Part 01
RAYUWAR DA NA ZAƁA
Part 01...
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai.
“Ke wai Maryam yaushe za ki gusa ki ba mu guri? Kullum kina makale a cikin ɗaki, kamar wata bokanya. Dubi kawayenki ki gani, duk sun yi aurensu, wasu ma daga cikinsu har ƴaƴansu. Amma ke kullum kina zaune a gida, abin ko damunki ba ya yi."
Muryar Inna ce take dukan kunnena kamar saukar aradu. Na ja dogon numfashi, idanuwana suka cika da kwalla, na kasa cewa uffan. Ina zaune a gefen gadona, na lumshe ido ina jin yadda ɗacin kalaman da Inna take furta min yake ratsa zuciyata.
“Inna, don Allah ki yi hakuri. Shi aure ai lokaci ne, idan lokacin ya yi ai zan yi.” Na faɗa da muryar da take rawa, ina kokarin danne kukan da yake neman kubuce min.
“Wane lokaci kuma Maryam? Shekararki talatin fa! Talatin fa Maryam! Har yaushe ne lokacin nan zai yi? Idan kina tunanin karatu ko aikin office ne ya hana ki aure, akwai mata da yawa da sun fi ki komai, amma suna nan a zaune gidan mazajensu. In banda abinki Maryam, me kike taƙama da shi a duniyar nan? Kyau? Ko ilimi? Duk karshen mace ta gari shi ne gidan mijinta!” Inna ta karasa tana bugo kofar ɗakina da ƙarfi, ta fice tana ta faman mita...
Na kifa kaina a kan gwiwoyina, kuka ya ci karfina. Wannan ne kalubalen da nake fuskanta kusan kullum. A wajen aiki, kallo na ake yi a matsayin tsohuwar budurwa. A gida kuma, an maida ni saniyar ware. Ko hira ake yi, idan na saka baki, sai ka ji an ce, “Ke dai bari mu yi maganar manya, ai ke har yanzu yarinya ce tunda ba ki san zafin nakuda ba.”
Wani lokacin takurawar takan kai ni bango, har na ji na tsani kaina na duniyar gaba ɗaya. Na taba kallon madubi na ce, “Me ya rage wanda nake jira? Ko dai akwai wata cuta da take damuna wacce ban sani ba?”
Duk matsin lambar nan, ni kadai na san irin mutanen da suke zuwa nemana. Wasu idan sun zo, ina yi musu maganar aure sai su daina zuwa kwata-kwata, wasu kuma da zancen banza suke zuwa idan na nuna musu ni ba mutuniyar banza ba ce, sai su yanka min rashin mutunci su yi tafiyarsu wasu kuma gani suke tunda na dade ban yi aure ba, zan amince da kowane irin wulakanci.
Ina cikin wannan kukan, wayata ta shiga ruri. Na duba naga sunan da nake fargaba ne yake yawo saman screen din wayar... Alhaji Sani ne. Mutumin da kowa yake so in aura duk da halinsa na rashin mutunci, saboda kawai yana da kudi.
Cikin sanyin jiki na dauki kiran zuciyata cike da fargaba, ƙatuwar muryarsa ta daki dodon kunnena, “Maryam, gobe zan turo magabatana. Ko kina so ko ba kya so, wannan wasan kwaikwayon ya zo ƙarshe!”
Zuciyata ta buga da ƙarfi. Shin zan sadaukar da farin cikina na auri azzalumi don kawai in faranta wa iyayena rai?
Hussain Yusuf✍️