Chapter 2
*🪴 TUSHEN MU ƊAYA 🪴*
*PAGE2️⃣*
*_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_*
*KARKU MANTA COMMENTS RASHIN GANIN SA ZAI IYA SAWA NA DAKATA*
Follow the TASKAR MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️ channel on WhatsApp: ***
*DAN SAMUN DAMAR CIGABA DA KARANTAWA KUYI FOLLOWING ƊIN CHANNEL ƊINA GA LINK ƊIN A SAMA👆*
Sai da ta fara zuba abincin a kular bashir sannan ta zubawa Baba, haka ta cigaba bin kwanukan tana zubawa kowa. Sai da ta gama zuba na Ƴaƴan ɗakin ta tsaf, sannan ta jawo kula ta dake gefe ta zubamin, wannan abincin shine Ni da Ahmad zamu ci har dare abincin da bai fi mu cinye shi ba yanzu in mun samu ƙari ma ci da mu yi.
Maganar ta ce ta katse min tunanin da nake, na ɗago na kalle ta tace "Ke ai ke aminatu naga kina son ƙanzon shinkafa bari na zuba miki in yaso sai na rage shinkafar dama kinga kwanon Maman A'isha, yau abincin yayi albarka ban zuba mata ba."
Ta ƙarasa maganar tare da rage abincin kulata ta zubawa Maman A'ishar ta zuba min ƙanzon a madadin wanda ta rage.
Tana yi tana mita "Ai ƙanzon ya kamata ace na zuba miki baki ɗaya ma tunda ke kika bari abincin ya ƙone,
Ko daya ke ba kiyi niyar girkin ba shi yasa kika barta ta ƙone. Yanzu fisabilillah kalli wadda ta ƙone tayi cin mutum guda." Ta ƙarasa maganar tare da jan tsaki.
Ni dai ina tsaye ina kallon ta ina mamakin hali irin na Hajjo wato abin nata har ya kai abincin ma da ba zata iya bamu na kirkinba, hakan bai isheta ba har sai ta ƙara min da ƙanzo. Na rasa yau she nace mata ina son ƙanzo? A zuciyata nace Allah ka rabamu da san zuciya.
Nan ta shiga rabon miya miƙo min hannu tayi ba tare da ta ɗago ba tace "Bani kwanon miyar ku."
Ɗauko kular nayi tare da miƙa mata, ta amsa ta zuba min miyar ina kallon ta sai da ta yaɗe man miyar gefe tukun ta zuba min.
Amsa nayi na rufe na aje gefe sannan na tashi na shiga rurrufe sauran, haka na dinga ɗaukar kowanne da miyar sa ina kai wa ɗakin Hajjo har na kammala kai wa.
Ita kam Hajjo tana zaune ta loda abincin cike da filet tana ci harda ƙaton bushashshen kifi akan nata, wanda shi kaɗai ta bani tace na sa mata a miya. Wato ba zata iya siyan kifin da zai isa ta sawa kowa akan abincin sa ba amma ita zata sai wanda zata ci.
Ina shirin tafiya ta kira ni, tace "Wa kika bari da zai share bakin murhun?."
Dawowa nayi na ɗauki tsintsiya na share wajen tas, na ɗauke tukunyar da nayi abincin, na zuba mata ruwa na maida ta gefe, na dauko faranti na jera abincina da miyar na ɗauka.
Har zan tafi gudun nayi laifi nace "Hajjo sai anjima."
In ta tanka ni to bangon dake wajen ya yi magana.
Ban wani damu ba dan na riga da na saba da shirun ta in yan mulkin suna kusa, ko na mata magana in dai ba ta so ba bata kula ni.
***
Ina shiga lunguna na tarda Ahmad yana alwala, hannuna riƙe da tiren abincin nace "Au wai har lokacin sallah yayi.?"
Ɗagowa yayi yana gyara hannun rigar shi yace "Eh har saura minti biyar a shiga Masallaci."
Ya miƙe ya aje butar a bakin ƙofar ɗakina yace "Sai na dawo."
A dawo lafiya na masa na wuce ɗaki.
Aje farantin hannuna nayi ina kallon gyaran ɗakin da Ahmad ya min, ya yi ƙoƙari kam ya share shi tsaf. Sai dai gyaran gadon da aka min ne gashi-nan-gashi nan ne, dana ga yadda ya shimfiɗa zanin gadon sai da nayi murmushi.
A zuciyata nace _Bawan Allah shi dai yana son yaga ya kyautata min, Ya Allah ka bani ikon kyautatawa wannan bawa naka_
Ƙarasawa nayi na ƙara gyagygyara inda bai ɗame ba, na shiga nazari akan yanayin rayuwar aure na.
Gashi dai nayi dacen samun miji nagari wanda ke ƙauna ta, sai dai banyi dace da uwar miji ba haka dangin sa.
Ajiyar zuciya na sauke sai kuma tunawa, dama ba lallai ne bawa ya samu abinda ya ke so duka a rayuwar shi ba,
To ni nawa ta ɓangaren miji daɗi dangin sa kuma aka aka sin haka.
Saɓanin wasu matan da su kuma mijin ke takura musu, dangin sa na son su In da hakan yafi ciwo tun da ba dangin ke zaune da ke ba ai soyayyar bata da amfani.
Rage kayan jikina nayi na ɗaura zani nasa ƙaramin hijabina, na zuba ruwa a botiki na nufi banɗakin wanka nayo ina fitowa na ɗaura alwala na shige ɗakina.
Doguwar abayar dana ware dan Sallah kawai na ɗauka, na saka na sa hijabina na tada sallah. Ina idarwa bayan na kammala addu'o'i na, na tashi na ɗauke abin sallar na maida shi wajen da nake ajiye shi.
Gaban madubi na na nufa kai tsaye, na ɗauki humrata mai daɗin ƙamshi na shafe jikina da ita.
Na ɗan murza man shafawa tare da da kwalli na taje girata.
Na nufi wardrobe ɗina na buɗe a hankali nake kallon kayan dake ciki, ina tunanin wanne ya kamata nasa? idanuna ne suka sauka kan wata atamfa ta wadda ke ɗauke da launin ja da sirkin fari da baƙi an mata ɗinkin riga da sket.
Ɗauko ta nayi na aje a gefen gadona tare da ɗauko ƙananan kayan da zan sa a ciki.
Nan na shiga shiryawa.
Koda na kalli kaina naga yadda kayan suka zauna a jinkina ɗas, sai da na ƙara sawa telar da tamin ɗinkin albarka.
Dan dama ban taɓa sa kayan ba sai yau yana daga cikin kayan fitar bikina.
Tunawa da ban kwashe ƙanzon dake kan abincin da Hajjo ta zuba min ba, yasa nayi saurin zuwa na jawo kular na kwashe ƙanzon dan bana so Ahmad ya dawo ya gani, saboda nasan ran shi zai ɓaci.
Bayan kyaure na kai ƙanzon na ɓoye, da nufin anjima na kai na zubar.
Ai ni ko gidan mu duk da mahaifina ba wani ƙarfi ne da shi ba, amma mutum ne me ƙoƙari akan iyalin shi, baya taɓa barin mu muyi kukan rashin wani abu bare har akai ga muci ƙanzo, haka baya taɓa bari muji a ranmu mu marayune duk wani ƙoƙarin yana mana dan ganin min samu abinda mu ke so.
Wajen madubi na koma na taje gashin kaina tsaf na tufke shi da ribom. Ina ƙissimawa araina yakamata ace nayi kitso tun satin farko da aka kawo ni, gashi har na kai sati biyu ban yi ba.
Rannan dai nawa Salaha maganar wa ta sani da zata zo ta min kitson a gida? Hajjo ta zo taji muna maganar.
Salaha nason bani amsa Hajjo ta cafe maganar "Babu wasu masu kitso da ke bin mutum gida su masa a garin nan, dan nan ba Kano bace da kuka saba lalaci ace mace sai son jiki, sai dai ki bar kitson har zuwa ranar da zaki fara fita ta rakaki a miki."
Sai kuma ta fara mita ita kaɗai "Ji min wani sabon sanabe, sai kace wata hamshak'iyar mace zaki wani ce sai anzo gida za'a miki kitso, saboda nuna isa da
dai ba asan asalin balbela bane sai tace daga Madina ta zo." Ta kai karshen zancen tare da ƙwafa.
Tuna hakan yasa nayi murmushi a zuciyata nace
_Ohh Hajjo rigima_
Kallon agogo nayi ganin ya Ahmad ya isa dawowa, yasa na tashi da sauri na ƙarasa na ɗauki ɗankwalin kayan na zauna na tsara ɗaurin ɗankwalina zamani wanda ya zauna ɗas a akaina gwanin burgewa.
Sai na fito a amaryata sak ina murmushi na ɗauki turarukan feshe masu daɗin ƙamshi,na fara feshe jikina dasu sam bana wasa da harkar ƙamshi dan shi kanshi Ahmad in nasa turare wani lokacin dan daɗi har tambaya ya ke,
shin wanne irin turare nake aiki da shi? dariya nake nace masa "Gasu nan dai akan mirror."
Haka zai ta dubawa yana fesawa sai ya rasa wanne ne ke ƙamshin Ni kuma naƙi ce masa haɗawa nake.
Tsayawa nayi gaban madubin ina kallon irin baiwar da Allah yamin ta wani irin sihirtaccen kyau, wanda atashi ɗaya inka kalleni da wuya ka gano shi lokaci guda.
Ban kasance kyakykyawa ta ku zo mugani ba, amma ina da kyau na daidai gwargwado, baza'a sakani a layin kyawawa can can ba haka baza'a sani a layin munana ba na kasance tsaka tsakiya.
Ban kasance doguwa ba kuma baza'a kira ni gajera ba, jikina a murje ya ke Ni ba mai ƙiba ba, haka ba lukuta ba ƴar daidai misali ce ni.
Haka ina da diri me kyau ana yawan faɗa min hakan, saboda haka tun ina budurwa nake ta ammali da hijabai, da wuya ka ganni da mayafi saboda duk kayan da zan sa sai ya bayyana ƙirar hips ɗina.
Kallon madaidaiciyar fuskata nayi, tana da ɗan faɗi amma ba sosai ba, sai hancina masha Allah yana da tsayi ƙasan hancin kuma ɗan ƙaramin bakina ne wanda innayi murmushi jerarrun hakorana farare tas kan bayyana, sai idanu da Allah yamin su masha Allah dara-dara dasu tubarkallah farare tas asaman su kuma Gashin girata ne kwantacce me yalwar cika.
Haka launin fata ta Ni ba fara ba, haka baza'a sani a layin baƙaƙen ba, wankan tarwada kenan.
A hankali na furta "Alhamdulillahi Ya Allah ina ƙara godewa Allah ga tarin baiwar shi gare ni.
Turaren wuta na ɗauko na tsinke kasancewar lokacin damuna ne, kuma bana son komawa gurin Hajjo dana samo gaurashi nasa na itace.
Amma tunda babu sai nayi amfani dana tsinke, na sa ashana na kunna na sokashi ajikin kaskon turaren wuta, na ɗauki room freshener na ƙara fesawa a ɗakin. Take ɗakin ya gauraye da daddad'an ƙamshi me kwantar da hankalin wanda ya shaƙa.
Sallamar Ahmad da naji yasa na juyo, tare da amsawa na tsugunna na masa sannu da zuwa.
Ba tare da ya amsa ba ya ƙaraso ya buɗe min hannayen sa, alamar in taho.
Sai na noƙe kafaɗata nasa hannu na rufe fuskata da hannayena, alamun jin kunya.
"Haba ƴan matan mijin ta taho mana kin ji."
Kasa ɗagowa nayi baki ɗaya na ƙara ƙasa da kaina.
Ganin bani da niyar motsawa, Yayi dariya yace "Tunda ba zaki zo ba ai ina da ƙafa, Ni dai na zo ai."
Babu zato naji an ɗaga ni sama, da sauri na mak'ale shi cike da jin kunya na cusa kaina a k'irjin sa.
Sai kokawa ya ke dani akan sai na buɗe fuskata ya gani.
Daga ƙarshe sai da ya buɗe ɗin, cikin zolaya ya sauke ni yace "Eyye ashe haka aka caɓa min kwalliya ake ɓoye min?."
Ni kam tunda na samu ya dire ni, naja baya a shagwaɓae nace "Ni dai ka zo kaci abincin."
Ƙarasowa yayi ya rungume ni kawai, jin yaƙi saki na yasa na ɗan ɗago da kanshi da hannuna na kalli fuskar shi, sai naga idanun sa a lumshe a hankali ya buɗe su ya zubamin ido yana min wani irin kallo da yake sani ƙara jina cikin kunyar shi, da sauri na sunkuyar da kaina ina mai wayancewa naja hannun sa nace
"Kaga My muje muci abincin karya huce nasan kana jin yunwa."
Mak'ale kafaɗa ya yi kamar yaro ya maida kansa jikina, da ƙyar ya sake ni amma yaƙi sakin hannuna.
"Ai ni da kin barni da babu wani abincin da zanci yau, ɗumin jikin ki ma ya ishe ni."
Ɗagowa nayi na zaro masa dara-daran idanuna nace "Rufamin asiri muje yunwa ai ba wasa bace."
Murmushi ya yi tare da busa min iskar bakinsa yace "To mai da idanun haka a daina hukuntani da su."
Kunya ta rufeni na kauda kaina ina murmushi, cikin dubara na zame hannuna na, na ɗauko flet na zuba masa abincin na shimfida darduma na ɗauki farantin abincin na kawo na aje naje na ɗauko kofin ruwana na ciko shi da ruwa randar ƙasa ta me sanyi, na saka cokula biyu a flet ɗin abincin dan baya son yana nan inci abinci banjirashi ba yafi son mu ci tare.
Nan ya zauna nima nakaraso zan zauna, yayi saurin jawoni ya min masauki bisa cinyar sa, ya ɗauki cokalin yafara ɗebo abincin na bude bakina a hankali tare da bismillah a kunyace na amsa.
A haka ya dinga bani shima sai yace na bashi
Haka nake bashi a kunya ce.
Babu zato naji an turo ƙofar net ɗin ba sallama,
Kafin nayi magana ta shigo. Da sauri na zabura na sauka daga cinyar Ahmad na ɗan matsa gefe cikin takaicin wannan lamarin.
Ba wata bace ta shigo face Salaha ƙanwar Ahmad, ko uniform ɗin jikinta bata cire ba da alamar yanzu ta dawo makaranta. Haƙiƙa halin Salaha na cimin tuwo a ƙwarya, ita data ke mace ma kenan tana haka ina ga mazan gwara su za'a musu uzuri, ita kuwa macace ko banza gidan wani zata.
Amma sam bata da ɗa'a da tarbiya in anyi magana intayi abu Hajjo tayi caraf tace ai yarinyace zata daina.
In ba Hajjo ba yarinya me shekara goma sha hudu itace zatayi abu ace yarinta ce, ko tayi wani ance yarinta ce ai wani ya wuce yarinta sai dai wauta.
Haka ta tsaya ta shiga binmu da kallo sai da ta zaɓi wanda zata gaisar tukun tace "Ya Ahmad ina wuni." Ba tare da ta gaishe ni ba.
Da "Lafiya ƙalau" ya amsa mata yana kallon ta ko zata gaida ni, sai yaga taƙi sai na nufar kujerar ɗakin da tayi da nufin zama.
"Ita Menah me ya hana ki gaishe ta?"
Cewar Ahmad kenan.
Juyowa tayi ta haɗe rai ta cikin ɗacin rai tace "Ina wuni."
Da Lafiya na amsa ina jin takaici yanzu fa zama za tayi ta samu gaba haka kawai.
"Sai yanzu kika dawo daga makarantar?"
Ahmad ya tambaye ta.
Tana ɗan sosa kai tace "Eh rubutu aka mana me yawa shi yasa."
"Ba wani rubutu Salaha kin dai tsaya biye biyen gidajen kawayen ki ko?"
Shiru tayi ta miƙe tsaye ta dawo bakin ƙofa alamar dai ta aikata.
Ƙwafa Ahmad ya yi yace "Hmm kinyi kenan? Yanzu Salaha bakya jin magana ko? Ace a taso makaranta ba zaki dawo ba sai kin gama yawon ki, ki daina hakan baida kyau ke yanzu kin wuce wannan yarintar, in an tashe ku kidinga ƙoƙari wajen dawowa gida akan lokaci, kinga ko wasu yan ayyukan kya dinga taya Hajjo.
Zum'bura baki ta fara magana ciki-ciki.
A hankali ya ɗauke idon shi a kanta ya girgiza kai yace "Allah ya shirye ki, in kin ga dama ki je tsakar gida ki share ƙofar ɗakin nan."
Sai da ta kaalle ni ta ɗauke kai tace "Gaskiya ni na gaji Yaya."
Tasowa yayi kamar zai dake ta.
Nayi saurin cewa "Dan Allah ka ƙyale ta ka barta ta gaji, kaga fa tana shigowa nan ta shigo, haka kaima kafara mata faɗa taya zata iya wani aiki."
Na ƙarasa faɗa cikin son ɓoye laifinta duk da nasan rainine ya kawo hakan.
Wani kallo naga tana bina dashi tare da gallah min harara, taja wani dogon tsaki, cikin tsiwa tace "Wallahi na tsani baƙin munafurci a rayuwata, ace mutum ba'a sa dashi a magana ba sai ya jono bakin sa, haka kawai muna maganar mu ta ƴan uwa."
Ta ƙarasa maganar tare da murgud'a baki ta fice.
Wata irin zabura Ahmad ya yi zai bita, cikin sauri na riƙo shi cikin lallashi nace "Kaga ƙyale ta yarinta ke damunta dan Allah kar ka bita."
Cike da zallar ɓacin rai ya kalleni yace "Haba Menah yaya ina kallo zan bari ƙannen na su rainaki, in ita Hajjo tayi miki a matsayinta na uwa dan nayi shiru, sai su ƙannene na su miki abin gaba ɗaya babu mutumci kenan."
Nan dai na shiga bashi haƙuri, cikin lallashi na ɗauki cokalin abinci na shiga ƙoƙarin bashi. Dan ganin na kawar masa da tunanin abin da ya faru.
Girgiza min kai yayi yace "Bazan ci ba na ƙoshi." Cikin lallashi nace "A'a fa dan Allah kaci me kaci da har ka ƙoshi? da ƙyar ya yarda muka ci gaba da cin abincin.
***
Da ihu ta ƙarasa ƙofar ɗakin Hajjo tana tumami iya ƙarfin ta, tana isa ta faɗi tana birgima tana kiran "Ya kashe ni Hajjo wayyo Allah na."
Hajjo da idar da sallar ta kenan taji ihun Salaha , a guje ta bazamo ganin ta a ƙasa yasa hankalin ta tashi tace "Ke Salaha keda wa yanzun nan daga dawowar taki makaranta har an samu wanda ya doke min ke?."
Cikin kukan da take ta shiga cewa "Ba Yaya Ahmad bane daga zuwa ɗakin su dan na tarar da su sun rungume junansu suna ba juna abinci a baki, shine kawai yace nawa Aminatu shara dan nace na gaji, ya hauni da faɗa a gabanta ita kuma da baƙin munafurci harda bashi hakuri, dan nace bana son munafurci ta daina sa mana baki a maganar mu, sai Ya Ahmad ya mammareni." Ta ƙarasa tana mai cigaba da birgima kamar ƴar shekara uku.
Madadin Hajjo ta tsawatar mata akan yadda ta bayyana sirrin yadda ta same su, ita hakan bai dame ta ba. Hankalin ta na kan marin da ƴar gwal tace anmata. Da ƙarfi tace
"Mari? Shi Ahmad ɗin ya mare ki? Kan bala,i akan waccan Figaggiyar ya mare ki? to wallahi bai mari banza ba tashi muje maza maza Ido na idonshi ya fadamin meye hujjar sa na marinki."
Sai kuma ta kama haɓa tace "Oh duniya in kana raye baka gama kallo ba, wai akan mace yaron nan ya daki ƙanwar shi?" ta ƙarasa tana mai kama hannun Salaha ta miƙar da ita.
Ita kuma munafukar sai kifkifta ido take tana murza su. Haka ta figi hannunta suna tafiya tana banbami suka nufi sashin Aminatu.
Maman Aisha ce dake kofar dakinta tana wanki, duk a kan kunnen ta komai ya faru ganin Hajjo zata wuce ta, ta dago tace "Wai Hajjo Ahmad ɗin ne ya daki Salaha da gaske akan matar shi?
Juyowa Hajjo tayi cikin takaici tace "To akan wa kika ji muna magana uwar iya? Ahmad ne ya dake ta amma zai san ya dake ta, dan tunda nake da shi bai taɓa sa hannu akan ƙanen sa ba, amma yau saboda waccan bak'ar kadarar ya da kar min ƴa, Ƴar da koni da nasha wahalar naƙudar ta bana dukanta, sai shi sallamamme zai dake ta." Ta ƙarasa fadar cikin takaicin abin.
Cike da zuga Maman A'isha tace "Hmm ai kwa dai gwara kiyiwa tufkar hanci tun kafin abin ya girmama gaskiya karya fara sa hannu kan yaranki ina dalili."
Gaba Hajjo tayi tana faɗin "Ai ba yarda zanba yanzu zanje in shata masa layi akan Ƴaƴan ma duka, tunda ta shanye shi ya fara tsanar ƴan uwan shi, to ni bata shanyeni ba bokan uban nata bayyi nasara ba."
Taja hannun salaha tayi gaba.
Da sauri Maman A'isha ta tsame hannunta daga ruwan wankin da take, tana wani munafukin murmushi, tabi bayan Hajjo ahankali ta tsaya daga ƙofar lungun aminatu saboda bak'ar gulma. Cewa tayi "Ai Wallahi sai naji yadda zaku kwashe." ta faɗa tana mai kasa kunne.
*_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_*