AYSAM

Chapter 48

by @fatoumspassion

(My fault) Ahankali tabude idonta tasoma gani dishi dishi kafin ganinta yasauka tarwai akansa yana shirya kanshi gaban mirror ashirya tsaf cikin wani farin yadi me laushi wanda yake daya daga cikin kayan datafi qauna taga yasa saboda kyawun dasuke matuqar yimasa. daga kwancen take fadin "SAM ina kuma xakace bayan kasan akwai exam yau," juyowa yay don beyi tinanin ta farka ba yaqaraso gefen gadon. yana afadin "so your awake Aysh," "good morning," tace "morning bebey" tana miqo masa hannunta kamawa yay yana dagota xuwa jikinsa hannunta akan kafadunsa take maimata, "ina xaka? "Uhm case din baffane mungama waya dawani abokinsa anan maitama yake yasa baki sunce xamu iya xuwa muganshi amma dole se tareda ammi yanxun haka sunqaraso suna tasha xanje nadaukosu muje can efcc din," dan jim tai kafin tace "are you ok," yace "of cause" yana shafa cheeks dinta tasan sarai yana cikin damuwa don jiya tana ganinsa duk juyin daxatai idanunsa biyu yana danne danne a laptop bayason kawai tasan yana cikin damuwar don karta daga hankalinta.tace "toh Sam xanbiki," yace "aysh no kixauna anan kinga sauri nakeyi yanxun kanki gama ma mutafi sungaji dajira,i don wanna keep them waiting kinji," turo baki gaba tai cikin shagwaba take furta "nima inason naje naga baffan pls kaje dani," riqo waist dinta yay yana qara manneta da jikinsa yace "xakije kiganshi,i promise kinji amma bayauba," harara tagalla masa taxame jikinta anasa tanufi toilet murmushi ne yakwace masa domin wai ita aladole tayi fishi dashi,yace "haba babyn sorry mana,bayanma seda namaki girki before komai dana tashi,i cooked your favorite" juyowa tai tana dan tabe baki tace "meka dafa," yace "Honey pancakes,with hot americanno" ,duk yajja taso boye smiling dinta kasawa tai tatafi dagudu tarungumeshi tana fadin " I love you,Allah yadawomin dakai lpy,Allah yafitar da baffa daga wnn halin dayake ciki," ya amsa da ameen yana kissing forehead dinta,har tsakar gida tarakashi tana tina masa kar yawuce 2 sunada exam's yace in sha Allah baxe wuceba. Bayan tafiyarsa duk setaji gidan yamata fadi tashiga tai wanka tafito farar T shirt din daya cire jiya tadauka bayan tagama shinshinata tanajin sansanyan qamshin sameer dake tashi jikin rigar xirawa tai takawo mata har gwiwa tadauki system dinsa takoma parlor, kitchen tashiga tadebo breakfast dinta taxauna saman kujera tasoma karatu tana yi tana kallon agogo,ahaka har akai kiran sallar azhar miqewa tai ganinsu lilly sunsoma kiranta domin sunyi timing endless celebration na final paper ennan sosai. daki takoma taciro musu gogaggun uniform dinsu daya wanke yagoge tun wancan satin tasa asaman bed tashiga tadauro alwala,ta xo tai sallah ganin har 1:30pm bedawoba yasanya tasoma shiri cikin uniform dinta tatsaya gaban mirror tana qarema kanta kallo wani irin glowing skin dinta yaqara yi abin yabata mamaki,gawani murmurewa datake kuma yi,tashafa cheeks dinta tana fadin "karfa kiyi qiba babyn yace yadena sonki, i need to keep on diet as soon as possible," waya tadauka tasoma danna masa kira kira baya picking ganin haka yasa takoma parlor taxauna,skirt din uniform din yadan kamata sbd jikin data dan qara hakama rigar ,batasa hijab ba sbd kar xafi yadameta kafin yadawo tadaiyiwa kanta ponytail amma harta da sock's da takalmi taxira,motsin bude qofa taji dasauri tamiqe domin tasan baxe wuce shiba tunda shikadai keda makullin gidan,kallon agogo tai taga biyu da minti 20 xata bude qofar parlor shima yana qoqarin budewa karo sukaci tababbake aqofara tana riqe qugu alamar se yanxun ko, dariyama tabashi yadan karkatar dakansa alamar banhaquri domin yagane batasan bashi kadai bane,agogo tanuna masa tana fadin "banace karka wuce 2 ba sokake muyi late ko," muryar moon taji tana fadin " yaya kamatsa inshigo mana," dasauri aysha tamatsa tana fadin "moon," shigowa yay moon tabiyoshi abaya mama dake tsaye tana sauraronsu tachoge bakin qofa. rungume juna moon da aysha sukai,c ikin alhini aysha kemata gaisuwar rashin daddy dasukai,ta ansa tanai mata godiya ganin ammi bata shigoba yasanya sameer yafita yana sake lallabata kan tadaure tashigo in sha Allah xuwa goben xasu bari taganshin. shigowa tai fuskarnan ahade kmr bata taba dariyaba, aysha jikintane yay sanyi ganin irin mugun kallon da ammin kebinta dashi,ahaka tadaure tana yimata sannu daxuwa tanuna mata gurin xama. xama tai tana tabe baki,aysha tadurqusa ganin yajja sameer keyi inxe gaidata, tace "ina.... inayi ammi ya haquri," tace "da godiya ba yabo ba fallasa a muryarta," tace "ashe haka abu yafaru da baffa,Allah yakiyaye yatsare sannan Allah yay gaggawar fito da mafita in sha Allah xefito ammi," tace "ameen" tana dauke kai. sameer ne yakalli aysha yana fadin "bari naje na saka uniform dina,I'll be quick" bata iya dagowa takalleshi ba yawuce ciki tananan tsugune gaban ammi, moon ce tace "dimple samomin ruwa insha pls kishi yadameni " dasauri tace "toh tana miqewa," kitchen takoma tabude fridge tadakko masu ruwan roba mesanyi wanda take sha ta ajje agabansu, bata iya shan ruwan leda ba hakan da sameer yafahimta yasa yake iya aqoqarinsa wurin ganin ya ajje mata wanda tasaba amfani dashi akoyaushe, moon dauka tai tana kwankwada. komawa tai kitchen tadebo musu lemon ginger meshegen sanyi ta ajje agabansu ammi ko kolla be isheta ba, aysha taxauna gefen moon tana wasa da yatsunta, kana kallonta kasan adarare take gaba dayanta,sameer ne yafito cikin full suit uniform dinsa yana fadin "aysh I'm done shall we," miqewa tai tana kallon su ammi tace "sameer matafi mubarsu cikin kadaici kuma," moon tace "haba dimple aimu ba baqi bane karki damu kije kiyi jarrabawar ki bakomai wallahi," aysha takalli ammi tana fadin "ammi xamu wuce," tace "toh," sameer ne yamiqo mata hijab dinta yana fadin "kinmanta," girgixakai tai tana fadin "inasane dashi," yace "toh ammi munwuce pls kicire damuwar komai aranki in sha Allah komai xai warware" tace "uhm hakadai kace," Allah yakiyaye yabada sa'a jiki asanyaye aysha ta rataya daya daga cikin chanel handbag dinta tunna gidansu tafito seda suka kai bakin qofa taji yariqe mata hannu tajuyo tana kallonsa,yace " I'm sorry," yana qasa dakansa,tace "for what? yace "nasan by bringing my whole family here hakan xe iya takura miki amma bayajja xanyine nasan alaqar dake tsakanin ki da ammi batada kyau sosai,nasan your nervous around her aysh,munje suncanxa mgn kusan I spent half of my day roaming around efcc da maitama qarshe madai cemin akai Alh babaye yayi tafiya wanda natabbatar bahaka bane aysha,ina qoqarin neman mafita amma abin yaci tura,aysha ammi is worried, tace baxata koma kano ba harseta ga baffa daman gidan Alh suke xama idan yanagari,toh yanxun they have no place to stay dan Allah ina roqar alfarmar ki daure kiyi haqurin xama dasu har suga baffa," dasauri ta girgixa masa kai tana fadin "sameer kadena roqata,I'm your wife duk abinda yashafeka yashafeni,your family are mine donhaka we'll stay together harse lokacinda komai yawarware," jawota yay jikinsa yarungume yana fadin " Allah yay miki albarka," fitowa sukai cikin sa'a suka samu mai taxi har cikin imperial yakaisu 3:00pm daidai suka qaraso,dake exam din ta 2:30 har ansoma, suna shiga ICT lab en tsit kakeji, kowa idonsa nakan, System dinsa,kowa yasan sit number dinsa da number system dinsa hakan yasa ita tana gaba gaba shikuma yanacan baya, invigilator ne yaxo yasanya musu passwords dinsu questions din yabude suka soma jarrabawar. Hudallah da Arsal ne xaune gaban CCTV camera room na imperial gaba daya. AD smith dawata xufa takaryo masa yakalli hudallah yana fadin "are you sure akan abinda kikeso ayiwa yaronnan," Arsal cikeda fusata yake fadin "harsau nawa kakeso tamaimaita maka wadannan tambayoyin she's very sure kawai kadanna," yace "arsal ina tausayinsane after everything dayay going through ace mubata a final paper dinsa," hudallah kallonsa tai tana farfara ido kafin tataso taxauna saman lap dinsa, arsal wani kyamarta yaji yasake yi ganin kalar rashin ajinta ashe shi yadade yana xalintar kansa dabin wacca bata cancanta ba, AD smith wani wicked smile yay yana danna wa yay hacking laptop din sameer. Daga bangaren hall kuwa lokaci daya,laptop dinsa tahau qara,sosai takeyin jiniya hakan yasa hankalin security da invigilating director's shigowa ICT din da sauri shida abin yadaure masa kai ganin yana cikin exam different abubuwa nata popping cikin system din yatsaya chak sukansu students abin yadaure musu kai, security hoto suka faraiwa system,invigilator ya umarci sameer daya miqe sufita gudun distracting other students, students naganin hakan sunsan exam malpractice aka kama,aysha dake gaba bata hango abinda ke faruwa can baya,bata damuba taciga da exam dinta tana metausaya wannan wanda yay babbar asara don tasan straight korace tare da bacin suna daxe biyo atakardun duk wanda aka kama, taqofar baya suka fitar da sameer, bayan tagama exam's tana submitting tamiqe tana me kallon baya ko sameer yagama ganin benan yasa tace "my guru husband harka gama kenan," fitowa tai taqofar gaba me makon ta tarar da celebration se dandaxon dalibai data gani group group ana magana qasa qasa can tajiyo wasu kmr suna rigima,kalmar data faraji taruda kwakwalwarta itace "ashe daman kwakwalwar duk tabogice tasatar answer Allah yatoni asirin sa sameer S fulani dubunsa tacika," can tajiyo muryar xahrah cikin fada take fadin, "wllh gaba dayanku baku da kirki sameer duk qoqarin sa yarasa me xeyi se satar answer gaskiya nidai banyarda ba sedai in sharri akaimasa wannan subject dinma karku manta duk shiyake mana tutorial dinsa amatsayinsa na TA, meyasa xesaci answer," watace ta ke fadin "ketafi can duk bugece,wllh nidai nayarda daman qoqarin nan da akecewa yana dashi yawuce misali ashe ashe qungurmin barawon answer ne," jakar hannunta ce tafadi qasa jin maganganun da student keyi akan Sam dinta tasoma girgixa kai no sameer dinta wannan kaddarar tafada it can be him, "dimple,dimple" taji ana furta wa daga nesa lilly ce taqaraso tana haki,tatsaya tana kallonta kmr statue,hawayen lilly yaqara daga mata hankali tace "lpy" tace "it's meenah and meemee yanxunnan dad dinsu ya aiko da wasu soldiers suka tafi dasu,they sort of kidnapped them,they are going back to the US with their mother this evening," wani hawayene yaballemata shaaa kikeji,lilly ganin halinda dimple ke qoqarin shiga take fadin "I try to stop them har mommy nakira,dimple tarabamu dasu tace idan munason mucigaba da alaqa dasu sedai mubiyosu US Abinda baxe taba yiwuba kenan kinsani nasani because baxaki iya tafiya kibar Sam ba nikuma i can't go without you," taqarasa tana rungume ta dimple cikin sanyi take fadin lilly "thank you!. Cikin sanyin jiki take tambayarta kotaga wanda aka fitar daga hall for malpractice tagirgixakai tana fadin "I was in front sit meya faru," janye jikinta tai anata tana yin gaba tace " it's sameer" lilly daskarewa tai tana bin bayanta office din interrogation suka nufa bayajja basuyiba aka hanasu ganin sameer, Mr Raphael sukeje suka samu, aysha nakuka take roqarsa yabari taga sameer yace "taya haquri case din yabar hannun makaranta hukumar jarrabawar ce xata dau mataki,tareda bata haquri yana metabbatar mata yayarda da sameer dari bisa dari baxe taba aikata abinda ake xargiba kuma yamata alqawari xeyi iya yinshi gurin ganin anwanke sameer daganan office din Abuya suka nufa bayajja basuyiba fafur sakatariyar sa tace yana conference bawanda xeshiga,bayan ada kome yakeyi they have no limit suda office dinsa," wayarta taciro hannunta narawa tasoma dannawa Arsal kira, yadaga cikin kuka take sanar masa da duk abinda yafaru tana fadin "ita mutuwa xatai idan ba abarta taga sameer ba baxe taba satar answer ba yatemaka mata" cikin nuna alhininsa yake fadin "taya haquri tadena cewa haka in sha Allah xetemake ta he'll find a way tana ina gashinan xuwa tasanar dashi tana qofar building din Abuya," cikin qanqanin lokaci kasancewar yana makarantar yaqaraso lilly dai duka adarare take, suka shiga motarsa yay driving suka koma interrogation room din, wayarsa yadaga ya answer few phone call's before yace "tashiga taganshi xasu barta," ahankali tafito tana kallon samudawan masu gadin Gurin tana binsu da harara taqarasa akaimata jagora har cikin dakin duhun, babu komai sewata jarfitila dake kawowa da daukewa agurin,sbd bawani jonin wutar arziqi agurin tamkar prison yake tafin hannunka ma baka iya gani,gashi yamma takawo kai,xaune ta hangoshi aqasa yana yahada kai da gwiwa,cikin rawar murya take fadin "sameer" dasauri yamiqe sbd betaba expecting xasu barta taganshin ba, qarasawa tai tarungume shi yaqanqameta yana fadin "aysh i didn't do it,someone trap me aysh,sunyi amfani dasanina da computer sunqullamin kan cewan xan iya duk abinda nakeso alokacin danaso da ita bantaba mis using knowledge dina da technology ba daidai darana daya aysh they set me of,I'm tired dawannan abubuwan seda sukaga karatuna yaxo qarshe all this while,aysh idan har narasa wannan damar banida hanyar surviving,aysh pls kiyarda dani," "shsshshs" tana dora yatsanta saman lips dinsa tace "I trust you,nasan baxaka taba hakanba kuma gaskiya xatai halinta in sha Allah I'll fine the culprit," yace "aysh menai musu," tace "ba abinda kai sameer your a good person and i know you'll surely be something great kmr yajja popsy ke fada," shiru yay yana dora kanshi awiyanta yana shinshinata daddadan qamshinta mekwantar masa da hankali,tace " meyasa baxasu barka katafi gidaba," yace "suncemin indai inason suyi freeing dina without suieng me dolene nakarbi laifin cewar nayi malpractice kinsan kuma idan nai admitting abinda xebiyo baya they'll ruin everything I work had for," tace "karkayi kaimun alqawari baxaka taba karbar laifin daba nakaba" yace "I do aysh," bamban taji bugu aqofa yana furta "miss AJ your time's off" riqe hannuwansa tai gam gam,yace "take good care of my mum she really need me now inason kimaye mata gurbina arayuwa," "miss AJ" cewar security cikin daga murya, kissing lips dinta sameer yay yana fadin "promise me aysha," tace "i promise Sam," security shigowa yay yana nuna mata hanya tafito tana hada hanya sbd jirin dayake neman kwasheta, amotar arsal taqarasa fashewa dakukan shida lilly se haquri suke bata dakyar dai tasamu tai shiru, Arsal yace "lilly tatafi da ita gurinta sbd she can't stay alone abaqon guri," girgixakai taitana cemasa yakaita gida kawai don sunada baqi acan bayajja beyiba gurin ganin taxauna anan taqi suka wuce shida lilly suka rakata har gida kafin yadawo ya ajje lilly a nasu gidan, daganan yakoma gurin sameer yana xuwa security suka bude masa qofa cikin ixxa da isa yashiga gurin beyi mamaki ba ganin duhun gurin, ahankali domin fitilar datake kawowa tadauke tagama mutuwa, jin motsi yasanya sameer miqewa yana fadin "wayenan," arsal smiling yay duk da baya iya ganin sameer yasan atsorace yake,yace "your wife's future husband in sha Allah," cikin mamaki sameer yake fadin "wannan wana irin jahilcine" yace "yahaquri yaro bangama magana ba idan arsal noon namagana ba a tanka masa musamman matsiyata wanda basukai matsayin ma sukula shiba," sameer cikin wani calmness yake furta " shi matsiyacin wanda bekaiba shidin akaxaba akabar mekudin dayakai," arsal murmushi yay yana fadin "yaro yarone kaihar yanxun kana tinanin akwai wata soyayya bayan ta kudi awannan duniyar toh kuwa kayi kuskure megirma,kudi nada power da daraja metarin yawa,biyayya ga kudi yasa katsinci kanka ahalin dakake ciki,I set you up kuma inada wani daddan albishir daxan baka dangane da tsohon dattijon ubanka dake efcc,ciwan sa yatashi yanxun haka ma yana babban asibitin gwamnati dake garin abuja," cikin halin rai da mutuwa hakanne yasanya hukumar wasa da hankalinku sbd baya ciki" cikin kaduwa da rashin gasgata abinda arsal kefada sameer yace "qarya kake mahaifina nada lpy kuma gobe gobennan xanje naganshi kasani shikuma karatu idan karabani dashi gaskiya xatai halinta kuma aysh promise me xata bancika taganomin wanda ya aikata hakan kuma idan har tagane cewar kaine ka shiga uku she'll hate you," dariyar qeta arsal yayyana furta "nine source of binciken dakake cewa xatai nine nataimaka nasa akabarta taxo nan kana tinanin xata yarda dakai sama danine," yace "tabbas aysh seta yarda dani sbd nine mijinta," yace "inkagama iko da auren fankon,deal naxo muyi inkuma bakashirya ba xankwata taqarfi da yaji," yace "kamarya deal bangane ba," yace "yanxun xanganar dakai,inason kasakarmun aysha in return xansa hannu asaki mahaifinka tareda wanke sunansa,sannan xansaka abarka da karatunka nikuma kabarmun ita," tabbas sameer da yana ganin inda arsal yake ba abinda xehanashi ruba mishi baki dawadannan qaxaman kalaman dayake fada, begama tinani ba yajiyo wata muryar alamun wani yashigo "nikuma naimaka alqawari xanbaka jari,metarin yawa wanda xakaxama attijiri akaf fadin danginku,xansiya maka gida da mota inma wani auren kakeso xanmaka kafadi farashinka,karabu da sister na" koda ba afadaba yasan muhsin AJ ne cikeda takaici sameer yaxauna aqasa duhun dakin nasashi jin wani irin jiri jiri,yace "aysha batada farashi agurina kusani babu abin duniya wanda xe iya rabani da ita kunada kudi kunce kudi namaganin komai toh banda wnn matsalar taku domin aurena da aysha kmr rubutune akan dutse," "qarya kake dan matsiyata" cewar yaya muhsin "kaida baka gaji arxiqi ba toh kaxuba ido kaga yajja xamu sakata taji tatsaneka tatsani rayuwar talauci datakeyi ayanxun badai taqamarka kanada muhallin sataba kana iya siya mata abinci wanda ada irinsa koma wanda yafishi karan gidansu yakeci,toh duk abinda yabiyo baya ruwanka mara tinani kawai," jiyay andafashi yamiqe dasauri muryar arsal yaji yana fadin "amma katafka asara mafi muni arayuwarka" kafin yaji anbude qofa sunfice. Adaki arsal keta juye juye yakasa tsaye ya kasa kwance tabbas sameer nada mugun taurin kai,jawo hankalinsa bashine ba gara yalallaba yabi plan din hudallah wanda abaya yaga kmr baxe bulleba amma tabbas aysha kadai zasuyi blackmailing susamu abinda suke so,waya yadaga yana karawa akunne cikin narke mata yake fadin "honey kixo mana i want you." Aysha ce tafito daga wanka jikinta asanyaye take tinawa da irin yajja mama taxuba mata ido lokacin data gama fadamusu abinda yafaru amakaranta moon ce taringa rantsuwar yayanta baxe hakaba sharrine, hammanta kaxa hammanta kaxa,mama qala batace se Allah yasawwaqe kawai. kitchen tashiga moon sanin bata iya girkiba yasanya tun suna gida tashiga tarangada musu girki mekyau, aiko aysha taji dadin hakan suka fito a plate daya sukaci abinci ammi kuwa dahar lokacin bata motsaba yasanya aysha nuna mata hanyar bed room dinsu tace "koxata shiga tahuta itada moon sesu kwana a parlor," cikin bacin rai ammin kefadin "idan ba qaddara bama mexe kawota har gidan da don tsabar tarenata shine ma take cewa tashiga dakin da danta kehada shimfida dawata toh ahir dinta ita idan agarinsu fitsararru ne haka ake toh ita bahaka takeba," aysha sosai tadiririce tana kwalla tasoma bata haquri kafin ammin taja tsaki tadau daddumar datai sallah takoma tsakar gida, fashewa dakuka aysha tai tana binta tsakar gidan ba irin lallashi da banbakin da bataimata tace baxata koma parlor dinba anan xata kwana moon ce taxo takamo aysha tadawo da ita ciki tana bata haquri tace "kidena kuka akan abinda ammi keyi kinji kisani abubuwa dadama sunfaru gawannan abin dayasamu yaya tana ganin kamar duk lefinki ne tana Neman wanda xata daurawa lefine," aysha cikeda takaici take fadin "I tried my best moon mahaifiyarku bata sona bata qaunata yaxanyi," tace "kidena fadar haka dimple in sha Allah xata soki xata qaunace ki," tace "when? tace "someday in sha Allah" murmushin takaici tai tana fadin "banajin that day xetaba xuwa" tamiqe tana shigewa daki. meyasa wadannan abubuwan suke faruwa dasu haka shinmeye laifinta gurin ammi dontana san danta kawai tana matuqar buqatar dan uwa yanxun wanda xebata shawara akusa wayarta tajawo tana dannama hudallah kira seda tai ringing tagama batai picking ba aiko se gata tabiyo kwance take jikin arsal sai spoiling dinta yake da salonsa irin na namijin duniya tanata narke masa shine yaji ringing din yana dubawa yaga dimple tana katsewa hakan yasa yakatse duk abinda sukeyi tareda saka hudallah agaba tabita taji me yafaru kodai matsalace tataso. Tace " dimple lpy ykk," Cikin muryar kuka take fadin "hudallah maman sameer batasona," hudallah acikin ranta tsaki taja tana fadin " Allah shiqara amma afili setace ayyah meyafaru ne maman sameer din tai kuma" nan takwashe duk abinda yafaru tafadama hudallah, wacca afili murmushi kawai take xubawa jin rayuwar data soma tanadarwa dimple yafara aiki quncin,kuka,baqinciki itace abinda take fatar taga dimple tadawwama akai, "kiya haquri kinji dimple,amma gaskiya kema da lefinki koh ummifa bakya dagawa qafa idan taimiki abu shine xaki biyewa uwarmiji taringa takaki where is my little sister,tana fada miki kimayar mata raga matan dakike yine yake sawa tatakaki yajja take so kinaji dimple," jim tai kafin tace "sameer love's her more than me idan yaji nawa mamarsa rashin kunya he'll be very disappointed in me," tace dimple nima bance kimata rashin kunya ba kawai kibawa banxa ajiyarta" tace "anya hudallah he ask me to take care of her" tace "shikenan tunda bakyajin shawara kinsan baxakiji ba kuma kika kirani," tace "I was hoping ko xakixo ki tayani lallabata ko xuwa gobe,tunda aunt dinkice" tace "tam idan nasamu lokaci xanshigo kinji kidena damuwa aranki baby sis kinsan inaji dake sosai" murmushi tai tana fadin "thank you," tace "toh take care of yourself good night" takatse wayar tana sake komawa jikin arsal wanda tunda yaji muryar dimple yaji abun duk ya isheshi itakadai yake da buqata arayuwarsa ganin abinda hudallah ke shirinyi yasanya yamiqe yana fadin "I'm coming" yay wucewarsa bathroom yana sakarwa kansa ruwa medumi, tabbas dole yasan yajja xeyi yayi amfani da both muhsin da hudallah awajen buga game dinsa batareda sungane hakan ba musamman muhsin dayake mara wayo daya saba buga kansa bakamar hudallah dayake kaffa kaffa da itaba. yana fitowa yakalleta tana nan yajja take tacika tai FAM cikin hade rai yake fadin " xanje hospital I'll take care of something's xaki iya kulle qofa domin acan xankwana" tsaki taja tana fadin "seka dawo" takwanta shikuma yawuce abinsa. Qarfe goma daidai ammi naxaune takunna redio din wayarta tanaji sauran dayake cizonta take bugewa da hannu,amma tsabar taurin kai taqi shigewa ciki,kwankwasa qofar gidan taji anayi sosai gabanta yafadi tinawa da sameer begidan yasanya tamiqe dahanzari taqarasa tana fadin "waye? banxa akaimata ba a answer ba taqara cewa waye nanma shiru moon ce tafito tana fadin "ammi kibude kodai yayane? bude qofar tai ahankali ganin mutum yajuya baya yasanya tadan ji tsoro kafin yajuyo tatsaya tana kallonsa, tundaga kan wani arnen crazy Jean's dayake jikinsa,wata wide open neck shirt ce ajikinsa wacca takeda dogon hannu amma rabin faffadan qerarran jikinsa awaje yake, kansa yatara suma me tarin yawa akansa anyi kitso da kusan rabi rabin kuma an daureshi da ribbon fitilar dake qofar gidan yasa ammi sake qare masa kallo yana yamutsa fuska da alama kallonsa datake ya isheshi straight xaki iya siffantashi da irin black Americans dinnan skin dinsa hutu yaxauna cikin gadara yake fadin "ina masu gidan? cikin harshen turanci ammi cikin tsoro take fadin "maimunatu xokiji meyake so turanci yake,tambayeshi gurinwa yaxo," moon ce taqaraso tana qarasa qare masa kallo kafin tasaki murmushi tace "yayan aysha ne ammi,twin's din AJ ina ganinsa a magazine" xaro ido ammi tai tana fadin "mekikace" tace " eh nasanshi a magazines sannan ina ganinsa a IG koba kaine muhsin AJ ba" kwabe baki yay yana fadin "ina qanwata? ammi jinjina kai tai tana fadin "tirqashi yanxun haka bintu talalata yayanta yaro kmr bayahude ashe ita tananma fitsarar dasauqi," aysha data jiyo kmr hayaniya tafito aiko suka bar bakin qofar ganinta, sanye take cikin silky night gown data kawo mata harqasa kanta bako dankwali tamanta cewar ba ita kadai bace yanxun agidan, ganin muhsin aqofar gidan yay matuqar bata mamaki,cikeda mamaki take fadin " yah muhsin what are you doing here?cikin wani irin tone da tamanta rabon dataji yayi magana acikinsa yake fadin " popsys princess baxa kixo kiyi hugging brother dinkiba didn't you miss me" wani kukane yakwace mata sbd tsananin kewar mahaifinta dataji ta mamayeta awannan lokacin girgixakai tai tana juyawa, "you should go kace you have nothing to do with my life mekakeyi kuma anan," dasauri yashigo yana jawota xuwa jikinsa tafashe dawani mugun kuka tana shashsheqa kallonsu moon dasuka xuba masa ido yay qasa qasa yaja tsaki yana fadin "jekisa dankwalinki kisameni amota," yasaketa yana ficewa daga gidan komawa tai taxira hijab, ammi kefadin "ke ke ina xaki,kudaman haka ake auren kintambayi mijinkine daxaki sakai kibi wancan me kalar arnan," kokallon ammi batai ba taiwucewarta. Qofar motar tabude tashiga yakalleta yana fadin "aysha are you enjoying life now," kallonsa tai tana daure fuska tace "i thought you didn't care, why did you ask? yace "hummm dimple kenan kisani kedin bad omen ce arayuwar sameer sbd daf yake dayarasa komai ta dalilinki," tace "kamarya," yace " kamar yajja kikaji nace atinaninki all this things dasuke faruwa daya bayan daya is fate" xaro ido tai tana kallonsa,yace "is not fate is our plan me and your mum," daqarfi taware hannuwanta tasoma dukan qirjinsa tana fadin "you bastards how dare you! me sameer yamuku you've ruined his life,meye baban sameer yayi maku daxakuyi involving ensa," riqe hannunwanta yay daqarfi guri guda tana sakin kuka yace kekadai xaki iya stopping en wannan abun idanba hakaba I'm ready to kill sbd kidawo garemu," kuka tafashe dashi tana fadin "yah muhsin popsy berene ka donka xama monster ba meyasa kake biyema ummi kaidin ba yayana bane dana sani your just a monster" tasoma kici kicin bude qofa yadatse yana fadin "kisaurareni kinajina dimple,idan har kika amince kika saka sameer yasakeki nikuma nayi alqawarin xansa hannu asaki mahaifinsa I'll provide good life for all of them,xanbiya duk wani tara da xa aci sufyan,sannan xanwanke sameer daga uqubar dayake ciki xetafi canada karatu with his full scholarship,he'll built a better life there, kinsan yayi deserving fin haka,your the evil eye cikin rayuwarsa indai har kinasonshi toh baxa kibari wani abun yasake faruwa dashiba" yafada yana bude mata qofa, juyawa tai tana kallonsa ido cikin ido tace "over my dead body" tana tofar da yawu aqasa taikomawarta ciki,ammi dai dataji sauro xehallakata tini takoma parlor takwanta. daki tawuce fuuuuuu haka takwana ko rintsawa bataiba tanajin tsanar muhsin da mahaifiyarta na baibaye xuciyarta tabbas she should have known cewar all this shirine nayan uwanta gurin ganin sun rabatada sameer kuma kohda xata mutu batajin xata iya rayuwa babu sameer har abada. Da asubah farin taji ana shafa mata fuska, dasauri tafarka tana kallon sa ajiyar xuciya tasaki tareda fadawa jikinsa don daman barcin barawone yay awon gaba da ita gefin asubah,yace "shshhshs ya isa haka," "Sam kadawo,I'm so scared, Sam I couldn't sleep all night, kaci abinci mesuka maka sungane gaskiya ne" girgixa kai yay,tace "meya faru toh," yace "ayeesh xasu yanke shawara next week sunce inje amma konasa hannu kobansa ba sesun koreni tareda batamin paper's duka," hawayene yaxiraro mata ahankali yasa hannu yasoma gogewa yana fadin "stop it mana haba babyn kaddarane,Allah daya haliccemu yana kallo xebullo mana dawata hanyar kisani mutum baxe taba gujema fate dinsaba," da yayi deciding fada mata abinda su arsal sukai masa yau amma ganin damuwar datake ciki yasanya yay going against it don baya tinanin kwakwalwarta xata jure she'll hate her brother abinda baxeso yafaru ta sanadinsa ba,aranta take fadin "Its not fate sam,its me,its all my fault dana shigo rayuwarka nasa suka batata sallar asubah suka farayi bayan sun idar ganin bata samu ishashhan barciba yasanya yajata xuwa bed dakyar yalallabata tai barcin shikam ko rintsawa beyiba yana tinanin maganganunsu tabbas dole yaje general hospital gobe don sannin gaskiyar maganar arsal gameda baffa. Lokacin data farka nemarsa tai tarasa adakin ahankali tamiqe xuciyarta namata wani irin nauyi taqarasa bathroom wanka tai tafito ganin har lokacin beshigo ba yasanya tafito daure towel tana fadin "babyn where are you?" da ammi taci karo tanata jin radio dinta,kallo daya tai mata tadauke kai itama dauke kan tai tawuce kitchen. a kitchen tatarar da moon tana girki tace mata "ina kwana" tace "inakwana moon,kinga yayanki kuwa" ,tace "eh daxun da sassafe naga yashirya yafita yacemin nace miki he's in a rush xeje yadawo" gabantane yafadi tanajin kamar akwai wani abun dake shirin faruwa, se asannan moon takalleta tana fadin "aysha ahaka kika fitowai ammi na parlor bedaceba kinji" tace "toh" tana tura baki tafito, se asannan tatina bata gaisheta ba tace "ina kwana ammi," qin ansawatai dimple bata jiraba tai shigewarta ciki don Allah nagani baxata iya son wanda besonta ba tayi iya yinta,garama sameer yaxo don gara itadai takoma gidansu lilly indai har lokacin tafiyarsu beba baxata taba jurema wannan wulaqanci na ammi ba. Tana xaune saman stool din mirror tana shafa lotion aqafafuwanta tajiyo qara daga parlor,dasauri tafito don ganin meke faruwa moon ce ta kifar da tray din breakfast din data hado jin wayar da ammin keyi hannunta nakakkarwa tana neman xubewa agurin dasauri aysha da ammin suka tareta lokaci daya ayshan tana tambayar meya sameta wani matsanancin kuka ne yakwacewa moon tana kallon ammi kicemun abinda naji bagaskiya bane kicemun mahaifina yananan lpy ammi, ammi cikin halin tausayawa diyar tata take cewa "yana asibiti ashe tunxuwansu abujan beyi lafiyaba mutanen nan suka boye mana,moon babanku yana cikin wani hali namutuwar barin jiki yanxun sameer kefadamin," faduwa yay sanadiyyar jin abinda yafaru da Alh dikko, ga cancer dinsa tarigada taqarasa matakin qarshe qanqanme aysha moon tai tana fadin "aysha wannan wace iriyar qaddarace take biyo rayuwarmu,kina gani aysha we are simple people me mukaiwa wadannan mutanen me mahaifina yatabai musu idan baffa yatafi yabarmu daidai yakeda tarwatsewar rayuwarmu gaba daya baxan iya rayuwa babu shiba,aysha ba yan uwanki masu kudi bace,aysha do something for us,aysha you are a heir a family din AJ one say daga family dinki xasu saka asakar mana mahaifi aysha kitemaka mana " taqarasa tana jijjigata qamewa tai qam tana qoqarin analysing kalaman moon daya bayan daya dawanda yah muhsin yay mata adaren jiya cikin tsawa mama take fadin "maimunatu kishiga hankalinki cemiki akai baffannaku yarasu ne kike mana wannan kuka kuje kushirya sameer nacan baxe iya dasuba dole yana buqatarmu" ay dasauri aysha tashige daki shafa man dabata qarasaba kenan kayanta taxira sannan taxurmo qaton jelbab hijab enta tafito tana ta tinani tabbas abinda yan uwanta sukai wa ahalin sameer Allah baxe barsu da haqqinsu ba baxata bari tanaji tana gani arabasu da mahaifinsu ba, tasan xafin rashin mahaifin kuma haryanxun tana fuskantar quncin rasashi,idan da akwai idon mahaifinta waye ya isa yabiyo rayuwar aurenta da bita da qulli haka,she'll do whatever it take's don tafitar da su sameer daga wnn hali batareda taqarbi offer din yaya muhsin ba. Dakyar suka samu taxi takaisu straight xuwa general hospital, waya ammi taiwa sameer yafada mata ward din dasuke taqaraso,lokacin yana office din doctor,aqofa suka tsaya jiransa ahankali yafito jiki asanyaye kansa aqasa dagowar daxeyi taga yajja fuskarsa tasake fadawa,tayi jajir kana gani kasan yayi kuka idanuwannan sunyi ciki ciki yana qoqarin boye kwallar data kawo idon, wani abu taji yatsaya mata aqirjinta dakyar tasamu gefe tatsugunna tana ambaton sunan Allah baxata iya jure ganin abinda tafiso duk duniya yana suffering saboda itaba, jitai mama tana maimaita kalmar "innalillahi wa inna ilaihirra'ji un" kukan moon nasake mata yawo akwakwalwa sosai tafarajin numfashinta yana daukewa maganganun su nayawo akwakwalwarta AMMi a'ina xamu samo wadannan kudaden sameer, MOON one say daga family dinki all this will end YAH MUHSIN Kace baqar qaddarar dake cikin rayuwar Sameer SAMEER duk abinda xefaru karki barni,aysha we will survive everything and every hard moment together I love you kiyimin alqawari. Ahankali take bude idanuwanta taqurewa fankar sama dake cikin daki tana xagaya ido,dakin shiru ba motsin kowa ajiki seyanxun take tinawa ashe sumewa tai agurin baban sameer meye yasameshi kudin kuma me ake nema abinda take tambayar kanta kenan before tai saurin yunqurin miqewa, riqeta taji anyi tana fadin "koma kikwanta haryanxun jikinki bakwari" dagowar datai ga mamakinta ammi ce kefadamata hakan, fuskarta ba annuri ko kadan, cikin son neman ba'asi take fadin "ammi meyasamu baffa dan Allah kifadamin," jim ammi tai kmr baxata bude baki ba sekuma tace " aiki sukace yake buqata wanda yake buqatar maqudan kudade" xaro ido tai tana fadin "kmr nawa ammi," jim tai kafin tace "mexakiyi dakike tambayar nawa kisani shigowarki rayuwarmu ba alheri bace aysha nidaman nafadawa safiyanu cewar ahalin bint ba abinda suke kawowa iyali se tarwatsewa da matsala kinxama baqar qafa arayuwarmu tunda sameer ya aureki hankalinmu betaba kwanciyaba daidai da rana guda bantaba barci me dadi ba, ayanxun sunce xasu barshi afita dashi anema masa lpy da sharadin anyi gwanjon komai nasa harta da gidan damuke ciki aysha sunkarbe da motarsa da kayan shagonsa gonarsa ma daya gada daga mahaifinsa sunkarbe kamar yajja sukaiwa ahalin Alh dikko,sannan sunbiyomu bashi dukda haka,auren moon da aka qulla na alqawari rawa yake sbd sunfara xarginmu akan wnn lamarin aysha ga batun aikinnan dame sameer xeji,dakika suma allurar da akaimiki kadai dubu dari biyu yabiya yasiya ahaka ma qaramar ce bawacca akasaba miki ba shiyasa kika kwana kika wuni ahaka," dasauri tafara kalle kalle yanxun harta kwana tawuni ahaka, kuka sosai takeyi,ammi tatabe baki tace "kinadai gani komai tattali dataka tsantsan din damukeyi da rayuwarmu bamuda komai,bamuda kowa se Allah se kuma mahaifin yarannan tabbas nasan safyanu yamutu sameer baxe iya rayuwa ba nasan tsananin qaunar dayake ma mahaifinsa yarage naki kiragewa sameer nauyin da yahau kansa,bansan ina xeje yahado kudade har miliyan 36 ba amma nasan idan kikabar rayuwarsa meyuwa wani miracle din yaxo yay aiki" tana qarasa fadar haka tamiqe,likita yace 'karki tashi harse yaxo yadubaki kixauna anan kinji," ficewa tai aysha jin kalar abinda tafaraji jiya dasauri tayakice abin tinanowa da idan harta bari weakness din xuciyarta yafi qarfin ganganjikinta sameer ne xe cigaba dashan wahala,hannunta takalla tana murxa xoben diamond din dake kai,wannan xoben yakai shekaru uku ahannunta,popsy ne yabata shi tareda roqon duk rintsi duk wiya karta bari tayarda wnn xoben yaya noorah tataba duba musu kudinshi online alokacin shekara daya dasuka wuce xeyi kimanin miliyan 32 tabbas idan tasaida xobennan xata iya temakawa sameer dawani abu dawannan tinanin tai saurin jawo wayarta tana kiran lilly, "Hello gurl" ta answer muryarta ba walwala tace "kixo general hospital now xaki rakani wani wuri" tace "inaa gurl mekikeyi a hospital are you sick," "Uhmmm" kawai tace kafin tawatsa mata tambayar "kinsan inda ake seda danyar diamond ring" tace what? mexakiyi siya xakiyi" tace "a'ah I'm selling it," tace "bansani ba sedai xantambayi new driver ena." tace "amma lilly......." sallamar sameer ce tadakatar da ita daga abinda take niyar fada tace "sekindai qaraso kawai" ta kashe tana ajje wayar qarasowa yay yana forcing smile akan face dinsa wanda ita tasan yana hakanne kawai don karta shiga damuwa gefenta yaxauna akan gadon itama tasakar masa fake smile ahankali,tana shigewa jikinshi,kissing hargitsatsan hair dinta yay yana fadin "don't fall sick again kinji aysh,I was so scared I thought I'm loosing you," tace "sameer you will never lose me in sha Allah,because kaidin heartbeat dinane and you know aysh can't live without her heartbeat," smiling yay this time genuine smile yana fadin, "ina matuqar qaunar ki,you are the best thing that ever happen to me," dasauri tadago tana kallon kwayar blue eye's dinshi datai kalar masu jinbarci domin kwanansa biyu kenan korintsawa bayayi, yace what? Komawa tai talafe asaman chest dinsa ahankali take fadin "but some say I'm a curse tunbayan shigowana rayuwanka alot of thing's change waini baqar qafa ce," xaro ido yay yana kama hannunta yace "who? tell me,kifadamin waye yafadi hakan," girgixa kai tai tana fadin "no I'm just saying......." muryarta yafara rawa yasan sarai idan xatai qarya haka takeyi bata iya taba fada straight in his eye's setana dabur dabur tana kalle kalle yace "look at me aysha," tace "ok,ok I'll tell you it's your mom," miqewa yay yana fadin "ammi," "yah she did said but she...... " tana qoqarin kada yafusata jitai yace "I'm coming" dasauri yafice tabi bayanshi, a common room din da ammin kexama dawasu yan uwan masu jinya bayan sallar la'asar yasameta, Allah yasa bakowa agurin daga ita se moon dake ninke sauran kayan daxata koma dasu yau, cikin dan fushi yake fadin "ammi can we talk," miqewa taitana fadin badai jikin baban naku bane,yace "nope," aysha ce tariqo kafadarsa ahankali tana fadin "it's ok sameer you don't have to do this," xamewa yay yana fadin "aysha get out let me handle this," "noo" tafada tana girgixakai, moon ma miqewa tai ganin haka,yace "moon take your sister out," ammi dai tatsaya tana kallon ikon Allah jawota moon tafarayi tana tirjewa harseda tahaqura suka fito bakin qofa,bataji me sameer yace ba sejin fadan ammi tai tana fadin "au fadamaka tai ubana kaxo kaimun fada dakake hayayyaqomin haka kana karantan hadisai aicema akai bantaba xuwa makarantar islamiyya ba ga jahila wacca bata yarda da qaddara ba ko,nafada matarka diyar bint baqar qaface a ahalinmu tunda tashigo abubuwannan ke samunmu,kuma baxandena fadar hakan akan ra'ifiyar matarka ba,mace kullum cikin ciwo ni anyama ba bugun aljanu bane ake wayance mana dawani ciwon xuciya,sedai kaje kaiduk abinda xakai tamutu ba damuwace ba asontai bacin rai kace koh ga yar gwal, toh nikuma naqulli damarar bata mataran naga mexe faru," dabaya dabaya aysha tafice daga cikin ward din batareda tabari moon talurada hakan ba lokacin dasuka gama sauraron fadan da ammin keyi. Aqofar hospital lilly tasameta ganin halin datake ciki yasanya tafara saka sabon driver din da aka bata nababu gaira babu dalili biyawa gida dasu,bata cemata komaiba bata tambayeta komai ba itama tashiga tahada mata ruwa medumi tai wanka tadauro alwala.

kitchen tanufa tasaka cook dinsu yimata lafiyayyan farfesun kaza da hadaddiyar veges soup da cous cous takawo mata har dakin, bayan ta idar da sallolin dake kanta dakyar lilly talallabata ta ci veges soup din da cous cous kadan,tahada da chilled choco smoothie,lilly takalleta tana fadin "yakira kina wanka donkar hankalinshi yatashi nacemasa muna tare you just need some space yakyaleki kidan samu hutu anan tukunna" yace "idan kinfito inkirashi tunda kinbar wayar taki acan hospital din" fashewa dakuka tai tana girgixakai,tace " lpy aysha meya faru me sameer din yay miki kike kuka meya hadaku tell me," tace " its not him,mamarsa ce lilly she hate me to the extreme,fada fa yakeyi da ita akaina," lilly taqarasa tana riqe yatsun lilly tareda fadin "baxan bari alaqarsa talalace da mahaifiyarsaba kmr yajja tawa tatarwatse lilly ina cikin tashin hankali" nan takwashe duk wani abu dayake faruwa tasanar mata hartada xuwan yaya muhsin gidanta ba abinda taboye mata,dogon numfashi lilly taja kafin tace you wouldn't do that right? Aysha cikin rashin fahimta tace "do what lilly? tace "baxakiyi accepting wannan selfish offer dinba ko" tace " i will not koda a numfashi naqarshe,good cewan lilly," kafin tadorada cewa "kedin ba baqar qafa bace aysha karki taba saka wannan superstition din aranki ke alherice yan uwankine sukai creating hakan domin sucimma abinda sukeso kuma nasan yaya muhsin will go to any extent don ganin yasamu abinda yakeso saidai Allah yafishi aysha addua xaki riqe,Allah xekawo qarshen hakan yanxun muje aseda xoben sameer namatuqar buqatarki xaki koma kixauna tareda shi cikin kowana hali duk abinda xasuyi basu isa su saka ki abinda Allah yarigada yarubuta shine kadai xefaru. miqewa tai jikinta asanyaye tana fadin hakane lilly "thank you," tace " I'm sorry Abuya is behaving strange this day's yayi blocking credit cards dina takardun motana yakarba I think this is all under muhsins influence," tace "toh inbashiba waye xeyi hakan," lilly cikin dan shakku take fadin "Arsal mana who will benefit the most idan kika rabu da sameer," cikin harara dimple tace "xaki fara koh kitaiwa bawan Allah sharri dabeji ba begani ba," fitowa sukai,lilly tayi mamaki lokacin da tace wa driver yabata makulli taje inda yakwatanta mata bamusu yabata tasaba kullum sesunyi tata burxa takarba cikin farinciki. suka nufi shagon hanyar shuru kasancewar magrib takawo kai da mugun speed suke tafiyar hakan ne yasa lilly bata luraba ganin wani mutum yashige gabansu ta bigeshi "subhanallah" tafada tana tsaida motar aysha cikin rudewa take fadin " lilly what have you done,kaddai kinkashe shi," xaro ido lilly tai tana bude motar ayshama budewa tai ganin bakowa yasa lilly atsorace tai kan mutumin tana fadin " bawan Allah,bawan Allah juyowar daxaiyi taga yasaita ta da wuqa yana fadin "kudi kudi bani kudi kona kasheki," ihu lilly takwala tana neman guduwa yashaqo wiyanta, aysha ganin haka tai saurin juyawa xata nemo dauki taga wani da mask a fuskarsa agabanta,bindiga yake saitawa,ahankali cikin ta yaduri ruwa sai hawaye, "dan Allah karka kasheni banida komai,karka cutar dani," cikin wata iriyar murya taji yace "ciro xoben hannunki,sosai abin yabata mamaki domin xoben popsy yace mata secret shine ne dashi idan har bakasan menene ba kodakai waye aharkar baxaka gane diamond bane seta bude wani abu asaman,tace "wannan" tana nuna masa " xoben qarfene kawai xaku iya tafiya da motan I can't give you this ring " fusgota yay yana fadin "xankasheki kenan tunda kina qoqarin yimun qarya ciroshi kona harba bindigar nan akan yar uwarki" lilly data cika gurin da kuka ido yayi wuri wuri cewa take aysha kitemaka xasu kasheni cirowa tai hawaye nadiga a idonta bacin qaunar xoben datake matuqar yi shine last source din datakeda tabbacin xefitar da sameer daga halin dayake ciki sun kwace, sakinta yay yana warce xoben yaywa dayan da alama suwuce motar suka jaa suna cillo wayar lilly qasa suka fice rungume juna sukai lilly nakukan tsoratar da rayuwarta da a kai aysha nakukan rabuwa da xobenta wayar lilly tadauka tana mamakin kalar barayin da xasubar tsadaddiyar iPhone dinnan koda yake sundau abinda yafita tafada tana goge wayar da screen din yatsatsage sakamakon wullotan dasukai, yah noorah takira tana mesanar da ita abinda yafaru dasu din,aysha dif dai tai tana kukan xuci kawai har yah noorah taxi tadaukesu takasa cewa komai.

Comment Like & Share. [08/09, 13:21] Makoda: AYSAM Its Fatoums Passion's Love,passion,betrayal,romance,hatred and power between two different world's.