Chapter 4
*🪴 TUSHEN MU ƊAYA 🪴*
*PAGE 4️⃣*
*LITTAFIN💫 KOWA YAƘI JI💫*
*YA KAMMALA COMPLETE DOCUMENT ƊIN SA, GA DUK MAI BUƘATAR MALLAKAR NATA SAI KI MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER ****
Follow the TASKAR MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️ channel on WhatsApp: ***
*DAN SAMUN DAMAR CIGABA DA KARANTAWA KUYI FOLLOWING ƊIN CHANNEL ƊINA GA LINK ƊIN A SAMA👆*
_*🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️*_
Ya cigaba da kallon idona yana magana, "Wallahi Hajjo duk yadda naso na yi kallon nan, ina ji ina gani ta min buƙulu sai hakura nayi, kema na zo in faɗa miki naga kinyi barci dole na je na kwanta."
Cigaba da zuba kunun Hajjo ta yi tana jinjina kai tace "Au ai da ka tasheni wlh da ko uban barci za suyi sai ka kalla, jimin sabon iskanci ai ba daga gidan uban kowa aka kawo kayan kallon ba bare a nuna isa da tak'ama akan su, daɗin abin nan aka zo aka tarda su."
Nasan so take naji zafi shi yasa tasa sunan mahaifina a ciki, haɗe da gorin data saba min, sai na kauda kaina na danne zuciyata dake min zafi na yi kamar ban san suna yi ba, dan kauda maganar sai nace "Hajjo zuba mana kokon."
Dan naga bata da niyar zuba min ɗin, kofin dai na riƙe a hannun ta tana zuba mita.
Juyowa tayi ta kalle ni tayi ƙwafa ta fara kokarin zuba min.
Ji nayi an wani gogi jikina anshigo, da sauri na juyo dan ganin waye haka zai shigo bai san yace na matsa ba sai ya gogi jikina, banwani bane face Ɗanladi, kuma nasan yana sane ai ba a tsakiyar hanya na tsaya ba ina daga gefen bakin ƙofar ne.
Wucewar shi ya yi kamar bai san abinda ya yi ba.
Cikin mamaki nake kallon shi, ace duk faɗin hanyar nan bai ga inda zai wuce ba sai ya gogi jikina?.
Cikin bubbud'awa ya ƙarasa kusa da Hajjo daga shi sai singlet da gajeran wandon, ya wani kalle ta kamar sa'ar sa yace "Yane Hajjo masu ƙosai basu zo ba?."
"Basu zo ba tukun, Allah yasan me ya tsayar da su."
Tsaki yaja ya juyo ya kalle ni, ya kalli Hajjo yace "Yane Hajjo naga wannan ta wani tsayawa mutane ahanya lafiya ko?."
Ɗagowa Hajjo tayi ta bini da kallo ta kauda kai taja tsaki tace "Kasan shi munafuki duk inda yake sai ya nuna kanshi, wai ashe jiya Shamsu ya je ɗakin su kallo, shine ita isasshiya tasa Ahmad ya koro shi wai ba zai musu kallo ba dare ya yi barci suke ji."
Wata iriyar juyowa Ɗanladi ya yi, ya wani watsamin wannan ɗan iskan kallon nashi daya saba yace "Kin san abin ka da ba sabanba, shine take nuna mulki tunda ba irin shi a gidan tsoho ai dole mu a nuna mana iko."
Ya ƙarasa maganar yana me ƙyalƙyalewa da dariya harda buga ƙafa.
Gaba ɗaya ji nayi wasu irin hawaye sun ɓalle min babu shiri, wai me suka ɗauke ni ne? Yau zagin ya wuce ace Hajjo ke min har Ɗanladi ya isa ya zage ni, wai babu a gidan tsoho haƙiƙa naji zafin maganar shi, kuma abin takaici Hajjo itama dariyar take ko a jikin ta.
Shamsu dake tsaye ne yaja tsaki ya miƙawa Hajjo kofi yace "Ni kinga Hajjo gashi ki zubamin kokona, yau da wata uwar yunwa na tashi gashi bani da ko asi, ki ara min naira hamsin zan siyo ƙuli na haɗa haka nayi maneji."
Amsar kofin tayi ta zuba masa, tana faɗin "Wallahi abu ɗaya zai sa na baka kuɗin nan shine kaima baka min rowa." Ta buɗe gwangwanin data ke aje kuɗi ta ɗauko naira ɗari ta miƙo mai tace "Gashi nan sauran ka riƙe min chanji, kana siyo wa ka kawomin chanjina dan ina da buƙatar su."
Amsa ya yi ya juya ya fita yana faɗin "Ai Hajjo sai dai ki yi Haƙuri amma fa babu wani chanji da zan dawo da shi."
"Zaka ci ubanka na in baka bani ba, ai gobe zaka dawo."
Ta cigaba da masifarta.
Ni dai ina tsaye har na fara gajiya da tsaiwa, baƙin ciki goma da ashirin zafin zagin da suka min, ga abin haushi ta ƙi sallamata na tafi.
Gani nayi Ɗanladi ya fito daga uwar ɗakin Hajjo hannun sa riƙe da sallaya, babu kunya ko kaya bai nema ba bare yakara suturta jikinshi ya tada sallah.
Cikin mamaki nake bin sa da kallo, dama wai bai yi sallah ba ya zo ya tsaya ikon Allah kenan.
Salaha dake barci a uwar ɗaki ce ta fito tana miƙa, ba tawa kowa magana ba wuce su, koda zata wuce ta wajena bata ce na matsa ba sai ni na bata hanya nasan ita ma yanzu za tayi alwalar.
.
Sai da Hajjo taga dama dan kanta ta miƙo min kofin kunun, tana faɗin "Ke da wai kina tsaye ba zaki yi magana ba, dana manta na gama rabon ai da kun huta sai kuci babu."
Bance mata komai ba na amsa jiki a sanyaye na juya.
***
Ina komawa ɗaki, na tarar da Ahmad yayi wanka yana zaune yana danne dannen shi a waya.
Ya ɗago ya kalle ni yana murmushi tare da ajiye wayar hannun sa yace
"kin dawo?."
Amsa masa na yi da "Eh" na ajiye kofin kokon hannuna.
Na cire hijabin jikina na jefa kan k'yauren ƙofar.
Sai shima ya miƙe yana faɗin "Bari naje na amso miki abin da za ki karya, dan nasan ba iya shan kokon nan za ki yi ba, in kinga kirana a wayar ki kawai ki fito ta wajen katangar bayan ɗakin nan ki amsa, dan bana son Hajjo taga leda a hannuna tace wani abu na siyo."
Da "To"na amsa nace "A dawo lafiya Allah ya kiyaye hanya."
Zuciyata duk ba daɗi na wuce na kwanta a kan doguwar kujera, na faɗa duniyar tunani wanda a yanzu ya fara zame min jiki.
Jin ringing ɗin wayata na tashi nasa hijabina na fito, na tsagaya ta can bayan ɗakina kasancewar katangar wajen ba wani tsayi ne da ita ba, ina zuwa nayi ƙasa da murya ta nace "Gani" a hankali saboda kar wani ya jini, dan nasan masifar Hajjo zata iya zuwa bamu sani ba.
Miƙa min ya yi yace "Ki sa a hijabin ki."
Ina amsa na juyo jikina a sanyaye, ina tunanin wannan jarabar, Ahmad bai isa ya shigo min da abu a leda ba saboda Hajjo, tun banfi kwana huɗu a gidan ba na fahimci halin ta, da farko in zai shigo zai shigo da ledar shi a hannu kai tsaye zai wuce ɗakin Hajjo, in ya mata sallama ya taho wajen mu, to da tayi shiru bata cewa komai.
Daga baya sai in naje da safe ta yi ta yada min magana, akan ledar da ya ke shigowa da ita wai Ni na koya masa rowa ita baya siyowa da ita.
Ranar da ta min maganar na same shi, na nuna mai rashin kyautarwar sa nace in zai shigo ya dinga siyo biyu, ita ɗaya ni ɗaya dan a zauna lafiya.
Daya fara haka kamar abin arziƙi sai ta daina magana, sai dai idon ta kullum na kan ledar tawa tafi tata ko tata tafi tawa? Ƙarshe ma sai ta amsa ta duba in taga nawa ya kai nata tofa saita rage, acewar ta ai su sunfi mu yawa ga ƙannen sa suma Sa'adu ci, haka zai bata ta rage ta bashi sauran ya kawo min haka.
Hakan bai ishe ta ba, saboda baƙin cikin kar ma a kawo min koda kaɗan ɗin ne naji daɗi.
Sai ta fara tsiro da maganar ai yana ɓannar kuɗi ya daina siyo naman, ita ta yafe ya daina ɓata kudin shi a banza, gwara ya dan ƙara musu kuɗin cefanen da ya ke bata akara yawan abinci adinga zubamana wanda zai kaimu har dare.
_Ni kuwa nace ashe tasan baya isar mu, mugunta ce tasa take hakan._
Farko ya amshi shawararta ya kara kuɗin, duk da ba wai ya so hakan bane dan shi mutum ne mai son kyautatawa iyali, amma da yake ta saba sai taƙi ƙara hannu a abincin.
Inda na godewa allah shima yana ganin abincin ba ƙara war tayi ba akan yadda tasaba zuba mana, gudun kuma karta ga ya cigaba da shigowa da leda yasa ya bullo da dubarar d
miko min ta katanga. s
Saboda ɗakin hajjyo setin ƙofar shigowa ya ke, duk wanda ya shigo idonta na kansa harda wata kujerar ta ƴar tsugunno a bakin ƙofar, in ta zauna sai ta ɗan buɗe labule tana ganin kowa dake shige-da fice.
Ɗaki na shiga na zauna a ƙasa saboda wata Iriyar yunwa da nake ji, ina buɗe ledar naga indome ce soyayyiya sai soyayyen ƙwai daban, sai wata leda dana taɓa naji zafi da alamar shayi ne aka ƙulle a leda.
Kofi na ɗauko na Juye na zauna na fara ci ina shan shayin, nasan Ahmad ba shigowa zai yi yanzu ba wataƙil yana wajen abokan sa.
Ina gamawa na tattara ɗakin na nufi wajen Hajjo, dan nasan in banje Bama aikowa za tayi.
Ba ɓata lokaci na amshi komai kamar yadda ta saba bani a k'ididdige na ɗora, ina kammalawa na sauke kamar yadda aka saba yauma shinkafa ce da miya, wadda tunda nazo gidan ba ataba canjawa na kullum ita ake, sai lokacin da taso ana sa taliya leda ɗaya a haɗa da ita.
Zama tayi ta hau rabo kamar yadda ta saba.
Sai dai yau munci sa'a ba'a zuba mana ƙanzo ba.
****
*BAYAN KWANA BIYU*
Yau gaba ɗaya jikina a sanyaye ya ke, sakamakon yau ne Ahmad zai koma wajen aikin sa hutun da ya ɗauka ya ƙare. Da ya ke irin aikin painting ya ke amma shi a ƙarƙashin wani kamfani mai suna _(Fine coat)_ In da in kwangilar wani aiki ta taso kamfanin kan amsa sai su bawa su Ahmad kai tsaye kamfanin ke biyan su, dama hutun da suka bashi sati Uku ne saboda auren da ya yi, yanzu kuma ya cika sati ukun.
A hankali na ke zuge zip ɗin jakar dana haɗa masa kayan sa, kamar bana son zip ɗin ya kai ƙarshe na gama zugewa.
Har zan ɗauke jakar sai na tuna da bansa masa brush da makilin ba.
Sai na tashi na ɗauko, na buɗe gefen jakar nasa na ƙarasa wajen madubi na ɗauki man shafawa da turaren sa nasa masa a ciki, sai da na tabbatar duk wani abu da zai buƙata nasa a ciki, tun daga sabulun wanka soso da dai sauran su .
Zuwa lokacin ya kammala wankan da ya shiga, na tashi na taimaka masa ya goge jikinshi, duk cikin sanyin jiki nake komai ina lura da yanayin sa shi kanshi dauriya ya ke, dan a sanyaye ya ke gudanar da koman sa tun wayewar gari.
A haka na taimaka masa har ya shirya.
Juyawa ya yi yace "Bari naje na sallami Hajjo na dawo."
Na koma bakin gado na zauna nace "To" Yasa kai ya fita cikin hanzari.
A hankali na ɗaga kai na kalli agogon dake manne a bangon ɗakin naga ƙarfe tara na safe 9:am
Ina lissafe sauran minti talatin motar su ta iso, za'a turo a ɗauke sa ne da ya ke akwai wasu kaya da kamfanin su suka kawo farin
****
Yana zaune gaban Hajjo kan shi sunkuye yana sauraren ta, ana ta buga mai lissafin abubuwan da za'a siya, da kuɗin da zai bada na cefane.
Bayan duk ya gama cake mata kuɗin, sai da ta tura ƙasan ledar tsakar ɗakin ta, tukun ta karkace tace "Yanzu kwana nawa zakuyi in ka tafi?."
Girgiza kai ya yi yace "Ban san yanayin wajen da za'a tura mu ba Hajjo, sai mun je zamu dan kwana nawa zamu gama tunda bamu ga yanayin wajen ba."
Taɓe baki ta yi tace "To kaga kenan kuɗin cefanen daka bar mana, ba lallai ya ishe mu ba tunda kai ma baka san ya tafiyar zata kasance ba, gwara ka ɗan ƙara mana dan gudun mu zo muna kame-kame."
Cikin ladabi yace "To Hajjo kamar nawa kike ganin zan ƙara muku.?"
"Kai kasan yanayin lokacin ai, ba sai na ƙara maka bayani ba."
Ta wani kauda kai..
A hankali yasa hannu a aljihun sa ya irga dubu goma sha biyar ya miƙa mata, yace "Wannan ai zai isa kuyi maneji ko? in naje naga mun daɗe sai na tura muku kuɗi ta account ɗin Shamsu.
Sai da ta kalle shi ta kalli kuɗin babu alamar zata amsa, can ta nisa tace
"Amma dai kasan ba haka muka saba yi da kai ba, koda nace ka ƙara ai yana fin wannan ka ke bani."
Cikin ladabi yace "Na sani Hajjo kema kin san yana fin haka ɗin, amma kinga tunda akayi bikinnan ba wani fita mukayi ba, kuɗin da ke waje na ne mukayi ta ci, banda Allah ya taimakeni da gudummawar da aka dan babbani, inaga da tuni na koma wajen aiki dan zaman haka ai ba zai yiwu ba, sannan kinga yanzu ga Aminatu nauyi ya ƙaru a kaina, dole in zan tafi ita ma zan bar mata wani ɗan abu saboda in buƙatar kuɗi ta taso mata ta yi."
Tsaki Hajjo taja cikin jin haushi tace "Kai kuwa banda abinka me Aminatu zata yi da wani kuɗi? yoh inama ta sani bare tace ga abin da take so, in dai abinci ne akwai shi a gidannan anayi kowa yana ci."
Ta miƙa masa hannu tace "Kaga babu maganar bata wasu kuɗi kawai ka ƙaro mana dansu ishe mu."
Zuciyarsa babu daɗi saboda yadda ta nuna son kai kai tsaye, matar shi ce fa zai bawa kuɗi take cewa karya bata.
Cikin lallashi yace "Ki yi Haƙuri Hajjo duk da haka akwai wani abun da dole sai ta nema in bana nan, gashi ba wani take dashi da zai bata ba sai ni.
Ganin alamar ba bata zai ba yasa tace "To bani wanda zaka bata ɗin in ajiye mata, inya so in tana da buƙatar sai kace tazo gurina ta amsa, dan inka bar mata ma aban zata ajiye su ba amfani, tunda ba sanin darajar su tayi ba."
Dan dai a rabu lafiya, ya ɗauko dubu biyu cikin dubu biyar ɗin da ya yi niyar barwa Aminatu, yace "Gashi Hajjo."
Tasa hannu ta amsa tana haɗa dana hannun ta tana faɗin "Ko kai fa."
Tashi ya yi yace "To Hajjo zamu tafi, na riga da nayi sallama da Baba da muka haɗu a masallaci in yazo ace masa na wuce."
Ita ma miƙewa tayi tana gyara ɗaurin zanin ta tace "To shikenan Allah ya tsare hanya ya bada sa'a."
Da "Amen" ya amsa ya fita.
Wajen Aminatu ya koma, ya tarda ta zaune ta zabga tagumi, a hankali ya ƙarasa ya zauna kusa da ita ya kama hannun ta ya cire tagumi.
Na ɗago na kalle shi ina cikin ƙoƙarin maye fuskata da murmushi nace "Ka dawo?"
Bai bani amsa ba sai rungume ni da ya yi, ya fara raɗa min magana a kunne, cikin tashin Muryar ya ke lallashina.
Har sai da ya ga na fara dariya ya sake ni, ya tashi yana gyara zaman wuyan rigar shi.
Ya sa hannu a aljihun sa ɗauko sauran kuɗin dake ciki, ya lissafa dubu goma ya miƙo min yace "Gashi ko wata buƙatar zata taso miki, nasan dai kayan shayin dana kawo miki jiya zasu ɗauke ki wasu yan kwanaki, ki yi hakuri kinji insha Allah bazan daɗe ba koda ba akammala aikin ba zan dawo na ganku."
Amsa nayi ina ƙoƙarin maida ƙwallar data taru a idona nace "To nagode Allah ya kara buɗi na alkhairi da wadata ya tsare ka ya kare ka aduk inda kake, Allah ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya cikin aminci ya kuma bada sa'a akan abin da aka je nema."
Da sauri ya jawo ni jikinsa ya rungume ya amsa da "Amen Menah ta Allah ya bar min ke, ki cigaba da min wannan addu'ar taki me tsada, Wallahi Dear zan yi kewar ki sosai da ba dan nema ya zama wajibi ba, bai kamata na tafi na barki ba amma karki damu ba zamu daɗe ba."
Ƙara ƙanƙame shi nayi ina kara tusa kaina a k'irjin shi, ina ƙoƙarin hana kukan da ya tahomin fitowa.
A hankali ya ɗago fuskata ya zuba min ido, yanayin kallon da ya ke min yasa na rufe idanuna a hankali ƙwallar dana ke riƙewa ta zubo.
Girgiza min kai ya yi yace "Kar kiyi kuka mana kinji Babynah ba zan daɗe ba fa kuma kin ga zan dinga kiran ki."
Ya ƙarasa tare da ɗan langwaɓar da kanshi.
Ƙara shagwabe fuska nayi ina taɓe baki alamar kuka, sai dai bai bani damar wannan ba.
Ai babu shiri na had'iye kukan nawa, sakamakon abinda ya yi.
A hankali na kwantar da kaina k'irjin sa nayi lamo ina sauke numfashi, shima ya kasa saki na gaba ɗaya.
Ringing ɗin da wayar shi ne yi shi ya fargar damu lokaci, ya ɗan taɓa jikin sa da nawa ya sa hannu a aljihun wandon shi ya fito da wayar ya ɗaga tare da karawa a kunnen sa.
"Ok kun karaso to ganin fitowa." Shine abinda ya ce kawai, ya ɗauki kakar shi da ke ƙasa ya nufi ƙofar ya juyo yana kallona yana faɗin "To sai Allah ya dawo damu."
Tuni kukan dana ke hana kaina ya taho min, dan har ga Allah na kasa riƙe shi nasan zanyi kewar mijina sosai, ga fargabar halin da zan fuskanta daga su Hajjo data kamani.
Da sauri ya dawo ya ajiye jakar ya rungume ni cikin lallashi yace "Ki daina kukan kin ji, karki karya min gwiwa na kasa tafiya."
Ina share hawaye na nace "To" na zame daga jikin sa na ɗauki hijab ɗina nasa, na ɗauki jakar shi da kaina ina mai binshi a baya muka fito.
Sai da na raka shi har bakin lunguna, gudun karna bishi wajen Hajjo inyi laifi na juya ɗaki cike da kewar shi jikina a sanyaye ina share hawaye.
Haka na wuni cikin kewa, ko aikin yau na daure ne na je nayi ayyukan dana saba, abincin yau kam an zuba min shi kamar irin na roƙa ɗin nan, ni dai amsa na yi na baro wajen ɗan damuwar da nake ciki bana jin zan iya cin abincin ma.
***
Kwanaki sun shura yau Kwanan Su ahmad biyar da tafiya, kuma tunda suka tafi su Hajjo suka buɗe sabon babin takuramin, sai dai ina ƙoƙarin ɗauke kaina in nuna bansan suna yi ba.
Yanzu maimakon girki da wanke wanke da shara da kokon safe da nake yi, ganin Ahmad baya nan har wankin Hajjo dana Salaha da Umar Ni nake yi.
Nice gyaran ɗakin ta gugar uniform din su Salaha, duk Ni kaɗai kullum bani da wani hutu a rayuwata.
Dan har addu'a nake Allah yasa kar akawo Nepa da dare, saboda daga ankawo bani babu barcin wuri, sai su zo su cika min ɗaki da sunan kallo, duk su ɗane min kujeru tunda dama ɗakin ɗaya ne haɗe da kujeruna da gado na komai a ciki ya ke, bana yarda su hau min gado duk iskancin su kuwa.
akwai kujeru guda biyu cikasu suke sumin kaca kaca da ɗakin su fice abinsu, ga abokansu da suke gayyato wa gasu wai abin kunya harda Ɗanladi a masu zuwa kallo.
Yau bayan sun gama kallon ina kwance kan gado, sai naga Salaha bata tafi ba ta zauna.
Wai ashe Hajjo ce tace ta zo ta taya ni kwana babu wanda ya faɗa min cewa zata tayani kwanan, buɗe baki na yi da nufin tambayar ta me take jira bata tafi ba, sai gani na yi kawai tana ƙoƙarin hawo min gado ta kwanta.
Da sauri na tashi ina kallon ta nace "Ke me kike nema kika hau min gado?"
Salaha kike kokarin hawa gadon ta dakata tana turo baki gaba yace "Hajjo ce tace na zo na kwana a nan tunda ke kaɗai ce Ya Ahmad baya nan."
Tashi nayi na ɗauka daga gadon na janyo ta baya, na kalle ta nace "To sai aka ce miki haka a ke saivkiyi ƙoƙarin hawa gado, bayan ga kujera in kwanan zaki taya Ni."
Buɗar bakin ta sai ce min ta yi, ai Hajjo cewa ta yi ta kwanta a gado dan ita bata saba kwanan ƙasa ba.
"Lallai kam to Ni kam ba zaki kwanta min a gado ba, ki koma kan kujera in kwanan za ki taya ni, amma wallahi kinji na rantse ba za ki hau min gado ba. In kuma kujerar bata miki ba ki tafi ɗakin ku dama bani na kira ki ba."
Fita ta yi ta wani banko min ƙofar da ƙarfi.
Nabi in da ya wuce da kallo, na taɓe baki a zuciya ta nace
_Wallahi ko Hajjo ce ta zo banga fitsararriyar yarinyar da zata haumin gado ba, in ba rashin tarbiya da ɗa'a ba ina wata Salaha yarinyar ƴar shekara goma sha huɗu zata hau min gado fisabilillah._
"Hmmm nayi ƙwafa na hau gado na kwanta banma rufe ƙofa ba, dan nasan tabbas sai Hajjo ta biyo bayan ta.
Aikwa ban gama tunaniba sai jin maganar ta nayi, da ƙarfi take cewa "Wuce mu je inji in ta zo da gadon ne daga gidan ubanta." Daidai lokacin ta dawo kai ɗakin nawa.
Da sauri na diro daga gadon, kafin ta ƙarasa shigowa na coge bakin ƙofa ina kallon sun
Ƙarasowa tayi ta kalli yadda na tsaya ɗin tace "Ke Aminatu ke ce kika ce Salaha ba zata kwanta miki a gado ba, saboda Ubanki salisu ya siya ko? naga uban naki saboda tsananin talaucin sa da shegen son banzan sa ko katifa wannan bai siya miki ba bare ayi maganar gado.
Shine saboda kin samu guri har wani nuna isa da takama ki ke akan gadon, ke gaki me miji ba za'a hau gadon shi ba, ai in ke mijin ki ne ita Salaha yayan ta ne, in ke kina taƙamar mijinki ne kinsan kuma wata kusan tafi wata ko?."
Ta wani jawo hannun Salahar ta turo ta gaba tace "Salaha wuce ki kwanta kan gadon."
Saboda tsabar yadda zagin yau ya min zafi, ga gori ina ji a zuciyata ko me za ta yi wallahi sai dai ta yi amma ba zan bari ta kwana a gadona ba.
Na ɗago da kaina a sanyaye zuciyata na min zafi na daure nace "Hajjo ta ya Salaha zata kwanta akan gado bayan babu kyau, Hajjo ce mata nayi ta kwanta a kujera be dace ta kwanta gadon da yayanta ke kwantawa ba."
Na ƙarasa maganar cikin dan dakewa.
Tafa hannu ta fara tana faɗin "Ah lallai to gwadamin ke kinsan daɗin namiji, nace faɗa min ba a hawa ba gadon da ma aurata ke sunnah? ke harni za ki yi wa wani wa'azin ki na banza da wofi."
Tana ta bambamin faɗan ta wai ko zan matsa, ganin ban dai matsa ba bare su shigo, ko ta gaji ne ko me ya gani? Oho.
Cikin masifa tace
"Salaha wuce muje ki kwanta wajena, bari ni in kira Ahmad ɗin naji ko shine yace kar adinga bari kina zama da kwantawa a inda ki keso?"
*_😍MAMAN DAN ALBARKA CE_*😍✍️