Ƴar gwoggo

Page 4

by @barista

ƳAR GWOGGO 

***
Book 1
Page 4


 *Masarautar sarki  Amadu* 
 
A hankali ta ke tafiya cikin sanɗa har ta iso ɗakin MAHEER, tayi ko sa'a ba kowa a cikin ɗakin sai ta tura ƙofar ta shigo kamar wata barauniya kai tsaye ma'ajin kayansa ta nufa da niyyar buɗewa amman kuma sai tajisa a kulle, taja wani dogon numfashi ta sauke tace "ga ƙoshi ga kwanan yunwa", sai da ta samu ta shigo amman ace ba halin ɗaukawa kut yau ko ta halin ƙaƙa sai ta ɗauka. Wasu kaya ta gani a ajiye a gefen bedside da alamu yau aka kawo su daga wajen guga shiyasa ya ajiye anan ta ɗauki set ɗaya da kuma warin takalmi tayi ficewarta. Tana shiga ɗaki takira aminiyarta a waya ta ce "an dace" aiko Hajjiya Zulai ta ce "gobe zaki ganni ke dai bari ina nan zuwa". Su kayi sallama. Wani ajiyar zuciya Hajjiya Ummah tayi dan gani take wannan karon zasu yi sa'ah, dan ta ƙosa taga mulki ya dawo hannun ɗanta Abdul Maleek. Ta ɗauki shekaru 27 dan jiran anaɗa ɗanta a kujerar sarauta, ba irin gwagwarmayar da bata shiga ba don burinta ya cika amman ranan naɗin sarautar aka naɗa MAHEER wai saboda ya bawa Abdul Maleek wata shida. Wannan abin ba ƙaramin tadawa Hajjiya Ummah hankalin ba ta bazama wajen bokaye dan ta samu akwace kujerar yarima abawa danta Abdul Maleek. Amman har yau shuru kakeji kamar ma ba a yi. Amman ta ɗauki alwashi wannan karon za tayi nasara.



REST HOUSE yana kwance akan 3setter shi kansa bai san wane irin tunani yake yi ba, bai san dalilin da yasa yake aikata wannan ta'asar ba. Acen baya abin da ya fi tsana kenan amman gashi a cikinta sundum yake, kai in fa bai aikata ba jin kansa yake kamar yayi ƙaramar hauka. 

Sheshekar kukanta yaji ya taso yayo inda take, ganin ta yayi a inda ya barta, tana ganinsa ta mike tsaye ta fara magiyar ya barta ta tafi. 

Ahankali ya tako zuwa inda take, yayi magana cikin cool voice yace "kina son tafiya?" Cikin ƙuna da maganarsa tace "eh" yace "to inkinaso kitafi sai kiyi min abin da nake so", tace "to me kake so?" Yace "good question, da alamun kanki naja, ya fara cire kayan jikinsa, tana ganin haka tace "me zaka yi?" tana waro idanuwa waje. 

Wani murmushi yayi wanda ya sake fito da kyaunsa,wanda ba zata iya fassara sa ba, na farin ciki ne ko na mugunta.

Yace "kefa kika tambaye ni me nake buƙata, to ai shine nake so na nuna miki abin da nake so", kawai ya janyota ta faɗi jikinsa yace "kul in ki kayi gardama tofa kwana zamu yi anan in kuma kika bari har na gama abin da zanyi to zaki iya tafiya yanzu ba".
Ai ko dajin haka ta hakura ta nutsu sai da ya gama duk abin da zai yi da ita ya cillamata da bounch na kuɗi yayi shigewarsa toilet yace "ki tashi kiyi tafiyar ki". Dajin haka ai ko minti biyar bata ƙaraba tayi waje.

************************_KAUYEN KUKAWA_ 

Suna kwance a ɗan ƙaramin harabar gidan su suna shan iska dan garin akwai zafi gashi ko bishiyoyi basa kaɗawa, sai da suka wasa ruwa kafin Deeje tayi musu shimfiɗa, bayan sun kammala cin abinci.

 Gwoggo tace "Deeje ɗauko min ragowar magunguna na sha danko ba zan yi asaraba" Deeje tace "kai Gwaggo yanzu kam ai kinyi sauƙi, harfa abinci mara ɗaya da rabi kika cinye tas har da suɗe kwano amman kice sai kin sha magani, Allah ki bar wannan maganin dan sanya ki ci yake" ta faɗa tana murtuke fuska dan ko Gwaggo a wuni sai taci abinci sau biyar ma tun da ta tashi daga jinya kuma ta tabbata magungunan da Auwal ya haɗawa Gwaggo akwai na cin abinci. Gwaggo tace "kai Deeje na nemo abinci da gumina amman sai a hanani ci to ahir ɗinki sai naci, ko mara goma naci ina ruwanki" Deeje da taje ɗauko magani tace "ai yau sai na toshe kunnuwana danko na tabo mita", aiko kamar a kunnen Gwaggo tace "Deeje nice sohuwar mita to kuwa yau sai kinci gidanku", Deeje tace "kai Gwaggo baki dai jini da kyauba" ta ƙaraso da maganin ta ajiyewa ta yi baya. Gwoggo tace "Deeje yauwa ɗauko canjin nan kije ki shagon Salisu ki karɓo min ruwan rober na sha da magani, dan kin san maganin ance asha shi da ruwan Bature" 

Aiko Deeje sabar dariya tace "kai Gwaggo ba turawa ke yinsa ba, anan ƙasarmu ma anayi, anya kuwa in nayi kuɗi zan iya tafiya da ke ƙasar waje? tab anan zan miki gini abirni ki zauna"

Gwoggo tace "ja'irar yarinya to wallahi ƙafata ƙafarki ai ko bangon duniya zaki sai na biki", ta sake cewa ni dai kizo ki
 karɓo min ruwan Bature"

Ta dau hijabin ta ta fice , tana isan shagonsa ko tayi sa'ah yana nan zaune kuma shi kaɗai, tace "akwai ruwan rober?, dajin muryanta yace "ke Deeje meye haka, ko sallama babu? wallahi har kin firgitani" 

Nace "ai ba sallama nazo yi ba, sayan abu ne ya kawo ni in kuma baza abani ba na ƙara gaba"

Yayi murmushi ya ce "Deeje kenan" dan yasan kaf ƙauyen nan babu shagon da suke sayar da ruwan rober sai shi kuma yasan haline ya motsa. Kuma gashi tun randa tazo yana ganin ta ɗan girma yaji kamu da sonta. Yace "haba dai Deeje me yayi zafi shi ba wuta ba? ba dai ruwan rober ba akwai, ya ɗauko min na miƙa masa kuɗin amman yaƙi ansa wai ai Gwaggo tashi ce. Na juya zan bar wajen yace "yauwa DEEJEE jimana" na juyo ina kallonsa ya wani karkata kansa gefe, sannan ya ce "akwai abin da nake son faɗa miki ko ya zaki jisa?". Nace "Salisu faɗi damuwarka idan me yuwa ce to in kuma ba me yuwa ba ce inyi gaba"

Yaja dogon numfashi yace "ina sonki Deeje kuma da Aure ni in kin amince ma ko gobe a daura"

Nace "Salisu anya kuwa kanka ɗaya ni kake so kuma da Aure? sannan idan na amince gobe za a daura, to ban amince ba in kuma na dole ne sai ayi mugani"

Yace "haba Deeje baki fahimce ni bane wallahi ina son ki Deeje kuma,

 Nace "Salisu Auren ne ma nace ba zan yi ba, to ma ya kake so nayi da karatuna ne, kuma ma dududu shekarun nawa nawa nake?, 15yrs ne fah"  Ya katseni da cewa "to Deeje in baki aureni ba wa zaki aura ni na yarda muyi aure a haka ko da ba dangin ubanki kinga ai na rufa miki asiri"

Kut na daidai ta tsayuwana na kallesa sama da ƙasa duk da wajen ba wani haske ne dashi ba nace "to yanzu na fahimci inda ka dosa, to bari kaji ko maza sun ƙare a duniya ba zan aure ka ba" naja wani dogon tsaki na wasa masa kuɗin nayo gida, ina shiga gida na fashe da wani matsanancin kuka. 

Ba ƙaramin razana Gwaggo tayi ba da ganin yanayina ina isowa na faɗi gabanta ina kuka, Tace "me ya faru Deeje kin fita kina farin ciki kuma kin shigo min da kuka wai menene haka?"

Cikin kuka nace "Gwaggo wacece ni kuma su waye iyayena? meyasa bama tare da ko da dangin ɗaya daga cikin iyayena ba?

Ai Gwaggo ba ƙaramin kaɗuwa tayi ba dajin tambayoyin da jikarta Deeje tayi mata tab wannan shine ranan wanka ba a boyen cibi. Abin da yake binne yau za a tonosa tab to ta ina ma zata farabaiwa Deeje amshoshin tambayoyinta. Amman yau yakamata ta faɗawa Deeje asalin WACECE ita.

Wani dogon numfashi Gwaggo ta ja sannan ta sauke ajiyar zuciya, ta kurawa jikarta idanu ko ta yaya Deeje za ta ɗauki wannan al'amarin?

Tace "Deeje da farko ina me miki nasiha da ki yarda da ƙaddara mai kyau da mara kyau, sannan Allah yana iya jarabtan bawansa ko ta wane hali kuma babu wanda ya isa ya gujewa hakan. Sannan ina so kisani ni mai kaunar ki ce ko a wane irin hali kika sinci kanki, ba zan taba gujemiki ba, Deeje kece rayuwa ta, zan sanar da ke labarin yadda akayi kika dawo hannuna kuma abinda na sani shi zan faɗa miki. 

Babu wata alaƙa ta jini a sakaninmu, ke ba jikata tajini bace, a zahiri ke jikatace amman a baɗini ke ba kowata ba, asalima a hanya muka haɗu, kuma ni karan kaina ban san asalin iyayenki ba"

Wani razani da firgici nayi da jin kalaman Gwaggo, gaba ɗaya hankalina ya tashi, to ya akayi na dawo hannunta? kuma meyasa ta reneni?

Kamar Gwaggo tasan me nake ayyanawa a cikin raina tace "yanzu zaki ji yadda akayi kika dawo hannuna"

 _LABARIN DEEJEE_ 

Asalin sunana Hajara, kuma a birni nake da zama, na auri maza har biyu amman duk rasuwa su kayi ba wanda muka rabu.To tun daga wannan ban sake yin aure ba, sai na fara neman na kaina. Na fara saro kaya daga birni sai na kawo ƙauyen kukawa na sai da ranar cin kasuwa.

Bana manta wata Asabar  da wani sabon al'amari ya faru dani kuma shine sanadiyyar haɗuwa ta dake. Kuma ana gobe cin kasuwa, dama anan nake zuwa na kwana a tashan mota, gari yana wayewa sai nazo cin kasuwan lahadi na nan kukawa.

To sai a wannan ranan asabar aka yi ruwa kamar da bakin ƙwarya, Kuma ga hanya duk chaɓi da taɓo babu yadda mota zata wuce, sai direba ya dire mu baki ɗaya a gefen gari, dan mu ƙarasa da kafar mu.

Ina cikin tafiya sai naji bawali ya kamani, sai na sami ɗan wani maraɓa na rabe nayi, sai naji wucewar mutum aguje, na ɗan tsorata dan garin ya soma duhu magrib ya kawo kai. 

Nace "wayene? Sai naga matar ta juyo cikin sauri ta zo inda nake tana isowa ta danƙa min yarinya ƴar shekara biyu tace min ga wannan ki riketa amana kuma dan Allah kada ki tambayeni ko daga ina nake". Na kura mata idanuwa sanye ta ke da kayan sarauta ajikinta da alamu daga gidan sarauta take. Zan yi magana muka ji kamar ana dosowa inda muke a tsorace tace "sune fah dan Allah ku gudu", sai nayi yadda tace, ina barin wajen sai naji muryoyin wasu mutane suna tambayarta cikin daga murya suka ce "ina yarinyar take" sai kuma ta ce dasu "nima ban sani ba, ɗaya daga cikin su ya wanketa da mari, ta faɗi ƙasa, ɗayan yace "to tun da ita bata nan hukuncin da za muyi mata ya dawo kanki".

Na dan leƙo daga maɓuyata dan ganin wai suwaye waɗannan mutanen ne?, sai naga mutum biyu ne kuma sanye suke cikin kayan fadawan sarki. Ɗaya daga cikin su ya ɗago da matar sama ya shaƙota. Da ganin haka na tsora zan bar waje sai naji muryan matar tana cewa "duk abin da kai wa wani wataran zai ko ma maka, in ma mai kyau ko akasin haka, kuma su da suka baku umurnin kasheta kuma wataran da hannunsu zasu kasheku. Har tsawon yaushe zaku ɗauka suna baku umurnin kisa, kun ɗauki rai bil adadi kuma yanzu ma kuna shirin ɗaukawa, to kusani lokaci yana nan zuwa da suna ji suna gani mulki zai dawo hannun waɗan da basu su.... Bata ƙara she zancenta ba, ɗayan ya daɓa mata wuƙa aciki.

Tasa wata ƙara ta faɗi agun ban karashe ganin abinda zai faru ba na yi cikin daji. Tafe nake ko waigawa ba nayi har na iso wani dan tudu na kwantar da ke, kuma gashi anyi ruwa garin ya ɗauki damshi da raba, a zaune na kwana.

Ina farkawa sai naga ba kya numfashi, da sauri cikin ƙiɗimewa na fara neman hanyar fita daga dajin, sai ko nayi sa'ah ashe a bakin gari muka kwana na hango wani madaidai cin shago kuma da alamu magunguna ake sayarwa. Muna isowa sai naga da mutum a zaune ɗan saurayi. Ko sallama banyi ba na faɗo masa a kai, nace "dan Allah ka taimaka wa wannan yarinyar ta samu ta fara numfashi"

Ya ɗago "ya kallemu sai yace "ina iyayenta?" Nace "jikata ce kuma bata da lfy ne". Yace ina sam shi bai yadda ba wannan ba jikarki ba ce kuma da alamuma kamar sato ta kika yi, bari na sanarwa 'yan sanda. Dajin zai sanarwa da 'yan sanda gaba ɗaya hankalina ya tashi. Na duka har ƙasa ina mai roƙonsa, sai jikinsa yayi sanyi, yace "to ki faɗamun gaskiya ni kuma zan bata taimakon gaggawa" na kwashi duk abin da ya faru daga jiya zuwa wayewar gari na faɗa masa. 

Sai naga ya fini shiga tashin hankali da sauri ya bata taimakon gaggawa da ƙyar numfashinki ya daidaitu. Ya saka miki drip da wasu allurai,  Nima daga zaman jira sai bacci yayi awun gaba da ni. sai bayan la'asar na farka na ganki a hannunsa yana wasa dake, jin motsina yasa ya juyo yace dani "sunnu Gwoggo" sannan ya miƙomin ke amman fir kika ki, yayi murmushi yace "kin fi son zama anan sai kika gyaɗa kai alamun eh". 

Yace"" to Gwaggo ina kuka nufa daganan?" Nace "nima ban san inda zan je ba amman ko da ɗan rumfa na samu zan zauna aciki na wani lokaci". Yace "sunana Auwal kuma anan Kukawa nake tare da iyayena, liyi na biyun nan ne layin mu muje na kai ku in yaso sai mu nemo inda zaku zauna daga baya. 

Nayi GODIYA nace "Auwal" Yace "na'am Gwaggo" nace "ina so ka rufa wa yarinyar nan asiri kada kowa ya san ba jikata ba ce, wannan ya zamo sirri a sakaninmu" yace "in sha Allahu babu wanda zai ji"

Auwal ya kaimu gidansu, mahaifinyarsa ta karɓe mu da hannu bibbiyu. Sai da mu kayi sati guda sannan Auwal ya kama mana hayan wannan gidan, kuma ya bani jarin ya samamin inda zanfara tuyan kosai. Akai sa'ah ko ina farawa na samu karɓuwa sai ciniki nakeyi, har kika zo wannan shekarun.

Duk da Auwal bai faɗawa kowa cewa ke ba jikata bace hakan bai hana mutane segumiba wasu suce satoki nayi wasu ko cewa suke tsintarki nayi kaɗan ne dai suka amince cewa ke jikatace, wannan dalilin yasa ake kiranki da Ƴar Gwaggo"

Gaba ɗaya ilahirin jikina ya daina aiki, jina nake kamar mutum butumi, naso ace mafarki nake amman sai kuma naga fah idanuwana abude suke, wasu hawayene naji suna kwararuwa a fauska ta, Allah sarki Auwal dubi irin rashin mutuncin da nake masa ashe shi yayi min riga da wondo, in ta tsula tsiyata baya magana sai dai yayi murmushi. Sai kuma tausayin kaina ya kamani na fara tambayar kaina to ina asalin iyayena suke, to menene dalilin da yasa ake son kasheni?

Na juyo na dubi Gwaggo sai naga itama ni take kallo, na kwanta akan cinyoyinta, ina sauke ajiyar zuciya. Da gani har ita ba wanda yayi magana ahaka bacci ya dauke ni.

Gari yana wayewa bayan na kammala dukkan nin ayyu kana, sai na cewa Gwaggo zani shagon Auwal Gwaggo tace "yauwa in kin je ki gaida min shi, amman yanzu kamar yana gidansa dan kin san bayan tafiyar ki yayi aure. Na washe baki cikin murna da farin ciki, nace "kai Gwaggo Ya Auwal yayi aure amman na tayasa murna" Gwaggo tace "wallahi kuwa ai Suwaiba ya aura hadda ɗansu ɗaya, nace "tab amman yayi daccen mata".

Na fito nayi shagon Ya Auwal, ina isowa na tadda shi kadai ne a zaune yana 'yan rubuce rubucen sa na magunguna nayi sallama na shigo shagon, masha Allah shagonsa ya 
bunƙasa kuma har girman shagon aka ƙara. 

Bai ɗago ba yace "ah Deeje ce? A hankali nace "Ya Auwal ina kwana" ba shiri ko ya ɗago dan tabbar da Deeje ce ko wata ce, aiko Deeje ce. Ganin yana mamaki yasa nace "Ya Auwal ya kasuwa" haba ko mamakinsa ya sake fitowa ƙarara, yau Deeje ce ke kiransa da yaya. Sai ya ce "Deeje lfy ko?" Na ce "lfy lau" yace "yauwa ɗazu naje na kammala miki registration naki nan da sati me zuwa zaku koma makaranta, idanuwanane suka ciko da ƙwalla, kawai nace  "na gode Allah ya saka da Alkhairi"

Ya sake ɗagowa a karo na uku, har yanzu mamaki bai barshi ba, yayi murmushi yace "Deeje ba komai" sai kuma yaga kamar ina cikin damuwa, Na sake cewa "ashe kayi aure?" yace "eh fah harda yarona ɗaya" Nace "Allah yaraya sa bisa musulunci, ya kuma albarkaci rayuwar sa"

Ya Auwal yanzu kam ya  daina mamaki sai jin abin yake wani iri gaba ɗaya ya maida hankali nsa kaina sai yaga kamar ƙwalla ce kwance a idanuwana yace Deeje" Na ce "na'am ya Auwal yace "lfy kam yau duk na ganki haka ina Gwaggo? Nace "lfy lau, Gwaggo tana nan tace a gaida ka. Yayi ajiyar zuciya a ransa yace ba mamaki Deeje ta fara hankali dan girma ya fara bayyana, amman inko hakane yana ma Allah godiya. A fili yace "ina amsawa"

Nace "na tafi zan yiwa Gwaggo siyayya. Yace ah to kin kyauta ga wannan ki kai mata kuyi miya dashi. Na ansa leader da ya miƙomin yace "sai a fara shirin tafiya senior secondary School ko. Nayi murmushi nace "to in sha Allahu mungode" Nayi tafiyata shiko Auwal sai mamaki yake lokaci guda na nutsu kuma fa shekaran jiya fah ya gama case nawa da Fauziyya, to ko nasihar da yayi minne ta rasani.