku,ita dimple din da tai nasara kisani bawayanta ne yasaka tayi ba Allah ne kawai yabata kinajina,kuma itafaduwa kanta nakoyar damu wani darasi cewar bakomai muke nema musamu ba aduniya failure is part of success my child,sassauta kukan nata tai tana furta "uncle kuma yanxun su dimple zasu sake fara making fun of me cewar parents dina basuzo ba banada kowa da yakesona," yace "xahra baganiba idan ba sooraj wakeda haqqin kula dake kinada wani bayanni ne abinda nakeso kisa aranki cewwar wannan dimple din datai nasara nima nawa lokacin zaizo kinji kuma itadin yar uwata ce yakamata intayata murna ko," tace "Toh uncle nima xandau hoto dakai insaka a social media ta donmasu cemin nidin yar kalar danginka ce sudena," smiling yay yana furta " wa ya isa yace kedin ba jinina baceba xahra," tace " ba dimple da qawayenta bane suke zuwa sunacewa mutane nidin yar kalar dangice" murmushi yay sarai yanajin zafin sukar datakema diyarsa amman yanason alaqarta da ita tagyaru ko yayane sbd koba komai sunan jini daya ne uba daya yahaifa mahaifansu suke amsawa,sameer dake gefen pool zaune tabayansu ba abinda bejiba akan irin kwantar dahankalin xahra da Alh Aj yayi. tabbas shidin mutumin kirkine yafada azuciyarsa,bashida girman kai kodagawa ya ayyana aransa yajja mutane ke qissifashi sam bahaka yake ba, dimple yahango tana tahowa inda mahaifin nata yake batareda talura dashi ba ganin suna daukar hoto da xahra yasa tai kicin kicin da ido tana fixge wayar xahra,raurau xahra taida ido dontasan ba makawa dimple goge hotunan xatai sameer daya miqe tsaye yatsaya yana kallon mamakin qarfin hali irin nata, "inace shidin ba babanki baneba daxa kisa sa agaba kina daukar sa hoto da banzar wayar ki," kallon popsy tai tana furta " popsy wannan dakake daukar hoto da ita xahra ce uwar gulmar makarantarnan itace tadauki video na da sameer don tsabar munafunci kina saita wannan glass din fuskar naki amma sekinyi gulman wani," "Dimple" popsy yafada da kakkausar murya dagowa tai tana kallonsa ranta ahade domin wallahi yace Xehanata goge hotunan nan ruwa xata jefa wayar aishi din ba baban xahra bane popsy dinta ne itada yan uwanta kadai, Yace " my dear kiyahaquri kibata wayarta kinji wannan karon cikin sassanyar murya mairatsa zuciya,yacigaba "kitinafa yau ranar farincikinki ce kuma xahra babare bace she's your cousin sister" tura baki tai tana juya masa baya juyo da ita yayi sarai yasan halin abarsa yazare wayar ahannunta yamiqama xahra aiko wuf tai tawuce tana masa godiya,shiko Alh rarrashinta yacigaba yana nuna mata tasassauta qiyayya datakewa xahra kodan darajar zumunci, still fuskarta bayabo ba fallasa tace "toh taji" rungumeta yayi aiko charaf idonta yasauka kan sameer da yajuya xetafi tace " laaaa SAM" juyowa yayi yana dan kallonta taqasan ido popsy ma juyawa yayi suna facing each other fuskarnan tasa mecike da haiba da kamala tadattawa sameer yakasa hada ido dashi. Kubiyo mu next chapter donjin yajja xata kasance AYSAM daban yake,tafiyarsa daban take salonsa ma dabanyake bissalam Pls comment and share AYSAM AYSAM Love,passion,romance,betrayals,and power of two different world's. It's Fatoums Passion.