06
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
*06*
Cikin kuka mai tsanani da shessheƙa Ummu ta sanar ma da Baɗɗo abin da ke faruwa. Lamarin da ya girgiza duniyar Baɗɗo kafin Ummu ta gama ba ta labarin halin da ta ke ciki hawaye sun gama jiƙa ma Baɗɗo gaban doguwar rigar atamfar dake jikinta.
Tana kuka Ummu na kuka suka haɗu suka rumgume juna suna ta kuka a tare, ita Ummu kukan halin da ta tsinci kanta a ciki take yi da tausayin kanta sannan tana kukan takaici na har a yanzu tana yi ma Habib uziri, har yanzu tana tunanin cewa zai dawo gare ta, har a lokacin tana tunanin wasa yake yi yana son ta sannan kuma yana son haɗa zuru'a da ita. Ga gaskiya ƙiri-ƙiri amma soyayyar Habib ta rufe mata ido daga ganin wannan gaskiyn.
Baɗɗo kuma kukan tausayin Ummu take yi. Tausayi mai yawa ganin irin halin da take ciki, gani ta ke yi kamar a mafarki ba domin Ummu ce da kanta ta e faɗa mata wannan labarin ba sai ta ƙarya ta ko ma waye, Habib ne fa? Ba ta taɓa tunanin zai iya aikata haka ba, ba ta taɓa tunanin Habib jahili ba ne mara ilimi sai da Ummu ke ba ta labarin shi.
"Ya zan yi? Na rasa yadda zan yi Baɗɗo gani na ke yi kamar a mafarki, gani na ke yi kamar ba Habib ba ne."
Ummu Ta sake faɗa tana gunjin kuka kanta a saman cinyar Baɗɗo ya yin da ita kuma take shafa kitson da ke kanta alamun lallashi amma ita ma kukan take yi, hawaye sun kasa tsaya mata saboda tausayin halin da Ummu take ciki? Lalle ta ƙara sarewa da lamarin mazan wannan zamanin masu sauya launi a duk lokacin da suka ga dama, za su kuma iya juya rayuwar wanda ya yarda da su daga sama zuwa ƙasa.
"Ya ce ba ya sona sannan ba ya son haɗa zuru'a da ni. Ƙarya yake yi ko? Ke ma ai kin shaida irin son da ya ke yi mini ko Baɗɗo?
Ta sake faɗa cikin kuka tana mai riƙo hannayen Baɗdo a cikin nata. Baɗɗo ta kalli Ummu kafin ta share hawayenta duk da ta fahimci Ummu na son Habib ba za ta fasa faɗa mata gaskiyan da soyayyarsa ta rufe mata idon da ta kasa fahimtar manufarsa ba.
"Ummu-Salma ta so nan ki saurare ni ki ji."
Ta faɗa lokaci ɗaya tana taimaka mata ta tashi zaune suna fuskantar juna hannayenta Baɗɗo ta riƙe duka biyun kafin ta sake kiran sunan ta.
"Ummu-Salma."
Ta amsa mata cikin shaƙewar murya saboda kuka.
"Ki kalli gaskiyan dake gaban ki. Da gaske ne duk abin da Habib ya faɗa, domin wanda ke son ka shi ke ƙaunar haɗa zuru'a da kai, kin ce ya faɗa miki da bakin shi sannan ya yi ƙokarin aikata hakan a aikace, kin ga kenan zaman ki tare da shi ma hatsari ne, tun da ya sha alwashi zai iya miki lahani domin ya ga ya cimma burin shi."
Ta ƙarishe faɗa cikin ƙura ma Ummu ido tana so ta ga yadda ta ƙarɓi mganar, tun da ta ce mata tana cikin halin wannan laulayin amma bai damu da ita ba, shi dai burin sa ta zubar da cikin jikinta da kuma yadda ta faɗa mata matakan da ya bi domin ganin ya cimma manufarsa ta tsoraci Habib da lamarinsa ta kuma tabbatar da yadda yake son cimma burinsa zai iya komai in ta ce komai tana nufin komai domin ya ga cikin jikin Ummu ya fita ko da ita za ta shiga haɗari ne.
"Ya zan yi.! Ina son cikina Baɗɗo sannan ina son Habib."
Baɗɗo ta taɗe tana kallon ta kafin ta ce" Ni ma ban ba ki goyon bayan ki zubar da cikin nan ba domin ba ki sani ba ko shi ne kaɗai ƙwan ki a duniya ba. Shi ma jahilci ne da rashin tunani sannan da manufarsa ta auran ki, mganar kina son shi duk ki cire shi Ummu tunda da bakin ki kika faɗa mini ya ce shi bai taɓa son ki ba, sannan bai aure ki domin haihuwa ba."
"Habib ne fa Baɗɗo. Habib na sona ke ma kin sani?
Ummu ta katse ta cikin kuka hawaye sun kece mata da ƙarfi kuma tana yin kukan mai fidda sauti. Baɗɗo ta yi mata uziri domin ko ita tantaman Habib ta ke yi, in ta yi nazari duba da tun daga lokacin da suka haɗu da Ummu da irin soyayya da ƙauna da tattali da ya nuna mata suma saboda ita duk ya ƙaunace su, ita kanta ba domin Ummu ce da kanta ta ga zahirin Habib ba za ta iya ƙaryata wannan labarin, Ummu na cikin damuwa ta kasa gasgasta Habib ne zai yi mata haka? Tunani ta ke yi kamar ba zai iya nuna haka ba saboda ya gurɓata rayuwarta cikin so da ƙaunarsa tare da kuma Aminta da shi.
"Mun sani a baya yana son ki ayadda ya nuna mana a aikace Ummu. Yanzu kuma ya fito da zahirin manufarsa a kan ki."
Baɗɗo ta sake faɗa tana jijjiga hannayen Ummu dake cikin na ta.
"To ya san ba ya sona me ya sa ya zo ya nuna mini so da ƙauna har ya aure ni?
"To wannan kuma manufarsa ce tun da bai faɗa ba, ba za mu iya yanke masa hukunci ba. Amma duk namijin da ya ce ya aure ka ba domin yana son ka ba sannan ya nuna ba zai iya haɗa zuru'a da kai ba to dalili biyu ne, na farko ko ya yi auran fansa dake domin rama wani abu da kika yi masa na biyu kuma ko ya yi auren sha'awa da ke Ummu."
Ummu ta ƙura ma Baɗɗo ido tana mai tsiyayan hawaye. Ta fi amin ta da auran sha'awan da Baɗɗo ta ce in ta yi duba da yadda Habib ya tsara zamantakewar su ta aure, yadda ya mai da abin cin tuwo ba dare ba rana ko ba ta da lafiya bai damu ba sai ya aikata abin da yake so da ita.
"Ni na fi tunanin auren sha'awa ya yi dake Ummu."
Baɗɗo ta faɗa hawaye na sake kece mata Ummu ma ta sake fashewa da kuka suka sake curewa waje ɗaya suna kuka kamar wasu ƙananun yara. Baɗɗo ce ta fara haƙura da kukan ta koma tana mai lallashin Ummu da kalaman ban haƙuri da cewa ta yi hakuri Allah na sama kuma yana sane da ita zai saka mata.
"Ya zan yi Baɗɗo? Zuciyata zafi take yi ji na ke yi kamar na rasa komai a duniya"
Ummu ta faɗa muryanta ma ba ta fita saboda dishewar da ta yi.
Baɗɗo ta sake share hawayen ta kafin ta ce" Kina da yadda za ki yi ko Ummu, kuma ke ce kike da kowa. Wannan mganar ba shuru za ki yi ba dole ne su Baffa sun san abin da ke faruwa"
Da sauri Ummu ta waro jajayen idanuwanta tana kallon Baɗɗo jin ta ambaci su Baffa in mgana ta kai wajen su Baffa ai shike nan kuma.
"E dole su sani saboda mgana ce da ta wuce tsakanin ku. Neman fa cikar burin sa ya ke yi saboda haka zai iya yin komai saboda haka. A dalilin haka ma zai iya yi miki illa Ummu."
Kai Ummu ta ke girgizawa lokaci ɗaya tana faɗin" Habib ba zai iya cutar da ni ba. Ba zai iya ba."
Baɗɗo ta yi kasaƙe tana kallon ta kafin ta ce" Nima na yi tunanin haka a baya. Amma yanzu kam ban yarda da shi ba. Ke da kan ki kika ce ya saka miki mganin da zai lalata cikin jikin ki har sau biyu a lemu bai yi nasara ba, na ƙarshen ma kin ce da karfin tsiya ya so ya yi miki ɗure, kina da tabbacin maganin ba zai yi miki lahani ba ke a karan kanki bayan cikin dake jikin ki? Ko kina da tabbacin ke ɗin za ki tsira?
Sai jikin Ummu ya yi sanyi ta koma ta yi lakwas tana tsiyayan hawaye.
"To kin gani dole iyaye su shiga ciki Sisna, in sha Allahu komai zai daidai ta."
Ta faɗa tana mai share mata hawaye da hannayenta duka biyu.
"Ina tsoro, ina tsoron kar su Baffa su ji wannan abun su raba ni da Habib."
Ummu ta sake faɗa da har sai da Baɗdo ta ji kamar ta sake fashewa da kuka saboda tausayin Ummu, wata kila ya yi kusa zuciyarta ta aminta da cewa Habib ba masoyin ƙwarai ba ne a gare ta, ba yanzu za ta tantance girman yaudaran da ya yi mata ba wataƙila sai anan gaba.
"Ba raba ki da shi za su yi ba. A matsayin su na iyaye za su shiga su gyara ta in da aka samu ɓaraka ne"
Ummu ta jinjina kai kafin ta ce" Ba yanzu zan sanar da su ba Baɗɗo "
"To sai yaushe?
Ta tambaaye ta cikin mamaki."
"Mu sake ba ma Habib lokaci. Wataƙila wasa ya ke yi, wataƙila yana gwada ni ne ya gani."
Kallon ba ki da hankali Baɗɗo ke yi mata ta ma kasa mgana saboda mamaki, mutumin da a cikin idanuwan ki ya ce ba ya son ki ba domin ki haihu ya aure ki ba, sannan ya yi ƙokarin lalata cikin jikin ki da karfin tsiya amma har a yanzu kare shi Ummu ke yi! Tana tunanin wai wasa Habib ya ke yi?
"Kin ga kar mu yi gaggawan sanar ma gida, in ya zo muka daidaita fa ?
Baɗɗo ta kasa mgana saboda ta rasa ma abin cewa saboda tausayin Ummu da mamakin ta.
"Kin ji? Mu sake ba shi lokaci na yi miki alƙawarin in bai sauya ba da kaina zan je gida na faɗa ma Baffa duk abin da ke faruwa."
Baɗɗo ba ta da cewa tun da Ummu na ta mata magiyan kar ta faɗa ma kowa, ita da kanta za ta je ta faɗa ma su Baffa in har Habib bai sauka daga kan gudirin shi ba.
"Na ji ba zan faɗa ma kowa ba. Sai dai ina tunanin yadda za ki cigaba da rayuwa a haka da shi, ina tsoron kar ya sake yunƙurin cimma burin sa ya yi miki lahani wata rana."
"Allah ba zai ba shi sa'a ba"
Tunda ta ce Allah sai jikin Baɗɗo ya yi sanyi amma jikinta da zuciyarta suna cike da tausayin Ummu ne, ganin yadda ta koma duk ta lalace sannan daga ganin ta, tana bukatar ma ganin likita. Ummu ta faɗa mata magungunar da aka rubuta mata a asibiti Habib bai siya ba sannan ga yanayin da take kwana tana ta shi a ciki.
"Gaskiya ya kama ta mu je asibiti."
Baɗɗo ta faɗa lokaci ɗaya tana miƙewa. Ummu ta kalle ta a sanyaye kafin ta ce" Nima ina son na je asibiti ba ni da lafiya sosai."
"Yanzu za ki tashi mu je."
Ummu ta sake kallonta kafin ta ce" Habib bai sani ba."
Baɗɗo ta ji kamar ta rufe Ummu da duka saboda baƙin ciki da takaici.
"Kina ganin in na fita bai sani ba, ba matsala.?
Ta sake tambayan ta a sanyaye.
Sai da Baɗɗo ta ya fa mayafin ta sannan ta kalli Ummu tana faɗin" Yana gidan kike fama da ciwo amma bai damu da ke ba, kin ga kenan in kin fita domin neman lafiyarki hakan ba matsala ba ne."
Ummu ta girgiza kai kafin ta ce" A'a bari dai na kira shi na sanar da shi."
Kasa ma mgana Baɗɗo ta yi sai ma ta koma ta zauna tana kallo Ummu ta tashi tana dafe dafen bango ta koma bedroom ɗin ta sai ga shi ta fito da wayarta a hannu tana ta kiran wayar Habib amma sai a saka kiran na ta a forwording.
"Ba na samun shi."
Ta faɗa a sanyaye
Baɗɗo ta yi kamar ba ta ji ta ba haushi duk ya ishe ta.
"Ya zan yi yanzu?
"Ki zauna sai lokacin da kika same shi a waya, in ya ce ma kar ki je ki zauna ki mutu"
Ta faɗa cikin haushi jin haka
Ya sa jikin Ummu ya sake yin sanyi ta zauna kusa da Baɗɗo tana mai marairaicewa.
"Ya zan yi to? Na rasa tunanin da zan yi?
Ta faɗa hawaye suna taruwa a ƙwarmin idanuwanta.
"Ki ta shi na raka ki asibiti a duba lafiyarki Ummu-Salma."
Baɗɗo ta faɗa tana mai sake miƙewa tsaye wannan karon har tana rataya jakar da ta zo da ita ba yadda Ummu ta iya haka ta ɗauko hijabi ta da ƙaramar jakarta da Atm ɗin ta ke ciki ba ta da kuɗi a hannunta, kulle ɗakin suka yi suka fita zuwa bakin titi sannan suka hau Keke Napep zuwa asibitin da Ummu ta ke da fayel, boshon clinic da taimakon Baɗɗo dake riƙe da ita. Suna zuwa suka ga likita da ya ke ta je da katin ta, likitan na ta faɗa cewa babu wadattacen ruwa a jikinta sannan akwai maleria mai zafi a tare da ita.
Riƙe ta suka yi bayan sun saka mata drip sun yi mata allurai har da na barci ta samu barci sannan likita ya ce Ummu ba ta cin abinci sannan ga jinin ta ya ɗan hau shi ya sa za su rike ta zuwa yamma su gani. Baɗɗo ce ta zauna da ita a asibiti nan tun kafin azahar sai gabda mangariba kuma ba ta kira kowa ba, Ummin ikki dai ta kira ta ganin duhu ya shiga ba ta dawo ba sai ta ce mata ta samu Ummu na fama da zazzaɓi ta ɗan taya ta ayyuka ne amma in dare ya yi sosai ba ta dawo ba to za ta kwana tare da ita, ta yi ma Ummin ƙaryan cewa Habib ba ya nan ya yi tafiya.
An sallami Ummu tare da magunguna da dokokin likita bayan ta sha leda uku na ruwa sai kuma ta ji daɗin jikinta ta daina jin jirin nan da ciwon kai, ya ce ta samu hutu sosai ma'ana sun ba ta bedrest sannan ta riƙa cin abincin domin inganta jaririn dake cikin ta. Ba su suka shigo gida ba sai ana kiran sallar isha'i kuma har a lokacin Habib bai dawo ba, Ummu wanka ta yi ta shiga rama salollin da ke kanta ita kuma Baɗɗo bayan ta yi sallar isha'i ta zage tana gyara gidan duk ya yi ƙura tun da Ummu tana ta kanta ba ta gyaran gida ba, har fashasshen kwalban da ke saman dinning Baɗɗo ce ta kwashe shi ta gyara wajen lemun da Habib ya saka ma mganin ita ta kwarara shi a tiolet ta saka kwalayen exotic ɗin a dusbin
sannan ta yi ma Ummu faten wake ta so ta saka allayahu amma babu, kuma in da ake siyarwa sai kasuwa.
An ci sa'a kuma Ummu ta ci faten waken bai dawo mata ba sai ta ɗora da ruwan lipton mai zafi ya samu ya warware mata ciki sannan Baɗɗo ta ba ta magungunar ta tasha, ta ji daɗi da Baɗɗon ta ce mata sai gobe da safe za ta tafi in ta ga jikin na ta da sauƙi. Suna zaune a falo Ummu na kwance kanta na saman cinyar Baɗɗo suna kallo gefe ɗaya kuma suna hira sama sama sai aka kira Baɗɗo a waya wata class mate ɗin ta ce, ganin suna mgana ne ya sa Ummu ta shiga tunani mai zurfi tsoron ta in mganar nan ta je kunnen Baffa har yayyenta suka ji labari sai Habib ya gane ba shi da wayau sannan tana da tabbacin sai sun raba auran nan da nan a cikin su akwai waɗanda ba su so auren nata ba, ba wai don ba su son Habib ba, a cewar su karatu ya kamata ta cigaba da yi ba aure ba ita kuma ba saboda haɗuwarta da Habib ba. Tun tana ƙarama da ta fahimci ba ta da ƙwaƙwalwar karatu ta ce ita daga sakandiri ba ta son ta cigaba da karatu.
A lokacin ba tasa aure a lissafin ta ba domin ba ta ɗauka za ta haɗu da Habib a gabar ba, shi ya sa son auren ma baya cikin lissafin ta, ba ta taɓa tunanin za ta haɗu da Habib a lokacin ba ballanta har aure ya shiga tsakanin su ba. Abu ne da ya faru lokaci kaɗan haɗuwarsu da auren su wattani biyar ne a wancan lokacin Hamma Kabiru ya yi ta faɗa da cewa an yi gaggawa ya kamata a ɗan sake jira, shi kuma Baffa ya ce tunda dai Ummu tana so kuma shima Habib ɗin ya shirya bai ga amfanin ɓata lokaci ba. Tsoron ta ɗaya in suka ji mganar ba ta san yadda lamarin zai ƙare ba, wataƙila ya yi lalacewar da kafin lamarin ya gyaru za a ɗau lokaci.
Ta yi nisa cikin tunaninta ba ta san shigowar Habib ba, sai da ta ji ƙamshin turaran shi sannan ta farga, tana ɗagowa suka haɗa ido huɗu da shi yana tsaye yana kallon su. Da sauri ta miƙe zaune tana kallon shi, jikinta har rawa ya ke yi saboda ganin Habib ba ta san ta yi kewarsa ba sai da ta gan shi, ta ji wani irin sanyi a cikin ranta.
"Sannu da zuwa Noori."
Ta faɗa lokacin da take miƙewa tsaye. Baɗɗo na zaune tana ganin ikon Allah. Sai da ta ga Habib sannan ta san a ɗazu ba haushin shi take ji ba, yanzu ne ta ke jin kamar ta rufe shi da duka da ta gan shi. Barin ma yadda yake bin Ummu da wani kallon banza ita ko baiwar Allah hannu ta miƙa za ta karɓi jakar hannunsa da sauri ya kauce ya kuma raɓa ta zai wuce ciki Baɗɗo ta ga ba za ta iya jurewa ta miƙe a fusace.
"Habib."
Ta kira sunan shi a kausashe, sai ya tsaya kafin ya juyo fuskar nan kamar bai taɓa dariya ba. Yadda ya yi ma kamar bai taɓa ganin Baɗɗo ba.
"Ina son mgana da kai."
Tana kallon cikin idanuwansa ta faɗi haka.
"SisNa kar ki ce masa komai don Allah."
Ummu ta faɗa tana mai rike hannun Baɗɗo cikin magiya.
"Bar ta ta faɗi abin da ke bakin ta, in tana tunanin za ta iya sauya tunanina ne akan mganar da za ta yi Bismillah."
Ya ba ta amsa har yana wani ɗaga hannu, Baɗɗo ta kalle shi cikin wani yanayi shima kai tsayen yake kallon ta.
"Na san ta faɗa miki abin da ke faruwa, in har ke yar'uwata ce da gaske gwara ki ba ta shawaran ta bi umarnina in tana so ta tsira da sauran abin da ya rage mata."
Ya faɗa cikin gadara sannan yana nuna Ummu kamar ya ga abin ƙyama.
"Domin ba ta da wani sauran wani abin da ya rage a tsakanin mu yanzu."
Ba Ummu ba, hatta Baɗɗo sai da ta ji ta muzanta idanuwanta suka kawo ruwa sai ta yi saurin shanyewa.
"Habib Allah ya fika."
Haka kawai Baɗɗo ta faɗa ta ja hannun Ummu suka raɓa ta gefen shi, Ummu tirjiya take yi amma Baɗɗo ba ta sake ta ba sai da suka shiga cikin bedroom ɗinta ta kuma ma yar da kofa ta rufe, suna jiyo dariyan Habib na tura haushi.
"Ki bar ni na je na ba shi haƙuri."
Ummu ta faɗa tana nufar ƙofar Bedroom ɗin da ƙarfi Baɗɗo ta ce" Wallahi in kika fita daga ɗaki nan, sai na kira Baffa na faɗa masa duk abin da ke faruwa."
Kalaman Baɗɗo suka sarƙe ta, ta kasa gaba ballanta baya, kuma yadda Baɗɗo ta ɗau alwashi ba za ta fasa abin da ta ce ba shi ya sa ta koma kawai ta kwanta a saman gado ta fashe da kuka.
"Ina son Habib. Ina so na bashi hakuri mu dawo kamar baya."
Dole Baɗɗo ta sauko ta fara lallashin Ummu domin ta fahimci tana son Habib kuma tana son cikin ta, ba ta da wata mafita ne a yanzu. Sun daɗe ba su yi barci ba Baɗdo na sake ba ta baki sai dai ta ba ta tabbaacin in har Habib bai daina yunƙurin zubar mata da ciki ba to ta koma gida kar ta sake zama yana wulakanta ta alhalin tana da gata.
Ita ko Ummu a zuciyarta addu'a take yi Allah ya sassauta zuciyar Habib in ya rabu da ita ina za ta saka kanta tana ji gwara su cigaba da zama a haka ta tsira da shi, sannan ta tsira da cikin jikinta da auran ta gabaɗaya tunani take yi zuwa nan gaba kaɗan Habib zai yi nadama zai dawo ya ba ta haƙuri su gyara rayuwan auren su, in shi ba ya son ta ita tana son shi sannan za ta iya jure komai saboda ta tsira da auran shi, shi ya sa ba ta kaunar mganar ta je kunnen Baffa, in ya ji kamar duka yayyenta sun ji, in kuma akwai waɗanda za su yi shuru to akwai fusatattu irin su Hamma Kabiru da Hamma Abdulrahaman da ba su da wasa ko kaɗan tana da tabbacin ko za ta mutu sai sun raba auren ta da Habib, ita kuma tana son shi tana fatan ta rayu da shi har karshen rayuwarta.
Washegari ma Baɗɗo ta yi ma Ummu abin da za ta karya kunin gyaɗa ta dama mata sai ta yi musu fanke. Habib da Baɗɗo sun haɗu lokacin da ta fito daga kitchen shi kuma ya yi shirin fita zai bar gida kowa ya yi kamar bai ga kowa ba
Baɗɗo ta kitchen ta ke leƙen Habib har ya bar falon lalle Duniya juyi juyi na gaba ya koma baya yau wai ita ce Habib zai gani ya yi kamar bai gan ta ba, ita fa mamaki ta ke yi yadda lamarin nan ya sauya. A baya ganin irin dacen da Ummu ta yi sai ta ke mafarkin ta samu miji kamar sa, amma yanzu ta ji auren da namijin ma gabaɗaya sun fita kanta, ba su da tabbas ba su da garanti ka aminta da su su ha'in ce ka, ka ba su Amana su ci, sun san salon yaudara kala kala, su kuma ga su ba tukwane ba ne ballanta ka fara ƙwanƙwasa wa kafin ka ɗauka, ba ka isa ka gane manufar su ba sai ka shiga da ga ciki, tana aiki tana hawaye Habib ya cutar da zuciyar Ummu, sannan ya cutar da kuruciyarta suma na tare da ita ya cutar da zukatan su. Damuwarta ɗaya tunanin halin da Ummu za ta shiga matuƙar Habib ya sake ta ko in iyaye suka shiga mganar ba a samu masalaha ba, tana tsoron kar damuwa da zafin zuciya su yi ma Ummu illa. Sai da ta gama shan kukanta ta share hawayenta saboda kar Ummu ta fahimci ta yi kuka itama ta fara ta samu ta yi shuru ta daina kukan da ta kwana tana yi.
Su na gama karyawa Baɗɗo ta wanke abubuwan da suka ɓata ta ɗan gyara mata gidan ta yi wanka ta yi shirin tafiya Ummu ta fara hawaye ita mai idanuwan kuka da cewa Baɗɗo ta ƙara kwana.
"Aa ba zan sa ke kwana ba, kar mijin ki ya zo ya sake ganina, karon mu ba zai yi daɗi ba."
Ummu ta na ji tana gani Baɗɗo ta yi mata sallama ta tafi ta bar ta, bayan ta jadadda mata ta kula da kanta ta riƙa samun hutu domin kiyaye dokar likita. Sannan in ta ga wata matsala kar ta zauna ta kira gida in tahowar ba zai yuyu ba Ummu ta amsa da to za ta kiyaye. Baɗɗo na tafiya ta koma ta kwanta tana ta kuka, kukan da ya fara zame mata jiki a acikin kwanaki nan.
Bayan tafiyar Baɗɗo maimakon lamarin Habib ya gyaru sai ma ya sake lalacewa. Ba ya ma nuna cewa akwai wata hallita a gidan, in sau goma Ummu za ta yi masa mgana ba zai amsa ta ba, a cewarsa in ta ga ya dawo yana kula ta sai in har ta bi umarnin sa, umarnin da Ummu ta gwammace su zauna a haka da ta amince da buƙatar sa na zubar da cikin, cikin da duk duniya yanzu ba ta da wanda take so sama da shi. Ba ta san dare nawa ta ɓata tana kuka ba, ba ta san sau nawa ta duka a gaban Habib tana kuka akan cewa ya yi hakuri ya yafe mata. Amma bai kalle ta ba yana nan akan bakan sa, ko ta zubar da ciki ko kuma su cigaba da zama a haka kafin ya yanke hukunci a kanta.
Baya cin abincin ta, ba ya neman ta bai damu da ita ba ko za ta mutu bai damu ba, ba shi da asara sai ya raba dare yake dawowa sannan ya zauna a falo ya yi ta waya cikin harshen turanci. Ummu ta yi kuka, kuka har ya zame mata jiki saboda halin da ta ke ciki. Wato ga ta jahila wacce ba ta jin turanci shi ya sa in zai yi waya sai ya sauya yare, ba kuma wai ba ta jin turancin ba ne, ta na ji daidai misali na iya karatun ta, mayarwan ne ke yi mata wahala ko in an faɗi wasu manyan kalamai a cikin turanci sai ta daburce shi kuma Habib ya iya turanci na fitina kamar wanda aka haifa a ƙasar waje.
Har kuma gobe ba ta ji Fargar jaji ya kamata akan rashin cigaba da karatun ta ba, ra'ayin ta ne kuma har yau ba ta ji ta sauka akan wannan ra'ayin ba.
Kullum sai Baɗɗo ta kira ta a waya domin ta ji lafiyan ta. Har Ummin ikki sun yi mgana ta yi mata sannu tun da Baɗɗo ta faɗa mata ba ta jin daɗi. Baffa ma suna waya amma ba su fahimci wani abu ba, tunda ba ta ba da damar haka ba.
**
Zuwan Baɗɗo da kwana goma Shamsiya ta zo, kwatsam kamar daga sama domin sun daɗe ba su yi mgana da Ummu ba. Sannan ba ta kira ta ba shi ya sa ba ta san da zuwan ta ba sai dai ta gan ta, ashe sun samu hutun makaranta ta dawo gida shekaranjiya ta yi kewarta ne shi yasa ta zo domin ta gan ta.
"Allah sarki Bestie ya makarantan?
Ummu ta faɗa tana mai zama a gefen Shamsiya wacce ke zaune a saman kujera mai zaman mutum uku bayan ta kawo mata ruwa.
Shamsiya Black beauty ce, sai dai siririya ce sosai da ba ta da wani tsarin jikin mata, a shekarun ta ba za ta wuce sa'ar Ummu Salma ba.
"Alhamdulillah Bestie, mun gama mun dawo gida hutu muna komawa kuma za mu shiga aji uku."
Shamsiya ta faɗa cikin mirmishi, Ummu ta sake rumgumeta tana yi mata fatan alheri.
Shamsiya sai kallon Ummu take yi cikin alamun tambaya yadda ta ga ta koma amma ba ta yi mgana ba.
"Ina Habib? Ko yana wajen aiki ne?
Da kai Ummu ta amsa mata, ba tare da ta yi mgana ba.
Sun fara hira Shamsiya dai ta ga ramar Ummu ta yi yawa sannan lokaci bayan lokaci tana ta shi ta shiga tiolet ta zubda yawu.
"Bestie me ke damun ki ne? Kin rame!
Tana so ta danne yanayin ta amma ta kasa domin damuwar nata ya fara bayyana a saman fuskarta.
"Ko kina da ciki ne?
Shamsiya ta tambaya lokaci ɗaya tana washe baki.
Wannan karon ma kai Ummu ta sake ɗaga mata alamun haka ne, da sauri Shamsiya ta rumgume ta cikin tsananin farincikin da ya kasa ɓoyuwa daga zuciyarta ya bayyana har a saman fuskarta.
"Congratulations Bestie na. Mun kusa zama iyaye ni da Baɗɗo."
Ba ta sani ba Ummu kuka take yi, sai da ta ji tana shashesheƙa sannan ta ɗago ta sai ta samu fuskarta caɓe-caɓe da hawaye.
"Subhanallah kuka kuma Bestie? Me ya faru?
Shamsiya ta faɗa cikin harshen fillanci.
Kasa mgana Ummu ta yi, ban da kuka ba abin da take yi kuka kuma sosai har da sauti. Hankalin Shamsiya ya tashi ta ruɗe gabaɗaya tana tambayan Ummu abin da ke faruwa. Sai da ta gama shan kukan ta sannan ta iya labarta mata abin da ya faruwa da wanda ke kan faruwa.
Shamsiya ta yi tsam kafin ta ce" Topha, innalillahi shi Habib ɗin ne duk ya aikata miki haka Bestie?
Ummu ta jinjina kai kafin ta ce'" Na yi duk abin da zan iya yi na gaza bestie. Ban san sau nawa na duka na ba ma Habib haƙuri ba amma ya ce yana nan akan mganarsa. In ina son mu cigaba da zama kamar baya har sai in na amince na zubar da cikin jikina."
Shamsiya ta kalle ta kafin ta ce" To ki bi umarninsa mana Bestie"
Cikin mamaki Ummu ta kalle ta kafin ta amsa cikin mamaki.
"Na zubar fa kika ce?
"Yes, ai ba matsala ba ce. Wata kila ba yanzu ya shirya ku haihu ba ki bi umarninsa ki zubar Bestie nan gaba za ki samu wani a lokacin da shi ya shirya ma hakan"
Sai Ummu ta yi shuru tana mai kallon Shamsiya sai take ɗan hango ƙamshin gaskiya a kalamanta ganin haka ya sa ta riƙo hannayen Ummu cikin na ta tana cigaba da faɗin.
"Kuma ina tunanin duk mganar da ya faɗa miki na ran shi so ko wani abu cikin fushi ne da haushin ƙin bin umarnin sa ne, amma ina da tabbacin Habib na son ki , ke ma kuma kin san haka"
Kalaman Shamsiya suna shigar ta sai ta ji ta aminta da mganarta amna kuma tana son cikin ta ba ta son rabuwa da shi.
"To amma Bestie ina son cikina fa."
"Allah zai kawo miki wani, kin manta a baya ma kin samu ya zube, yanzu kuma ga shi Allah ya sake baki wani ba? To haka anan gaba zai sake baki wani in sha Allahu.'"
Lamarin ba mai sauƙi ba ne, tana son auran ta, tana son ta yi komai saboda tsira da auren ta amma ba ta jin za ta iya zubar da wannan cikin da ta faro dukkan wata gwagwarmaya saboda shi ba.
"Da na ce zan bi shawaran Baɗɗo ne na je gida na sanar ma Baffa watakila in ya shiga mganar komai zai yi daidai ba sai na zubar da cikin ba Bestie."
Shamsiya ta yi shuru kafin ta ce" Kina da tabbacin in mganar ta kai wajen su Baffa komai zai yi daidai? Ni fa sai na ke ganin sako su a ciki zai iya ɓata komai, ki sake ɓata ran Habib har ya yanke miki hukunci cikin fushi."
Ummu ta yi zuru tana kallon Shamsiya kamar wata doluwa cikin bugawar zuciya ta ce" Wani hukunci zai yanke a kaina?
"Hukunci rabuwa da ke mana, kin ga ya cuce ki ya cutar da iyayenki ya sa kin zama ƙaramar bazawara."
Gaban Ummu ya amsa! Tana son Habib ba za ta iya juran rasa shi ba.
"Ki tsira da auran ki Ummu-Salma, kuma ni ban ga laifin Habib ba, haka na faruwa ko wata da muke ɗaki ɗaya a makaranta mijinta ya ce sai sun shekara biyar da aure za ta haihu kuma ta amince. So normal ne kawai fahimta ce tsakanin ma'aurata, ke kan ki Ummu nawa kike? Kina da sauran damarma ki masu tarin yawa ma anan gaba ni ban ga laifin Habib ba, ra'ayin shi ne kuma girmama ra'ayin juna a zamantakewa kamar dole ne."
Ummu ta jinjina kai cikin sanyin jiki kafin ta ce'" Ina son aurena sannan ina son cikina Bestie."
"To sai dai ki zaɓi ɗaya ko auran ki, ko cikin."
Ummu ta kasa zaɓan wanda ya fi sauƙi a ciki, duk tana son ta tsira da su da auran da cikin jikinta.
Shamsiya kuma ta yi ta nuna mata ba matsala in ta zubar yanzu gaba za ta iya samun wani a lokacin da suka shirya suna da dama, tun da lamarinn nan ya fara faruwa ba ta ji ta samu salama ba sai da ta yi mgana da Shamsiya sannan ta samu jin wani abu ya faɗa daga ƙirjinta.
Shamsiya ba ta tafi ba sai da Ummu ta ba ta tabbacin za ta amince da umarnin Habib. Ita fa Shamsiya ƴar boko ce, sannan renon yan boko su a ganin su hakan ba matsala ba ne bayan tafiyar Shamsiya Ummu ta yi ta tufka tana warwara, shawaran Shamsiya ta fi zama mata sosai a cikin zuciyarta duk da tana son cikin ta amma kuma tafi son Habib a kan cikin, kamar yadda Shamsiya ta faɗa ne in tana son Habib to ta bi umarnin sa sai su zauna lafiya. Za ta amince da a zubar da cikin amma sai ya ba ta tabbacin zuwa yaushe yake son ta haihu ? Allah na gani tana son haihuwa har mafarkin tana shayar da jariri take yi. In har ba zai wuce shekara biyu ba to za ta iya haƙuri a zubar da wannan amma in dai ya gota ba za ta iya haƙuri ba.
***
A RANAR.
Habib Ya fito daga wajen aiki kenan misalin 4:40pm, ya tsaya tare da wani abokin sa suna magana. Ya ji saƙo ya faɗo wayarsa amma saboda suna mgana bai duba a lokacin ba sai da suka yi sallama kowa ya nufi in da ya yi parking ɗin motar shi ya shiga.
Shi dai yana shiga cikin motar na shi jakar hannun sa ya sauke a gefen kujeran mai zaman banza. Sannan ya fiddo wayarsa dake cikin aljihun wandon shi saƙo ne daga M.S kamar yadda ya yi zato tun farko.
"Habib lokaci yana ƙure mana fa, ina jin tsoro, tsoron kar maganar nan ta je kunnen iyayenta daga nan waliyanka su ji labari alalan mu ya yi ruwa, tsarin mu ya lalace ba yadda muka shirya ba. Don Allah ka yi wani abu da gaggawa ba mu da lokaci"
Mirmishin sarari ya yi kafin ya tura mata da amsa.
"Kar ki damu ba abin da suka isa su yi. Ba kuma wanda ya isa ya lalata mana shirin mu."
"In cikin bai zube ba fa?
"Ba wanda ya isa ya sa ni na karɓi abin da na ce bana so. Da gaske bana son ta sannan ba na son haɗa zuru'a da ita, in kuma ta cigaba da taurin kai to zan saka rayuwarta da na iyayenta a uku."
Yana turawa ba jimawa sai ga wani saƙon ya sake shigowa.
"Ka yi komai, in dai ka san ba zai hana shirin mu tafiya ba."
"Zan yi."
Da haka ya ma yar da wayar na shi cikin aljihun wondon shi ya kunna motar ya yi riverse ya bar haraban bankin, yana tafe yana wani tunani matukar Ummu ta cigaba da taurin kai to komai zai ƙare a tsakanin su, ta je can ta riƙe cikin sai ta zame masa uwa da uba. Abin da ya sa ya aureta tuni ya gama samun shi babu kuma sauran wani abu da ya rage a tsakanin su
**
Da wuri Habib ya dawo kamar ya san Ummu ta tsala kwalliya tana jiran dawowan shi, da yake ta ji sauƙi tana samun ƙarfin jiki ya sa har girki ta yi masa ta gyara gidan yana tashin ƙamshi.
Lokacin da ya dawo tana falo tana zaman jiran shi, bai yi mata mgana ba sai ita ce ta ce masa ya tsaya ya saurare ta.
"Na faɗa miki ba wani sauran mgana a tsakanina da ke malama."
Ya faɗa a fusace yana ƙoƙarin shigewa ɗakin da yanzu ya ke rayuwa a ciki.
"Ko da a ce maganar na amincewa da ɓukatar ka ne?
Ta faɗa a sanyaye, ai yana jin haka da sauri ya juyo yana kallon ta.
"Me kika ce?
Ya tambaya yana ɗan rage ɗaure fuskar da ya yi.
"Cewa na yi ko da maganar tawa na cewa na amince zan bi Umarnin ka ne?
Kamar walƙiya sai ga shi a gabanta yana mai sakin jakar hannunsa kafin ta yi wani yunƙuri ya rumgume ta ƙamƙam cikin matsanancin farinciki.
"Haba ko ke fa Baby, sai yanzu na ji na samu natsuwa."
Murna yake yi a zucci da sarari nan da nan ya fara sumbatar ta a ko'ina na fuskar ta, yana mai nuna mata farincikin sa bisa amincewa da ta yi da bukatar shi, zuciyar Ummu ya cika da farinciki ganin yadda Habib ya ke yi mata rawan jiki, ta faɗa masa ta amince da buƙatar sa amma zuwa wani lokaci ya shirya ya zama uba ita kuma ta zama uwa.
"Nan da shekara ɗaya Baby. Lokacin duka mun shirya zamo wa iyaye amma by now mu cigaba da cin lokacin mu."
Ya faɗa yana yi mata mirmishi, wannan mirmishin da shi ya yi amfani ya sace zuciyarta.
Sai ga shi ranar tare suka yi Dinner yana ba ta abinci a baki tana bashi, ganin ta ɗan yi sanyi sanyi ya sa ya ke sake jadadda mata kar ta damu zai kai ta asibiti a bata maganin da cikin zai zuɓe ba tare da an samu wata matsala ba yana faɗa mata cikin ƙarami ne ba za ta fuskanci wata matsala ba.
Duk da Ummu ta amince da buƙatar Habib sai ta ji ta kasa samun natsuwa, a cikin zuciyarta ta kasa samun natsuwa cikin ta kawai take shafawa tana jin wani iri, sai take ganin kamar abin da za ta aikata ba alheri ba ne.
"Ummu-Salma ki sake tunani."
In ta amince aka zubar da cikin tana da garantin cewa Ubangiji zai sake ba ta wata damar! Ko kuma ranar gobe ƙiyama cikin da ta zubar ya tambaye ta a gaban Ubangiji da cewa wani laifi ya aikata mata da ta yi masa haka? Ba ta da amsa a wannan lokacin sai ta ji ta sare son cikin ta ya sake shigan ta, tuni ta ji ta sauya shawara gwara ta ce ma Habib ya yi haƙuri tun da cikin ya shiga ya bari in ta haihu sai su tsayar da haihuwar har zuwa lokacin da ya ke so.
Da wannan tunanin ta tsayar da shawara tana ɗakin ta ne Habib ya je ɗakin sa ya dawo ba jimawa sai ga shi ya shigo da gajeren wando jikinsa ba ko riga tana so ta yi masa mganar amma bai ba ta dama ba haka ya fara naniƙarta da sam ta ji ba ta bukatar hakan amma ta kasa yi masa gaddama. Bai bar ta ba sai da ya samu yar natsuwa sannan ya ɗan dakata a gefenta yana mayar da numfashi.
"Gobe Baby za mu je asibiti, ko kuma kawai na siyo miki mganin ki sha zai fi sauƙi ko?
Ya faɗa yana leƙen fuskarta, sai ta yi shuru ta kasa mgana haka kurum ta ji zuciyarta ta karye.
"Kin yi shuru."
Sai da haɗiye miyau sannan ta ce" Habib na sauya shawara."
Yadda ya miƙe zaune a firgice ne sai da Ummu ta ji tsoro itama ta tashi zaune tana mai rufe jikinta da bargon dake gefen ta.
"Raina mini wayau za ki yi?
Ya faɗa a fusace yana kallon ta.
"Aa wallahi."
"To me hakan ke nufi, mun gama mgana kuma yanzu kina faɗa mini wata maganar banza."
Ya katse ta a fusace yadda ya ta so mata in ta yi wasa zai iya kai mata duka.
"Ina so ne, ka bari sai na haihu."
Ta faɗa hawaye na kece mata kanta na ƙasa domin kauce ma wani mugun kallo da Habib ke jifanta da shi.
"Kin haihu a ina?
A gida na? Ba ki isa ba.'
Ya faɗa a fusace kafin ya diro daga kan gado.
"Sau nawa zan faɗa miki bana son na haihu da ke ne Ummu-Salma, ?
"Ai ka ce zan haihu nan da shekara ɗaya shi ne na ce tunda ina da cikin yanzu ka bari in na haihu daga baya sai na bari sai lokacin da ka shirya sai in sake haihu."
Kafa ya sa ya daki gefen gado cikin ƙaraji ya ce" Ke wata irin daƙiƙiya ce,? Da wani yare zan faɗa miki ki yarda da mgana ta?
Ya faɗa kamar ya kai mata duka, Ummu ta takure waje ɗaya tana mai kuka ƙasa-ƙasa.
"Na faɗa miki ba na son ki, bana son ki me ya sa ƙin ki gane hakan ne?
Ummu ta ɗago tana kallon shi da idanuwanta masu zubar ƙwallah.
"Ko ƙwaƙwalwarki kike so na buɗe na saka miki mganar ne sannan za ki fahimce ni?
Ya gama faɗa yana dafe kansa.
"To ka san haka me ya sa ka aure ni, ka nuna mini so kuma?
Kamar zai dake ta haka ya taso mata da hargagi yana faɗin.
"Ke wai har yanzu ba ki ba ma kan ki wannan amsar ba?
Sai na faɗa miki dalilin da ya sa na aure ki da bakina sannan za ki yarda?
Ya faɗa yana zare mata ido, Ummu ta runtse ido hawaye suka ke ce mata.
"Sabo da ina so na ji daga bakin ka."
Ta ƙarishe faɗa cikin kuka har da shessheƙa.
"Sabo da ba ke na ke so ba, ban kuma aure ki domin ki zo ki haifa mini yara ba."
Sai da ya kalleta sannan ya yi wata dariya kafin ya ce" Kawai ni jikin ki na ke so, auran sha'awa na yi da ke kuma Alhamdulillah na samu biyan buƙatata a wajen ki, ko a haka kasuwa ta watse na ci riba."
Idanuwanta a runtse amma hawaye na ƙwaranya, kukan zucci ta ke yi, da Baɗɗo ta faɗa ta ji zafin mganar ta kuma kasa gasgasta hasaahen ta, sai da Habib ya faɗa sannan ta fahimci yadda komai yake, maganganunsa sun yi zaman da'ira a cikin zuciyarta cikin lokaci kaɗan suka fara yi mata illa, shi ya sa ashe take ta mamakin me ya sa kullum abu ɗaya? Ashe dalilin da ya sa ya aure ta kenan saboda jikin ta, kuma kamar yadda ya faɗa ne ko a haka kasuwa ta tashi shi ke da riba, tunda duk ya gama more wani albarkatun jikinta ya cuci rayuwarta ya lalata mata mata goben ta, tuni ta ji zuciyarta ta yi baƙin ƙirin ɗin da ta ji gwara da ba ta zubar da cikin jikin ta ba, wataƙila da shi ne kaɗai za ta iya tsira a rayuwarta da Habib ya lalata.
Tana jin shi yana ta mganganu ya sake ba ta tabbacin shi bai taɓa son ta ba auran sha'awa ya yi da ita ba auren soyayya ko ta zo ta haifa masa yara ba. Akwai wacce ya yi ma wannan tanadin amma ba ita ba
Daga ƙarshe ya ce ba zai sake ce mata ta bi umarninsa ba amma ta sani sai ta yi nadama daga nan ya bar mata ɗakin har yana banko mata ƙofa.
Yana fita ta saki kukan ta a fili, kuka take yi kamar ranta zai fita, ji ta ke yi kamar zuciyar ta za ta fito waje saboda yanayin da ta ke ciki, mutumin da ta ɗauka a masoyin ta da bayan iyayenta ba ta da kamarsa, mijinta sirrin rayuwarta wanda ta aminta da shi ashe ashe shi a zuciyarsa ba haka ya ɗauke ta ba, yana da manufarsa a kanta. Ta daɗe tana kuka kafin ta iya tashi ta faɗa tiolet ta tsarkake jikinta sannan ta fito ta saka wata doguwar riga, ta shimfiɗa darduma tana salla tana kuka, bayan ta idar da sallar isha'i ba ta san awannin da ta shafe a saman darduma tana kuka ba.
Abu ɗaya ta sani ba ta ji ta tsani Habib ba, sai ma ji ta yi yanzu take son shi, amma dai ta yanke shawaran gobe za ta je gida ta samu Baffa ta faɗa masa halin da ake ciki. Sai dai za ta za ta roƙe shi ya kira Habib ya ba shi haƙuri, za ta faɗa masa tana son shi kuma ba ta son wani abu ya samu auran ta.
*Janafty*