Page 3
by @barista
ƳAR GWOGGO
***
Book 1
Page 3
GIRLS BOARDING SCHOOL ( G B S)
Taku na fara da nufin barin wajen sai suka jawo ni na dawo da baya, wai sai na wanke zanbar wajen.
Nace bayin Allah, ban sanku ba, ban san daga ina kuke ba, sannan ba wata alaƙa a tsakanin daku yau fa na fara ganinku amman sai ku ɗauki kiyayya ƙarara ku nunamin"
Yanzu sakaninku da Allah ko ku aka sa ku wanke wannan jibgegiyar tukunyar nan ba iyata za ku yi ba dan haka nima ba zan iya ba"
Wacce ake kira da Headgir ce ta ɗauki hannu zata mare ni na riƙe nace "kut wallahi ba'ayi kiba saboda cin zali hadda mari", dambe muka fara yi na zage dantsi sai nausansu nake, wai akace gidan yawa, kwantar dani suka yi su kayi ta jibgata. Ihu nake kamar wanda aka soke da wuƙa nayi waje aguje na ɗauko ƙaton dutse ina binsu suna guda har office na principal.
Aiko muna shiga kaɗan dutsen ya faɗo kansa yayi wani backturn ya diro ta baya, saboda akan kujera yake. Cikin tashin hankali gaba ɗaya sun razana gani suke sabuwar mahaukaciya ce ta biyo su aiko principal aguje yayi office na vice principal ya kulle.
su kuma suka yi waje suka shige toilet suka rufe kansu. Zama nayi a bakin kofar banɗakin ina jiran fitowar su, wata ce da alamu mallamace a makarantar, ahankali tazo inda nake ruwa ta mikomin agora tace "ki sha" sai da na kwankwaɗe sa tas nayi gyatsa nace "Alhamdulillah"
Tace "ya sunan ki?" nace "Deeje nake ƴar Gwoggo" Tace "to me ye ƴan matan nan su kayi miki kika biyosu? nace "kyalesu ƴan mantan uba zalina suka ci alhalin ban san me nayi musu ba. Yau mai rabi ni da su sai Allah"
Ashe matar principal ne, shi ya kirata yace tayi sauri ta fito daga Quarters na makaranta zuwa cikin makaranta, akwai wacce aljanunta suka tashi tazo tai mata ruqiyah. Bata ɓata wani lokaci ba shine ta iso. Cikin dabara tace "ki kyalesu ni da kaina zan;miki maganinsu dan basu kyautaba biyoni mu:tafi, duk a tunaninsu aljanune da ni na biyota cikin office mun ɗauki wasu mintina tana ta faman yi mini addu'ar.
Na koma hostel na kwanta Zeenatu ce ta shigo ta sameni a kwance, tace Deeje lafiya naga kin biyo wasu ɗalibai aguje?" Nace "ke dai Zeenatu bari", na kwashi yadda mu kayi na bata labari. Aiko Zeenatu dariya har ƙasa tana "yeee sai Deeje ƴar Gwaggo nta, muka sha hirarmu kamin ta tafi naci gaba da baccina akan gado mai laushi.
**********************
*MASARAUTAN sarki Amadu*
A saye yake a tsakiyar dakinsa, hannunsa riƙe da mararsa yana jujjuya kansa saboda wani irin azaba da yake ji, bakin sa na ambaton Allah.
A daddafe ya ɗauka maganin da amininsa DOCTOR KAMAL ya kawo masa, da sauri ya haɗiyi guda biyu amman haryanzu ya naji, ya haɗa lemon tsami shima yasha sannan ya fara jin sauki duk yayi zufa.
Tambaya yake wa kansa wai meke damu sane yake shiga cikin wannan yanayin? a duk sanda yayi 4eyes da mace to baya iya controling kansa, har sai yajisa ajikinta kamin ya sami nutsuwa.
Baya manta daren da wannan abin ya fara faruwa dashi. Yana kwance har bacci ya fara ɗaukansa yaji wani abu kamar ya shigesa, zumbur ya miki saye yaji kansa yayi masa nawi, ya din ga zagaye ɗakinsa kamar wani sabon taɓeɓɓe, luu ya zube ƙasa sumamme.
Lami hadimar sa tayi sallama akan ya bata izinin shigowa amman taji shuru, sai ta ayyana aranta yayi bacci ne amman bari ta shigo ta ajiye masa tea, saboda muddin ya farka zai sha. Hakan ya zame masa jiki ko min dare in dai ya farka to sai yasha bakin shayi haɗin gargajiya, wannan dalilin ne yasa aka nemomasa wacce ta iya haɗawa, kuma yayi sa'ah ta iya.
Tana ajiye wa tayo inda yake kwance a kofar banɗaki, fridge ta bude ta dauko robar ruwa ta kwaramasa afuska, a kiɗime take dan haka ta ta cire hijabin da ke jikinta ta fara masa fiffta.
Sai da tay 30 minutes kamin ya fara motsi, tace "yarima MAHEER" a hankali ya bude idanuwansa yana kallonta, tace yarima ka tashi a bakin toilet kake ka koma kan gado, ya kasa kau da kansa daga kallonta.
A hankali ya kai hannunsa ya fara shafa fuskarta zuwa wuyarta, taga fa abin nasa gaba yake yi kuma tayi tunanin bai gama dawowa cikin hankalin sa ba, tai sauri ta miƙe da niyyar barin wajen kawai ya janyota ta faɗo jikinsa yayi sauri ya manne bakinsa da nata, komai yana yin sane cikin ƙarfi kamar mayunwacin zaki, tsoro da fargaba suka kamata ta fara turesa amman ina jitake kamar dutse ko motsi bayayi.
Gam, take jinsa, ya rabata da kayan jikinta yayi ta romancing nata, ta zamo kamar mutum butumi sai yadda yayi da ita.
A tunaninta fyaɗe zai yi mata amma sai taga akasin haka. Ya ɗauki tsawon wasu mintina a haka, daga baya ya hankaɗeta gefe yana nishi yana haki kamar wanda yayi gudu. Ta kasa tashi saboda bugu wanda tayi gashi tasha jijjiga a hannunsa. Ya fara dawowa cikin hankalinsa ya yunkura zai tashi sai alokacin ya lura babu kaya ajikinsa, waro idanuwansa yayi ya fara bin ɗakin da kallo, idanuwansa suka sauka kan Lami wacce take kwance ba kaya ajikinta matsawa baya yayi da sauri ya ce "ke me ki ke yi anan?"
Ta kasa magana ta fashe da kuka, ya fara tuno abin da ya faru. Da sauri ya mai da kayansa, yace ta tashi ta fita amman ta kasa aransa yana addu'ar Allah yasa ba fyaɗe yayi mata ba.
Da ƙyar ta tashi ta mai da kayanta ta fice tana kuka, tsayawa yayi yana takaicin abin da ya faru gabadaya kunyar Lami yaji, ga wani haushi kuma ace ya rasa wacce zai haka da ita sai ƴar aikinsa? wasu zafafan hawaye ne yaji suna bin ƙuncinsa, dakyar yabawa Lami hakuri dan aikinma taso bari amman da ta fahimci ba a hayyacinsa ya aikata ba shine ta hakura amman akan sharadin zai sha barasa yabari sai bayan takawo masa tea. Yace ya amince sai alokacin yayi tunanin wato ita ta ɗauka yana cikin mayene.
Wani ajiyar zuciya yayi bayan ya dawo daga doguwar tunanin rayuwar baya. Ya ɗauki wayarsa yayi fadar sarki mahaifinsa.
Tana ganin zai fito tai sauri da nemi maɓoya dan kar ya ganta, bai gantaba yayi wucewar sa.
Dariyar mugunta tayi tace kaɗan ma kagani, "ni boka Hudu dama haukataka yayi gaba ɗaya ka shiga duniya" inji Ummah mahaifiyar Abdul Maleek.
Hajjiya Ummah mahafiyar Maleek macece mai son duniya da abin da yake cikin ta, burinta shine sarauta ta dawo hannun ɗanta kuma ta kudiri hakan aranta akan koma yaushene sai ɗanta ya mulki wannan masarautar.
Kuma in dai akan mulkine ashirye take da tayi kisa A dalilinta wannan gidan ya tarwase har yau ba asamu daidaiton rayuwa ba.
Babbar matsalanta shine YARIMA MAHEER tayi² ta kawar dashi daga doron ƙasa amman abun yaci tura. Dan boka Hudu yace mutuwar MAHEER bata nan kusa mutum ne mai tsawon rai sannan ga rabon aure da ƴaƴa. Shine tace to a ɗaura masa larurar hauka, boka Hudu yayi² ya turamasa larurar hauka amman ina har yanzu abin yaki dan MAHEER mutum ne mai yawan ibada, shine suka turamasa larurar sha'awa, sunyi sa'ah amman kashh har yau burinsu bai cika ba dan so suke yayi wa mace ciki dan a korasa daga masarauta.
Dokar wannan masarautar shine duk wanda yayi wa mace ciki to za a haramta masa zama aciki na har abada. Wannan dalilin ne yasa sukasa boka Hudu yasa masa sananin sha'awa dan ya samu ya yiwa wata ciki kuma a saukesa daga kan kujerar Yarima kuma a korasa, to amman sun manta da cewa Allah yana nan kuma MAHEER mutum ne wanda baya wasa da ibada. Waya ta ɗauka ta kira ƙawarta Hajjiya Zulai dan sanar da ita haryanzu babu ci gaba har yau ba suji labari ko ya yiwa wata ciki ba.
Hajjiya Zulai ba irin bokayen da bata sani ba indai za a sakar mata aljuhu to zata kai mutum wajen manya manyan bokaye, Hajjiya zulai irin gogaggun ƴan barikine wanda suke cin dukiyar su da tsinke. Itace takai Hajjiya Ummah wajen boka Hudu dan su kawar da MAHEER amman ina har yau hakan su bata cimma ruwa ba. Hajjiya Zulai tace "kada ki damu akwai boka Gundala zamu kai masa wannan aiki kuma zaki ga nasara, ko da shine dutse to ina tabbatar miki cewa sai yayiwa wata ciki kuma sai an korasa, danki kuma ya gaji kujerar YARIMA"
Hajjiya Ummah wani daɗi taji da zancen aminiyarta tace "aiko da kin ga tukuici mai yawa ke wani matsayi ma zanbaki", haba Hajjiya zulai baki harkunne ana murna.
Bayan ya bar wajen mahaifinsa dakin Diddi kakarsa wa wuce. Tanana zaune yai sallama, ta amsa tana maheeru kaine?, yace "kai Diddi i don't like that name? Meye kuma mahiru ku tsofaffi akwai ku da batawa mutum suna", tace "kaji ka maheeru shine ɓata suna ai shine daidai, ja'iri kawa, ya turaren nawa ne?" yace "Diddi anjima zanje wani plaza nan kusa damu zan siyo miki" tace "to madallah ko kai fah".
Ta sake cewa maheeru ya zancen auren kane? haryanzu ba kayi aure ba, kuma girma fa kake yi, yace "kai This old woman, ni bazan yi aure yanzu ba sai nan gaba kuma dududu shekaru nawa nake dashi da za ace sai nayi aure". Diddi ta fashe da kuka "maheeru ba zaka yi aure ba tun ina raye sai bayan mutuwa ta za kayi to baka isa ba ko acen ƙauyen kukawa zan faɗawa ƙanina ya nemo maka mata".
Yace "kutmelesy ba zayyu ba kamar ni na auri ƴar ƙauye, dube ni da ajina inna yarda" Diddi tace "to in an aura maka yarinya ka kasheta". Yace "shaƙota zan yi Diddi a daren farko mu"
Cikin tsoro tace "maheeru kana nufin zaka yi kisan kai? to Allah wadai da halinka". Dariyar ya dingayi kasa kasa. Tace ya tashi ya fice haka adole ya fice.
*********************
*GIRLS BOARDING SCHOOL ( G B S )*
Akwana a tashi Deeje ana final year na junior set jss 3 a G B S GIRLS BOARDING SCHOOL .
Anata shirye shiryen zana junior wyc su Deeje anfara girma amma hali yananan dan bata bari a cuceta kuma kowa shakkan taɓata yake yi, tun rana ta farko a makarantar da tai musu hauka basu sake shiga lamarinta ba, tayi ƙawa a makarantar Maryam ƴar nan birnin ce sun shaku a zaman da suka yi na shekaru uku haka ma matar principal ta zama uwar ɗakin Deeje, dan bata aiken kowa sai Deeje dan ta iya siyayya ita ko Deeje ana aikenta take kiran Maryam ta rakata sai su zagaye gari suyi ta yawo daga bisani sai su kawo mata, ita ko daɗi take ji dan haka duk hutun da ake yi a gidanta Deeje take zama Hajjiya Iklima na kaunar ta amman wannan karon Deeje zata je ƙauyen kukawa hutu dan hutun mai ɗan tsawone kuma sai sunyi registration na SS1 kamin sufara fitowa.
Deejee sai murna ake za a koma gida taje ta gono Gwoggonta.
************************
A saye yake a farfajiyan wani plaza mai ɗan karan kyau.
Yasha kyau iya kyau dan MAHEER kyakkyawan gaskene, yana da tsawo da faɗin ƙirji, gashinsa coiling hair ne da V face nashi mai ɗauke da dogon hanci da saje kwantacce a fuskansa sai jerarrun hakwaransa farare rasss dasu.
Mutum ne mai ji da kansa baya daukan raini kuma ga sarauta ga kudi. Kamar kullum al'adar sa ce muddin yazo shopping baya so yaga kowa aciki, yana tsaye kowa ya fara fitowa bayan guard nashi sun sanar dasu, kowa ya fito itako ta gama siyayya tana kan fitowa sai suka yi kicibus a ƙofar shigowa yace "what wannan daga ina take?"
Guard nasa yace "Oga we informed all of them to come out but, we didn't know.... Kafin ya ƙarasa YARIMA MAHEER ya daka masa tsawa cikin sanyanyar muryansa yace "what? kana wasa da aikinka?", ya nuna yarinyar da yatsansa yace "a lokacin da ake sanar da cewa a fito zan shigo kina ina?".
Ko kallo bai ishetaba ta juya zata fice ya dawo da ita baya yace "ok taurin kai za ki yi min ko? that's good" umurni ya baiwa guard nasa su kai masa ita mota su kulle in ya gama sai su tafi da ita REST HOUSE nasa, ba ƙaramin kaɗuwa tayi ba dajin batun nan ko kulata bai yi ba yai ciki abinsa.
Sauran guard ɗin suka tsaya a wajen, akwai guda biyu wanda a kullum sai sunyi ƙorafi akan ogansu ɗayan yace "wai shi YARIMA baya gajiya da ƴan mata ne a satin nan fa mata goma sha takwas ya kwanta dasu shi ko gajiya ba yayi".
Ɗayan yace "to mu ina ruwan mu tunda yana sakar mana kuɗi yayi ta kawo mata ɗari ma ruwansa ne. dariya su kayi.
Sai da ya kammala shopping ɗin ya ɗauko wa Diddi turaren da take so sannan ya fito yana shiga mota yace su wuce cen rest house nashi,
Yana isowa ya shige ɗakinsa yace a kawo masa ita, yauma kamar kullum kawai nutsuwa ya samu da ita bayan ya kammala ya jefeta da kuɗi yace a kaita gida.
Ya ɗauko wani abin busa ya kunnah ya fara sha yana firzadda iska da kuma hayaki wani takaicine yakamashi me yasa sai bayan ya aikata haka yake jin nadama wani kwalban lemo ya ɗauka ya haɗa shi da gini.
Ya tattake abin busarwarsa ya koma gefe yana hawaye da jin zafin abinda ke faruwa dashi.
Da ƙyar ya samu ya kawowa Diddi turarenta.
************************
*KAUYEN KUKAWA*
Daidai tsakiyar ƙauyen Kukawa motar da ta ɗauko ƴan makarantar GIRLS BOARDING SCHOOL ( G B S ) Deejee ta fito daga cikin mota ta na ta farin ciki da murnan an dawo gida dan tsawon shekaru uku rabonta da kauyen nan.
Fauziyya ce tace "Oh su Deeje sai wani rawar jiki ake za a ga Gwoggo, ni banga wani dadi a ƙauye ba, da zanyi wani murnan zuwa gida naga abincin cen ya fi na nan". Wani juyowa da Deeje ta yi kamar zata tashi sama ta ce "ah dole a faɗi haka mana babu a house ( wani sabon tsara Deeje ta koyo a makaranta) ayini da abinci kala ɗaya daga shi kuma sai dai a ɗau na annabawa. A birni kuwa an sami na bati aci har sau uku ayi kashinsa. Mu dole muyi murna dan abincin gida ya fi na waje. Kowa ya gan mu yasan da kiɓar mu muke bawai sai munci na banza ba".
Fauziyya ce ta ce "tab mu kam ba sai mun fita kan layi mun tuya ƙosai ba kan mu samu mu saka a baka, muna ci muna sha sai godiyar Allah, sutura kam sai dai mu bada sadaka". Fuu tai zata wuce Deeje ta dawo da ita ta baya, ta nunata da ɗan yatsa.
"To da ba a san asalin belbela ba da ance daga ga sama faɗo, to ai gwanda mu da sana'ar mu kasan mu, akan masu zuwa bara gidan sarki sai an wulakanta su kamin abasu"
To fah an taɓo Fauziyya maganar ta dake ta har zuciya wani wawan naushi takaima Deeje amman ina Deeje ai gwanar dambece tuni ta tare, ta hankaɗe Fauziyya kasa demm.
Da ganin haka driver nda ya kawosu ya shiga tsakaninsu yana cewa ana hana ku kuma sai kace ba daga makarantaku ke ba?. Da kyar ya rabasu.
Ai ko Fauziyya zance bai ƙare ba ba ta finciko tayo inda Deeje take tace "mu ko a kasan asalin mu ke da sintacciya ce harwani wai da ba asan asalin belbela ba za ace daga sama to faɗo, mun san komai wallahi".
Ran Deeje ya ɓaci in akwai abinda ta tsana shine a shegen tata tun tana yariyar take jin irin wannan zantuttukan to fah yanzu abin ya fara damunta dan yanzu Deeje ta fah koyi rayuwa, da ƙamshin gaskiya a zancen da ake yi in ba haka ba ina iyayenta sannan bata taɓa jin ko da labarin su a wajen Gwaggo ba amman wannan karon zata tambayi Gwaggo.
Na iso kofar gida na hango Salisu a shagon sa jiya iyau ba abinda ya canza, yana ganina ya ɗaga min hannu ban tankamasa ba nayi ciki abina.
A zabure na tsaya na dafe ƙirjina nace "me nake gani? Ya Auwal na gani zaune akan kujera, Gwaggo na kwance an makala mata drip.
Na ce "me zan gani? Ba Auwal ba hatta Gwaggo sai da ta firgita, Auwal yace "Deeje" Cikin mamaki, Gwaggo ko da ƙyar ta mik'e daga kwanciya ta ɗan kishingiɗa tana so ta ganni, tana ƙoƙarin miƙa min hannu da sauri na ƙarasa inda take na rushe da kuka.
Ya Auwal yace "Deeje yin hakan da kika yi zai sake tada mata da hankali, ya kamata kema ki rarrasheta".
Nace "Ya Auwal me ya faru da Gwaggo ta?" Yace "zazzaɓi ne fah kuma bata cin abinci shine ta rasa karfin jiki shine na saka mata drip". Nace "har tsawon yaushe take fama da zazzabin? Yace "yau sati guda" nace "Nagode Ya Auwal Allah ya saka da Alkhairi" Yace "Ameen"
Na shiga jinyar Gwaggo ba kakkautawa. Alhamdulillah ta fara samun sauki. Gashi ina son tambayarta asalin ta rihinmu sannan me yasa ake shegantani amma ba halin tambaya.
************************
*BIRNI*
*Masarautar Sarki Amadu*
Hajjiya Zulai ce zaune gaban Hajjiya Ummu tana labarta mata yadda suka yi da boka Gundala.
Boka Gundala ya cewa Hajjiya Zulai bayan taje wajensa a wani bakin daji, yace "wannan ƙaramar matsalace kika zo min da ita ba dai so kuke yayiwa wata ciki ba?", tace "eh boka gundala, yace kusa aranku a inuwa, aiki kamar an gama sai dai muna bukatar wani bangare daga suturansa da kuma warin takalminsa. Sannan mun gani akwai wata wacce zata shigo rayuwar sa ta zame masa inuwa a dai yi hattara da dokokin mu"
Wani ajiyar zuciya Hajjiya Ummah tayi dajin batun boka Gundala a bakin Aminiyarta tace "to Hajjiya Zulai yaushe zaki zo ki amshi kayan?" Tace "nan da zuwa jibi in kin samu kin kammala haɗa kayan".
MAHEER ne ya shigo har ɗakin da suke yayi sallama ba wacce ta amsa masa, ya gaidasu cikin girmamawa sannan ya fice. "Wahalalle kawai" inji Hajjiya Ummuh su ka kwashe da dariya. Hajjiya Zulai tace "yaro sai kace maye ayi ta abu amman baya cinsa dubi uwarsa ma haka ta bamu wahala kamin boka Hudu ya tura mata aljani da kyar ta mutu. Kai jininsu yana da karfi".
MAHEER ne a hanyar sa ta fitowa ya haɗu da ɗan'uwansa Abdul Maleek. Ya ce Maleek ina kake zuwa kwana biyun nan mahaifinsu yana shiga damuwa rashin zuwan ka gaida shi". Malik ya nunasa da yatsa yace "ka fita a harkata maheer ina ruwanka da rayuwata, ka rabani da samun muƙami a wannan masarautar, sannan yanzu so kake ka shiga sakanina da mahaifin mu to na kusa taka maka birki" Yayi wucewar sa ko akwalarsa .
MAHEER yana mamaki irin kiyayyan da Maleek da Hajjiya Ummuh ke nuna masa shifa ba wai da kansa ya daura kansa a matsayin yarima ba. mahaifinsa ne ya ɗaurasa kuma hakan ya zamo laifi?"