Chapter 15
by @khairatup01
ADNAN
(THE ARTIST)
NA UMMULKHAIR S PANISAU
(KHAIRATUP)
15.
Tunda ya kafa wa wayar sa ido bai sauke ba tsahon minti biyu yana kallon cikin wayar kamar dai abinda yake kalla ɗin zai fito ta ciki ne. Ya sauke ajiyar zuciya ya ɗaga kai a hankali ya kalli Imran alamar yana buƙatar karin bayani.
Imran ya muskuta kaɗan yace "Ban sani ba, ban san ya aka yi ba amma na lura da hakan na faruwa a kai-a kai."
"Tun yaushe?"
"Ban sani ba amma ana yi."
"To me bincike ya nuna? Mummy ta sani?"
"A'a bata sani ba hasalima ni kaɗai na sani babu wanda ya sani sai accountant ɗin da muka yi aikin tare."
"Asusun waye?"
"Ana tracking amma na fi zaton gaskiya na gida ne."
"Nima hakan ne a raina amma muna da buƙatar proof."
"Zan saka ido."
"Ya kamata kuɗin da yawa kar Mama ta san da hakan."
"In sha Allahu."
"Ya batun appointment ɗin ganin likitan Salim?"
Ya sa yatsan sa ya murza hancinsa sanann yace "Ina jiran amsarsu har yanzu bai bani amsa ba amma zuwa ajima zan sake duba email ɗina na ga ko akwai wani feedback."
"Khairan in sha Allah babban Yaya."
"Mu shiga mu ci abinci."
Suka shiga ciki tare suna hira haka.
Mummy na zaune da wayar ta a hannu tana duba abu a ciki ta ga sun fito gwanin burgewa da ban sha'awa tana son yaranta dukaninsu shi yasa har yau hankalin ta bai bata cewa yaranta biyu sun rasu ba...
"Mummy tunanin me kike yi?"
"Kawai ina godewa Allah da Ya bani zaratan maza kamar ku ya kamata ku motsa gaskiya hakan nan ina son na ga matan ku kafin ƙasa ta rufe min ido."
"Mummy!" Fu'ad ya faɗa yana zama.
"Ba wani Mummy, ya kamata ka dawo cikin hayyacin ka hakan nan all your mates are married."
"Mummy zan yi aure amma ba don sa'anina sun yi aure ba."
"Yen yen wai kai mai hankali ko?"
Suka yi dariya tare.
Imran yace "Mummy ni a shirye nake fa kawai so nake ki ce na yi."
"Marar kunya kawai sai ka yi ai na gani."
Fu'ad ya make masa ƙeya.
A hankali ragowar ma suka fito falon suka zauna a nan suka ci abinci suka yi hira a hankali kuma ɗayan bayan ɗayan suka dinga watsewa. Imran da Fu'ad tare suka fita daga gidan motar Fu'ad suka shiga Fu'ad ke tuƙin Imran na aikin magana.
*
"Daga ina kike?"
"Aiki na samu Baba bari ka ga...."
Hannu ya ɗaga mata a hankali sanann yace "Aiki a ina kuma yaushe?"
"A wani gida ne wai wani gida ina wannan mawaƙin Adnan the Blaze? Shi ne ya kai ni gidansu ya sa Maman shi ta bani aiki. Ba ku ga kayan yan gayu ne a jikina ba?"
"Kai! Kai! Baba ka ji maƙaryaciya wani ne fa aka ce ya ɗauke ta a mota ya tafi da ita sai yanzu zata dawo da wasu kayan da magriba ta ce wai aiki aka bata kuma aikin ma wanann shahararren mawaƙin kun ji wata narkekiyar ƙarya."
Sai da ta juya ta zabga mata harara kafin tace "Na ji wata lukutar masifa yau wai me na tsare miki ne Atika wai me yasa kike bina da sharri a rayuwar nan don Allah cigabana ne ba kaya so ko me?"
"Ah! Ɓata mana suna da kike ƙoƙarin yi ne cigaba in ko haka ake cigaba to Allah Ya tsinewa cigaban nan na ki ya kwashe masa albarka."
Baba yace "Ya isa haka! Ke Lamrat ina kika je ban san ƙarya da shashanci so nake yi ki gaya min gaskiya."
"Baba na rantse da Allah da Annabi aiki aka bani kuma wanann mai kuɗin ne ya bani aiki shara da goge-goge."
"Lamrat ki ji tsoron Allah." Babar su Atika ta faɗa hannu a kan haɓarta."
Sai da ta yanka mata harara tukunna sannan tace "Aje mana a tambaye su a ƙure mai ƙarya wannan abu mai ɗan sauƙi."
Baba ya yi gyaran murya yace "Ko ba ki faɗa ba Lamrat zan je na ji ba'asi indan kuma kika gayan ƙarya za ki ga kalar da baki taɓa gani ba a tare dani."
"Baba ba zan ma gani ba kyakkyawar fuskar ka kawai zan gani."
"Wuce ki shiga ciki."
Lamrat ta shiga ciki tana ji suna zuga Baba. Ranar bacci tayi mai daɗi ta ga masoyinta Adnan.
*
Doguwar riga ta saka fara ta sha attach a kanta. Farin takalmi ne a ƙafarta flat shi ma da yake tana da tsayi bata fiya saka mai tsini ba tana da kyau daidai na ta kuma fara ce sosai.
Tun da ta fito Maman ta kalle ta tace "Da kyau mai gadon zinare yau so nake ki tashi kan shi da na uwarsa bana son kiyi abinda zai janyo miki baƙin Jini har ki rusa mana shirin mu kin san dai tarin dukiyar da Adnan yake da ita wadda shi kan shi bai san adadin ta ba so nake mu mallake ta fiye da yadda Fatima ta mallake uban sa."
"Mama kar ki damu a hankali zan janye ra'ayinsu kuma ni na san yadda zan yi musu kwantan ɓauna na shiga jikinsu ko ba don dukiya ba Mama ina son Adnan."
"Bana son maganar son nan soyayya tana kassara mutum, soyayya tana saka zuciyar mutum ta zama raguwa mai tausayi Bilkisu bana son ki ɓata min rai idan ba za ki yi iya ni zan sauya da Meenal."
Miƙewa tsaye Bilkisu tayi ta gyara tsayuwar ta kawai ta zaro gilashin ta baƙi ta yi waje.
Kaitsaye gidan su Adnan ta isa a can ta zauna da akwatin ta guda na kwanaki biyu kamar yadda aka kulla mata don a haɗa ta da Adnan.
Mami ta kalle ta tace "Fatan dai kin shirya?"
"A shirye nake Aunty Fati."
"Na san za ki iya ba a banza na sako ki a cikin shirina ba kuma na san Yaya ta baki bayanin abinda nake so? Bana son a samu akasi ko wasa mu da kika gan mu ba ma ɗaukar wargi ko tsiya ki tsaya kawai kan aikin ki bana son batun so."
"In sha Allah!"
"Haka nake son ji. Ki tashi ki kai kayan ki ɗaki anjima zan saka yar'uwar ki ta raka ki gidan uwarsa ki samu ki shigar da kan ki wurin ta."
"To." Kawai Bilkisu ta faɗa tana miƙewa tsaye sai kuma ta kira sunan ta ta juya tace "Na'am Anti."
Hannu ta saka ta kama kunnen ta tace "Bilkisu bana son wasa ko cin amana Wallahi da rana ɗaya idan na gane so kike ki maida ni rana sai na miki mummunan illa ina son ki ɗauka yanzu kamar ke wata ubangida ce wadda rayuwarsa take cikin aku ina fatan kin fahimce ni?"
"Na fahimta Anti kar fa ki wani damu ko kin manta ni ɗin jinin ku ce? Ta yaya za ayi barewa tayi gudu ɗan ta ya yi rarrafe?"
"Haka ne da kyau ɗiyar kirki za ki je wuri mai nisa a tare da ni."
*
Ita fa Lamrat ba kai ne da ita ba tunda ta shigo Mami ta bata break ta karya tayi over load cikin ta ya birkice bata zo ba sai da suka zo da Baba ya ga wuri kuma ya yi magana da Mami sannan hankalinsa ya kwanta ya tafi ya kuma ja mata kunne kan rashin ji.
Mami tace ta hau sama ta gyara ɗakin Blaze bata ma yi tunanin yana nan ba ta zaci ya fita bayan ta gaya mata abubuwan da za ta yi ta ce mata zata shagon ta anjima zata dawo an kawo mata kayane.
Lamrat ta hau sama ta shiga cikin ɗakin ko kan gadon bata kalla ba ta kunna fitila saboda ɗakin sa duhu labulayen a sauke suke ta samu ta kunna makunin haske sai ga ɗakin ya yi tar banɗaki ta shiga ta haɗo kayan mopping ta dawo wata tusa ta zo mata bata yi wata-wata ba kuwa ta saki tusar nan ga wari harda wani ƙarni-ƙarni take yi. Tana buɗe baki tace "Alhamdu Lillahi."
Daga bayanta ta ji ana salati tuni ta ware idanunta waje ta firfito da su ta juya da sauri idanun ta kamar zasu faɗo kasa tace "Innallillhi wa inna illahi rajii'un ban san kana nan ba ,ban san da mutum ba na shiga uku."
Da sauri ya dirgo gajeren wando ne a jikinsa ko riga babu bare singileti gashin kan sa ya cika sosai har ya cucure baki siɗik da shi girar kan shi sun haɗe saboda masifar da ke cin sa yana huci ya isa gabanta bai ma san yadda aka yi ba sai gani ya yi ya ja hannun ta ya buɗe ƙofar ɗakin ya jefa ta ya kuma komawa ya rarumi bokitin mopping ɗin ya watsa mata ya buga ƙofar bang! Yana shiga ya lalaubi turare ya fesa a ɗakin yana toshe hanci, ya ji warin tusa iri-iri amma bai taɓa cin karo da mai tsami da ƙarni irin na wannan yarinyar ba gabaɗaya hancinsa ya fita daga hayyacinsa banɗaki ya afka ya kulle sai kuma ya sake fitowa ya buɗe tagogin ɗakin ya dage labulayen tuni fresh air ya fara shiga.
Lamrat kuwa bata taɓa riskar kanta a irin wannan yanayin ba na kunya ta ji kunya sosai.
"Wayyo Allah! Na bani ina zan kai wannan abin kunyar?" Ta runtse ido ta sauka ƙasa da sauri ranar a gurguje ta dinga yin aiki bata son su haɗu bata son ya gan ta in ya sauko.
Misalin ƙarfe sha biyu na rana ta gama komai ta gayra ko ina shirin tafiya ma take yi don ba zata iya yadda ta haɗa ido da Adnan ba. Mata biyu ne suka shigo cikin falon Mami ko ba a faɗa ba dayar tayi kama da Adnan don kamaninsu basu ɓuya ba a ranta tace ƙila ƙanen shi ne.
Kallon raini suka bita da shi kafin Meenal tace "Ke! Ina matar gidan?"
In dai Iskanci ne basu san Lamrat ogar su ba ce ta yamutsa fuska tace "Baku iya sallama ba ku kuwa kamar ya'yan maza Taresa?"
Meenal tace "Ke wace ce ke? Kin san ni kuwa?"
"Gaskiya ban ma taba ganin ki ba kawai dai addininmu ya koyar da ku ɗa'a ta shiga wuri ne kung don ban kula ku ba bani da wani laifi."
Meenal ta saki baki tana kallon Lamrat ranta a ɓace zata sake magana suka ji gyaran murya daga sama duk suka ɗaga kan su ko ba a faɗa ba mai gayya mai aiki ne cikin wando tthree quarter da riga baƙa an rubuta Blaze a jiki sai ya saka wata facing-cap baƙa hannunsa da wani bracelet an rubuta sunan sa a jiki na azurfa ne. A hankali ya soma saukowa su kuma suka bi shi da kallo Bilkisu kuwa cikin ranta yaba kyau na Adnan take yi a fili ma ya fi kyau ashe Camera na rage masa kyau tabbas in ta auri Adnan ta gama dacewa.
Ba tare da ya kalle su ba ya wuce kan dinng inda Mami ta ajiye masa abin kari.
Meenal ta juya tace "Yaya sannu da fitowa."
Da yake ko a da ma ba wani damuwa ya yi da ita ba sai kawai ya amsa mata da ka ya na saka bread a baki sandwich ne Mami ta mai ga sha jam a ciki.
Ya juya ya kalli Lamrat ya maka mata harara tuni ta bar wurin jikinta na rawa ita fa yau ta kwafsa tunda har ta yi tusa a inda yake ai da kunya Wallahi.
Meenal ce ta yi ƙarfin halin kiran sunan sa "Ya Artist." Ya juya ya kalle ta haɗe da rungume hannunsa a ƙirji yana kallon ta ba tare da ya ce mata uffan ba. Wani kalar kwarjini ya yi musu duk su biyun. Kusan sakanni biyar babu wanda ya ce komai da ya gaji ne ma yace "Ya akai kin kira ni kuma baki ce min komai ba ina sauri ne."
"Dama Daddy ne ya ce na rako Bilkisu....." Bata iya ƙarasawa ba saboda wani irin harara da ya maka mata sai da ta ji kamar ta saki fitsari a wando sai kuma ya saki fuskar ya juya ya kalli Bilkisun yace "Gani ya aka yi?"
Sai ta nemi dukkanin wani yawu ta rasa a bakin ta. Ƙishi ne ya kama ta ma sai ta soma shafa maƙogwaron ta.
Ya saki siririn tsaki ya juya yace "Ku jira ni na je na dawo ana jirana na ga baku shirya magana ba kun san lokacina mai tsada ne."
Bai basu damar amsa masa ba ya yi waje da sararrafa,suka bi bayansa da kallo.
Bilkisu ta saki ajiyar zuciya tace "Ya na da kwarjini sosai na kasa magana na nemi kalmar da zan furta na rasa Ya Allah!"
Meenal ta kyabe baki tace "Ku ma da ban san me yasa kuka dage sai kin aure shi ba kina gani dai ba kirki gare shi ba yayana ne amma tsoronsa nake duk iskancina bana iya katabus don ya fi Yaya Soja ma zafi."
"Hmm!" Kawai Bilkisu ta faɗa.
*
Yana fita ana kiransa a waya sai da ya yi tsaki sannan ya ɗaga wayar.
"Ina hanya babu wata matsala ba zasu iya komai ba am on my way." Ya kashe wayar ya sa a cikin aljihunsa ya zaro key ɗin motar sa ya kunna ya shiga ciki horn ɗaya ya yi aka buɗe masa gate ya fita sa gudu. Ko kan ya isa Sahib ya yi mai kira biyu duk bai ɗaga ba sai da ya isa airport tukuna sannan ya kira shi.
"Bana son wulaƙanci Artist."
"Na sani gani kuna ina ku?"
"Muna wurin customs."
"Ok." Kawai ya faɗa ya ajiye wayar. Bai wani ɗauki dogon lokaci ba ya isa. Sahib ya fara hangowa da wani matsashi a tsaye da customs officer's biyu mace da namiji.
Hannu ya miƙa musu suka gaisa sannan ya ja su gefe.
Kusan minti biyar suna tattaunawa kafin suka gama ya koma yace da Sahib "Muje. Ka ce mai ya ɗauko kayan."
Sahib ya buɗe bakinsa yana kallon sa da mamaki kasa yin sai da ya tanka masa yace "How did you do that? Me ka ce musu?"
Murmushi ya yi kawai yace "Brain."
"Ƙarya kake Wallahi!"
Shi dai dariya ya mai bai ce komai ba.
"Amma wa ke da hannu a ciki?"
"Ya kamata na isar musu da gargaɗi ,na ga ruwa ya fara shan kai."
"Haka ne. Amma yanzu sai ina?"
"Zamu yi catching flight anjima."
"Ina zamu je?"
"Adamawa."
"Adamawa?"
"Yes Adamawa."
"What time?"
"Ka dai shirya sai mu haɗu anjima a nan zan gaya maka lokaci ta waya ka je ka sallami matar ka da Jnr zamu iya yin kwana biyu."
"Wai me yake faruwa?"
Bai ce mai komai ba ya shiga motar sa ya yi reverse yana dariya ya sauke masa glass ɗin motar yace "Sai anjima." Ya maida glass ɗin ya yi gaba a guje ya bar Sahib da bin bayan motar sa da kallo kawai. Ya san Artist kuma bai san Artist ba har yau wani irin mutum ne kamar wahainiya."
"Yallaɓai na samu tip."
"Ta yaya?"
"Ta hanyar na hannun dama na undercover officer ɗin mu akwai matsala dole sai na je ana ta kama yaran mu."
"Are sure zaka iya?"
"Zan iya mana Yallaɓai kawai so nake a bani dama."
"An baka dama ka kula kai ma na samu labarin an saka wasu suna bibiyar ka sun saka maka ido na san ka san aikin ka kuma ba zaka bada wata ƙofar da za a samu wani clue a kan ka ba."
"A yadda wasan yake tafiya Yallaɓai bana jin zasu iya bankaɗo waye ni ba."
"Haka ne All the best."
"Thank you sir!"
Ya ajiye wayar.
To fa me yake faruwa ne?
*
Yamma lis Mami ta dawo daga shagon ta bata yi zaton ma zata kai haka ba sai ga shi aikin dole sai ta sa ido za a yi. Tana shiga ta ci karo da yan'mata a falo suna kallo.
"Wa nake gani kamar Meenal?"
Meenal ta juya a hankali tace "Mami sannu da zuwa."
Mami na dariya ta amsa. "lafiya lau,Tun yaushe kuke nan?"
"Mun jima ko nace a nan muka wuni Mami ni da Bilkisu ce."
"Wa ce Bilkisu?"
"Mami yar Aunty Suwaiba daga Kaduna ta zo ta gaishe ki Daddy ne yace mu zo."
Sai lokacin Mami ta gane wacce ake nufi wadda aka haɗa da Adnan kenan. Dole ta sa ta saki fuskar ta haɗe da zagayawa ta zauna kan kujera. Bilkisu ta sunkuya ƙasa kwasar gaisawa.
"Mami sannu da zuwa Barka da yamma."
"Barkanmu. Tashi ki zauna tashi daga tsugunon nan."
Bilkisu ta miƙe tsaye ta koma kan kujera.
Lamrat ta fito daga kitchen da ruwa mai sanyi da kofi ta tsugunna gaban Mami tace "Hajiya Barka da dawowa."
"Barka Lamratu ya gidan?"
"Lafiya lau."