TUSHEN MU ƊAYA

Chapter 5

by @mamananalbarkace777

*🪴TUSHEN MU ƊAYA*

            *PAGE 5️⃣*

   *_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_*

*LITTAFIN KOWA YAK'I JI YA KAMMALA COMPLET DUCOMENT, GA MAI BUƘATA TA MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER ****

Suna wucewa, na sawa ƙofata sakata na yi shirin barci nayi addu,o,ina dana saba na kwanta, ina mai ƙoƙarin ganin na yakice tunanin baƙaƙen maganganun da Hajjo ta yaɓa min a  zuciyata.

Allah sarki Hajjo kenan, bata san rayuwa me ake cewa ƙaddara ba, nima bani na zaɓawa kaina auran ɗan ta ba, Allah ya ƙaddara mijina ne tun tuni amma ita kullum tana nuna kamar bata so auren mu ba. 

Duk wannan gorin da take min, nasan da mahaifiyata na raye zai yi wuya wasu abubuwan da ake min gori amin su,  saboda Ummana ta kasance jajirtacciyar mace me ƙoƙarin akan ƴaƴanta, wajen kula da tarbiyarmu  da kuma ƙoƙarin taimakon mahaifinmu akan harkokin gida, dan bata zama haka tana da sana'o'in ta da take a cikin gida, kuma suna kawo mata ƴan chanji.
Sai dai mutuwa da ta mana yankan ƙauna, Allah ya amshi ranta daidai lokacin da muke tsananin buƙatar kulawar ta gare mu.
Kullum ina wa Ummanmu addu'a, akan Allah ya jik'anta ya mata rahama yasa aljanna ce makomar ta.
Zuciyata cike da tunani kala-kala barci ya ɗauke ni.

****

Allah yayi dare gari ya waye, yau tunda na tashi da safe nake fama da wani irin ciwon mara.
 Sakamakon baƙon wata na da ke shirin zuwa, haka ya ke min kowanne wata in zai zo, ina matuƙar shan wahala sosai.
Duk lokacin da ciwon ya fara, tofa banda aiki sai kwanciya, ko lokacin da nake gidanmu haka ya ke ƙannena ke aikin gida.

Dan haka yanzu ina kwance ne kawai, amma hankalina na kan Hajjo da aikin da nasan ya zamar min farillah.
 Juyi kawai nake a tsakar ɗakina, hannuna dafe da marata, duk yadda nake ƙoƙari wajen gwada tashi nakasa tashi.

Bisa dole na maida kaina na kwanta.
Nan da nan wani wahalallen barci ya fara ɗauka ta, cikin barcin naji ana magana a kaina sama-sama. Umar ne tsaye yana kallo na, ban ma san lokacin da ya shigo ba saboda barci.

"Hajjo tace me kike har yanzu baki fito ba?."
Ya faɗi hakan yana kallona yadda nake yatsine fuska.

Cikin cije baki na ɗan ɗago kaina nace "Umar ba zan iya tashi ba, dan Allah kacewa hajjo bani da lafiya ba zan iya aiki yau ba."

Cikin tausayawa yaron ya kalle ni, muryar shi a sanyaye yace "Meke damun ki Aunty Aminatu?."

Tunda nake da yaron bai taɓa kirana da Aunty ba sai yau.
Haka kawai sai naji daɗi cikin Muryar da tayi laushi saboda ciwo nace "Kaina ke ciwo Umar."

Girgiza kai ya yi yace "Allah ya baki lafiya, bari na je na faɗa mata."
Yasa kai ya fita a ɗakin.

Fitar umar bai fi minti uku ba, sai ga Hajjo ta shigo ɗakin, bina ta shiga yi da wani irin ƙasƙantaccen kallo, a wulaƙance tace
"Me ki ke nufi da kika ce ba zaki iya aiki ba? Wallahi karya ki ke makira.Wato saboda tsabar makirci shine ki ka ce kanki na ciwo ko? aikinne ba za ki yi ba shiyasa kika tsiro da rashin lafiyar ƙarya, to Allah yasa mutuwa ki ke kina dawowa, ba abinda ya shafeni da hakan ki tashi ki wuce ki min ayyukana yanzu."

Da ƙyar na iya ɗagowa cikin wahalalliyar murya sakamakon wata irin kartawa da marata ta yi nace "Hajjo cikina ke ciwo, wallahi ba zan iya tashi ba Hajjo, ki yi haƙuri dan Allah."

"Wanne irin ciwon ciki? Au tanan kika ɓullo kenan?."

Babu zato na ji tasa hannu ta wani fusgoni, cikin tsawa tace "Dallah tashi mu je, wa ki ka aje da zai min ayyukan? kinyi kaɗan ki sani aiki bayan ga ki, iskancin da rashin kunya da rashin tarbiyar da kika nuna min jiya ma ya isa, wato dan kinga na ƙyale ki shi yasa yau kika tashi da sabon salon iskanci ko."

Yanda ta fusgoni haka na koma yaraf na kwanta, na fashe da wani irin kuka gwanin ban tausayi, saboda har ga Allah ji nai wata irin azaba ta ratsani lokacin data fusgoni.
Saboda cikin mugunta ta fusgoni tana matsa hannuna, ga azabar  ciwon da nake ciki.

Kuka nake harda shashshek'a, dan ina ganin shi ne kawai zai rage min zafin da nake ji.

Tafa hannu ta shiga yi cikin ɗaga murya yadda kowa zai ji tace "Ku ji min yarinya da munafunci, salon wani yace na dake ki ne kona miki wani mugun abun, shine  kika ɓare baki kina kuka."
Ta ƙarasa faɗar cikin daga murya inda na tabbata duk mutanen gidan suna ji.

Aikuwa sai gasu sun fara shigowa lunguna,   Maman A'isha ce ta fara shigowa, sai matan can cikin gidan su Hajara suka biyo bayan ta.

"Lafiya Hajjo me ke faruwa mukejin ihunki da sassafennan?."
Cewar Maman A'isha kenan, idanunta a kaina.

"Hmmm ke dai bari Maman A'isha, wallahi yarinyar nan makircin ta yayi yawa, daga cewa ta fito tayi aiki shine wai harda ƙaryar rashin lafiya, bayan ga ayyukana can ajibge suna jiran ta dan ko shara banyi ba yau.

Ɗaya daga cikin su ce, wadda ake kira da Yawo jummai tayi caraf tace "Haba Hajjo yarinyar nan na ƙoƙari, kinga kulum ita ke yin aikin, yau tunda bata da lafiya ayi haƙuri kin ji."
Ta ƙarasa tare da tsugunnawa kusa dani, ta kama hannuna tana tambayata me ke damuna.

Wata ce daga cikin su wadda ko sunan ta ban sani ba, ita ma ta amshi zancen, cikin Hausar ta da bata gama zaunawa a bakin ta ba tace "Aba Ajjo tunda baka da lafiya yace, ai saika yi maka ayyukan inka samu lafiya sai ka cigaba."

Cikin tsawa Hajjo ta ɗaga musu hannu tace "A'a fa karku shiga abinda babu ruwan ku, bawani rashin lafiya gulma ce kawai ke damunta, ku barni da ita ni zan sa ta tashi yanzu."

Duk maganganun da suke, Ina kwance har lokacin ina murk'ususun ciwo, haka suka dinga maida magana, wannan ya faɗa wannan ya faɗa wasu na cewa tayi haƙuri, wasu na faɗin na daure na je nayi ai mace ce ni.
Irin su Maman A'isha kenan ƴan fadar ta.

Da ƙyar su ka samu suka  lallaɓa Hajjo akan ta bari na huta, aikuwa ta kalle ni tace kar nasa rai da abincin karyawa yau, tunda nace ba zan yi aiki ba.
Haka dai suka jata ta fita. 

Matar nan ce wadda bata ji Hausa sosai ba, ta dawo ta tsugunna kusa dani.
Cikin tausayawa ta kira sunana "Aminatu."
 
A hankali na ɗago da ƙyar nace "Na'am."
Dan zuwa lokacin wani irin zazzafan zazzaɓi ya rufe ni.

Kama hannuna da tayi taji zafi, yasa ta sake ni da sauri tana faɗin "Me ya damunka?."
Duk da hausar tata bawani iyawa tayi sosai ba, na fahimci abinda take nufi me ke damuna.

Dan haka cikin cijewa nace "Cikina ke ciwo."

Fuskar ta ɗauke da yanayin tausayi tace" Kaasa oku."
 Tasa hannu tana taɓa wuyana zuwa hannaye na.
"Oh jikinka kayi zafi, sannu ka ji."

Allah ya sani naji daɗin yadda ta tausaya min, cikin jin daɗin hakan nace "Yawwa."

"Kanada magani?."
Ta tambaye ni.

Girgiza mata kai na yi, alamar "A'a."
Tace na kawo kuɗi ta bawa ɗan ta ya siyo min.
Nuna mata ƙasan pillow nayi nace akwai kuɗi ta ɗauka.
Tasa hannu ta ɗauki ɗari biyu ta fita,  babu jimawa ta dawo hannun ta ɗauke da maganin.

Tambaya tayi naci abinci? Nace hanci ba.
Tace bari taje wajen  Hajjo ta amso min.

Duk kaiwa da kawowar da take Hajjo na kallon ta, ta cika tayi fam tana ganin hakan a matsayin munafurci ne kawai.
Shi yasa da taga ta nufo wajen ta ta haɗe fuska.

Da zuciya ɗaya tace Ajjo ina abincin Aminatu? zan kai mata na bata magani."
 
Wani kallo Hajjo ta watsawa matar tace "Wallahi ba zan bata ba,   kun riga da kun bani Haƙuri akan kar ta yi aiki, to na haƙura da wannan, amma ba zan zage na dama koko ba in zuba mata bayan ta barni da ayyuka ni kaɗai.*

Cikin sassauta murya da Hausar ta da bata gama nuna ba tace "Haba Ajjo kayi ankuri mana, ka bashi bashi da lafiya  Ajjo."

Cikin tsawa-tsaww Hajjo tace "Kinga yawo jummai ki wuce ki je in kina da abin yi ki yi, abinci ne kinji na rantse wallahi yau gaba ɗaya ba zan bata ba, taje taci rashin lafiyar tunda mugunta ne abin."

Girgiza kai Yawo jima'i tayi, tana mamakin hali irin na Hajjo gata dai bahaushiya amma bata da hali irin na hausawan data sani, a sanin ta hausawa mutane ne masu tausayi, haƙuri tawakkali saɓanin su yare da wasu basu san wannan ba. duk da a kowane yare ana samun iyayen miji na ƙwarai, da kuma irin Hajjo, amma na Hajjo ya yi yawa.
Duk mutanen gidan  suna sane da irin takurar da Hajjo kewa surukar tata, har mamaki suke yi wai a haka ance ƴar ɗan uwan mijin Hajjo ɗin ce Aminatun. Anya kuwa hakane? Ya jummai ta tambayi kanta. Dan Hajjo tace yar ƙanin mijinta ce amma basu ga wata alama ta mutumci ko riƙon amanar da aka damka mata ba, kullum cikin takura yar mutane take sai kace ita bata haihu ba.

Jiki a sanyaye ta dawo ɗakin nawa, ta ƙaraso ta tsugunna tace "Ka yi haƙuri Aminatu bai bani ba, za ka sha kununa in  inkawo maka?."

A hankali na girgiza mata kai, tun farko naso nace mata kar ta je wajen Hajjo dan ba shan kunun zan ba.
Amma gudun taga kamar ban yaba ƙoƙarin ta ba, yasa nace ta also ɗin.

Gashi tana batun ta bani kunun ta, nasan Hajjo ta hanane shiyasa tace zata zu bomin nata. Ni kuma har ga Allah koda ina shan kunu ba zan iya shan nasu ba, saboda yadda Allah ya yi ni da k'yank'yami.
Su kuma babu ruwansu robar da ake wanki da ita, zaka iya tardata bakin famfo ana ɗiban ruwan sha da ita ko ana tatar kamu da ita, hakan ba komai bane a wajen su.

Ganin yadda ta damu akan naci wani abu, sai nace mata "Ina da kayan tea dan Allah ki ɗauki nera ɗari biyu ki ba Husaini ko Hassan, su siyo min  ƙosai Ina da biredi.

Sai da tamin sannu sannan ta ɗauki kuɗin ta fita. Babu laifi nasamu na ɗan ci ƙosan da biredin kaɗan, duk da babu wani daɗi daga gishiri sai dan atturuhu da albasa ko magi basa sawa bare maganar yaji. A haka dai na tuttura, na hada da tea ɗin data nemo ruwan zafi ta jika lifton din babu maganar dafawa tunda bana dora girkina daban.

Godiya sosai na mata tace bakomai, haƙiƙa yawo jummai ta min abinda ban samu daga wajen waɗanda ya kamata ace sun min ɗin ba. Zan iya cewa tunda nazo gidan ban taɓa ganin wani daga cikin mutanen gidan ya tausaya min ba, dangane da halin da Hajjo ke nuna min ba sai yau, koda kuwa suna ji tana zagina babu me fitowa bare su bata Haƙuri.

Ranar gaba ɗaya akwance na wuni.
Kuma kamar yadda hajjo tayi alƙawari bata bani abinci tsayin ranar ba.

Haka koda Ahmad ya kira bance masa komai ba, gudun kar hankalin sa ya tashi. Na dai ce masa bana jin daɗi ne kawai, saboda duk son da miji ke miki ko me mahaifiyar sa tayi miki, ba zai ji daɗi ba in kina yawan faɗa masa aibunta, dan duk son da ya ke miki bai kai wanda ya ke wa mahaifiyar sa ba. Saboda haka babu amfanin duk abin da uwar miji ta miki ɗan ta na dawowa ki kwashe ki faɗa masa, koda yana goyon bayanki mahaifiya tafi karfin wasa wataran zai fara ganin baƙin ki yaga kamar bakya girmama mahaifiyar sa.

_ALLAH YASA MU DACE_

******
   *BAYAN WASU KWANAKI*

Tun washe gari da naji sauƙi na koma bakin aikina,  sai dai fa ina shan baƙaƙen maganganu, sai na ke toshe kunnuwana inyi kamar bana jin me take cewa, haka zata ƙaraci masifar ta ta gama.

Da dare misalin ƙarfe Sha ɗaya,  lokacin ɗakina cike ya ke da ƴan kallo. Kama daga kan ƙannen sa zuwa yaran gida da abokanan su da suke gayyatowa, duk sun cika ɗakin har sun fara yagamin ledar tsakar ɗakina saboda yadda basa barin na huta.

Ina kwance kan gado na lullu'be da hijabina, dan haka nake gudun kar na yi barci in sun tafi sai na kulle ƙofa.
Sai naji kamar ƙauri-ƙauri na tashi kaɗan-kaɗan.
 Cikin barcin daya fara fysgata na tashi na zauna, saboda yau wani irin barci na keji da wuri naso kwantawa, sai ga Nepa sun kawo wuta, shine fa suka zo suka cika min ɗaki.

Cikin faɗa nace "Waya sa abu me ƙauri?."
Sai lokacin shamsu ke cewa "Ni ma ina ɗan jin ƙauri-ƙauri fa tun ɗazu." Ya ƙarasa faɗar cikin rashin bawa maganar muhimmanci.

Cikin sauri na tashi na sauka a gadon, na nufi wajen socket cikin ikon Allah sai naga ashe dutsen guga ne aka jona ajiki aka dire shi a kan ledar tsakar ɗakin, da sauri na sa hannu na zare shi nayi cilli da shi.
Har ya cinye ledar wajen ya yi jajawur.

Cikin faɗa nace "Waye a cikin ku ya jona min dutsen guga?." Nan fa aka rasa wanda ya yi, sai kallon kallo suke suna kallona.

Ni mamakin abin da ya kawo dutsen wajen ma nake, dan acan bayan Tibi na aje. Amma aka samu me jin maganar da ya janyo shi.

Ganin an rasa wanda ya yi kowa yace bashi bane, haushin hakan yasa na  kashe kallon nace "Kowa ya tafi yaje ya kwanta babu wanda zai min wani kallo tunda abin ya zama haka."

Haka suka tashi ɗaya bayan ɗaya suna fita. Shamsu cikin jin haushi ya kalleni yayi tsaki ya fita.

Gyara wajen nayi, na ɗauki buta nayi banɗaki dan inyi fitsari.
Ina dawowa kiran Ahmad na shigowa wayata, garin saurin in ɗauki wayar ya hana in tuna da rufe ƙofata kwata-kwata.

Haka muka shiga fira dashi cikin nishaɗi, mun ɗauki dogon lokaci nuna wayar har sai da na fara jin barci, yace na kwanta na huta zai kira da safe.

 Haka na ja bargo na kwanta, tare da yin Addu'o'i na na shafa.

Can cikin barci na ji kamar numfashin mutum a setin fuskata, ana kuma ƙoƙarin janye bargon dana lullu'ba da shi.
A firgice na tashi  zan fasa ihu akayi saurin sa hannu aka 
Rufe min baki.

*_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_*