Ƴar gwoggo

Page 2

by @barista

ƳAR GWOGGO 

***
Book 1
Page 2
 


Muna tafe muna hira ni da Zeenatu, Maryam da Abida,  mun tashi daga bakin rafi daman nan muke zuwa muyi wanki a ranakun da bamu da makaranta, yunwa muke ji sosai nace "Zeenatu yunwa nake ji" itama hakan tace  yunwa take ji.

Wata gonar Geɗa muka gani muka shiga muka fara cira muna ci, nace "kai wallahi ɗanyar Geɗa da daɗi take", Zeenatu tace "ai kya ce da daɗi tun da an samin na banza", nace "ki jita Abida tasa munjaye dai mun sami na banza" aiko muka kwashe da dariya, har mai gonar ya jiyo mu, wata ƙatuwar itce ya ɗauko yayo kanmu da gudu muka bar gonar muka kwashe kayan da muka wanke mu ka yi gaba, sai surfa bala'i ya keyi yana "zanyi maganinku marasa hankali".  

Wani babban lambu  muka hango wanda yaji ƴaƴan itatuwa, wani nunannen mangoro na gani har yayi wani ja dashi, nace "wai yau sai naci wancan mangoro ko mai zai faru sai dai ya faru, maryam tace "kul Deeje wallahi kina shiga yau sai yadda akayi dake, kin manta wannan lambun na mai garine fa", nace "sai me su sun ƙoshi sun bar mu da yunwa wallahi cira zanyi in sun kamani su yanka", suma su kace "to mu shiga". 

Kayan wankin muka ajiye daga gefe, daman wani wando burgujeje da riga kamar mutum biyu su shiga na saka dawani hijabina duk ya fara fita hayyacinsa na saka, hijabin na cire na daura damara dashi na nanneɗe ƙafar wondo da ta hannu na haura saman ginin na faɗa ciki ina murnan naci nasara.

 Nace su jirani ta waje zan dinga jeho musu idan na tsinko, aiko ina tsinkowa kuma ina jefa musu su kuma a kan kayan wankin mu suke tarawa, banga kowa ba a cikin wajen dan haka na haura wani ƙaton itacen mangoro na dinga tsinkowa ina jeho musu kawai na wullo wani ƙaton mangoro kan wani ba fade jikake kau...

 Sun zo wucewa ta cikin wajen dan suna ɗan jin alamun motsin. wai ƙara ya saka dan kuwa sai da yayi wani super ya diro ta baya. Dariya na kyalkele da shi, dan kuwa har sun so su jini, ɗayan bafaden yace "kai Alqur'an ka bugu daman na faɗa maka akwai aljanu akan bishiyoyi nan" yace "aradu na bugu wannan jifar na mutanen boyene, ya taimaka masa su kayi waje.

 Sai da na tsinka iya wanda zai ishe mu na fara ƙoƙarin saukowa, wasu manya manyan karnuka na gani masu gashi sai wani gurnani suke, haba da sauri na koma daga sama, aiko suna jin motsina suka fara haushi, na wani kurma ihu danko ɗayan karan yayi wani tsalle da kaɗan ya kamo kafa ta ya diro dani ƙasa, sai ga fadawan sarki suka shigo, suna duddubawa hangoni su kayi a saman bishiya duk na rude,  subkace "kai aljana da rana saka? Lallai yau mun yi gamo" aiko da gudu suka ruga suka yi gidan sarki, suka sanar da sarki wai sun kama aljana.

 Abun ka da ƴan ƙauye sai gasu cikin lambu da sarki da ɗansa yarima wai sun zo ganin aljana. Ina makale asama, su Zeenatu ko tun yaushe suka ari na kare su kayi gida.

 Yarima Abdallah yace "ke aljana mai bayyanuwa da rana, me yasa ki ka zaɓi zuwa nan a masayin maɓoya? To kisani yau ni ɗan sarki yarima Abdallah sai na kasheki" Wani uban ihu na kurma da naga an saita min takobi dai dai kaina, na faɗo daga saman bishiyar ina cewa ƴan'uwana bil adama wallahi ni mutum ce kumin rai Gwaggo bata san nazo nan ba" har ƙasa na duƙa. 

SARKI yace "ku dakata gaskiya ne ba aljana bace kungan nata nan". Yarima cikin izza da mulki yace "to uban wa ya shigo dake tanan? kuma ta ina kika bi kika shigo? Duk da naji ya ambaci uba sai naji tsoronsa ya fita  zuciyarta nace, "kul Yarima akan mongoro zaka zagi ubana mai yamaka? Yace "eh lallai mutum ce yayi wani tsayuwa ya wankeni da mari na faɗi ƙasa yace "kaf ƙauye nan har akwai wanda zan yi  magana ya maida min?" FADAWA suka ce "hattara dai yarinya". 

Sarki ya dakatar da yarima yace "ke me yasa ki ka shigo nan ko dai abinki ne ya faɗo ki ka shigo ki ɗauka?". Nace "ƙarya haramun ce Wallahi ba ko ɗaya, yunwa nake ji kuma naga kafin naje gida zan iya galabaita shine na hau ta wannan garun na diro dan in saka a bakin salati"

wani kakkarfar ajiyar zuciya sarki ya sauke  yana mamakin yarinyar. Yarima Abdallah yace "nayi tunani ba a hayyacinki kika shigo ba ashe dai mahaukaciya ce"

Nace "ni ba mahaukaciya bace ras nake da hankali na gani nayi kun ajiye ku baku ci ba mu baku bamu ba, ga mabukata na so, wasu su kwana da yunwa amman ku ko a jikinku. Ya sake yunkurowa zai sake marina Sarki ya dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu. Cikin bakin ciki ya tsaya yana kallona kamar ya shaƙoni.

 Sarki yace "kin tabbata cewa mutan gari suna son abinda muka shuka amman ba suda halin cira shine suka hakura? bayan kowanne ƙarshen wata ina sanyawa a cire buhu hamsin na kowanne kayan itatuwa a rabawa bayi da kuma mutan gari  to ina ake kaiwa? Yarima yace baba karka yadda da ita tayu ƙarya take, dan na fuskanci bata da cikakkiyar lfy". 

Nace "tab lafiya ta lau gaskiyar kawai na faɗa". Jikin sarki yayi sanyi tabbas ana ha'inci amman zai sanya idanu. 

Yace "ke ƴar wacce unguwar ce anan ƙauyen? Nace "ina layin Sabuwar namba. Yace wa fadawa su ɗebo min duk wani ƴaƴan  itatuwan da yakenan asaka min a buhu a rakani gida dan yamma ta fara, Su kace angama sarki". 

Haka aka yi har gida suka kawo ni duk da magrib ya gabato amman layinmu cike yake da mutane dankuwa sun ji labarin wai sarki ya kama Deeje ankaini an kulle. Sai ko gani da fadawa har ƙofar gida aka ajiye min su kayi tafiyarsu. 

Na ƙwallawa Gwoggo ƙira ta fito duk ta shiga tashin hankali, tace "Deeje kece anan ina ta kuka nayi tunanin sun kashe ki gashi ba daman zuwa" Gwoggo harda kwalla. Wani dariya na kece dashi nace "kai Gwoggo mutuwa kuma ai da saurana dubi kiga ƴar yarinya dani, kin gafa abin da sarki yaban". Gwoggo ta ce "sarki usmanu ne ya baki Deeje? Nace "eh fah harda fadawansa suka rakoni. 

Yan gulma ko sai zuwa suke wai ah Deeje ta dawo inna basu labarin abin da ya faru sai su tsuke baki, Zeenatu ma sun zo muka sha dariya abin mu nace musu "kai wani nagani wai shi yarima wallahi kamar balarabe sai shegen mugunta, suka yi ta dariya har suka tafi.

 Ina kwance da daddare kawai nayi mafarki ga wannan karnukan lambun mai gari sun yo kaina wani ihu na kurma. Agigice na farka na lallbo na kwanta kusa da Gwaggo, ashe dai tana jina tace "Deeje  yakamata yanzu ki nutsu ita wannan rayuwar asannu ake binta kuma baki san watarana a hannun waɗanda zaki faɗa ba, tayu ki faɗa a hannun muggan mutane, zasu iya cutar da ke".

 Nace "Gwoggo ba abin da zai faru amman ba zan sake yi ba".

Bayan sati da faruwar haka sarki ya aiko da kayan lambu arabawa kowa kuma abi har cikin gida araba. 

Mutane sai sa masa albarka suke kuma har gida aka zo ana jinjina min wai nayi kokari. 


************************

Haka dai rayuwa taci gaba komai yayi farko yana da karshe mun kammala primary school namu  aka tura mu Junior secondary School acen birni makarantar kwanace da gangan headmaster yayi har ƙasa muka duka muna bashi hakuri ya janye amman fir yaƙi sauraronmu.

 Ina kuka na iso gida na zube agaban Gwoggo ina ta zabga kuka harda burgima sai tambayata take amman naki shuru ballantana na bata amsa sai da ta ɗauki bulala na yi shuru na koramata bayani aiko tafi ni shiga tashin hankali, tace "wai shi shugaban makarantar taku anya baya shaye-shaye? Ta yaya zai ɗauki yarinya ɗanya kamar haka ya kaita birnin kuma makarantar kwana ai ba zata sakuba, Bindiga a ruwa gobe zani wajensa sai ya jenye zacen nan"
 

Washe gari sai ga Gwoggo a makarantar su Deeje har office na headmaster ta shiga, tace "Hedmasti wato wai sotake tace ( Headmaster) kai ko me jikata tayi wanda yasa ka yanke mata hukunci haka har gidan yari na shekara uku".

 Headmaster cikin tsoro da mamaki yace hala dai baki fahimci inda kike ba koh to nan makaranta ce ba office na ƴan sanda ba ne".

 Tace "eh na sani amman abin da kake ƙoƙarin yinsa tamkar a offishin ƴan sanda ne". Yarasa abin faɗa kawai yayi shuru.

 Tace "ya ka yi shuru?" Aransa yace "this old woman she always disturbing me" Yayi ajiyar zuciya yace "ummm mama what I mean wannan ci gaba ne yazo wa ɗaliban mu, a da makarantar wuni ake yi kuma hakan takurace ga dalibai saboda ba muda secondary School anan sai anje birni, ga nesa ga kashe kuɗin mota shine gomnati ta taimaka aka yi makarantar kwana ita ta ɗauki duk nawinsu ba abin da zaki siya komai ta tanade shi harda gurin kwana kuma kowa da katifarsa sannan bangaren abinci, ana dafa musu sau biyu a rana kuma duk da haka kowanne ƙarshen mako gomnati zata dinga kamusu abin makulashe da dai sauransu"

 Cikin jin farin cikin zancen sa Gwoggo ta washe baki tace "Hedmasti har da kati fa kace dai jikata ta huta abinta" She dai Headmaster dariya kawai yake yi sai sambutu take yi Yace "nan da sati biyu zasu tafi anan makarantar zasu haɗu da sauran ɗaliban da kuwa mota ce zata zo ta kwashesu". 

Dajin haka Gwoggo tayo gida cikin jin dadi, ina kwance naji Gwaggo na ƙwalla min ƙira na fito na taddata zaune a kan taburma tana dama fura tana cewa "kai madallah". 

Nace Gwoggo in ce dai ya hakura da zancen tafiya karatu birni?" Tace a'a Deeje tafiya ai ta zama dole dan ko abin daga gwamnati ne ba daga shiba" Ta kwashe duk yadda suka yi da Headmaster ta faɗawa Deeje duk da haka Deeje ba tayi wani farin ciki ba dan bata so tayi nesa da Gwoggo dan babu mai taimaka mata tace "shikenan tun da haka abin yake" Gwoggo ta zuba min damammiyar fura na fara sha ina santi. 

 Bayan sati ɗaya 

Ana washegari su Deeje zasu je birni, Gwoggo taje kasuwa ta sayo dutsen goge kaushi da wata sabulu HALA SOAP ita wannan hala soap a KUKAWA amarene maso anfani da ita don suyi kyau wato dai ita HALAN . Acewar Gwaggo kar gomnati ta gane mata Deeje da dauɗa ta korata.

Aiko su Deeje anyi awa uku ana goge ƙafa. Gwoggo na tsaye a kanta tana gani idan takama ma ta tayata. Sai da ƙafar tayi wani ja dan durza sannan aka kyaleta.

 Gwoggo tace "to sai kuma wanka ki tabbata kinyi da kyau, a wankan ma anyi kusa awa 2 harda omo aka yi wankan tayi kyau.

 Tun da Deeje ta fito Gwoggo ta zuba mata idanuwa tana tuna abinda ya faru shekaru goma sha 12 da suka shuɗe. Irin mummunar ta'addin da ake so a aiwatar, wasu ƙwalla suka cika idanun Gwoggo Deejee tace "lfy kuwa Gwaggo kamar ƙwalla kike shirin zubdawa ko dai tafiyar ce baki so?"

 Gwoggo tayi murmushi tana karewa jikarta kallo tayi wani haske da tayi wankan Amare dama Deeje fara ce kal, tana da ɗan tsawo bata da jiki, gashi kam har ya yi mata yawa duk da ba wani samun gyara yake ba, hancin nan kamar zai shige baka.

Gwoggo tace "kawai dai mamaki nake yi ashe dai Deeje tawa kyakkyawa ce" Deejee sabar dariya da jin daɗi ta kusa faɗuwa ƙasa. Tace "kai Gwoggo ai wannan sabulunce da omo yasa nayi haske" wasu kayanta na bikin sallah ta saka a cewar ta daga gobe na daina sanyaku, har bacci ya ɗauke ta.

 Gari yana wayewa ko ƙarin kummallo basu tsaya yi ba suka yi gidan su Zeenatu dan su wuce, har makaranta Gwoggo ta rakota tana nan saye sai da taga tashin motarsu kamin ta koma gida, Gwoggo har da zubda ƙwalla gani take an rabata da Deeje.


***********************
          *BIRNI* 


A daidan wani katafaren shop a kayi parking motar, wani hadadɗen saurayi ne ya fito bayan guard sun bude masa ƙofar mota, ba zai wuce 27yrs ba ya fito daga mota fari ne kal, da wani kwantaccen gashi kansa kamarna larabawa yana da tsawo bashi da kiɓa, sanye yake da wata shadda kana ganinta kasan ta taci NAIRA ɗinkin half jampa aka yi wani farin glass ne a idon sa, daga gani dai kasan wannan daga cikin daula ya fito.

Masu mara masa baya suka mara masa har  suka shige cikin shop ɗin nan suka sanar ga YARIMA MAHEER ya shigo kowa ya fita zai yi siyayya. Bai fi mintina ba nan da nan kowa sai fitowa sake jiki na kyar ma aka saya daga gefe.

Sannan ya fara ta kunsa cikin izza da takama dan MAHEER akwai ji da kai bai son raini. Ya shiga shop ɗin sai da ya gama siyayyarsa tsaf sannan ya fito kamin nan naga mutanen da suke waje suka fara kusa kai cikin shop ɗin dan su kammala nasu siyayyan.

 Inanan MAHEER yaja motarsa da masu mara masa baya sukabar haraban wajen ... 

REST HOUSE nasa ya wuce yana shigowa kai tsaye ɗakinsa ya wuce ya tadda ta kwance da ita sai wani half vest da gajeren wando iya cinyarta bai kulata ba yayi toilet ya watsa ruwa.

 Ya fito ɗaure da towel a kugu da wani ƙaramin a hannunsa yana goge jikinsa da shi, ta taso tayi cikin nata  salon ta rungume sa ta baya, cikin hanzari ya dakatar da ita yace "bana sallame ki ba? Me yasa baki tafi ba" cikin cool voice yake maga danshi baya son hayaniya.

 Tace "I need.... Yadakatar da ita da cewa "get out, kin san ni bana sex sai romance so is better for you ki tafi sai na nemeki.

 Tsaya wa tayi tana kallon sa da ƙananun idanuwanta wanda suka cika da sha'awar sa ta rasa yadda zata yi kuma ta san halinsa abin da take nema ba zata samuba. 

Yakammala shirinsa ya jefa mata bounch na kuɗi yace "kada na sake ganinki" Ta ɗauki kayanta ta maida su jikinta tayi gaba. 

Waya ya ɗauka yace "ka shigo min da ita" Wata kyakkyawar budurwa aka shigo da ita ya tsaya yana kare mata kallo.

 cikin tsoro tace "dan Allah kabarni na tafi" taku yayi a hankali har zuwa kusa da ita yace "na kiraki shine kika gudu amman da na saka yarana su ɗauko ki ta ƙarfi shine zaki bani hakuri, to ki sani sai na gama duk abin da zan yi zaki tafi, in kuma bans ami yadda nake so ba anan zaki kwana"

 jikinta ya fara kƴarma cikin e"e"na tace ka...kaaa rufamin asiri wal...hi ...ban sani bane na hankaɗeta kamin rai" Sai ta fara kuka.

 Cikin Cool voice na shi yayi murmushi irin na  mugunta yace "kina tunanin zan kyaleki ne?"

 Gyallenta ya zame daga jikinta ya fara shafa gashin kanta yace ummm you look pretty but bakya ƙamshi, jikinta sai rawa yake yi a ranta ta ce yau ba mai kwatanta a hannun sa kayanta ya fara cire mata amman tayi saurin dakatar dashi ta hanyar matsawa baya,

 Ya sake yin murmushi ya ce "ummm da alamu anan zaki kwana ko?" cikin rawar murya ta ce "a'a ka kyaleni na tafi" janyota yayi suka faɗa kan bed cikin ƙarfi yaraba ta da kayan jikinta, ganin surar jikinta yasa ya fara fita hayyacinsa,  murya na rawa yace Do you need money? zan baki duk abin da kike so". 

Kuka take yi tace "a'a bana son komai ni kabarni na tafi". 

Yaga dai zata  ɓata masa lokaci ya fara luguigitata iya son ransa.

 Da farko yarinya ta tsorata a tunaninta fyaɗe za yi mata amman sai taga shi nema kawai yake  ya sami nutsuwa da ita. Yaringa wasa da ita har ya sami nutsuwa, ya mirgina gefe yana haki kamar wanda ya nome rabin gona. 

Yace ga kudi agaban mirror ki dauka ki tafi, cikin sauri ta maida kayanta ta ɗauki kuɗin ta fice. Yaci gaba da baccinsa. 

Yana farkawa ya tuna kiran da mahaifinsa ya yi masa ya hanzarta ya shirya ya fito yace wa driver "ka kaini gida" Bai bata wani lokaci ba sai gasu a wani haɗaɗɗen gidan sarauta, wani babban gate aka bude, suka shige.

 MAHEER ne ya fito daga cikin mota bayan masu tsaronsa sun buɗe masa ƙofar mota cikin tafiyar sa ta jinin sarauta yake taku, kai tsaye fadar mahaifinsa ya nufa, yana shiga fadawan sarki suka mike saye suna "barka dai Yarima" Hannu kawai ya ɗaga musu ya durkusa har ƙasa yana gaida maimartaba sarki Ahmadu. 

Sarki yace MAHEER "an kawo min labarin unguwar da suke nan gabas damu suna cikin mawuyancin halin rashin ruwa, dan haka kai zan daura akan kula da harkokin wajen sai ayi abinda ya dace, cikin girmamawa yace "in sha Allahu baza a samu matsala ba, za ayi komai akan lokaci" 

Mike wa yayi ɗakin kakarsu ya nufa, tana jin motsi ta fara magana "waye wannan?" sandarta ta ɗauko tana nunasa dashi alamun kar acutar da ita.

 Yace "kayya tsohuwa akwai ki da soro to nine MAHEER jikanki". Tace "lah kace min marajin nan, to ka shiga taitayinka dama kayi min laifi, ka hanani waccan turaren mai daɗi da naji ka fesa ranan".

 Yace "kai Diddi ke da kika kusa gangarawa kuma wane turare za'a siya miki sai dai ko na shafawa a likkafani?" Haba ƴar tsohuwa harda kuka, "Ni zaka ce zan mu? to ja'iri sai dai kai ka mutu mara mutunci" 

Yace haba Diddi wasa da nake"  Tace sam sai ya fita, hakan nan ya fita a hanyarsa ta wucewa ɗakin sane yayi arba da ɗan'uwansa Abdul Maleel wanda MAHEER yafi shi da watanni bakwai. Kuma dan kishiyar mamarsace wani harara Abdul Malik ya yiwa MAHEER ya wuce.

 Murmushi kawai yarima MAHEER yayi ya shigo ɗakin Hajjiya Ummah mahaifiyar Abdul Malik har ƙasa ya duka ya gaidata amman ko kallo bai ishe taba ballantana ta amsa cikin sanyin jiki ya fice inda sabo ai ya saba tun bayan rasuwar mahaifiyarsa.

************************

GIRL'S BOARDING SCHOOL ( G. B. S.)

Kai tsaye saye motar ta dire dukkanin ɗalibai a farfajiyar makaranta. Deeje na fito sai murna nake nazo birni, wani hostel aka kaimu. Ba laifi ɗakin yayi kyau babban dakine mai ɗauke da gado mai hawa uku har guda hudu abinda bai min daɗi ba, shine rabani da akayi da su Zeenatu dan a dakin ba wacce na sani.

 Kayana na fara jerawa a loka ina kammalawa na hau lafiyayyen gadona na kwanta ni ce ta hawa na biyu na kwanta abina.

 Wani bacci na din gayi harda munshari abinka da babu a house. Ji nayi an makeni a bayana har sau uku ina tashiwa cikin gigin bacci nima na wanke mai shi da mari.

 Wasu na gani a tare da wanda na mara suka ce "hke Headgirl kika mara yau zakici kol ubanki" Wacce suka kira da Headgir danni ban san ma me ake nufi da hakan ba dan turanci ba sonsa nake ba.

tace "ku fito min da ita ku kaita daning" ni dai ina biye dasu har daning muka shiga wani babban madafar abinci na gani tukunyar sai mu shige ta da gani har Headgir nasu ciki. 

Tace na wanke tunkunyar kuma yanzu za a daura abincin dare kuma na tabbatar tafita tayi kyau ko tabbare karta gani.

 Tsayuwa nayi mai kyau na kalli tukunyar na lalle su nace "tab tukunyar da ko iya sauketa ba ayi da alamuma amanne take  tab ba zan yi ba kuma wama yace bauta nazo yi ni karatune ne ya kawo ni, duk wannan zancen zuci ne.