TUN RAN GINI

Chapter 63

by @maryamlitee

Na saki ajiyar zuciya sai na snkuyar da kai, don ya tsare ni da idanuwansa.
Baba ya ce in je sanda na shirya in zo na tafi da ku. Sai dai zan mayar da Naana makarantarta, zan dauki dawainiyarta da komai da take bukata."
Wani irin ba dadi na ji gane ya gane saboda ya bar yi ma Naana dawainiya ya sa aka mayar da ita.
Zan tafi Lima sai mun yi waya." Ya fadi mini cikin tattausar murya na bude baki na yi masa addu'a, ya fice daga zauren kamar walkiya.
Na ja kafa na koma ciki.

Ban kula maganganun Mama ba, na fara shiri ta wankin kayanmu da guga.
Washegarin zuwan Hamid muna zaune da Bilkisu ina fada mata yadda za ta yi da Naana ta dube ni cikin murmushi "Yaushe za ki koma Aunty?
Sai da na dubi kofa na ce "Koyaushe Bilkisu. Daga zarar Hamid ya zo zan tafi. Ina so ki kula da Naana kula ba irin waccan da kika yi mata ba, saboda halin rayuwa. Kin ga a baya wadata ta sa muka jiyar da ita dadi da komai ya kare muka dandana kudar mu, domin ita dai ba ta san babu ba, abin da take so shi kadai ake mata.
Daddynta zai yi mata sayayya kamar da amma ki koyi boyewa sai za ta Sch, tunda ta fara koyon cin abin da aka dafa a gida ki bar ta a haka ta saba.
Idan ta fara kukan banza kan an taba mata abu ki zare mata ido, ba wai yawan duka ba don duka ba ya shiryar wa sai idan ta kure."
Murmushi ta yi tana rike baki "Wai yau Aunty ke cewa a zare wa Naana ido a hana ta abu."
Ni ma na yi murmushi "Lokaci ne Bilkisu a yanzu shekarun ta shida ne dole a fara koya mata idan babu ta hakura.
Ta gyada kai "Har na fara jin kewa idan kika tafi Aunty."
Na ce "Ai idan kina zuwa sai mu tafi tare."
Ta girgiza kai "Mun kusa komawa Sch da na bi ki Aunty."
Mama da ba mu san da wanzuwarta ba sai muryarta muka ji a kan mu "Kina wasa da magana ta ko Halima? To wallahi kin ji na rantse sai dai ki zaba tsakanin ni da mijin naki amma indai ni ce uwarki ba za ki koma gidansa ba!
Ni da Bilkisu muka yi shiru ta ci gaba da tattaka bala'i har sai da Abdallah ya shigo ta yi shiru ta fita Bilkisu ta ba shi labarin halin da ake ciki ya ce zai je ya fada ma Haj Iya abin da Mama ke shirin haifarwa ga aurena.

A ranar har dare ya raba ta hana kanta barci ta hana ni Bilkisu da ta gaji dakin Umma ta gudu.

Da safe na tashi da ciwon barin kai daya, har karfe goma ban karya kumallo ba ina kwance zuwan Hajara ya sa ni tashi na fara yo wanka tana rike da Sadiq na dawo na shirya jikina sannan na hada tea da Bilkisu ta kawo mini komai, na karya, ban boye ma Hajara komai ba na abin da Mama ke shirin aikatawa ta yi ta karfafa mini gwiwa kar na sa zantukan ta a rai, tana tauna tsakuwa ne don aya ta ji tsoro daga ta kasa samun hadin kaina dole ta hakura.
Na saki jiki muna hirar mu rabin ta labarin zama na a Karfi nake ba ta, takaici kuwa kamar ya shake ta sai balla mini harara take, na yi shiru ina sakin murmushi "Wai me na yi kike harara ta?
"Sakarci mana." 
Ta fadi kamar za ta falla mini mari "Ina amfanin matattar zuciya? Na gode ma Allah da bai ba ni irin wannan hakuri naki ba ina dalili.
Don uwar kishiya kin cinye naki ko karamar diyata ba ki iya san ma wa, don kan uwarki sai nawa ya samu ki sanya wani tsumman hannunki ki diba.
Na rantse da Allah kin ci uwar karya kin kwana da yunwa, surukar ta dade ba ta sa an sake ni ba, wallahi ba ta cin shi."
Na yi murmushi ina duban yadda take tada jijiyoyin wuya.
Na ce "Kwantas Hajjaju. Mai adabu ya ce hakuri kawa ne a yau kadan daga cikin mutane suke aikata shi, manzon Allah kuma ya ce Assabru ziya'un. Hakuri haske ne, duk mai hakuri ana yi masa kallon dolo wawa amma kuma babu wanda zai yi shi gaba bai ci ribar abin ba. Kin san Allah ba zan iya fada da Fauza a zo raba mu saboda abinci ba gaskiya zan ji kunyar hakan, ita dai da ta dauki abin hannunta wani kayan gabas to ta rike yau ina abin da ta cin ba sun kare ba ta dawo kan nawa da ta ci me ya rage ni? 
"Amma wallahi zan zunduma miki ashariya Halima da kika sayi doya don ta mayar da ke sakarai ta dauka ta dafa suka cinye wadda kika ce ta ajiye ma yarinya ma don rainin wayo ba ta rage ba."
Na yi murmushin takaici don har gobe na tuna wannan rainin wayon ina jin daci kawai dai ba zan yi fada da ita kan abinci ba ni ba matsiyaciya ba ce, don harkar tsiya na dauki abin.
Ta bude baki za ta yi magana Naana ta fado dakin tana kuka riris gabana ta fadi rarrashin duniya ta yi shiru ta fadi me aka yi mata ta ki yin shirun har sai da Bilkisu ta shigo ita ta fada mana yaron kanwata ta dakin Ummi da ya kwana biyu a gidan shi ya taba mata Teddy dinta.
Na dube ta na ce *Tashi Naana ki yi hakuri, ba yayanki ba ne?
Ta kara birgima ita sai an biya ta na fara waiwaye idona ya sauka kan tsintsiya na zaro biyu ba zato na fara tsula mata ai kam sai ga ta tashi ta gudu Bilkisu ta kama ta na ce ta sake ta, ta sake ta ba a son ranta ba, na zare mata ido na ce ta yi shiru ai kam ta yi tsit.
Bilkisu ta kama hannunta suka fita Hajara ta dube ni "Yanzu kika shirya zama uwa Halima."
Cikin rashin fahimta na ce "Da na yi me?
"Da kika fara tsawatar ma Naana ba komai ki bi ta da ra'ayinta ba."
Na yi dan murmushin "Wallahi tausayin maraicin ta ya sa ban iya dukan ta ban son kukanta, amma gudun kar ta tashi a haka dole na yakice komai na kwaba mata, ba ta duk abin da take so kuma ba lokaci daya za a zare mata ba idan mai dadin ya samu a bata, ranar da babu kuma dole ta hakura kamar yadda yanzu ta fara sabawa da hakan, duk da dai dakin Mama akwai kayan dadi."
Muka yi dariya.
Ana fara sallar Azahar Hajara ta tashi tafiya, duk kuma yadda na so ta tsaya ta ci abincin Ummi ba ta yarda ba, na raka ta har zaure ta wuce.
Ban tsammaci dawowar Hamid da wuri ba washegari ayam sai ga shi na fara ciro kayana yana zaune rungume da Sadiq ya fara dauka ya fitar ya yi ma su Mama sallama ta shigo dakin ranta bace tana duba na ina sanya mayafi "Wallahi kika bi shi ban yafe miki ba Halima." 
Na koma bakin gado na zauna na yi ma Abdallah txt na fada mishi halin da muke ciki da Mama.
Nan da nan sai ga amsar shi ya ce bai samu ya tafi gidan Haj Iya ba amma yanzu zai kira ta.

Ina nan zaune Mama ta karaci fadan ta ta fita Hamid ya ji shiru ya shigo ya gan ni zaune "Zama kuma my Lima mu da za mu kama hanya?
Ranar wanka Hausawa suka ce ba a boyon cibi. Dole na dube shi na ce "Mama ta ce ba ta amince da tafiya ta ba."
"Bacin rai ya bayyana a fuskarsa ya tsare ni da idanuwansa kafin ya juya ya fita na fara kiran sunayen Allah tare da adduar kar ya yi fushi ya tafi na san da Haj Iya ta ji dole Mama ta sauko.

Maimakon Haj Iya da na sa ran gani Baba ne ya dawo gidan cikin fushi mai tsanani ya ce in fito in bi mijina.
Mama ta ce matukar na taka kafata na bi shi ba na tare da albarkarta hawaye suka gangaro mini na tunanin me na yi wa Mama take gwada kamar ba ita ta haife ni ba? Ita da Baba kuma suka haura sama wanda har kishiyoyin ta suka fara ba da hakuri, shigowar Haj Iya ya sa Mama yin shiru ta shigo dakinta.
Haj Iya ta ba Baba hakuri sannan ta shigo ta samu Mama umarni ta ba ta ta sa ma aurena albarka ta bar ni na koma dakina matukar ta ci gaba da jifa ta da munanan kalamai to ta sani ita ma ta yi fushi da ita.
Dole Mama ta ce in tafi Allah ya tsare na mike ba ko waiwaye na fita dakin dakin Babanmu na fada na fadi kasan Carpet dinsa ina kuka ya tsaya bisa kaina ya ce "Tashi Halimatu, maza ki bi mijinki Allah ya yi maki albarka."
Na mike na fita su Ummi da Umma suka raka ni har zaure na fita na samu motar da Hamid ya zo cikin ta, na shiga ya sanya mini Sadiq a cinya ya tashi motar.
Naana ba ta gidan Bilkisu ta tafi da ita gidan Amina.
Tafiyar kurame muka yi babu mai cewa komai har sai da muka zo Kafur, ranar lahadi ne da ta kama ranar kasuwar garin ya ce ko akwai abin da nake bukata na girgiza kai ban yi magana ba.
Ya amsa waya sau biyu kafin mu shiga Karfi a daidai kofar gidansu ya ajiye motar, kamar koyaushe ni na fara shiga na bar shi a waje, wurin Anna na fara zuwa tana zaune a kujerar da zaman ta ya zame mata kamar al'ada.
Ta amsa sallama ta kadaran kadahan na shiga na zauna na soma gaishe ta muna cikin gaisuwar Salamatu ta shigo da fara'a sosai tana mini barka da dawowa yaranta kuma suna Oyoyo Naana oyoyo Sadiq.
Na yi murmushi har kasan zuciyata mun gaisa ta tambaye ni nono na ce ya warke ras sai godiya ta ce Ma sha Allah ai kin dorar Maman Naana."
Na yi murmushi ina mikewa tsaye na ce ma Anna da take sauraren mu zan shiga ciki ta ce. "Ba laifi."
Tare muka fito da Salamatu sai muka hade da amaryar Yaya Modibbo muka gaisa ita ma saukin jikina ta tambaye ni ta ce ina Naana da Sadiq na ce Sadiq na waje tare da Daddyn sa Naana na Zaria.
Na bude falon da key da Hamid ya ba ni tun a mota na shiga dakina sai da na gyara dakin sannan na yi sallar la'asar na idar na jingina da bango ina lissafin rayuwa Hamid ya shigo abinci ya miko mini na ci sosai don ina jin yunwa ya kwantar da Sadiq yana cewa ruwa zai watsa in tashi mu yi wankan na samu saukin zafi na girgiza mishi kai kawai ya shige wankansa daidai da daukar karar wayata na duba sunan Mama da na gani ya sa gabana tsinkewa kasa dagawa na yi har sai da ta katse ta kuma daukar kara kamar yadda na zata bala'i ta zazzaga mini ta kuma ce kar na sake tako kafata dakinta in zauna wurin mijina da na zaba a kanta.
Na hadiyi yawu na ajiye wayar a gefena na share hawaye.
Hamid ya fito daure da towel ya iso inda nake yana kama ni na ga karfin halin sa da yake so dole sai ya sanya ni nishadi ya kuma matsa mini sai da ya kwanta da ni ina fakaitar sa ina share hawaye bai ko damu da kwanciyar da na yi masa kamar gawa ba.
Da na samu ya bar ni na shiga na yi wanka da na fito ma ban shiga kitchen ba sai washegari sai a sannan kuma muka hadu da Fauza