TUSHEN MU ƊAYA

Chapter 3

by @mamananalbarkace777

*🪴TUSHEN MU ƊAYA🪴* 



*_🥰MAMAN DAN ALBARKA CE🥰✍️✍️_*


       *PAGE 3️⃣*

Follow the TASKAR MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️ channel on WhatsApp: ***

*DAN SAMUN DAMAR CIGABA DA KARANTAWA KUYI FOLLOWING ƊIN CHANNEL ƊINA GA LINK ƊIN A SAMA👆*

Muna tsaka da cin abincin, na fara jiyo hayaniyar hajjo ta doso ɗakina. Gaba nane naji yayi wata irin faɗuwa, cikin sauri na ajiye cokalin na kai kallona ga  Ahmad, sai naga shima ni ya ke kallo.

Raurau nayi da ido, irin ka gani ɗin nan ko? Na tashi na doshi ƙofar Shi ma sai ya biyo bayana.

Daidai lokacin da muka fita, Hajjo ta ƙaraso, tana ganina ta fara jawo Salaha tana faɗin 
"Wuce muje nace, wuce nace mana."

Ganin Ahmad yasa Salaha ƙara mak'alewa baya. 

Tafa hannu hajjo ta fara tana faɗin "Ah lallai kin maru, gashinan har kina tsoron zuwa wajen nasu, dakata anan ni bari naje naji dalilin daya sa ya mare ki akan shegiyar nan."
Ta ƙarasa faɗin tare da nuna ni da yatsa.

Sunkuyar da kai kawai nayi,  mamaki da al,ajabi ne suka daskarar dani a tsaye, me Salaha taje ta cewa Hajjo? kar dai dukan ta tace anyi, na shige su wannan wacce irin rayuwa ce Allah ya kawo ni.
 
Tunani na ne ya yanke saboda maganar da Hajjo ta fara, sai da ta zo har kusa da mu da alamun ma yanzu taga Ahmad ɗin, ta fara magana cikin faɗa "Dole ku tsaya ku zuba min ido, ku barni ina ɓaɓatu, marasa mutumci da arziƙi. Wato daga zuwan yarinya wajen ɗan uwan ta, shine kai mai mata dan bata gaida taba, kayi kukan kura ka marar min ƴa.?" Tayi ƙwafa tare da jefa min wani kallo ta gyara tsaiwar ta ta cigaba da magana
"Zuwa nayi ka faɗa min yaushe muka fara haka da kai? Kai da baka taɓa dukan ƙannen kaba,  meye dalilinka na dukan yau? Ka dai san ko ni nan bana dukan yarana, bare kuma wani ya taɓa min su. Sai kai daka fara yau ko kana son nuna min  kayi aure ne?"

 Na fuskanci shi kanshi Ahmad ya shiga ruɗu, cikin mamaki yace "Hajjo ita Salahar ita tace na mare ta? yaushe na mare ta?  Ta shigo ne babu sallama fa
 kuma bata gaida Aminatu ba, harda mata rashin kunya, shine na mata faɗa akan karta ƙara shigowa bata gaida ta ba tunda ita ce me ɗakin."

"Lahaula wala kuwwata illah billahil alaihil azem, oh ni yau naga abinda yafi ƙarfina ni Hajjo.
Yanzu ahmad Salahar ce zata maka ƙaryar ka mareta, sannan saboda tsaurin ido irin naka ka kalli tsabar idona, kace me ɗakin. To ka faɗa min wace me ɗakin? Nace wace me ɗakin ko da Aminatu zata zo gidannan an gina mata ɗakin ne daga can, ubanta Salisu ya ɗora mata aka ta kawo shi?." Ta wani rintse ido tana nuna shi da yatsa "To ahir ɗin ka, duk ranar da naji ka sake taɓa wani daga cikin ƙannen ka akan wannan abar,  wallahi tallahi kaji rantsuwar musulmi inka ƙara samin hannu kan yara saina saɓa maka, Shanyayyen banza Shanyayyen wofi kawai."

Ta juyo kaina, gaba ɗaya na gama cika da mamakin ta, ta zare min ido tace
"Ke kuma na dawo gare ki, wallahi duk taƙamar ki, da shige-shigen dakike, akan ki mallake min yaro, duk ina kallon ki babu abinda ban sani ba. Da sannu  sai nayi maganin ki, mu zuba nida ke Matsiyaciyar yarinya mara arziƙi, gadon tsiya kawai uwar gurmi."

Tana gama faɗin hakan ta juya, tare da kama hannun Salaha dake raɓe, ta barmu tsaye nida Ahmad cikin jimami da tsananin mamaki.

Ga mutanen gidan gaba ɗaya sun cika wajen, kowa na ƙus-ƙus an rasa wanda zai ce wani abu.

Suna ganin tafiyar ta, suka fara zuwa wajen mu suna bamu haƙuri, akan watarana sai labari da dai irin gulmar nan.

Bamu ce komai ba, Ahmad ya ja hannu na zuwa ɗaki, jikin sa har wani karkarwa ya ke da saboda ɓacin rai.

Zama muka yi jigum jigum, anrasa mai magana tsakanin mu.

Can na nisa nace "Dan Allah kayi haƙuri ka ji."

Ɗagowa yayi ya kalleni, da idanun shi dake cike da zallar ɓacin rai yace "Aminatu na fara tsoro, ina jin tsoron wannan abin ya  ɗore, a tsarina bana son inga matata da Mahaifiyata suna sa'insa. Iya abinda Hajjo tayi yanzu, yasa na fara shiga wasi-wasi akan barinki da zanyi in koma gurin aiki,  kinga fa ina nan ma abinda suke miki, bare kuma ace bana kusa. Ina tsoron abin da zaije ya dawo Menah."

 Tashi nayi na ƙarasa kujerar da ya ke kai, dan dama ina zaune ne a ɗayar kujerar.
Na ɗan tsugunna gaban shi, na dafa gwiwowin sa da hannayena.
A hankali ya ɗago ya kalle ni, nima kallon nashi nake zuciyata cike da tausayin kanmu nace "Ka daina damuwa da hakan, Hajjo fa mahaifiya ce duk rintsi ba zata yi abinda zai cutar damu ba, ko ka tafi babu abin da zai faru Insha Allah, zanyi ƙoƙarin gujewa duk abin da zai kawo matsala tsakanin mu."

Na ɗan langwaɓe kaina nace "Ina ce dai sai nayi ba daidai ba, za tace nayi laifi?  To Insha Allah zaka same ni me biyayyah, in dai dan wannan ne kar ka damu." Na ƙarasa maganar cikin murmushi, duk da ina dannewa ne, ina jin ciwo araina na irin abinda Hajjo ke min, ga tafiyar Ahmad da ta taso jibi zai koma wajen aikin sa, in ya tafi wa zai na lallashina?  ina zanje inji daɗi? Wani bangare na zuciyata yace Allah ba zai taba bari su cutar dake ba.
Wani sanyi naji ya ratsa zuciyata dana tuna hakan.

A hankali naji ya kama hannuna, Ya ɗago ni ya zaunar dani kusa dashi, ya fuskance ni, tare da kama hannaye na yace "Ni dai ina roƙon ki da ki yi haƙuri Menah."

Dakatar dashi nayi ta hanyar sa hannuna a bakin sa, alamar yayi shiru nace "Ka bar maganar nan ta wuce, bari na sama ruwan wankan kayi, naga  lokacin sallah ya kusa."

Ina gama faɗin hakan, ban jira abinda zai ce ba na tashi, na ɗauko flasks din ruwan zafi, wanda  bana rabo da zuba ruwa aciki saboda Ahmad baya wanka da ruwan sanyi, ga kuma yanayin gidan namu  shi yasa nake zubawa na ajiye.


Juyewa nayi a botikin wankan, na sirka masa  na kai banɗaki na dawo. Ni na taimaka masa, ya rage kayan jikin sa ya fita wanka.

 Kafin ya dawo na gyara inda muka ci abinci, ta hanyar ɗauke kwanukan, na share ko ina ya dawo fes, na kunna turaren wuta na tsinke.

Na buɗe Wardrobe, na fito mai da kayan da zai sa, na ajiye a gefen gadon.

A zuciyata ina jin takaici,   nasan dole in ya fita Masallaci, bashi da damar dawowa yanzu.
 Kuma nasan yana gudun jarabar Hajjo ne, bashi da damar zama a gida da rana ya daɗe a ɗaki.

Sai ta fara aiko ƙannen sa, wai ya fito waje ya sha iska, in taga bai fito ba, wani lokacin da kanta take zuwa sai ta tisa shi gaba ya fita tukun, ta ke komawa wajenta.

Ina zaune jigum ya shigo ɗakin, tashi nayi na tare shi, na shiga taimaka masa ya shirya tsaf.

Gani nayi ya nemi waje ya zauna.
Na ɗan nisa nace "Lokacin sallah fa my." Tare da nuna masa agogon dake mak'ale a bangon ɗakin.

Kallon agogon yayi yace
"Na gani sauran minti goma, yau ba zan je masallacin ba, a gida nake son muyi sallar tare."

Kama hannun sa nayi ina ɗan jan shi kamar me son ɗaga shi, na narke murya nace "Ni dai ka tashi ka tafi, kaga sallah a cikin jam'i tafi lada, nima zanyi tawa kafin ka dawo ka jiii."

Kamar ba zai tashi ba, can dai ya yunƙura kamar wanda ransa bai so ba, ya nufi hanyar fita ɗakin ba tare da yayi magana ba.

Bayan shi nabi da kallo, wani tausayin sa da son sa na ratsani, bawan Allah nasan baya son fitar ne, shi yasa yace muyi sallar a gida.

Ina idar da Sallah naji sallamar shi, cikin mamaki na ke binsa da kallo, tare da kallon bayan sa kamar me son hango wani abu.

Sai da naga ba kowa na tashi, na tare shi cikin ƙasa da murya kamar me gudun a jini nace "Wai dawowa kayi My?"

Fuskar shi cikin nuna baya jin daɗi yace " Haba my Menah ni nafi son in zauna gida na huta, bana son zuwa wajen nan fisabilillahi ace  bani da damar zama da iyalina,  mutum yayi aure amma a hanashi sakewa da iyalin shi." ya ƙarashe maganar cikin nuna abin na masa ciwo.

Kallon sa nayi cikin tausayawa nace  "Kayi haƙuri ka ji.."

Kama hannuna yayi yace "To muje ki bani labari kin ji.."

Ban ƙara magana ba, nayi shiru na bi shi muka zauna a kan kujera, dama nafison ya kasance a gidan, saboda banason shigowar da maman Aisha da hajara keyi ɗakina, kullum da zarar Ahmad baya gida sai su zo su sani gaba su hana ni sakat da surutun su.

Kuma nasan ba komai ke kawo su ba sai gulma. Sai suyi ta kawo min gulmar jama ar gidan, wani lokacin harda maganar Hajjo, sai suna cewa ai abinda take bata kyautawa, bata bari na sake da mijina, da sauran su.

Su yi ta  bugun cikina suna son suji nayi wata magana, ko wata kalma akan Hajjo dan suji daɗin idarwa.

Dana fahimce su, in sun shigo saina ɗaure fuska bana ma basu fuskar maganar. 
Saboda kullum suna tare da Hajjo, kuma in ka gansu wajen ta suna fira, sai ka rantse da Allah ƙawaye ne su, kuma yawacin ba wani abu suke ba, sai gulma da yaɗa jita-jita na mutanen gidan.

Ni kam, al adar su sam bata burgeni, dan a rayuwata na tsani gulma da munafurci.

****

Da dare yayi Ahmad ya tambayeni mai zanci, tunda yasan bamu da sauran abinci.  Tun da dama abincin da Hajjo ke haɗa mana ne, iya rana muke cinyewa.
In dare yayi dole muke neman abinda zamu ci

"Duk abinda kaga ya dace, kawai  ka siyo mana."

 Har ya juya ya dawo yace "Ki dai faɗi me kike so, tunda ban san abinda zaki iya ci ba, kin ga garinnan ba wai kamar can kano bane, ba kowanne abu zaka nema ka samu ba.

"To shikenan faɗa min abubuwan da ake sai dawa naji."

"Eh to akwai wata mai saida  masar shinkafa a bakin titi, in kina so.?"

Jin ya kira masa da murna ta nace " Yawwa don Allah ka siyo min, dama tunda na zo ban ci taba, a dai samin miya sosai dan Allah."
Dan Ina matuƙar son masa a rayuwata, ko wacce iri ina ci in dai waina ce.

"In ta ƙare asa miki yaji.?"

"Wanne irin yaji kuma, ƙuli dai ko?"

"A'a gaskiya bata da ƙuli sai yaji."

Cikin mamakin jin waina da yaji nace "A'a ni bana son yaji, taya  za'a ci waina da yaji? Ta dai samin miyar kawai."

Ya juya yace "To sai na dawo." Nace "Allah dawo da kai lafiya."

Ya amsa da "Amen ya fita."

Bayan tafiyar shi, shiru nayi ina tunanin wannan wace irin rayuwa ce, kayi aure ace sam babu wani daɗi ko hutu, dan masifa ace gidan ubanka ma yafi gidan mijin sakewa.

 Duk da dama akan samu hakan na faruwa, wata zata fito a gidan masu kuɗi ta auri talaka, wata daga gidan talakawa ta auri me kuɗi.
Amma ni nawa na rasa gane kan abin,  ace sau daya za adora tukunyar abinci a rana, baza'a yi na dare ba, in har an kasa an baka shikenan shi mutum zaici har dare. in kuma ka cinye sai dai ka nemi wani abin da zaka ci da dare a aljihun ka.
Ba kuma dan babu abincin da za'a dafa a Wadace ba.

Shinkafa kaɗai ta fi buhu biyu a ɗakin Hajjo, banda sauran dangin kayan abinci irin su wake masara har taliya kwali-kwali, amma dan shegen maƙo   ba za'a dafa a Wadace a ci a k'oshi ba.

Haka yaran Hajjo mazan kowane daga cikin su, in rana tayi zai aiko a amsar masa abincin shi. In dare yayi kuma sai dai kowa yaje  wajen me shayi ya siyi indome ko  shayi yasha.

Gwara Umar da salaha takan ware musu abincin daren su, dan haka su suna ci su k'oshi.

Baba Mijin ta kuwa dama inya bar gidan sai can dare yake dawowa, saboda yanayin sana ar shi ta saida kayan Kanti.

Allah Sarki bawan Allah  Baba, bani da matsala dashi ko kaɗan, tunda nazo ba zan ce ga abin da ya taɓa yimin na kyara ko hantara ba,  dan dama  shi ba mutum bane mai yawan  magana sam, yadda kukasan Hajjo ta shanye shi bashi da katabus.
Ko akan yaran ita ke zartar da komai, bai isa ya tsawatar musu ba, su kansu yaran basa wani ganin girman shi ko kaɗan.

Yadda taga dama haka take gudanar da komai,  kuma nasan duk matsin da nake fuskanta,  bashi da labari bare ya tsawatar,  to ko yaji bana tunanin zai iya magana saboda mugun tsoronta da ya ke ji.

Ina zaune Ahmad ya dawo, yayi sallama na amsa,  tare da tashi na  amshi ledar hannun shi ina mai sannu da zuwa. 

Na dauko flet na dauraye shi na juye wainar, sai tiriri take, kunce ledar da aka zubo miyar nayi.
na juye a wani ƙaramin kwano,  daga yana yin miyar na fara shakkar wainar. Wata irin miya ce kamar ruwa, sai abu abun alayyahu da ɗan fatsi-fatsin kayan miya kawai da zaka gani, shi zai nuna ma miya ce, harda nama a ciki yanka huɗu.

Gaba ɗaya ƙarnin kayan miyar ya dame ni, madadin ƙamshi.
Ji nayi zuciyata na tashi 
Ba abun ince bana ci ba, nasan  ba zai ji dadi ba.

 Nan na daure na jawo filet ɗin kamar zanci, na bude ɗayar ledar da ke kusa dani, sai naga kankana ce aciki da abarba sai robar yugourt irin ɗan jarkar nan guda biyu da sanyin sa.

Wani daɗi ne ya ratsani, na kara ɗauko flet na juye kankanar dan ayanke suke na cire yugourt din aledar, na jere su gaban shi.

Na ce "Bismillah My."

Zaman shi ya gyara sosai, na daure na gutsiri wainar, lomar farko da nayi nakasa haɗiyewa, wani irin mugun tsamine yafara min sallama, sai uban attaruhu da aka cika a miyar ga ta salam, sai warin ɗanyen kayan miya da karnin naman da take.
Alamar dai ko silala naman ba'ayi ba, akayi miyar dashi.

Ganin yana kallona, na daure na haɗiye ta farkon da ƙyar, ai ban iya kai ta biyu ba naji amai na shirin taho min. Ganin zan cutar da kaina yasa na tsame hannuna nace "My bari nasha kankanar da abarbar, bazan iya cin wainar ba."

"To ai nima ba iyacin wainar nan zanba Menah,  kin san ni waina bata dame ni ba, dan dai kince kina so ne na siyo. Dan tunda nake bantaba siya ba sai yau, janyo mana flet ɗin  musha frunt ɗin da yugourt kawai ki aje wainar.

Kallon sa nayi nace "To yaya za ai da wainar tunda bamu ci ba."?

"Ki rufeta da safe azubar dan ba zai yiwu akaiwa a wakin Hajjo ba, kinsan da zan shigoma Shu'aibu naba ledar, nace ya mikomin ta bayan katangar can,  na shigo kuma saida na fara zuwa gurin hajjo tukun, danma karta ce nayi wata siyayyar shiyasa ban biyo ta gurinta ba.

"To shikenan amma inba dole ba babu kyau wulakanta abinci."

Bayan mun kammala na tattara wajen na dawo na zauna,
Muna cikin magana sai ga yan Nepa sun kawo wuta, tashi nayi na jona chargen wayata da tashi wayar, na zuba ruwa a heater na jona ruwan zafi, dan in cika flarsk ɗina.

Ruwan nayin zafi na juye a flarsk, na jona wani na juye ruwan naje nayi wanka, ina fitowa na juye nashi na kai masa ban ɗaki, nace ya je yayi wankan kamar yadda na saba masa.

Fitar shi kenan sai ga Shamsu yazo yayi sallama, Hijabina na ɗauka nasa, na leƙa na ganshi tsaye hannun sa riƙe da kaset.

Ban kawo komai ba nace "Lafiya ko?"

Girgiza min kai yayi yace "Ba wani abu bane, dama kallo nazo ki kunna min, na samo sabon film zazzafan gaske."

 Bin shi na shiga yi da kallo, yaro kamar shamsu dan shekara kusan goma sha takwas, shine zai shigomin ɗaki a irin wannan lokacin da kowanne mai rai ke neman hutu.

Bayan haka ma kamar shamsu inhar za abi ƙa'idar addinin musulunci, ai bai kamata ace harda shi a masu zuwa kallo ɗakina ba,  tunda ba wani ɗaki ne dani daban ba,  bare ince na bar musu intafi wancan.

Muna nan tsaye saiga Yayan shi ya fito wankan, riƙe da botiki ya tsaya yana kallon shamsun, ganin yadda yake tsaye nima ina tsaye yace "A'a shamsu ya akai?."

"Yaya Ahmad dama na zo ne, zan kunna kallo film ɗin nan nake son kalla yau."

"Kai haba wanne irin kallo yanzu Shamsu, baka duba agogo bane, goma saura fa, yanzu kaje da safe ka zo ka kallah, dan barci muke ji dare yayi."
Ya ƙarasa faɗar cike da son ganin ya gamsar da yaron.

 Juyawa Shamsu yayi, yana gunguni, da magana shi kaɗai Allah yasan mai ya ke cewa.

Cikin sauri na  janyo hannun Ahmad nace "Baka tunanin abin da zai je ya faɗawa Hajjo, kaga fa karta zo tana ma faɗa kota ce Ni na zuga ka ka hana shi kallon, ka bari ya zo ya kalla kawai." 

"Kin ga Menah in ke zaki iya jiran ya gama kallo sannan ki kwanta, Ni ba zan iya ba. Dan yadda na gajin nan wallahi babu yaron da zai zo ya samu gaba ya hanamu sakewa, da darennan yanzu fa ƙarfe 9.30pm. Ta ya za'a kunna mana kallo, kallon ma shamsu fa. Ni koda rana da suke janyo abokansu suna shigo miki ɗaki ba so nake ba Wallahi, bai kamata ba sam."

Yana gama faɗin haka yaja hannuna zuwa ɗaki, tare da rufe ƙofar ya dawo mukai shirin barci muka kwanta.

***** 

Allah yayi dare gari ya waye. Da asubar fari Ahmad ya tashe ni, muka yi alwala muka gabatar da raka,atanil fijir, sannan ya wuce masallaci,   bayan na idar da sallah na gabatar da azkhar ɗina cikin sauri, dan gari ya fara wayewa.

 Tashi nayi da sauri na kunna heater, dan nasan karfe shida nayi  Ƴan nepa zasu ɗauke wuta,  insun ɗauke bansan ina zan sa ruwan zafi ba, tunda Hajjo ba bari za tayi na ɗora a wajen ta ba.

Ɗakin na fara tattarawa, cikin azama na gyara gadon, na dauke kwanukan wanke wanken na fitar dasu ƙofar daki, na share ledar tsakar dakin, na ɗauko tsumman dana Ware musamman dan goge ledar tsakar ɗakin na jiƙa shi a bokitina karami, na dan zuba  kllin aciki  na goge ledar tas, na  na kunna turaren tsinke na fesa room freshener sannan naja ƙofar na fita.

Kwanukan ƙofar ɗakin na kauda gefe, nasa tsintsiya na fara share sumintin ƙofar ɗakin, ina cikin sharar sai ga Ahmad ya shigo, na ajiye tsintsiyar na bishi ɗaki ina mai sannu da zuwa.

Yana murmushi ya amsa da  "Sannu da aiki."
 Da "Yawwa" na amsa.

Na tsugunna cike da ladabi nace "Ina kwana."
Hannu yasa ya ɗago ni tare da kara ni jikin sa, yace "Lafiya lau ƴar albarka, Ya kika tashi ya gajiya.?"

Kaina sunkuye nace "Alhamdulillah."

Ƙoƙarin zame jikina nake, ya ƙara riƙe ni yace "Ina kuma zaki je?"

Ina ɗan sunkuyar da kai nace "Dama sharar zan ƙarasa, sai na tafi na hura wuta wajen Hajjo."

Sakina yayi yace "To Yi sauri ki ƙarasa sharar, ki zo ina so kafin kije wajen Hajjo mu ɗan kwanta mu huta, tunda kinga gari bai gama wayewa ba."

Ganin na sunkuyar da kaina ina wasa da yatsun hannuna. Alamar akwai magana yasa,
Ya kalle yace "Naga kamar kina son magana, mene ne ? Faɗa min."

Ɗagowa nayi cikin rashin sa'a idanuna suka faɗa nashi, da sauri na ɗauke nawa idon nace "Dama nafi son naje nayi aikin ne da wuri, kaga jiya sai da tayi maganar ban fito da wuri ba, yakamata kafin ta neme ni in je."

"Shikenan ki je Menah." Yace hakan alamun bai ji daɗi ba.

Jikina ne yayi sanyi, a sanyaye nace "Kayi haƙuri My ka jii, ka kwanta ka huta kafin na dawo."

A daƙile ya amsa min da "To."

Juyawa nayi na fita, 
Sai da na fara ƙarasa sharar, na koma ɗaki na ɗauko hijabina nasa, na tattara ƴan kwanikan wanke wanken da basu da wani yawa, na doshi wajen Hajjo.

A makwarara na aje kwanikan, tare da karasawa  ƙofar ɗakin Hajjo, na tsugunna nace "Hajjo ina kwana."
Sai da nayi magana ya kai sau uku, ba a amsa min ba, sai  can daga ƙuryar ɗaki naji tace "Lafiya lau." 

Jin hakan sai na tashi naje inda take aje tsintsiya, sai da na ɗauka na share tsakar gidan tas, tukun na zagaya lungun da Sani yake kiwon ragunan shi da akuyoyin sa, nan na na share kashin su, ina yi cikin kyankyami, dan duk sun zubar da ruwan shansu a gurin wajen  ya dame, babu kyan gani sam.

Ina gamawa naje bakin murhu, nasa itatuwa dan Hajjo bata yarda da girkin gawayi ba, in dai ba miya za'a ya ba, ita ma awanda take kashewa ne na icce, in ya bushe za ayi amfani da shi.

Ina kunna wutar, na ɗauko tukunyar da take dora ruwan koko, na dauraye na zuba ruwa na ɗora.

Sallama Baba yayi, na  ɗago na amsa, na baro bakin murhun na tsugunna gaban shi na ce "Ina kwana Baba."

Kallona yayi cikin murmushi cike da kulawa yace "Lafiya lau Aminatu, fatan kuntashi lafiya?"

Da "Lafiya lau." Na amsa.
Ya ce "Masha Allah tare da shigewa cikin ɗakin.

Komawa nayi cigaba da aikina, ruwan dana ɗora na tafasa na ɗauki gasarar kokon, na tace ruwan dake sama, na ɗebi gwargwado na zuba abotikin da take dama koko, na ɗan ƙara ruwa akan sauran, na ajiye gefe. Sannan na dama kokon.

Ina gamawa, na koma farlon Hajjo, na tarraro sauran kwanikan wanke-wanke, har zan fita  naga kwanan Bashir bai cinye abincin sa ba, sai na nemi wata yar karamar tukunya na juye na rufe, na aje mata dan nasan tana sane da shi. Hajjo kenan nace a raina, na fice da sauran a hannuna.

Nan da nan na gama wanke-wanken, 
na ɗauko guntun abincin Bashir na ɗora, na tattara gurin na kai botikin kokon ɗakin ta.

Wannan kokon da shine kowa zai karya, sai dai in mutum yana da chanjin shi, in  masu ƙuli sun kawo da gyada mai gishiri mutum ya siya ya haɗa, akwai wata waina da ake kawowa ta wake, Suna kiranta da  gbanbara, ita kuma hamsin-hamsin ce, siyan sai mai kuɗi.
In kuwa baka dashi, sai dai  kasha kunun haka, ka jira abincin rana.

Ina saukewa ɗumamen, na koma ɗakina na ɗauko kofin kokon Ahmad,  na kawo na ajiye a wajen da ake  rabon.

Na fita na zauna a kujerar dake gefen ɗakin Hajjo, ina jiran ta raba na ɗauka dan kar na tafi nayi laifi.

Maman Aisha ce ta fito daga ɗakin ta, ta kalle ni tare da miƙa tayi hamma, bakinta duk miyan bacci idonta harda abin kwantsa, wai nan sunan tayi a sallah komawa barci tayi.

 Nufo ni tayi tana gyara ɗautin zanin ta dake shirin kuncewa, ta fara magana "A'a Amarya har anfito kenan, har kin kammala aikin safen ki kin huta."

Madadin na bata amsa, sai na zame daga kujerar dana ke zaune nace '"Ina kwana? Ya kwanan su Aisha."

Tana ƙoƙarin zama kan dutsen dake gefena tace "Lafiya lau Amarya, ya kwanan me gidan.?"
Da "Lafiya" na amsa mata, ganin bance komai ba duk surutun da take, sai ta tashi ta ɗauki buta tayi hanyar banɗaki, da alama fitsari ne ya matse ta, dan sai sauri take.

A hankali na bita da kallo, a zuciyata ina takaicin halin ta, ga mace har mace, amma daga  haihuwa uku ta maida kanta kamar wata uwar mata, ba tsafta ba gyara, in ba lalaci ba fisabilillah dan mace ta haifi yara uku, har wani lokacin barcin bayan asuba kike dashi, a bar maganar abinci ma, ina batun shirya yara makaranta, bare ke ki gyara jikin ki kafin fitar me gidan.

Shi yasa ita yaranta kullum sai sunyi lattin zuwa makaranta, hankali na ne ya dawo in da Naji motsin buɗe ƙofa.
Tsaki naja cike da takaici na kalli ɗakin samarin gidan, da aka buɗe.

Sai lokacin suka tashi daga barci, dan tsabar rashin kula da addini. A hankali suka fara fitowa ɗaya bayan ɗaya, su huɗu ne, hakan ya nuna ɗan Ladi yana can barcin asarar, shi bai shirya tashi ba sai lokacin 
da yaga dama ya ke tashi.
Kuma babu kunya ya ke sallar shi, a gaban kowa  a ɗakin Hajjo, wani lokacin har ƙarfe tara na safiya rana tsage tsage ya ke sallar. 

Abin takaici kuma ban taɓa jin Hajjo ta tsawatar musu akan rashin sallar ba. A matsayin su na maza da ya kamata ace sallar asuba bata wuce su, sai gashi ko ta safen ma sai rana suke yi.

 Gwara Baba yana ƙoƙarin tashin su, in dai zai je masallaci yana buga kofar su kullum, inaji daga ɗakina amma basa tashi.

Haka suka dinga ɗaukar butoci, kowa da ɗan gajeran wandon shi abin babu wani tsari,  suka nufi inda za suyi alwalar.

Baba ne naga yafito daga ɗakin, da shirin sa na zuwa wajen sana,ar sa, Ya kalle Ni yace "Aminatu sai na dawo."

Adawo lafiya na masa, ina kallon shi ya kalli yaran ya girgiza kai ya fita.

Yana fita kamar jira Hajjo take ta ƙwala min kira.
Tashi nayi na shiga ɗakin, ganin bata farlon sai na wuce uwar ɗakin nata, Salaha na gani kwance tana narkar barcinta a kan gadon Hajjo.

Cikin fushi ganina tsaye ta ɗago tace "To meye sai kin wani biyoni har uwar ɗaki? ki je falo kijira ni ina zuwa."

Na ɗan ji babu daɗi da tamin haka, sai na juya na fita na zauna a farlon, kamar yadda tace.

Haka ta zo ta sameni, ta kalle ni tace "Ina kofin kokon naki naga kin kawo nashi shi kaɗai.?" 

" Ki haɗa mana kawai, tunda ni ba wani sha nake sosai ba."

Sai da ta wani kalle ni a wulakance tace "Ke dai kam kinyi asarar halinki Aminatu, tunda nake ban taɓa jin cewa mutum talaka kamarki,  yace baya shan koko ba sai ke. Wato kin samu waje harda zaɓen abincin, Ai ko shi uban naki Salisu nasan ba arziƙin shan shayi ya ke da shi ba, bare kice min shi kuke sha acan Kano ɗin."

Shiru nayi ina jin zafi a raina, babu abin da na tsana irin kiran sunan mahaifina da Hajjo keyi kai tsaye tana ƙoƙarin aibata shi, ina iya jure komai da Hajjo kemin, amma inhar zata sa mahaifina cikin zagin ta sai naji abin na konamin rai.

Ni kaina nasan a gidammu bamu da ƙarfin shan shayi, amma mukan ɗora tukunya sau uku a rana,  safe da rana da dare, da safe akan dama kunun tsamiya saboda mahaifina yafi sonshi, wanda yaga ba zai shaba akwai dumame tuwo nike ɗora wa, duk me so yaci.

Ni dama nafi son ɗumamen, shi nake ci abina don gaskiya ba kasafai nake shan kunu ba, sai randa nayi sha awar shi inba mu tashi da ɗumamen ba,wani lokacin ma akan aika bahijja ko Ilham su amso mana waina da kuli musha kunun da  ita.

Firgigit na dawo daga tunanin dana tafi, sakamakon maganar Shamsu da naji.

Yana cewa "Hajjo ban faɗa miki ba, jiya  dana je ɗakin yaya Ahmad kallo, ido da ido Yaya Ahmad yace wai dare yayi ba zan kunna musu kallo ba, kuma fa da badon Aminatu ta hanani shigaba kafin ya fito wanka da inma yazo ya tarar dani ba zai ce komai ba."

_*🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️*_