Page 1
by @barista
ƳAR GWOGGO
By Sayyada barrister Amanar Nimcy SARAUTA 🥰
***
YOTA 13
Reposting
Book 1
Page one
_Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai_
BORNO STATE
*_ƘAUYEN KUKAWA_*
"Tafe nake ina rera waƙar da jiya mallamar mu ta makaranta ta koya mana, ji nayi ance ƴar Gwoggo" Na juyo naga wane dan rainin wayonne yake tsokanata yau, a kullum in har na fito sai an tsokaneni.
Ashe ma Salisu ne daman shi na fito nema dan na anso kuɗin ƙosai, nace "kai salisu ina kudin ƙosai na? kai kullum in dai kaci bashi baka biya, to wallahi yau sai kabiyan" kee Deeje anki abiya tunda ma rashin kunya kike min" yayi wucewar sa ya barni a tsaye nace, "kan uban nan yau za kasan da Deeje kake" dutse na ɗauko nace, "Salisu juyo ka gani" Aiko yana juyowa na wulla mai dutse a goshi ji kake kau, na ruga a guje nayi gida abina.
Shi ko Salisu riƙe wajen yayi yana ihu, yana "Aradu zakici ubanki Deeje kuma a kuɗin ƙosan ku in na biya shege nake" Kan kace kwabo jama'a suntaru suna yiwa Salisu jaje dan kuwa yaji rauni sai jini ke zubowa a goshin sa gashi yakumbura suntum, pharmacy aka kai shi don adakatar da zuban jinin, aka wanke aka manne masa bandage, daga cen ya wuce office na iyan sanda mota guda su kayo gidan su deeje.
Deeje ko ina shiga gida na tarar Gwaggo ta gama aiki har abinci an ajiye min nace "washh na gaji" ɗan ƙaramin madafar abincin mu na nufa na ɗebo abinci na zauna na fara ci, Gwaggwa ko dajin ana taba kwanuka a kitchen tace, "lallai bunsurun gida inna mai kunu yau kwananka ya kare" ta ɗauko ƙaton katako tayo madafar abincin da niyyan rafkamai kawai taga ashe dai Deeje ce tace "ke Deeje wallahi yau da kin ziyarci lahira, ai na ɗauka wannan bunsurunne, amman bana hanaki shigowa babu sallama ba?"
Ƙofan gida mukaji ana bugawa, Kamar za a balleta, Nace "bari na leƙa ba zai wuci Salisu bane" nayi ƙofan gida, ina budewa ko naga wani dan sanda da ƙaton ciki da kulki a hannu ihu na saka ina cewa "Gwaggwo ki taimaka min zasu tafi dan" ai anan take na fara fusari a wando dan bana kaunar ganin ƴan sanda.
Yace "heee shut up your mouth" Nace aradu bani bace oga mai tumbi, kana wa Allah ka kyaleni, ya juya yace wa Salisu "is she the suspect?"
Aiko sai ga Gwaggwa ta fito, tace "meke faruwa ne ni Hajara me zan gani? Salisu yace "wannan yarinyar ce tamin haka kuma ina so itama ta ɗanɗana abinda tamin" What? Akan wannan yarinyar kasa muka ɗau rundunan ƴan sanda mota guda, hee how old are you?" nace "wayyo na shiga uku Gwaggo wai prison zanci har na mutu, wallahi da turanci ya faɗa" Aiko Gwaggo har kasa ta durkusa tana Yallaɓai kar ka tafi da jikata wlh bamu da kowa sai Allah"
Wani daga cikin ƴan sanda yake cewa "shekarunki nawa?" Nan ko Gwoggo ta tashi tace "aiko zata kai shekaru goma sha ɗaya" Yace "oga yarinya ce, to me yafaru har kika ji masa rauni haka? nace "zuwa nayi na anso kuɗin ƙosai, yau kusan kwana uku yaci bai biya ba, shine yace wai nazo da daddare na ansa, shine na masa haka, salati Gwoggo ta fara tace "Salisu amanar Allah zaka ci wannan, yarinyar amanace gareni" ta fashe da kuka yace "wallahi Gwaggo sharri ta laƙamin ba haka aka yi ba" Ɗan sanda ya daka masa tsawa yace "Wato kune masu ɓata yara ko za ka yi bayani, arrest him" yace wa sauran ƴan sandan a tafi dashi.
Muka koma cikin gida, aiko cikina ya ruɗe nayi banɗaki da gudu, na fito duk na galabaita nace "oh ni Deeje yau naga ta kaina" Gwoggo tace "Deeje zo nan" nazo na zauna kusa da ita tace faɗa mun gaskiya Deeje na san halin ki me yafaru ɗazu da nace ki anso kuɗin ƙosai wajen Salisu? Nace Gwoggo kin san halin salisu cewa yayi ba zai biya ba shine na yi masa haka" tace Deeje yakamata ki nutsu yanzu kam tun kina ƴar shekara uku kike jawo mun tashin hankali, yanzu abin ma harda ƴan sanda Deeje?"
Nace kema kin san ni bana shiga sabgar mutum amma in aka shiga tawa to bana bari, bari na ɓarza waken ƙosai ko Gwoggo" na tashi na fara aikin wake.
****
Washegari da wuri na tashi na ɗauko kayan tuyan ƙosai na fitar rumfar da Gwoggo take tuya! Anan bakin layin mune, na ajiye kayan na wuce na kai markaden wake, na dawo na tadda Gwoggo har ta hura wuta ni take jira, tace "sannu Deeje, yau kam kin ɗan jima ko da layi ne?" nace "ba wani layi kawai Habibah ce da shege ganda a hankali take niƙawa", na ajiye na sake cewa zanje na shirya na tafi makaranta kin san mun fara jarrabawa" tace "to ki hanzarta fah ki biyo ki anshi ƙosan ki tafi dashi" nace "to" nayi gida.
Bayan na shirya ne nayi wajen Gwaggo na anshi ƙosan da kudin mota dan hawan bus, saboda makarantar a bakin gari take KUKAWA PRIMARY SCHOOL" makarantar Gwamnati ce tazo ta gina mana a ƙauyen mu ( kukawa) ƙaramin garine amman akwai tarin jama'a, sannan ko wacce lahadi muke cin kasuwa har ƴan birni suna zuwa cin kasuwan kukawa ba abinda babu daga dabbobi har kayan lambu, kayan miyan gargajiya da na abinci.
Bayan mun tashi daga makaranta ne muke ƙoƙarin shiga bus daman ni ba wanda yake iya ja dani, dan kuwa za ayi tashi tashinan hankali, Bus ɗin ƴan makaranta ne a cikin, Zeenatu ce yau aka hankaɗo ta faɗo daga motar wai ai ba gun zamanta bane, inji fauziyya tayi shigewarta ta zauna, aiko nima na hankaɗo Fauziyya ta faɗo ƙasa dan kuwa ina cike da ita nace "ke wacece da zaki hankaɗe Zeenatu bayan ta rigaki zama, motar ta ubanki ce?"
Cikin jin haushi Fauziyya ta tashi ta riƙoni sai ta jehuni nima, aiko window motan na kama da ƙafa na hankaɗeta ta sake faduwa, haba kowa yasa dariya daman haushin Fauziyya kowa yake ji akwai ta da nuna gadara dan wai motar ta mijin yayar tace, tace "to wallahi daga yau ba zaku sake shiga motar nan ba, dan kuma bata ubanku bace", aka sake kwashewa da dariya, nace "ai mu dole ne mu shigeta mota kam ta uban kowace" nan ma aka sake shekewa da dariya, cikin fushi Fauziyya ta shigo ta zauna harara ta dankamin nima ko na rama dan ba amin na kyale, haka dai muka iso unguwar mu.
Na sauƙo nayi gida Salisu nagani a kofar shagonsa yana tsaye yana kallona yace "ke ƴar Gwoggo" Nayi banza dashi yace "zaki shigo hanuna Deeje sai kin yabawa aya zakinta"
Nayi cikin gida abina, kayan makaranta na fara cirewa nayo madafar abincin ina zancen zuci...
Yau ko me Gwoggo ta girka mana? Naji tace "Deeje zonan" Nace kai tsohuwar nan kina da damuwa" na shigo tana nan a ɗaki tace "aiko ga abincin ki nan muddin ba kiyi sallama ba ba zan baki ba" nace "kabdijam da a hanani abinci gara a hanani wanka" komawa ƙofar gida nayi na dinga rafka sallama harda ta iya shege, Gwoggo abin ya isheta ta fito da wani kwanu a hannu ta wullamin na sunkuya ina dariya tace "Deeje naga randa zaki yi hankali, sai ki wuce ki ɗau abincin" aiko da gudu nayi ɗaki na fara ci ina santi dan Gwoggo gwanar iya girkice, sai da nayi tas da abinci na tashi nayi sallah na koma bacci dan akullum sai nayi bacci bayan na dawo daga makaranta kafin na tafi karatun allu.
*********************
Yau take Asabar bamu da makaranta kuma duk sanda ba ni da makaranta ni nake tuya ƙosai Gwoggo ta dinga sayarwa, ina cikin toyawa sai ga Auwal yace "mutuniyar kwana biyu kinyi wuyan ganin" nace Ya Auwal kenan baka san gidan mu bane da zakace nayi wuyan gani"
Naci gaba da tuyata yayi murmushi yace "in dai na biye miki yanzu za mu yi faɗa" cen sai Bello yace waike tun ɗazu nake jiranki ki zuba min ƙosai sai kika miƙa wa Mallam Hashimu alhalin na rigasa miƙa miki kuɗi, to indai za'amin wulakaci adawomin da kudina"
Mallam Hashimu yace "ayya yaron nan aibansan ka miƙa mata kuɗi ba shiyasa na ansa amman kayi hakuri"
Nace Baba Hashimu wane irin hakuri kake basa in dai ba zai jira ba, ba a dole sai mutum yayi gaba abinsa", ko kollonsa banyi ba naci gaba da tuyata.
Yace Deeje ni kike faɗawa haka? ke harkin isa, wacece ke? To bari kiji abinda ki kewa wasu su kyaleki ni baki isa ki min ba dan kuwa tattakaki zanyi"
Na mik'e tsaye nace "kai Bello da kake cewa ni wacece, to ni ko nake da usuli tun da ni musulma ce, yace "dalla kan ina asalin yake? inda asali uwa da uba ake nunawa kinga ko tun da nake da uwa da uba aiko nafi ki asali, ke nuna min naki iyayen"
Cikin harzuka na miƙe nace "Bello har ka isa ka shegantani" Aiko ba iyayena to ai da kakata kaganni tun da ko ita ta haifi ɗaya daga cikin su, yaushe ka shigo musulunci ma da zaka san fari da baki..
Auwal ne yace "haba Bello menene haka baka ganin yarinya ce mai yasa ba zaka kaman kanka ba, Deeje dan Allah abar maganar nan haka naga abin naku yana neman ya zama babba" kuɗin na cillamasa nace "baza a bada ƙosan ba aje anema agaba" na fara zubawa sauran Gwaggo ce ta iso tana cewa wai hayaniyar me na ke ji ne? Anan Auwal yace ba fa komai kawai hira ce.
Nace "a'a Ya Auwal ka faɗi gaskiya, Gwaggo Bello ne wai dan na bawa Baba Hashimu ƙosai wai me yasa zanyi haka harda shegentani shine nace to bazan saida masa ƙosan ba".
Ran Gwoggo ya mutukar ɓaci wato dai har yanzu wannan batun ba a daina shi ba na sheganta mata jika to wlh Bello sai ya gane kuransa yau zata nuna masa iyakarsa.
Ta fara tattare kaya, Nima na fara tayata tace "Auwal ya tayani mu kai kayan gida zata je gidan su Bello. Cikin jin daɗi nace "to Gwoggo" amman araina naso inje ayi wacce za ayi agabana amman tun da za'aje karbomin ƴanci na hakura. Har kofan gida Ya Auwal ya rakoni da kaya a zauren ya dire min su, na mai godiya duk da irin abin da nake masa Ya Auwal baya biye min sai dai yayi murmushi yace yarinta ce.
Gwoggo na isowa gidansu Bello ta hau tsirfa bala'i tana "ina kuke masu gida da asali? Mahaifiyar Bello ce ta leko sakar gida tace "Gwoggo ne ki shigo daga ciki mana kya saya arana" Gwoggo tace "ai ba zama ya kawoni ba ina wannan ɗan naki maikama da inyamurai? To wlh ki shaida masa ya fita a sabgar jikata in ba haka ba to kararsa zankai ga hukuma"
Allah sarki madam Balki tace "sai hakuri wo i told this boy not to go carry rigima for me wo Bello za ka zo kasameni" Aiko Gwaggo tace "ni nake kariya (carry) wato bello ne mai gaskiya dan banyi boko ba (boy) to wlh ahir ɗinku na fi ƙarfinku nima jikata ai ƴar boko ce"
Madam Balki tace "No Gwoggo, what I mean kiyi hakuri ba zai sake ba" Sai ga Bello ya shigo gida yana what's going on? Chak ya dakata da ganin kakar DEEJEE.
Tace "nine goni kon (going on) to Wallahi ta faɗi akanka mara mutunci" Mahaifiyar sa tace ya bawa Gwoggo hakuri, yace "I'm so sorry Gwoggo" tare da riƙe kunnuwansa.
Aiko Gwaggo ta sake fusata tace "Saurayi (sorry) kuma kul kai ba saurayin jikata bane, ko ta rasa mijin aure ba zata aure kaba". Tashin hankali! sun fahimci tsohuwar abirkice take ba zata fahimci su ba suka fara lallabata, da ƙyar ta tafi tana tafe sai surfa bala'i take har ta iso gida.
Ina nan zaune ina jiran dawowar Gwoggo na ji ya aka yi sai ko ta shigo "ke Deejee zonan" Cikin hanzari na iso wajenta ta min wani wawan rankwashi akai wanda yasani na saki ƙara tare da rike wajen tace "ƴar kwal'uba ni zaki maida sakariya ashe soyayya kuke da Bello wai daga zuwansa yace wai ni goni kon (going on) kuma shi saurayin ki ne (sorry)" Cike da baƙin ciki nace "Aradu Gwoggo ƙarya yake min ni ba saurayina bane sharri ne, kuma sai na mai rashin mutunci"
Gwoggo na jin zan yi masa rashin mutunci ta san zan aikata tace "yauwa Deeje kin tabbata babu wata alaƙar soyayya ko?" nace "eh" tace "to magana ta wuce ɗaura mana tukunyar abinci, ki dafa mana miyar bushashshiyar kuɓewa dan Allah tayi daɗi irin na ran nan", Nace "to Gwoggo" fuskata a ɗaure dan har yanzu ban huce ba har sai na zazzagawa Bello rashin mutunci Ni zai ce muna soyayya wato haɗani da kakata zai yi na hura wuta nafara girki.
Gwoggo sai cewa take bi a hankali karki ƙone dan takula a daddafe nake girkin har na kammala ina zancen zuci. Na kagu gobe tayi na sami Zeenatu na faɗa mata abinbda Bello yayi min. Ina tashi da safe nayi sallah danko Gwoggo bata tashina wai ai sallah bata hau kaina ba dudu du shekaruna Goma sha ɗaya ne fah ake wannan badaƙalar. Ɗumamen da Gwoggo ta ajiye min ne na gani naci na watsa ruwa nasa uniform na makaranta na biya na amshi ƙosai da kuɗin mota nayi gidansu Zeenatu.
Ina zuwa ko na fara bata labarin abinbda ya faru tace "kina nufin yaci bulus?" nace "wallahi bai isa ba sai naga wanda zai kwace sa daga tuggun Deeje" Su kayi dariya suka tafa Zeenatu tace "ke dai muje makaranta kamin sajen Musa ya lakaɗa mana na jaki"
Da sauri muka fito daga gida mu kayi wajen Bus ashe ba agama hallaruwa ba muka nemi wajen zama muka zauna, Fauziyya ce ke harararmu mu kam ko kallo bata ishemu ba dan bamu da lokacin ta mu yau da Bello muke.
Muna isowa makaranta mu kayi aji uncle Sani ne a aji yace "yau ma kunyi late wai ku bakwa tashi daga bacci ne dawuri?"
Yace "oya on your Kneels" muka fara zuru zuru da idanuwa dan bamu fahimci me yake nufi ba bulala ya anso a hannun monitor ya fara zabga mana yace "dakikai ku rage tsawo nace, kun wani tsaya min akai sai kace an dasa ice"
Aikuwa ranan mun ci duka na cewa Zeenatu wallahi makarantar Allo zan koma ga karatu ga lada amman boko fah sai cin zali dubi uncle Sani da katon kai ga tsawo dama an ce duk dogon mutum hankalinsa a gwiwa yake" muka fara dariya ƙasa²
Yace "Au kun ma maida ni mahaukaci Khadijah Auwal and Zeenatu Ismail get up ku biyoni"
Biyo shi mu ka yi bayan aji ya kaimu akwai wani bola mai uban ɗoyi wai mu kwashe nace "Alkur'an ba zan kwashe ba haka kurum cuta ta kamani sai dai akoran" yace "haka kika ce? to yauko zaki bar makarantar nan" office ya nufa yasanar da headmaster.
Sai da yayi ajiyar zuciya yace "na gaji da case ɗin Deeje na kore ta ya fi akirga But her grandma ta bani tausayi she explained everything to me wai marainiya ce in aka koreta abun sai yayi yawa, shege da hauka. Daman ba karatun take so ba"
Ya aika mu zo muna zuwa muka durkusa har ƙasa muka gaida shi Yace "Khadijah Auwal and your friend I'm tired with your Case but zan ɗau kwakkwaran mataki akanku, go to your class"
Ya zaunar da uncle Sani yayi mishi bayanin komai ya nuna masa they're villages, so they need our help. Yanzu muna korinsu kaga bamu cimma abin da muke so ba ka ƙara hakuri Sani ni nasan matakin da zan dauka"
Muna shigowa aji ana buga bell an tashi ba abin da muka yi sai punishment yau jiki yayi tsami. Muna dawowa gida nasha magani na kwanta sai bayan la'asar na tashi, layin su Bello naje akace min ya tafi bautar ƙasa, cikin jin babu daɗi na dawo gida.
Comments and share fisabilillah