Chapter 21
(The real champion) Bude kwalin dayasha hadaddan packaging yayi yana fitoda tsadaddun wayoyin da ke ciki, The Goldvish Revolution, manufactured by a Swedish company called Goldvish, is the 9th most expensive phone in the world. It was produced with 29 VVS-1 graded diamonds and 18 pink and white gold carats that cover most of the body, making it one of the most expensive phones in the world. Wani ihun murna dukkansu suka buga wanda yasanya Alh toshe kunnuwansa,yana smiling, raba musu Mr bunyamin yafara yi nanfa sukaita godiya,bawanda ba'abawa ba banda dimple wacca tun last year tagama yayin tata designer phone din irin wannan,Mr bunyamin ne yakalli Alh yana furta "guda daya tai saura ba mutum dayan dana qirga dashi dazu," Kallonsi Alh yayi yanafurta who's missing dasauri Aysha tace "Mr bunyamin, kawo xankai masa,sameer ne kuma yatafi" Takarba wayar tana smiling, Samar ne cikin jin haushin nuna kulawar dataiwa sameer din,yace "Alh aiseda mukace yajira yaqi yayi tafiyarsa, Zaro ido Aysha tai ganin Samar ze shafama sameer baqin fenti na rashin jin maganar nagaba wanda tasan halin mahaifinta sarai da murdaddan iko da rashin son raini sarai, "Kai Samar karinga jin tsoron Allah tafada tanadan zare masa ido sameer dinda saida yayi sallama dani kafin yatafi yafada mun uxurinsa" tana qarasa fadar haka muryarta nadan rawa sbd qarya ba dabi'ar ta bace ba tamiqe tana furta "popsy ni bacci xanje nai nafara jin jiri" kodamar sake wata maganar bata bawa popsy dinba tai wucewarta daki, takwanta tana sakin nishi ta lumshe ido wayarta dake kan bed side drower tasa hannu tadauka tashiga group scrolling no dinsa tai,Sameer S Fulani sunan dake profile dinsa kenan, Profile picture dinsa kuma hotunan wasu atamfofi ne da laces anhada logo dasu jikin logon anrubuta,S Fulani textiles and more,aranta tace kodai shine small online business din dataji ance Sameer nayi kayan mata yake siyarwa wani irin murmushi tai sbd wata idea datazo mata duk aburinta naganin tashigewa sameer din,danna number sa tai taruntse ido tai dialing aiko nanda nan tafara ringing kamar duk ringing din datake yi da bugun zuciyarta yake qarawa daf dazata tsinke shidake daya bangaren dawani irin bacci me nauyi yadaukeshi yay picking atinaninsa moon ce yabalbaleta da masifa don ita kemasa wannan muguntar tashi sassafen, Sallama yay,jim kadan yaji anyi shiru yacire wayar daga kunnansa yana dubawa,number ne kawai basuna irin special numbers dinnan masu digits daya,ras gabansa yafadi donshi sarai yana kallon number dinta sau daya wayar Samar yadauke gaba daya akansa, yiyay kmr besan mekiranba, yace "hello waye?" kasa cewa komai tai sbd kwarjini damuryar nasa taimata, "ok lemme hang up now,tunda bazakiyi mgn ba," dasauri tace "toh a'ah nifa daman cewa kawai zanyi yakaje hostel din,kumama........" Saitai shiru Murmushi yasaki maisauti daga nasa bangaren yace, "toh naje lpy harna kwanta kinyi disturbing sleep dina" cikin tsokana wanda ya kanyita lokaci zuwa lokaci inyan quruciyar nasa suka motsa amma bakowa yakewa ba, tace "au nadameka hakama zakace ko,yama akai kasan nice did you have my number nadaisan bantaba kiranka ba," taqarasa tana danjan maganar cikin shagwaba, Lumshe ido yay baccin naqara nuqurqusarsa,yace "toh batashina kikaiba aibanyi qarya ba,number kuma nagantane gurin Samar" dasauri tace "shine kakarba," Yace "nop,ina gani kawai once ya wadatar special ne me digits daya," sosai taji dadi dajin wannan furuci nasa domin kuwa kobe fadaba directly tasan yahaddace no dinta, Tace "zaka shigo IMPERIAL yaune," dankarkata kai yayi kamar tana gabanta cikin narkar damurya yake furta "noooo,yau table tennis competition za'ai nidin bason wasannan nakeba,xankwanta nahuta kawai tunda jiya kinhanani baccin dare," bata fuska tai tana furta "kaikuma saikai disobeying maganar popsy kai tafiyarka bayan yace kujira kuyi breakfast," miqewa zaune yay yana furta "ni yaushe waya fadamiki,Aysh sharri kuma kika koya," tace "bawani sharri yau dabadan nashigar maka ba datini kashiga blacklist din popsy na kasan yajja bayason arainashi kuwa," yace "Aysh I'm sorry I never thought haka abun yake nadauka dayace sujira dasu Samar yake sbd kinga su almost all of them are like family to him,saida natambaya Samar at time din yace min i can go since I'll not be comfortable staying," aranta tasan dawata aqasa kenan Samar yana sane yasaka sameer tafiya don yanuna shidin yafishi a idon popsy aiko zatai maganinsa,amma afili tace "karka damu Sam nagyara komai ai popsy na yanada fahimta,and i have a surprise for," cikin sanyi da jikinsa yayi akan maganar mahaifin nata yace "What's the surprise?" tace "I won't tell you sai goben in Allah yakaimu bye" tafada tana kashe wayar,tana kyalkyala dariya barcin da sameer be komaba kenan sbd yanaso yasan meyafaru acandin da Aysh tace zeshiga blacklist din babanta. Samar yajira yadawo aiko tun abakin qofa yatareshi da maganar, Yace "OK har ta kiraka tafada maka kenan,toh kai ina ruwanka don Alh be sokaba semeye ne saikace wani sirikinsa kuma bagaskiyar nafada ba ai agabanka yace ajira," yace "amma aida nazo nacemaka zan iya tafiya cewa kayi eh if I'm not comfortable," yace "toh mekakeso nace na lallaba ka gaka dab gwal ko,toh bari kaji after last night ni dakai basauran ragawa ko tausayawa irin ta abokai sameer tunda sbd kaine takasa bani lokacinta ma har insanar mata sirrin dake raina kajata backyard ina kallonku kuna fira kome kuke cewa oho," mamaki ne yasa sameer daskarewa anan me Samar ke nufi meyadau alaqarsa da AYSH, dorawa Samar yayi yanafurta "bakaga abinda ke idanuwanta ba,kokai makahone,idan aka kira sunanka wani irin bright smile ne ke fitowa a face dinta, yaudin agaban mahaifinta tatashi tai depending dinka all because of what Sam kakasa ganewa,dogon numfashi yaja kafin yariqo kafadun sameer yana furta congratulations dimple is in love with you," yaqarasa yana juyawa ya ficewarsa adakin yana doko qofar data dan firgitar da sameer tunda yake shida Samar wannan ne karo nafarko daya daga masa murya haka arayuwarshi duk da Samar din yagirmeshi amma betaba treating dinsa badly ba tunda yake arayuwarsa sbd yadauke shi aboki kuma little brother dinsa,dimple is in love with him this is impossible baze i yuwuba kawai misunderstanding ne irin na samar da kishi kuma daya rufe masa idanuwansa, me dimple zatai dashi meze bata bashida komai wanda ze iya offering shidin bedace da itaba only Samar deserves her tayama za'ai yace dimple nasonsa,ganin tinanin na neman haddasa masa wani irin mugun ciwon kai yasanya yajuya dasauri yafada kan gado yanajin wani zafi na caccakar zuciyarsa. haka yawuni cikin wani matsanancin ciwon kai mezafi girki ma yakasa tashi yayi ko sallah yau kasa zuwa yayi Samar kuma betashi dawowa ba ma sai qarfe dayan dare kotakan sameer din bebi ba yay kwanciyarsa damugun zazzabi daciwan kai sameer din yakwana,gashi washegari zasuyi basketball kuma shine captain din team dinsu. Da asussuba Samar yafarka sbd sabon da sameer yamasa natashi sallar asuba duk kuwa da uban barcin dake kansa shima bayan yashiga yadauro alwala yafito har zewuce mosque yaga sameer betashiba wanda akullum shike tashinsa yana mita haka xe sashi agaba suwuce mosque, qarasowa yay saitin gaban gadon sameer yadan fara bubbuga gefen gadon sameer sanin S fulanin bashida dogon bacci,jin tsit yasa shi yaye blanket din da Sameer yarufa dashi, wani irin mummunar faduwar gaba tariskeshi ganin halinda sameer din keciki yadafa goshinsa sai rawar sanyi yake yana ambaton sunan Allah wani irin daci zuciyar Samar tai ganin halinda abokinnasa yakwana batareda kulawarsa ba wanda inshine baida lafiya,haka yake kwantawa yalangabe yayta wahalar da sameer din yana bashi order, Yace " S Fulani sannu meyasame ka,I'm sorry" Cikin zafin nama samar yada goshi yana jingina shi jikin gadon, yakasama tsayawa dakansa sai da Samar yasa pillow abayansa,ahaka yaringa kula dashi zuwa mosque din dabeba kenan yana jin haushin kansa da kansa na banzatar da sameer din da yayi sbd sukadai ne family dinjuna awannan gurin daba uwarsu ba ubansi sune gatan juna dakyar ya lallaba yatemakawa sameer din yasha tea kadan yakira doctor har dakinsu yazo yaduba shi allura yamasa straight sannan yace " in sha Allah nanda 1hour zedawo hayyacinsa duk daba lallai qarfin jikinsa yadawo ba sai ahankali," rasa abinyi yayi gashi tundazun coach yaketa kiran wayoyinsu shida sameer din yakasa dagawa besan meze ce masa ba. 8:30 pm basketball stadium din yacika maqil da students harma da parents ciki kuwa harda Mr and Mrs S Fulani dasuka xo don hukumar makaranta ta aika masu katin gayyata kamar yajja take aikawa kowana iyaye ranar da danka ko yarka zasuyi participating agasar tunjiyan suke neman layin sameer sunkasa samu, duk Ammi dinsa tabi tarikice ganin dalibai dayawa sunata harkokinsa batai tozali danata danba, kowane house sanye suke da jersey din gidajensu both maza damata,qarfe tara za'atake wasan daidai team din su dimple ne suka shigo sanye danasu dogwayen jerseys din sunyi kyau sosai kalar jersey din kanta abun kallo ce hannuwansu da different types of flowers irin na cheerleading team dai haka,kowa yana yelling name din house dinshi,itakadai ce tasanya danqaramin talhat hijab white daya rufe mata kanta gaba daya yagangara yarufe saman qirjinta,gurinsu leo taqarasa wanda sune players din nasu takalli Abbas tana furta "inasu Samar suke," yace " like seriously guy's dinnan nason taking tiger house down ace har yanxun basu qarasoba inata kiran wayar Samar din be dagawa ta sameer kuwa bata shiga kwata kwata,kinga coach canma yarasaa yajja xeyi domin yayi relying gaba daya akan wannan qaramin yaron sameer," wayarta taciro tasoma kiran sameer cikeda damuwa tafice a stadium din sbd hayaniya aqofar fita tahadu da Moon cikin dauki da murna sukai hugging juna tana tambayarta "kotasan inda sameer dinyake,their parents are looking all over for him ba'asan inda yashigaba" tace mata "tanaxuwa yanxun xataje tataho da sameer" aiko tai charaf tace "zata bita" tace "toh" suka kamo hanyar hostel,maida akalar kiran wayar tata tai xuwa ga Samar,kira biyu yadaga yakasa cemata komai masifa tahau yimasa amstsayinta na team leader cewar akanme zasu bata lokaci haka ubanme suke haryanxun dabazasu fito ba alhalin yasan xuwa dawurima na marking a matsayin incompetent, so suke suyi dragging dinsu down duka,chak tatsaya jin abinda Samar din yafada tadaya bangaren, "his sick S Fulani is sick and he cannot play like that I can't too because i have to take care of him," saurin datakeyi ne yatsaya chak kafin taruntuma dagudu zuwa hostel din namaza domin bazata iya jira tama yiwa megadi bayani ba ganin tasa gudu yasanya moon binta aguje megadin hostel din nakiransu sudawo amma ina saida suka shige,dakin tafada batareda knocking kowani abu ba, Sanye yake da farin bathrub jikinsa duk alamun ruwa fitowarsa awanka kenan tashigo dakin, bama tatsaya duba dacewa ko rashin dacewar hakan ba taqarasa gabansa tana kallon idonsa dayay jajir sbd jigatuwar dayayi jiya Samar na cikin dan qaramin kitchen yana soyo masa kwai don yasamu yadanci koyaji qarfin jikinsa yaji bankowar dakin betaba kawowa Aysha xata shigo hostel din mazan directly haka batareda takirasa yashigo da itaba, "Sam meke damunka,how are you feeling now,let's go see doctor Sam?" abinda take fada kenan idanuwanta nakawo ruwa,kafin tariqe masa hannuwansa haryanxun da dumi ahannunsa tai qasa dakanta tana zubda kwalla, moon kuwa galala tai tana kallon subiyun haka zalika Samar da yay mutuwar tsaye agurin sbd yaudin feelings din aysha yafito zahiri takasa dannewa wato itaba ma ta team din takeba tunda taji baida lafiya tashi take yi,yace "Aysh' yana sa yatsa yadago da habar ta, "who told you I'm sick?stop crying kinji I'm more than OK bakiganni ba I'm strong now" yafada yana langabar da kai se alokacin ta ankare da yanayin dasuke ciki itada sameer din tadan zaro ido tana matsawa daga inda yake tai saurin juya masa baya se alokacin yalura da moon aransa yace "shikenan yau radio me labaran banxa taganshi se yajja hali yayi," itakuma ganin se yanxun yalura da ita yasata kallon gefe tana murmushi,rabawa yayi yawuce ta gefenta yana furta "kekuma saukar yaushe" cikin fillanci tace "ina zaka san inanan kana soyewa" dagowa yayi yawatsa mata harara yana daukar kayansa yakoma toilet don yasaka,aysha kuwa tarintse Ido takasa sake hada ido da moon din,Samar yakalleta yana furta " toh yatafi kina iya bude idanuwan naki Juliet," yakalli agogo yace "since kinanan kinzo nibara nawuce nadan temakawa sauran don nasan imba sameer ba abunda zasu iya gwara naje natemaka musu" yaqarasa gurin wardrobe dinsa yaciro jersey dinsa yana furta "dimple wannan fine gurl dinfa a ina kika sameta yafada yana kallon moon,da itama take kallonsa," tace "nidin qanwar sameer ce bakaga muna kamaba amma nafishi kyau ko," murmushi yay yana furta sosaima pretty girl,moon ko metashinmu daga barcin weekend kullum" Dariya moon tai tana rufe fuska sbd kunya irin tasu ta fulani, mamaki ne yacika dimple lokacin dataga sameer yafito cikin jersey dinsa yaqulle kansa da bandana yaqaraso gabanta yana furta remain5 minutes kinsan IMPERIAL basa jira ko, tace "but Sam........" Shshsh yafada yana dora hannunsa kan lips dinsa kafin yasauke yana furta "I can do it,I'm strong enough" yafada yana nuna mata muscles wai taga dagaske his strong din wanda masha Allah they are well built duk da qananun shekarun dayake dasu he has a manly body shape sbd yawan motsa jikin da yakeyi dakuma natural halittarsa mekyauce gatsayi domin duk tsayin qafarta datake gani idan tatsaya gaban sameer akafadansa take, Field din yacika da ihu har officials na makarantar sun qaraso,ahankali su sameer ketakowa cikin hall din kansa aqasa donshi mutum ne wanda yaqi jinin taron mutane tsayawa yayi gefe kafin team members suzo su fara musu fada shida samar kan lattin dasukai,coach ma yadau zafi ganin halin ko inkula da sameer din yanuna dayanai masa magana,aysha ce tatare hanzarinsa tahanyar fadamasa yadene masa tsawa ba lafiya gareshi yakyaleshi yaji da ciwan jikinsa ita in tanata za'a bi ma aiba xeyi wasanba, yakalleta lokacin data qarasa tsagalgale coach din yana mamakin kalar masifar ta yar qarama da ita sai fada daga idon dazeyi,idonsa yasauka kan amminsa wacca kefaman washe baki jin hall din yadau sunan danta yan tiger house se ihu suke suna kiran,S fulani,S Fulani,sosai abin yasata cikin farinciki ganin farin jinin dannata. Referee ne yabada umarnin su qaraso za'atake wasa nima fatima naqarasa daya daga cikin kujerun gurin domin nadakko muku rahotan abunda kefaruwa,aysha nagefe itama tana bawa tawagar cheerleader umarnin abunda zasuyi,ko minutes goma ba'ayi datake wasaba S Fulani yafara nuna zallar kwarewarsa tawasan kwandon nidai ba abinda nake ganewa saida naji ance goal,another shot for tiger house sameer S Fulani on top,aiko cikin qanqanin lokaci S Fulani ya ragargaza lion's wanda jikinsu yamutu maras, samar ma balaifi yana tabuka abin arziqi nagaske amma sunan sameer kadai kikeji anafadin champion yanmatan kwa sai gabatar da different routines dinsu suke na cheering mazan suna qara masu qarfin gwiwa ana tafiya half time nahango dimple dauke da towel taqaraso Samar nahango yana murmushi don yasan dukda dimple bata sanshi each year duk sanda suke basketball tana tattalinsa dabashi kulawa tamusamman don taqara masa qarfin gwiwa,amma me se yahangota tanufi sameer tamiqa masa ruwa da towel bamusu yakarba yana lumshe ido domin baqaramin gajiya yayi ba gajikinsa bakwari gaba daya yace "Thanks," tace "I'm proud of you Sam your my real champion," Samar da yaqaraso xemata magana yayi saurin juyawa jin abunda take cewa zarginsa yatabbata dimple is dying for Samyadena qoqarin fighting wannan war dinda yasan baze taba nasara ba,amma ze gargadi sameer kan kada yafada tarkonda xexame masa kogin halaka anan gaba sbd nisansa da yarinyar tamkar nisar sama da qasa ne, alhamdulillah antashi wasa lafiya field yadau ihun "champion,champion,S Fulani,S Fulani" kakeji student nafada tako ina sukansu seniors dayazama year dinsuce sun kiyayi yaron atake agurin aka gayyaci minister nawasanni naqasa don yakarrama sameer shida wani bature suka qaraso, aka bashi kyautar medal na zinare matsayinsa na best player dauriya kawai yake amma jikinsa yadau zafi ga kansa dake sarawa,aka bawa tiger house kyautar wata kwallon kwando ta akayita da zallar gold me azabar kyan gaske,minister ne yakarba micro phone yafara magana kan baturan yaxone daga qasar Netherlands namusamman don kallon wasan nasu kuma yayi selecting dalibai dayaga wasansu da kwazonsu yamasa yana musu tayin insungama high school suxo team dinsa dake Netherlands suzama yanwasa dayawan dalibai najiran irin wannan damar wacca zasu buga wasa a europe amma shi sameer burinsa bashine yashiga sport yatara kudi masu yawaba burinsa naga na'ura mai kwakwalwa yasan talents dinsa nacan sbd yanada creativities dayawa dazeso yafitoma da duniyasu sugansu koda ko bame appreciating wannan aikin nasa, baturan direct yakira sunan sameer S Fulani yace suna buqatarsa,sameer shiru yayi kafin ya amsa dacewar shi bayada sha'awar building career a wasanni yana qarasa fadar haka yasauko kan stage din tiger house tacigaba da celebrating, gurin iyayensa yanufa yana sakar masu murmushi suma murmushin suke suna samasa albarka musamman amminsa moon ko tana cikin yanmatan tsamo tsamo tana daukar hotuna kekyace sun shekara da sanin juna,fitowa sameer yayi tareda iyayensa yana qaramusu bayani kan abinda baturen yace wanda bawanda kegane wani turancin arziqi cikinsu dashi kuma answer daya basu, basusan mahimmancin abunba sukadai ce Allah yatemaka kawai,ammi tace "tayowa sameer side dishes masu dadi suje mota sudakko,ayau baffa zekoma kano itakuma ammi zata kwana suleja itada moon gidan wata yar uwar baffa dake aure anan," dimple ce taqaraso tareda moon tana furta "inayinin ku" tana kallon iyayen sameer din baffa ne ya answer yana tambayarta karatu ita kuma ammi tsira mata ido tai wannan gwara gwaran idanuwan na dimple tasan me irinsu ganin tana mata wani irin kallo da dimple taji ajikinta tadago suka hada ido daram taji gabanta yafadi ganin fuskar yarinyar tabbas tana matuqar kama da bintu matar dan uwanta moddibo a ina sameer yasamo wannan yarinyar har cikin zuciyarta taji tsanar yarinyar tadarsu itama dimple tagane kallon banzan da ammin sameer kebinta dashi wani zazzabi taji naqoqarin rufeta atake anan,takalli sameer tace masa "yatabbata yaje clinic kafin yakoma hostel ita zatawuce gida" tajuyo suka qara hada ido da ammin,sameer yalura aysha hankalinta bekwanta da mahaifiyarsu ba bakamar baffa da suka hadu wancan karan dayazo ba,dasauri yace "no Aysh karki tafi we have alot to do kinmanta," yana dan karkatar dakai,bata fuska taitana furta "itadai seta tafi" cikin shagwaba data dada narkar da sameer din,yace "nidai iindai baso kike nai fushi dakeba karki tafi pls" yafada yana hada hannuwansa biyu cikin yaran fulfulde ammi tadakawa sameer tsawa tana fadin "Uwarme yahadasa da yamace dayake cemata karka tatafi ubanme yahadasa da ita shidin shashasha yazama bata sani ba," qasa yayi da ido donshi yamanta gabanwa ma yake, moon ce tai charaf tana fadin "ayyah ammi qawarsa cefa ajinsu daya fa," ammi cikin fada take fadin yawuce suje wato duk gargadinsa datake akan yayi ta katsantsan da yaran masu kudinnan bayaji ko toh zatai maganinsa,tsit yayi donshi ba mutum bane wanda ya iya musu da iyaye aysha dake tsaye tana jinsu koda ba abinda takeji reaction dinsu yanuna fada akema sameer din kuma akanta sinsin taja jiki tabar gurin tanufi staff quarter, a parlour tasamu su meenah suna videos ko takansu batabiba tashige dakin aunty noora lilly nakan sofa tana wasa dayaron yayar tata dimple tashigo tafada gado takwanta tana tina fuskar babar sameer sosai taji tanajin shakkarta aranta tace "ai iyaye mata daman duk haka suke setaitawa sameer tsawa agabana ashe ba ummina bace kadai batasona shima sameer Allah sarki tasa mamar batasansa tanai masa tsawa" batasan maganar tata tafito filiba,lilly tace "dimple babu uwar dabatasan danta saidai kowacce daban salon nuna soyayyarta yake ko taki uwar tana sanki kawai dai qaramar kwakwalwar ki da masifar san zuciya yasa kika kasa gane hakan," miqewa zaune tai tana furta zaki fara ko "toh ni im banda shishshigi ma nace lilly ne amaganata dazaki tsomamin baki nida raina nake magana" tafada tana gallawa lilly harara,ita abun na dimple tunyana bata haushi yanxun kam dariya yake bata tace "aidaman ke gaskiya ce bakyaso kuma shi sameer dinse meye dan mahaifiyarsa tamasa fada ai itadin tanada damar haka kedai dakika qeqashe kikafi qarfin taki uwar sekije kiyi tayi" tafada tana daukar yaron tafara jijjigashi don yasoma kuka dimple tsaki taja tana furta "lilly bazaki taba gane wacece umminsu muhsin ba shiyasa," tace "dimple kenan ni abinda nake gudarmiki fa shine sakayya bakaiba ma ammaka ballantana kayi yajja kike wulaqanci da yiwa mahaifiyarki abunda kika gadama zakiso naki yaran suringa maki haka kema," dimple tabe baki tai tana furta "niwayace maki zanyi aure ne harna haihu," dariya lilly tai tana furta "namaki uzuri kanki dasauqi yarinyar nan" tafice adakin dimple tatabe baki tamiqe takwanta abunta bacci tasha bata tashiba se ana gab da magariba aiko ta hanzarta tai sallar la'asar wacca bataiba, tana idarwa ya noora ta shigo tana waya tai murmushi tana furta "gata tatashi" karbatai tana furtaa "hello" muryar Arsal taji yana furta "baby girl sannu da hutawa," smiling tai tana miqewa tanade sallar tafurta "kaima baby boy sannu dayin fishi dani," yace "dimpy waike bakya mantuwa ne," tace "bannayi seka kiyaye nangaba," "ya noora tafadamin cewa house dinku kuncinye Bball comp" tace "aikasan duk inda dimple AJ take nasara nabiyo bayanta", Yace " awwwwn your so full of your self," smiling tai tana furta "Waya koyamin yaya" Yace 'naji baby girl hutunnan dan Allah kizo NYC kinji nasan popsy baxe hanaba I missed you," Tace "abaki ba,niba inda zani bayan kasan bikin yaya muhsin za'ai memakon kaikaxo," Yace "Dear inada bad memories dana kasa mantawa a qasarku shiyasa nake gudunta," nisawa tai kafin tace "Ba'a taba moving on imba atunkari bitter past ba bestie," yace " toh naji but innazo zakimun masauki aduk inda kike don kinsan banison hayaniya ko" tace "karka damu your highness" yace " wane ni ina saurayinnaki,?" Tace "Wakekenan yace wanda akamun tas sbd shi," tace " xakafaaraa ko nina fada maka ba saurayina bane kaqi yarda suit yourself" taqarasa tana kashe wayar,yaya noora data xauna gefe tana sauraronsu tai murmushi tana furta "kishinne yamotsa kenan" tabe baki dimple tai tana furta "rigimace kawai irinta yaya Arsal,' tace ' dimple kenan bakisan matsayinki azuciyar Arsal baneba shiyasaka haka," tace "ya noora nima besan matsayinsa azuciyata baneba amma he's over protective wai ban isa inasake abokaiba saiyay tamun ihu aka nishiyasa kwana biyu nake baya baya dashi," tace "dimple ciwan sankine yasa arsal kematuqar kishinki kinsan dahakan ko," tace "what so,nida ya arsal din impossible ya noora your not serious" taqarasa fada tana ficewa adakin. Se qarfe takwas sameer yayi sallama dasu mama bayan yarakasu har suleja inda yamusu alqawarin zuwa gobe da sassafe ya rakasu tasha suhau motar kano, kamar kansa xetsage haka yadau taxi yakoma IMPERIAL,sosai abin yaringa damunsa yajja mamansa tai kicin kicin sanar dashi yayi gaggawar rabuwa da Aysh sbd waitamata kalar fitsararrun yara masu bata tarbiyyar yaran mutane moon ce tamaida ammin kakarta tanata tsokanarta kan ayshan ,sameer beji dadin abinda taiwa yarinyar ba,yasan mahaifiyar sa bamutum bace dakeda matsala dakowa betaba ganinta cikin wannan dabi'ar nasukar wani ta faraddaya ba se akan dimple,toh metai mata allahu ta'ala a'alam yabawa kansa answer, clinic yafara zuwa suka dubashi akabashi magunguna yanufo hostel. A dining table AJ's villa aysha keta juya abincin plate dinta takasa kai koda loma daya ne na abincin tana tinano abinda yafaru sosai mahaifiyar sameer tatsaye mata arai tanajin haushin matar na addabarta toh ina ruwanta ma tabakin lilly semeye don batasonta ai baban sameer nasonta, Alh AJ yakalleta yana lurada dukkan yamutse yamutsen fuskar datakeyi, tinani tacigaba dayi akan abubuwan datake ji gameda sameer din waishine so,toh meyema san ya akeji anajinsa,dagowa tai tana kallon mahaifinta tace "popsy kaida ummin muhsin auren soyayya kukai kuwa," abinci xekai bakinsa amma se yafasa ya ajje yana kallonta he never expect this question from her,muhsin yakalleta yana furta "kebakida lissaafi ko popsy din kike tambaya haka," tadago tana duban tareda fadin "toh kai zantambaya kaida nasan bamasan ya kudrat din kakeba," tajuya ga popsy tana furta eh inasan nasan meye soyayya kuma yayane ake auren soyayya," smiling popsy yayi yana furta " dimple why do you wanna know?" direct sbd bata boye boye tace masa "I'm confused sbd anacewa inason mutum biyu toh inaso nasan wanakewa so na soyayya aciki koda bata fadaba yasan Arsal da sameer take nufi wanda ranar dazata gane me takeji aranta yana ganin kamar yayi wuri amma dole ze answering question dinta gudun kada taje wani yabata answer da gurguwar shawara,yace "Love is an intense, deep affection for another person. Love also means to feel this intense affection for someone. Love can also refer to a strong like for something or to like something a lot. Yaqarasa yana kallonta, ni sawatai kafin tasaki murmushi tamiqe gunsa taje ta rungumeshi tagefe tana kissing cheeks dinsa tana fadin "Thanks popsy,I'm so grateful,I'm in love I'm no longer confused popsy,I'm in love" ta sakeshi tana qara fadin she's in love daqarfi, muhsin yamiqe yana furta "Waye kikeso fadamin dan waye is it arsal?" Muhsin yatambaya cikeda sonjin qarin bayani,murmushi tai tana girgiza kai kafin tafara kwallawa chief maid dinsu kira taqaraso dasauri tana furta gani hjy dimple tace "kishiryamun abincina kikaimun bangarena yau acan xanyi dinner" tafada tana kallon popsy tace "you're invited muyi celebrating tare," sosai yaji wani nauyi acikin zuciyarsa gameda abinda diyar tasa kefurtawa yasan cewa rana mekama dawannan zatazo be taba tsammanin zuwanta nankusa ba sbd yakuduri aniyar yarinyar sa nada burin dogon karatu beyi tinanin zatabawa soyayya damaba arayuwarsa, ficewa tai tana rangada waqar " I'm in love,I'm in love,' doctor bintu takalleshi tana furta "Alh kanaganin irin maganganun da yarinyarnan keyi agabanmu ko kunya wata yar mitsitsiya da ita wai she's in love shirmene fa na teenage age koyaushe tacika shekara shashida dahar take wannan iskancin gab an,......." "ya isa please bint," Alh yadakatar da ita,yacigaba "let her live her life koni ina high school I dated alot of girls amman duk shirmene ko,zatai hankaline,she's still a kid dole zaki bata lokaci imbataiwa iyayenta ba wakikeso tayiwa," tace "Alh kafasan dimple batada mijin dayawuce Arsal danhaka son wanima kmr batawa kanta takeyi kuma nasan kaidin ba auren wuri zakamata ba," smiling yayi domin indai akan dimple ne alh baka gane hukuncin dayake dauka,yace "bint kenan auren wurin haramunne na tambayeki iyayenmu da matan sahabbai duk basa kai kmr dimple suke aure donhaka if she wants early marriage baxan iya hanata ba" yafada yana miqewa yace "I'm done,gobe za'aje akai kayan lefan muhsin kano tunda already yaya hauwa tayimun waya tace sunsauka dazu," tace "Allah yakyauta kawai," yace "ameen" yana ficewa qarfin haline kawai yakeyi shikansa don yana tsoran zuciyarsa idan dai har akan farincikin dimple ne,seya iya bataran kowa dan yafaranta mata, Tana qarasawa part dinta tafada kan sofa tana lumshe ido pillow daya tadauka tana rumgumewa she's in love with Sam baruwanta no matter what anyone would se zata iya scrambling duka duniya tai troubling kowa sbd shi,fuskar mamansa take tinawa tadaxu kafin tatabe baki tanafurta "inaruwana ma dake kada kisoni din nidai danki nakeso kuma sena sameshi don bantaba neman wani abu narasa arayuwata ba," video call takirasu lilly aiko nandanan kowacce tadaga meenah tace "malama are you okay sewani blushing kike kmr wacca sanyi yataba," tace "meenah imba gaba dasanyine yakamani yau," Lilly tace " what's with that red cheeks meyafaru,?" dan far da idotai tana furta, "I'M IN LOVE WITH SAM," tafada da manyan baki,meenah dake kwance miqewa tai tana fadin "which SAM kenan," lilly da murmushi yakasa barin fuskarta, tadago, "akwai wani SAM dinne bayan sameer S Fulani," "What?" cewar Meenah tana zabura, Meemee tace "dimple you are mistaken is not love may be is just infatuation," "I don't care girl,ko love ko infatuation I just want to be with SAM forever," meenah tace "wannan maganar bata waya bace dimple kinmanta munyiwa junan mu alqawarin we'll never fell for anyone har sai duka munyi approving banyi approving kiso SAM ba," dariya dimple tai tana furta "only god can stop me from loving Sam kinaji meenah so karma kifara im bazakiyi supporting dinaba toh dan Allah kiyi kamar bakisanme nakeba," sallamar popsy yasa tadago tana kallonsa,suma sunji shigowar popsy din hakan yasa duka suka basu guri tahanyar katse video call din, Zama yayi akusa da ita yana kamo hannunta, Yace "dimple," tadago tana furta "yes popsy" yace "dimple lokacinda ina high school I had many feelings kmr abinda kikeji akan sameer but all that is not called love harse kayi spending enough time kasan mutumin dakake iqirarim kanaso sannan zaka tabbatar inzaka iya sansa for life koban fada miki ba kinsan cewar you are sick,you have a weak heart wanda in little things irin haka suna shiga zuciyarki zasu batamaki rayuwa babyna," kwabe baki tai kafin tace "popsy,i know someday or the other xanmutu,bazanyi doguwar rayuwa kmr everyone ba shiyasa nakeson living peaceful and happy life kuma sameer nacikin wannan life din danai choosing i hope you'll respect my feelings popsy," yace "dimple I'm afraid,inajin tsoron soyayyarki taqi nasara kmr tawa sbd is one sided shin shi sameer dinna feeling thesame thing dakikeji akansa," nisawa tai sannan tace "ko bayaji xankoya masa I'm beautiful,rich and educated inace maxaba iya wannan suke soba, xansa yasoni" Popsy girgixa kai yay kafin yace " that's the biggest problem dimple,he shouldn't love you because your beautiful or rich or even well educated he should love you for who you are kinaji beauty or riches shouldn't matter lokacin da xesoki wannan son shikadai xanyi accepting" Rau rau tai da ido kafin tace "I'll ask sameer out,banada doguwar rayuwa popsy kuma baran bari ya kubucemin ba no matter what " tamiqe tana furta "popsy kuma I'm sure cewar baka daya daga cikin mutanen dasuke duba matsayina duniya abakin komai zanje naci abinci daganan xankwanta bacci" tawuce next parlour da chief maid tahada mata dinner chilled chocolate smoothie kadai tasha sai pancake data dan tsakura kadan tawuce dakinta tasoma danna waya,popsy kuma qamewa yay agurin yana auna mugun taurin kan na dimple inta kafe akan abu dolene Arsal yadawo garinnan yafada yana miqewa a parlourn don duk atinaninsa rashin Arsal din kesaka ta bawa sameer wani matsayi nadaban azuciyarta. Sameer nakwance yasha magungunan da doctor yabashi ya lumshe ido yana jan dogon numfashi,ciwan kan yaji yana sauka ahankali yana tinano fuskar Aysh dinsa that beautiful smile datake bashi,what is this feelings yake tambayar kansa Samar ne yafito daga qofar bathroom yanagoge kansa da towel da alamun wanka yafito yaqarasa garesa yaxauna kan bedside drower din sameer din yataba shi donjin temperature dinsa, "yajikin naka SAM?" hannunsa yasa yaxare hannun Samar akansa yana juya masa baya yace "I thought you don't care about me,why did you help me,dakabarni namutu you'll get rid of that obsession dakake dashi kan aysh," smiling meciwo samar yayi yana furta "Sameer nahaqura dason Aysh nahar abada saidai kuma hakan bebada daman kaika sameta ba,Aysh din koni qarfin hali nake gurin santa amma nasan itadin baxata taba aurenaba sbd sudin basa'annin mu bane sameer,especially Aysh din dake sanka,sameer babanta dattijo ne me mutunci da tarin mutuntaka amma xan iya rantse maka koda zakayi arziqi nangaba family dinta will not accept you kaikasan suwaye family din AJ toh tsaya kaji taken da akewa yayunta maxa guda biyu kunqi jinin talaka sannan mahaifiyar Aysh kanta masifa ce megirma domin itace mamallakiyar kamafanin bint AJ ELECTRONICS,Matan masu kudi shakkarta suke sbd yajja take juya mijinta san ranta,Alh bayada wulaqanta mutum but muhsin da muhassin are nothing compared to him akwai lokacin da nafara xuwa gidansu tunmuna grade7 abinda muhassin yay minharyanxun yatsaye min arai yawulaqanta ni yasani naji namuzanta sbd alokacin mahaifina bashida shi kmr yanxu, sameer inajiye maka cin zarafi tunkan dimple ta tunkareka da maganar soyayyarta kai gaggawar takama abin burki matuqar kanason kaqarasa shekara dayar data ragema a IMPERIAL," juyowa sameer yay yanafurta "And so meye nawa dakake fadamin hakan kanaji I'm not in love with dimple,don haka lemme sleep peacefully" yaja duvet yana rufe fuskarsa,amma sarai yaji kuma yasaurara duk abinda Samar din yafada masa,kalmar sunqi jinin talaka yatsaya masa arai. It's Fatoums Passion AYSAM Don't forget to Comment Share Vote.***
AYSAM Love,passion,hatred,betrayals and power btw two different worlds.