AYSAM

Chapter 28

by @fatoumspassion

(Affinity) Yana kwance kan dan qaramin gadonsa sanye yake cikin wani farin wandon pajamas dinsa yana ta juyi maganar dasukai da both Aysh da hudallah nadawo masa kwakwalwa daki-daki, amaganar hudallah yafahimci tsantsar quncin da Aysha ke guma mata sannan yafahimce tana matuqar son alaqarsu tagyaru kota yanda ta amsa masa dayay addua daidai tuwar lamarinsu sannan tace masa indai Aysha batada matsala itama bata dashi Allah yasa sameer yaxama sanadin daidai tuwarsu bayan sun rabu da hudallah adaren yana xuwa daki yakasa barci yakirata cikin sa'a itama bata kwanta ba suna watching movie a Netflix itada su Lilly, bayan sungaisa tana ta tambayar yamai jiki ya answer mata tace "popsy nata santin nutsuwar ka yanamun gori" yay smiling cikin tsokana dason jin mexatace yace "sistern ki tace nagaisheki" straight tace "My Moon kace nima ina gaisheta namata magana ta WhatsApp batai reply ba I called her wayan beshiga," tinawa da ita kanta maganganun Moon din yay akan ayshan yace mata " don't bother to call her xan isar mata da saqonki mexakice mata," tace "ah a baxan fada makaba sirri ne girl's talk" Smiling yay yace " toh ba ita bace tace tana gaisheki" Jim tadan yi kafin tace "toh waye?" yace "sistern ki dai your real sister hudallah," straight tace masa "Your lying SAM" yace "what?" yanadan miqewa domin tabashi mamaki da dariya wato rashin kunyar na aysha har yakai tace mishi qarya yake duk da yasan qaryan yake aibe kamata straight taqaryata shiba ita bata iya tauna magana kafin tafada ba semuce malam sameer ayi haquri damu haka muke bamusan magana medadi komara dadi ba kawai tana xuwa ranmu fada muke,tace " yes,hudah....."voice dinta nadan cracking tadorada "will never said what you say now," yace "wainine nake miki qaryan Aysh," tace "Sam pls let's not talk about her karkai spoiling beautiful day dina at the last moment," yace "dimple meyasa kikace baxata taba cewa agaisheki ba," tace ' because we hate each other straight" tafada masa ba boye boye,yace "she doesn't hate you kinaji impact tanason ku shirya kusamu fahimtar juna tsakaninku,yadan ja numfashi kafin yadora " kuma idan babba yay qarya bawai straight kakecewa yayi qarya ba especially me daxan xama mijinki bakisan ba araina miji ba,' dariya ce taso kwace mata,nikuma fatima nace uhm kaji su sameer manya daga ganin sarkin fawa se miyatai zaqi,yana jinta tana dariya qasa qasa yace "au dariya ma kikeyi bangirmekin bane" tace ' SAM manya da shekara dayane fa kacal," yace "shekara dayanfa ko kwana daya nabaki aina girmeki kidena kinjiko aysha na" tace "toh SAM, amma aiba kyau qarya kuma qarya namaka ba qaryan kake yiba," yace "au kika sake maimaitawa kuwa ko saina saita wnn bakin naki dabai mutuwa,naji nadena qaryan kema kidena rashin kunya kuma I lied for you and your sister naxata you'll be overwhelmed with joy innace tana gaisheki," tace "Mr sameer borine dai kakeyi nagane ka, yace "naji mudawo maganrmu she didn't hate you,kuma kina bullying inta agida,Aysh Bakyau zalinci bakida bakin kare kanki sbd I witnessed many of your Bullying's before kinsan nasani both I love you,I'm accepting you for who are,hoping someday you'll change your way's of getting things done Aysh," shiru tai masa jin kalamansa agareta shima kenan bayan hudallah xebi meyasa suka kasa gane true color dinta she's a snake a venomous snake she'll snatch SAM she'll snatch him tinanin hakan yasa kawai tafashe dakuka for the first time in 5years dataima kanta alqawari baxata qaraiwa hudallah kuka ba baxata qara neman sulhu da ita ba kuma baxata sanar dakowa asalin halayyar yar uwar tata ba koda ko xa ake kallo amatsayin itace mara kirkin hudallah tasiye zuciyar kowa bawanda yake iya ganin lefinta se ita, rikicewa yay gaba daya yana fadin Aysh "pls stop Crying idan bakyason maganar andena har abada,kibari pls kinsan banason kukanki pls Aysh Stop crying," sassauta kukan nata tai tana fadin "kaima lefina kake gani nasani koda baka fadaba kafin sonta da yarda da ita akaina amma narantse maka sameer bantaba cutatar da hudallah haka kawai ba,tanamun ina ramawa meye aibu acikin hakan sameer seta rabani dakai nasani tunda taga insonka she's toxic sameer ina tsoron abinda xatai I'm really scared SAM," wannan kalamai na aysha sun tsaya masa arai bata qarya yasani yasan daga zuciyar ta wadannan kalaman suke fitowa amma bazaitaba yarda dacewar yar uwarshi hudallah ce melaifin ba dole akwai wani abu dasuke boyewa tsakanin su biyun da yagaza fahimta wanda yasan hudallah nada mugun wayo baxe taba ji abakinta ba but he'll go for Aysha xemata wayo tayajja dakanta zata fada masa matsalarsu shikuma in sha Allah xe maganceta yasaita alaqar dake tsakanin yan uwan guda biyu batareda kowa yasake jin kansuba ba. Miqewa yay yana tina yajja yasha lallashi jiya daga shi har ita sai kusan qarfe biyu da rabi suka kwanta suna maqale awaya, fitowa tsakar gidansu yay ammi yagani tana dibar ruwa ababban daron ruwan dake tsakar gidan mamakine yakamashi ganin rana tafito sosai beko duba agogo ba yafito,tadago tana kallonsa kawai seyaga tai masa nuni daya koma,yace "ammi ina kwana" tace "fara xuwa kasuturta jikinka tukunna karka fitomin nan bariga tunda bakajin magana," "au" yafurta yana kallon kansa yariqe kunne yana fadin " I'm sorry nadena" ,tace "sameer yawan tubewa aibaxaka taba denawa nidai zaman makarantar nan naka ba abinda kakoyo se dabi'un arna ace mutum bashida aiki se yawan tsiraici baccima wai seya tube yakejin dadi qaryar fillacin kakeyi ashe mara kunya," tacigaba da mita har seda yakoma yaziro jallabiya yafito yana mamakin fada irin na ammi bata gajiya kullum seta maimaita masa shikuma kullum kmr mekunnan qashi haka yake shigani yake bakomai bane yasaba rayuwa cikin maxa zallah baruwan kowa dakowa amma dayadawo gida se ammi tace " bakyau kul baxata lamunta ba yan matan yaya gareta hudallah da moon qato dashi yadena mata yawo ahaka Baffa kam baruwansa da fadan ammin da yaran nata," Parlor yashiga kmr yajja yasaba Baffa naxaune saman daddumar sallarsa yana laxumi da alama sallar ishraq(duha)ya idar, sameer xama yay gefensa harseda yakai qarshen chaxbahan sannan yayi addua yashafa sameer ma shafawa yay, yadago yatsira masa ido jiyay duk ya tsargu da irin kallon dayake masa, "jam weeti" Sameer yafada cikin fulfulde,ya amsa masa yana tambayarsa ya yake,yace "masa lpy lau almdlh", Yaqarada cewa " lpy babban mutum banganka a masallaci da asubahi ba nasan kullum kana rigani shiyasa daxan fita nai ragon axancin tashinka," yace "baffa banfarka dawuri bane shiyasa se shida natashi nayi kawai adaki," yace "haba babban mutum ba halinka bane akula nan gaba" yace "in sha allah baffa," shiru baffa yay kafin yadau chazbaharsa yacigaba da jaa, sameer ganin haka yasa yasan baffan baya son magana seya miqe daniyar fita kawai yatsinci muryar baffan yace "Muhammad" sunan dayake da girma abakin baffan indai yaji yakira shi da zallar sunan sa yasan ba qaramar magana me mahimmanci xeyi masa ba tinawa yay kodai har Daddy ya isar da saqonsa da wurwuri haka, "dawo kaxauna" yafada yana nuna masa gefensa,zama yay yana karanto duk wata adduar dataxo bakinsa Allah yasa baffa ya amince fatanshi kenan, yace "Muhammad sameer ashe kagirma har haka bansani ba," dan dago kai yay cikin rashin fahimta yana kallon baffan yace "meyasa tuntuni baka sanar dani kana buqatar aureba, aiwannan cutatar dakaine da nabi shawarar mahaifiyar ka ajje karatu kanemu sana a kasan shi aure seda abinyi" dan karkatar dakai sameer yay yama kasa maganar wato baffa fassarar dayay masa daban,bema taba kawo wannan tinanin cikin zuciyarsa ba tabbas yanason aure amma bada kowaba saida aysha kuma yasan koda giyar hauka yasha yanxun baza ataba bari suyi aureba sudin qananun yara ne a idon iyayensu har yanxun bayan shi yasan he needs Aysha now ko yanxun xa abashi aurenta he's physically and mentally ready for it amma bawai amatse yakeba kmr yajja baffa yake tinani he can wait for her, baffa yacigaba "kuma babanka dikko yafadamun cewar yar uwar hudallah kake nema koh," yagirgixa kai yay alamun eh yace " aishi aure lamarin ubangiji ne sameer ban isa nace kaida ita baku dace ko akasin hakaba amman dai sameer kasan dage bashida dadi,ina tsoron bakin mutane kasan xasu zargeka da yin aure kudi ko makamancin haka," sai alokacin yay magana yace "ai baffa bawai auren ne xa'ai yanxunba kawaidai baban yanason kugana kudashi kasan duniyar yanxun bayarda ne kuma maganar mutane baffa mutane baxaka taba iya musu ba duk abinda kai sesunyi magana,dan Allah baffa albarkar ka dagoyon bayanka nake nema aimana fatan alheri," Yace "babban mutum kullum addua ta tana tare dakai dan albarka amma dai xanje naji meshi mahaifin nata zece kasanar dasu sesu saka rana muzo koba hakaba tunda ance shidin mahaifinta mutum ne me uxurirrika dayawa," yace "toh baffa xanfada mata insha Allah," yace "toh bakomai babban mutum Allah yasanya alheri" jiyake wani farinciki na mamaye shi tabbas yasan Alh dikko mutum ne domin yasan halin baffansa Alh dikko kadai ke iya convincing dinsa kan abu shine sirrin dayakesa baffa yay abi koda bayaso sbd kara da yakana irin tasu tamutan da shike yanke hukunci kan yayansa shima kuma yayanke kan nasa yaran bame cire kai yace danme cikin matansu koyaran,gyara zama sameee yay yana fadin se maganar sana a kuma baffa ni inada wani business plan,yace toh masha Allah ina jinka,yace akwai kudinda Daddy yabani lokacin da kamal ya kammala makaranta yabashi nima yabani yace muja jari katina su yace natina su babban mutum sunan adane a account yace kudin sunkai kimanin miliyan daya baffa,sannan kuma nasamj kyautar miliyan daya a makaranta cheque din na gurin ammi har yanxun ban ko cireshi ba,kaga miliyan biyu kenan akwai wani shago abakin titi wajan makarantar al axhar sabuwan gurine ake ginawa inaga xansiya guda daya ciki yanxun sun kusa kammalawa nasan baxeyi tsada sosai ba musamman inka taya tun yanxun,yace inajinka babban mutum yace yanxun harkar karatu duka takoma online baffa irin yajja nabude maka anaka shagon toshi shagon xe xamana anbudeshi ne xamuke yiwa yan makaranta registration na jarrabobi irinsu jamb,harma da SSCE,CBT center dai sosai sauran kudaden muxuba na ura mai kwakwalwa da solar sbd tsaro kar aita jigilar siyam mai,sannan xamu ringa su photo copy da printing da yin abubuwa dai da dama har p.o.s duk xamu ringa yi,yace masha Allah babban mutum wnn tinani mai zurfi haka cikin qanqanin lokaci yace baffa nadade inason nai hakan kawaidai banason nahada karatu daneman kudine amman yanxun xan iya in sha Allah,hudallah dake labe cikin daki tana sauraronsi kwafa tai tana fadin aikin sakai aidole ka iya yanxun AJ dinne yace xegasu baffa duk yajja xa ai seta dakatar dawannan alaqar seta tarwatsata domin baxe iyu aysha tasamu abinda takeso ba,xamatai gefen katifar Moon tana daukar wayar ta,ringing biyu tadaga tana fadin dear ykk,tace ummi kituro driver yanxun yadaukeni it's urgent tace lpy kuwa are you ok,tace I'm not pls yay sauri tana kashe wayar. Sameer bayan yayi wanka shida Samar suka fice xuwa tambayar kudin shagon akai musu kwatance har gidan megurin cikin sa a aka dadaita kuwa sukai kan washegari xa axo dashedu sameer yamallaki shagon,haka suka taho cikin farinciki se ahanya Samar yatitsiyeshi seda yafada masa halin dayake ciki tsokanarsa yaringayi yana furta ashe ashe abun yana kusa wai angama hura musu hanci ba a soyayya segashi kainaka abun da xafo yataho mutumina gaskiya ina tayak murna yace kamal I'm so happy lokacin dana fara ganin Aysh at that very moment naji inasonta guy I just loved her without any reason sekawai tai breaking heart dina tahanyar takuramin a school like she show's me tatsaneni fa completely,kullum a class she cut me more than 5times ina kallonta sekawai naga tabasar like that didn't even exist sannan ga Samar irin son daa yake mata yasa naso nayaqi zuciyata akanta duk wani abu daxatai kawai nise naji yana birgeni guy Aysha tayi guy bansan haka nake matuwar santaba se rnr danaga babanta da ita a hospital she was sick batazo school ba rnr ko a banfahimta ba a karatun da ake me kamal yake bayan dariya yace ah lallai mutumina kakamu dayawa shine akexuwa ana wani basarwa kmr kmr ashe ashe suka kwashe da dariya suna tafawa yace kamal I'm happy kamun addua nasamu Aysha bantaba jin cewar baxan iya rayuwa inba wani abu aduniya ba se akanta,komai yafaru cikin sauri dani kaina narasa gane meke faruwa bantaba tinanin mahaifin aysha xe amince dani ba ashe shidin mutum ne me matuqar san farincikin diyarsa he's ready to do anything to make her happy kuma nima xanbi footsteps dinsa u can die for her dude yafada yana lumshe ido,kamal yace sameer karfa kasusuce malam duk ita xakaje kafadawa wannan baniba ko itamadai jan ajin kake mata,murmushi yay yana furta nifa inajin kunyarta,dan xaro ido kamal yay yana fadin kana ruwa kunya tab,yace nifa bakomai nake iya fada mataba shiyasa take ganin kmr bana wani jida ita batasan irin yajja take da tasiri a zuciyata ba har yanxun but not anymore tha AFFINITY Between us is growing strong nayau yafi najiya najiya yafi nayau kamal Aysh duniya tace,atafawa soyayya cewar kamal yana qaran gudun motar yace gaskiya S Fulani kakamu dayawa haka suka cigaba da raha yana bashi shawarwari har suka qarasa kasuwar kantim kwari inda sameer xexauna tareda yaron baffa yau kafin yawaware duka yakoma kasuwar. Aysha naxaune gefen popsy tana nuna masa garuruwan dazasu je a UAE yana cewa sunyi yawa tana tamai rigima akan ita tanaso tawuce ma tai umrah inta samu dama,yace mamana baxaki bari se Ramadan mutafi duka kmr yajja muka saba ba,tace nidai a ah popsy inaso naje kagadai da Ramadan din qila munfara mid term kuma karkace baxaka dani ba,yace shikenan as you wish,Muhsin ne yashigo yana gaidadda popsy ya answer cikeda fara a yana tambayar sa ya amarya sosa kai yay yana fadin tana gidansu yace ai yau xaku wuce Abujan Koh ya jinjina kai yace toh masha Allah Allah yasanya albarka,ummi ce tafito tana fadin yauwa Alh,muhsin gara da Allah yasa kunanan ina MUHASSIN kmr yasan maganarsa ake sallamarsa ta karade parlor tareda Anwar wanda yasauka ayaudin da safe,bema samj halartar daurin auren ba,yace gani naji ankira sunana lpy,ummi tace gata ku tambayeta tafada tana nuna Aysha wacca tadago tana kallonta cikeda mamaki,shima popsy itan yake kalla,xama tai tana kwalawa hudallah kira wacca basuma san taxo gidan ba,tafito anitse kanta aqasa tana wasa da gefen hijab dinta,tace xoki xauna achan tana nuna mata gefen inda aysha da popsy suke xaune batai musu ba taje gefen daf da popsy tazauna,yace lpy kufadamun meke faruwa,ummi ce cikeda takaici take furta maganar danai maka rnr daurin auren muhsim kaqi saurarena xamu tisa gadai yarinya,dimple seta dakko mana maganar daxata fi qarfinmu daman tarigada tagama fandarewa ai yanxun har maxa takebi har gidajansu kalmar fandarewa da bin maxa ta daki dodan kunnen AJ cikin baxata anyq kuwa bint tasan metake fada matsayinta na mahaifiyar data haifi Aysha,AJ yakalleta cikeda calmness dinsa dason controlling kansa yake furta metai har haka dakike aibatata da munanan kalamai irin haka bint tace imba fandararriya ba ace yarinya randa kika diro gari kika tafi gidansu saurayi nemansa saurayinma matsiyaci wanda yafi daga tsatson walijam kekam kinyi asara,bint ya isa haka yafada cikin daka tsawar datasa kaji wani tsit a parlor,Aysha kuwa qurawa hudallah ido tai tanason tasan metaje tafadama mahaifiyar tasu akanta inda sabo tasaba da makircin hudallah,mgnr popsy tasa tamaida hankalin ta kan ummi go straight to the point kuma kika qara aibatamun yarinya sena batamiki rai,dogon numfashi taja tanason daidaita bacin ranta tace gatanan hudallah tasanar dani dimple na soyayya da dan uwanta sameer,Alh AJ cikin halin ko inkula yafurta and so,ummi cikin mamaki take fadin bawannan yadameni ba yaron anmasa shaidar rashin kirki lamba daya bashida tarbiya ko kadan ko a unguwar tasu baya mu amalla dakowa,kowa yarabasa da dansa sbd shidin dan drug's ne namba daya bawata kwayar da bayasha hudallah dake kwana gidansu shedace yafi qarfin mahaifansa,xe lalata ta ne yaqarasa gurbata mata tarbiya alhassan indai baso kake dimple taqarasa fitsarewa ba karaba ta dawannan yaron,kallon zallar mamaki yakewa hudallah yadade yana zargin ita take juya kwakwalwar matarsa takesata mafiyawan abubuwan rashin kirki datake yi amma be tabbatar ba sbd bashida hujja both xefara samata ido daga yanxun,cikeda kulawa yakama hannun hudallah yana fadin daughter fadamun shin abinda mahaifiyarku tafada akan sameer gaskiya ne zakifi kowa sanin wanene shi,ta jinjina kai tana fadin popsy gaskiya ne both sameer da dimple yan uwa nane baxan taba so daya yacutar da daya ba ina tsoron itama tai joining dinsa subata rayuwarsu duka,dimple ce tamiqe cikeda bacin rai take furta your a bitch hudallah,why me sameer yataba miki,meyasa kika zaba tsanata da duk abinda nakeso hudallah me na taba miki,dagowa tai hawaye daya nabin daya afuskarta,dimple kiya haquri idan har abinda nafada yabata miki rai ina matuqar qaunarki dabazan taba shiru imbari ki cutatar da rayuwar ki ba sameer be dace dake ba shidin ba mutumin kirki bane ba,tau kakeji dimple tadauketa da mari tadaga hannu xata qara mata qaqqarfan hannun muhsin yariqe ta,dimple kishiga taitayinki kinaji ko,kika qara saka hannunki akanta senayi qasa qasa dake anan,MUHASSIN yace wai maganar mema kukeyi datazama tashin hankali wayene kuma sameer,meye alaqar sa da sister's dina,ummi tace gasunan katambayesu ita waccan dan uwan mahaifinta ne tasan komai gameda shi while itakuma waccan mara kunyar wau sonshi take soyayya suke,Anwar ne yaqarasa yakamo hannun dimple ganin se kuka take ba qaqqautawa ya xaunar da ita yana fadin calm down kinji shi AJ ma is speechless sbd a iya binciken da yayi betaba coming across da abu memuni haka ba arayuwar sameer something is fishy kodai shi binciken nasa anmasa badai daiba ciki kokuma kmr yajja dimple tafada hudallah qarya take dayan biyu kuma a ayi haduwar dasukai da sameer betaba masa kala da yaran banxa ba ballantana ya zargeshi da abinda hudallah tace,muryar hudallah suka tsinkaya tana fadin idan kuma baku yarda daniba xaku iya aikawa amuku bincike kan wannan abunda nafada,Alh AJ yace indai hakan yamaki xansake bincike akan S Fulani sbd duk wani abuda xaixama katanga da Farincikin dimple na gyara masa zama,indai har sameer bedace da itaba I promise senayi breaking alaqarsu,Aysha ce tamiqe taqarasa gaban popsy takamo hannunsa cikeda rauni take fadin narantse maka da Allah popsy sameer ko cigarette baya smoking balle drug's,sameer is a good guy,wnn dakake gani munafuka ce she just want to ruin me popsy,ummi cikin takaici take fadin zakimun shiru kosai na miqene,juyowa tai tana kallon ta da dara daran idanuwanta dasukai jajir tace daman nasan baxaki taba yarda dani ba tahada hannuwanta bibbiyu tana fadin amma naroqeki kifita daga wnn maganar sbd indai har kika cigaba da goyama hudallah baya wannan karon zuciyata baxata iya jurewa ba,muhsin ne yake fadin wai waye wnn din koshine wanda Arsal yafadamin yana soyayya da dimple kehar nawa kike daxaki fara soyayya bakisan soyayya tarwatsa mutum takeba tsugunnawa yay kusa da ita yana kallon zallar rauni cikin idanuwanta yace wannan raunin dimple get rid of it,it will destroy you,baxan taba bari ki shiga wannan halakar da sunan soyayya ba wayeshi meyake dashi daxe baki dimple you deserve more kedin me daraja ce baki dace da matsiyaci dan shaye shaye ba,kallonsa taitana fizge hannunta daga nasa tafara goge kwallarta tace ya kudrat ma aibata dace da kaiba koso kake nafadamusu abinda nagani a apartment dinka na Abuja, remember vodka,cocaine and........dasauri yatoshe mata baki da hannuwa yana zazzare ido me yarinyarnan take shirin yine xata kwanto masa ruwa bayan yagamaiwa popsy likimo yanuna masa cewar yashiryu yadena shan komai tun a Nevada city,popsy ne yamiqw yana fadin sakar mata baki muhsin kinsaki yay aikuwa Aysha ta gantsara masa cizo bashiri yasake ta yana yarfar da hannun domin yaji xafin cixon sosai,xare mata ido yake kantai shiru tana galla masa harara shi dan rashin kunya har yasa baki akan maganar lalacewa shidin meye bayasha,mamana tatsinkayi muryar AJ yakirat,tajuya tana fadin yes popsy,yace fadamin meki kaga yana sha a Abujan kallon muhsin tai tana fadin an eye for an eye axuciyarta, tace nida ya Arsal rnr da yadawo muka kamashi abuge a part dinsa bemasan halin dayake cikiba,yana shan kayan maye ya Arsal ne yay requesting karna fada maka sbd xakai fishi dashi nikuma I want to help them alokacin even ya kudrat knows cewar muhsin yana shaye shaye,la ila ha illallahu Muhammadur rasulullahi s.a.w,ummi kecan dogon salati tana fadin dimple sharri akan dan uwanki meya maki daxaki jefeshi da mummunan abinda wancan yaron ke aikatawa,taqaraso tana fixgota jiri jiri taji yana dibarta dasauri taruqunqume mahaifiyar tata don kar ta fadi aiko kmr wani kashi yahau jikinta tatureta daba dan Anwar yayi saurin tareta ba daseta fadi,AJ wani irin tausayin diyarsa keshiga ransa yanxun tayaya xe iya barin amanarta ahannun wadannan mutanen wai yan uwanta da mahaifiyarta fa kenan yana tsoro matuqa yana tsoron Allah yadauki ransa diyarsa bata tsaya akan qafafunta ba,tabbas xekoma gurin ya sheikh lamarinnan yafara bashi tsoro, Kamo hannun dimple yay yana fadin kiyi shiri mamana kidena kuka,badai sameer bane bawanda ya isa yaraba ki dashi matsawar na bincika naga maganar nan bahaka take ba muje ko karkice xaki saka wannan maganar aranki kinji pls stop crying,yakama hannun ta suka fice bangarensa yawuce da ita dakyar yakwantar mata dahankalu yana nusar da ita tadena saurin breaking down haka she have to be strong,tace popsy sameer trust her,sameer love her meyasa laifina xe shafeshi meyasa xata batasa a idonka,yace mamana koma me suke nufi in sha Allah you'll be happy,I promise you indai hudallah wannan karan qarya tai baxanyi sparing dinta ba I'll definitely take action akanta koda ko hakan yana nufin batawa bint ne awannan gabar,dakyar yasamu yabata magani takwanta barci anan bangaren nasa. Adaren ranar Alh yakira mr Bunyamin awaya suka hadu a office, Mr Bunyamin yagama sauraron abinda AJ din yake fada masa gameda sameer,yace Alh ba kaffara wllh duk wanda yaxo maka da wannan xancen manufarsa daya yatarwatsa alaqar dakake shirin qullawa dawannan yaron tun kana Atlanta kasani nai maka bincike akan yaronnan a Abuja beyi shaye shayeba se anan watana biyu chif chif inabin duk wani motsinsa batareda yasani ba kuma haryau bandena bin diddigin sa ba yaronda ko xaman majalisa bayayi daga masallaci se makaranta se gida tunda yadawo kano banga wani abun zargi atattare dashiba Alh amma xan bincika taban garen yan unguwar tasu domin abincikena nafarko bawanda yafadamun wani abun ashha akansa amma tunda kace asake bincikawa tabbas xan sake dubawa,yace nagode Bunyamin kasan cewar wnn abun yashafi dimple kuma kasan yajja nake daukar lamarin dimple cikin heart dina yace nasani Alh nasani,in sha Allah wannan karon xaka jini da cikakken bayani da manufar me manufa akan yaran biyu xuwa gobe da safe yaqarasa yana kallon agogonsa xanxo makada cikakken bayani me inganci,wani sanyi Alh yaji yanajin kalaman bunyamin din nasanyaya masa zuciyarsa. Dimple tafito sanye da loose and comfortable na gym datake tabawa lokaci xuwa lokaci kanta daure da bandana kmr wata baby face dinta yayi wani haske da kyau na musamman,tana tafe daga gym center tafito tana answer wayar sameer ko dawasa bata sanar dashi abinda yafaru agidansu jiyan ba sbd baxataso yasan kalar family din datake dasu ba inconsiderate,kuma bata sanar dashi me hudallah tace akanshi ba maganar tafiyarta UAE suke ya lalace mata se fada mata yajja xeyi missing inta yake itakuma tanajin dadi tanamasa shagwaban aiba dadewa xatai ba,waist dinta taji anriqe tabaya lokacin datake yunqurin tura qofar part's dinsu,juyowa tai adan firgice tana sauke numfashi ganin waye anan din,tace kaine xakasa na shide kenan smiling yay yana jan hancinta tabata rai tana doke mai hannunsa cikin wasa har lokacin wayar nacii bata kasheba,tace yah Arsal bakyau how many times nake gaya maka here tafada tana nuna waist dinta batareda tadamu dakomai ba ba property dinka bane kadena tabawa ko,smiling yay yana fadin dame property din kenan kike waya tun daga gym nake binki bakima Lura dani ba,hannu yasa xe xare wayar akunnanta tariqe gam tana fadin mexakamin dawaya,yace honey maida wuqan da babe in naki xangaisa ko shima gaisuwar yaxama lefi,turo baki gaba tai yatsaya yana qaremata wani mugun kallo data tsana,kayan jikinta yakebi da ido kmr xecinye ta,cikin tsiwa take fadin haba ya Arsal kallon ya isa haka mana,karkasa na fadi,yace honey inkin fadi base na tare ki ba meye amfanin hannuwan da baxasu iya temakonki ba lokacin da kike buqata,smiling tai tana fadin wato kai ba acinye ka amagana ko,yajinjina kai yace amma infada miki a inda ake cinyeni da sirrin cinyeni,tace eh fada inaji abunda Aysha batasaniba lokacin da Arsal ke qoqarin karbar wayar yasakata a hand free batareda ita ta ankare da abinda yay ba,matsowa daf da ita yasoma yi tace Arsal stop what are you trying to do?smiling yay yana fadin secret din mallakana xanbaki,tace no Arsal banason ji yanxun yace sannan har yanxun baki bani gift dina dakikace innadawo daga US xaki bani,tace I thought we are done with that chapter I hugged you right,yace hug is not enough yana mata rumfa dajikinshi tajingina abango tace ya Arsal kabari mana,I can't kiss you now,yace why meyasa da xaki iya amma yanxun baxaki iyaba,tace because,because tana rarraba ido ganin bakowa agurin daga ita seshi tace I have a boyfriend now I belong to someone,baxanyiba,yace aidaman bance kiyiba nixan temaka miki gurin cika alqawarin dakika dauka a kissed on the Lip's ko,yaqarasa fada yana shafa dan qaramun bakin ta,kit sameer yakashe wayar daga dayan bangaren waye wannan meyake nufi xeyi da Aysh dinsa baxata iyaba sbd yanxun tana da boyfriend hakan yana nufin dasunayi kenan shedan yatunxura xuciyarsa yafara raya masa ga dimple rungume dawani qato wani kuma someone kisses her hasbunallah yafara anbato kansa nasara masa wutar kishi naru ruwa acikin zuciyar sa who the hell is Arsal koma waye yasan ba dan uwanta bane ubanme yahadata dashi dazasuke irin wannan maganar take anan yaji tsanar sa da kishinsa shi mutumin dabe taba ganiba yana mamaye zuciyarsa,daga daya bangaren kuma Arsal yakalli screen din wayar seda yatabbata ankatse yasaki dariya yana dungure ma aysha kai yace nime xanyi dake keda bakya brush dakyauma nafi qarfin ki bugeshi tai tai wucewarta tana fadin abinda kasan baxaka samuba hadashi da bakaso kuma kasake mun irin wannan wasan sena fadaka popsy tana hayewa samanta,yau su lilly bawanda yakwana gidan sunwuce gidansu meenah can xasuyi packaging kayan buqatarsu itakuma sukai da yamma xata tarar dasu washegari daga gidan du meemee din suwuce airport jirgin safe xaitasho dasu xuwa UAE. Qarfe biyu Aysha tagama shirinta tsaf tafito da trolley dinta se handbag din channel yar qarama meshegen tsada ahannunta sanye take cikin pink Malaysian abaya ta dan yafa mayafin abayar saman kanta amma begama rufe gashin ganta ba sbd ba nadawa tai ba gaban gashin se sheqin gyara ingantacce dayake samu yake yi,a packing lot's tahadu da popsy sukai sallama kan gobe da safe xasu hadu a airport gaba daya suxasu fara gaba shikum se yabiya Abuja yana dawani unfinished business daxe qarasa xuwa farkon satim January xebiyosu,Arsal ne da muhsin sukai dropping dinta har gidan haj maryam din suka juya muhsin nabashi labarin abinda yafaru jiya dadare dayajja aysha tatona masa asiri yace natabbata yanxun popsy xeqara sakan ido baxe barni nakoma us ba amma inyasan wata aibesan wata ba har yanxun Visa na be qareba xanse ticket nasamu kudade masu tarin yawa awannan auren don haka xanbarmasu matar sucinye nikuma xanware kawai naje naqarar da cash din hannuna,Arsal yace muhsin wai yaushe xakai hankaline girmafa muke dada yikaine babba gidan AJ kuma barganin irin tarin dukiyar da mahaifinku kedashi kullum girma yake qarawa kasani idan yadora wani cikin yan uwanka wands kasani duk maxane sunfika hankali da sanin yakama ta MUHASSIN kansa trait ne arayuwarka twin dinkane barganin kaine babba tare dai aka haife ku he can always be the heir ayanxun kabi kasiyar da duk wasu share's dinka na companies din AJ kacinye kudin sukuma duk abinda xefaru they are part of that investment kacigaba da shirme idan harba popsy kaida babu duk daya awannan companies din yace kumafa hakane aboki popsy yana wurgawa komai zekoma hannun MUHASSIN innai sake sbd shike aiki tuquru,toh yaxanyi Arsal nifa gaba daya business baya birgeni nafison kawai nayi life without any takura or something like that,banason stress ko kadan I never asked for any of this,yace muhsin muhsin idan baka nutsu ka shiga hankalin ka kakarba girmanka acikin yan uwanka ba haka xa araba gado kowa yasamu abun arxiqi kai kaqarar danaka a gambling bata fuska muhsin yay yana fadin Arsal kai ka kashe mana uba dakake batun raba gado,ina ai popsy bayanxun ba bar ganin nidashi bama shiri ina qaunar abina sosai Allah yajada ranka popsy senayi hankali xaka tafi gaskiya yafada yana girgixa kai,Arsal yace dude waya fara xancen popsy xewurga yace naji nine amma aidaman kowa xetafi kuma subutar bakine,kaikuma seka fini uwa wani dansa ina ma ruwanka da gadonmu tafada yana cigabada driving Arsal banxa yamasa yana saqa da warwara azuciyarsa yasan dole popsy yanemeshi sbd yagane yamasa qarya kan addiction din muhsin da drug dole yanemo abinda xefada masa yakare kansa inya tunkareshi,bedace ace tunkan yamallaki dimple shida popsy su fara samun matsala ba. Yaukam ihu agidan haj maryam bamasaka tsinke yanmatan suka baje ana hira kamarba jiya jiyannan suka rabu ba dimple tasake cikinsu kmr ba wani abunda ke damunta ana hira ana ciye ciye kmr ba gobe,Lilly cetai suggesting anbude sabon gidan abinci anan kusa dasu gusto suxo suje suyi testingvarieties dinsu meemee tadaka tsalle tana fadin aje aje,meenah ma haka dimple suka tsaya suna kallo ita hankalin ta nakan wayarta tundaxun take kiran sameer baya dagawa tamasa text no reply sosai tadamu sbd sunsaba wuni suna maqale dajuna tawaya,dimpy kinyi shiru cewar Lilly tana daka mata duka dagowa tai tana fadin wannan ma aimugunta ce kawai kidakeni mena maki tace magana fa muke miki tundaxun kina kallon waya xamuje gusto will you tag along or not,tace but se takalli fuskokinsu tasani sarai this day's bata bama friends dinta lokacin daya dace basa spend time kmr da,karsu fara jin haushin sameer yasa tace karku cinye ni shikenan aje amman kunsan semun tafi da qartincan da popsy ya ajje awaje,meemee tace ina ruwanmu dasu suyi ta binmu wahalace bata ishe suba taqarasa tana fadin kuxo muje mufadama Mommy aikuwa dukansu sukai dakin haj maryam aka tambayota baruwanta tace se sundawo suka sa ihu anafadin mommy Allah yabar mana ke tana dariya take fadin Allah yashiryamunku sukace ameen suka qule dakinsu meemee suna sabon shirin titan.

AYSAM Love,passion,betrayals,romance,hatred and power between two different worlds. It's Fatoums Passion's