Page 5
by @barista
ƳAR GWOGGO
***
Book 1
Page 5
_BIRNI_
Hajjiya zulai ce zaune gaban boka Gundala, dan kai masa kayan MAHEER da kuma warin takalmi kamar yadda ya umurta.
Wani ƙwarya ya ɗauko ya jefa madubi a ciki sannan ya bar baɗa garin magani bayan yasa wani ruwa mai kama da jini. Cen sai ga wani haske ya bayyana acikin ƙwaryar.
Yace "Hajjiya ki matso ki duba dan tabbar da cewa yaron ne wannan ko bashi ba". Tace "boka Gundala ba sai na duba ba, na san shine ma, kawai kayi aikin ka.
Boka Gundala ya sheƙe da wata dariya sannan yace "an gama Hajjiya buƙata zata biya nan da kwanaki uku"
Cikin murna Hajjiya Zulai ta taho masarauta dan sanar da aminiyar ta ƙudurin su ya kusa cika. Kuma ta anso albishir na kyautar da Hajjiya Ummah tace zata bata.
MAHEER ne ya shigo side na kakarsa bayan ya dawo daga fada wajen mahaifinsa. Yana shiga ciki ya ce "tsohuwa mai ran ƙarfe barka da warhaka"
Tace "Maheeru kana nan dai da halinka da alamu ba kanzawa za kai ba. Yau kuma ina kayi tun safe nake cigiyar ka.
Yayi murmushi yace "Diddi wani aiki ne mai martaba ya sakani, sai fa yanzu na kammala"
Ya sake cewa Diddi me zan samu ne yunwa nakeji" yayi fuskan tausayi.
Tace "Maheeru yaushe zaka yi aure? zuwa yanzu kam ya kamata ka ajiye mace, amman ka zauna zaman jiran wacce baka san ranan dawowanta ba. Wata kila ma yanzu haka bata raye".
Wani dogon numfashi yaja sannan ya sauke. Diddi ta taɓo masa inda yake masa kaikayi, tabbas ya kamata zuwa yanzu yayi Aure ko dan ya daina aikata mummunar abin da ya ke aikatawa, duk da shi ba son abin yake ba, zuwar masa yake yi.
Sai dai shi zuciyar sa ta mace ɗaya ce, kuma tun lokacin da ya rasa ta yaji baya sha'awar yin soyayya ba. Har yau bai yi wata budurwa ba kuma baya cire sammanin zuwan ta.
Yace Diddi KHAIRAT tana raye, bata mutu ba kuma inaji ajikina zata dawo gareni dan a kullum ina yawan mafarki da ita wai ta girma tana tsaye tana kallona amman bana ganin fuskanta".
"Diddi tayi salati ta ce "Maheeru kar dai gamo kayi da aljana kuma so take ta aure, wannan aljanace kuma da sunnace akan namiji basa barinsa yayi aure. Bari na sanar da mallam Haruna yayi maka rubutu".
Murmushi yayi yace "kai Diddi ni fa lafiya ta lau kuma ba wata aljana KHAIRAT ce, kuma na tabbata ita nake gani a mafarki".
Diddi tace "KHAIRAT da tun tana karama aka neme ta aka rasa shine zaka ce itace to na san zuwa yanzu ta mutu, ai indai tana raye ya ci zuwa yanzu ta dawo. Dududu shekarun ka nawa wannan lokacin da har ka san wani daɗin soyayya, in za kayi aure kayi kawai"
Ya runtse idanuwansa yana jin sonta na daɗuwa a zuciyarsa kuma yana sa ran zata dawo wata rana.
******************
Hajjiya zulai zaune take a palon Hajjiya Ummah tace "Hajjiya ai kawai ki shirya da zama uwar yarima, dan boka ya tabbata yarima MAHEER ba zai ƙara sati a wannan masarauta ba".
Hajjiya Ummah ta washe baki tace "ah to barka, kice dai mafarkina zai zamo gaske" Kawai suka jiyo shigowar Abdul Maleek ko sallama babu yana "yau wallahi sai inda ƙarfina ya kare ace na bada kayan guga kuma angoge amman na neme su na rasa, tun jiya fah nake dubawa ko an kawo miki ne Hajjiya? TSayawa yayi cikin yanayi na maye yana kallonsu. Hajjiya Ummah ta ce ban gane ba ya za ayi ace kayanka ya ɓata a matsayinka na ɗan sarki.
Ya juyo yana kallon Hajjiya Zulai yace "ke ba na miki iyaka da wannan masarautar ba, me ya kawo ki yau? Duk wannan halin da nake ciki ai kece sila. Sallaman MAHEER suka jiyo, a hankali ya shigo har ƙasa ya duka yana gaidasu. Kamar yadda suka saba ko amsawama basu yi ba balle su san ma ya shigo.
Abdul Maleek ya nuna sa da ɗan yatsa yace "kai in ko nonon mayya kasha yaci ka bar shiga harkanmu yanzu".
MAHEER yaji zafin kalman musamman da aka danganta ta wa mahaifinyar sa, ya haɗiye wani ƙaton bakin ciki, baya so ya tanka masa, ya san in dai ya maida martani to nasa laifin za a gani.
Abdul Maleek yace "Hajjiya bari naje na nemo kayana a wajen Waleed mai wanki ko dai bai aiko min ba".
MAHEER yace "ah Maleek ashe dai kayankan, nima jiya ina shigowa na tadda an kawosu harda ta kalmanka kala biyu, to dai ina ga sun yi tunanin nawane. Bari na ɗauko maka su".
Hajjiya Zulai ta ce "ban gane ba kana nufin kayansa aka kai ɗakinka?"
MAHEER "yace "eh Hajjiya
Tace "ɗauko su mu gani"
Ya mik'e ya wuce ɗakin sa, yana shiga ya tadda kayan ya ɗauko su. Ya kawowa Hajjiya Zulai ba ƙaramin ƙidimewa tayi ba da taga kayan.
Tace "mugansu, ta anshi kayan tana dubawa, su kaji muryar Maleek ya ɗebo ashar ya dire yace "na bada ta kalmi ƙafa biyu kuma naga ƙafa ɗaya da rabi to ba zayyu ba". Gaba ɗaya hankalinsu yayi kansa, "kace wari ɗaya babu?" Hajjiya Zulai da Hajjiya Ummah suka haɗa baki a tare. Ya ce "eh fah duba ku gani". Aiko suna dubawa suka ga ba wari ɗaya kuma sun tabbata shine suka kaiwa boka Gundala. Sannan kayan ma haka rigar sun kai masa wando ne yayi saura. Hajjiya ta juya tana kallon Aminiyar ta suka tsaya kallon juya. To fah in dai hakane an sami masala.
Tab wai wannan shine in zaka tona ramin mugunta kai yi shi daidai tsawonka dan wataran zaka faɗa ciki.
_************************ƘAUYEN KUKAWA_
Ana washegari zan tafi birni dan cigaba da karatuna. Na gama shirya kayana tsab na tafiya.
Gwaggo ce tai sallama ta shigo. Nace "ah Gwaggo9 baki yi bacci ba? nayi tunanin kin yi ai shiyasa ban shigo ɗakinki ba". Gwaggo tace "idona biyu ya zan yi na runtsa bayan gobe warhaka bakya nan"
Nayi ajiyar zuciya nace, "haba dai Gwaggo ai zan dawo, hakan ba yana nufin mun rabu har abada bane". Mun sha hira da Gwaggo har sai da nayi bacci sannan ta tafi ɗakinta.
Ina tashi da safe naji muryar Gwoggo da Ya Auwal suna tattaunawa akan tafiyata na fito, na taddasu zaune, na duka har kasa nace "ya Auwal ina kwana" yayi murmushi yace "lfy lau Khadijah, ya shirye shiryen tafiya?" Nace "ai na kammala yanzu wanka ne kawai ya saura".
Yace "to ki hanzarta karki makara atafi abarki". Na waro idanuwa dara dara dasu nace "ah tab aiko da da ƙafa zani birni" Muka sa dariya tare nayi bayi dan wasa ruwa.
Auwal yace wa Gwaggo "ya naga yarinyar nan kwana biyu ta kanza, ta nutsu kamar ba Deeje ba? Gwaggo tace "umto nima na fahimci haka amman kuma ina ga ko dan na bata labarin rayuwarta na baya"
Ya Auwal ya ce "garin yaya hakan ta faru?" Gwaggo tace "wannan yaron Salisu ne ko wanene ya ce wai sonta yake" Gwaggo ta kwashe yadda abin ya faru ta faɗa masa.
Ya Auwal yayi ajiyar zuciya, yaji tausayinta rashin iyaye babu dadi.
Na fito na shirya cikin sauri muka fito dan tafiya, wasu hawayene naji suna zubo min dan zan yi kewar Gwaggo ta. Ya Auwal ne yace "Deeje saura minti goma mota ta iso kizo mu tafi". Ba don naso ba haka na bisa bayansa muka tafi muna isowa mota ma ta iso ba ɓata lokaci mu kayi birni
_*BIRNI*_
GIRLS BOARDING SCHOOL. ( G B S)
S S 1A shine ajin da nake yanzu, khadija Auwal shine ake kirana dashi sunan Deeje ƴar Gwaggo an mance dashi amman ban sauya ba in an taɓo ni to bana kyalewa. Tun da na san asalin labarina sai na dan canza duk dama girma ya fara bayyana atare dani.
Tun da nazo ss1 banyi wata rigima ba dan har yanzu babu me shiga tsabgata tsorona suke ji amman kuma da sun fahimce ni da zasu san cewa ni mutuniyar kirki ce.
Matar Principal kam kullum daɗa shaƙuwa muke tana bala'in ji dani ana tashi a class nake zuwa gidan ta nayi ma ta wasu aikace-aikace tana kuwa jin daɗin hakan.
Dan haka muna zuwa ss2 tasa a ban shugaban masu kula da kitchen da kuma gidajen mallamai saboda kai musu ruwa.
Kuma hatta Principal duk aiken da zai yi waje da makaranta ni yake aikawa.
Shekaru biyu da na ƙara akan shekaruna yasa na kara girma dan akalla yanzu ina da shekara goma sha bakwai.
Kyawuna ya daɗa fitowa komaina ya chichchiko, dama ni farace kal ko taɓo babu ajikina sai taɓon Allah a ƙasan laɓɓaina, hanci kam kamar ya shige min baki ga daradaran idanuwa na masu kama da na bacci, gashi kam ba a magana da tsawon sa ya kai gadon bayana dan ko kitso banabyi kai duk wanda yasan Deeje ada yanzu ya ganta to ba zai gane ni ba.
Haka dai na maida hankali ga karatuna da kuma kula da gidan mallamai.
************************
*MASARAUTAN sarki Amadu*
Hajjiya Ummah da aminiyar ta suna ɗaki suna ta safa da marwa,
"Hajjiya Ummah tace "Zulai kin cuceni kin bada kayan ɗana a maimakon na MAHEER.
"Hajjiya Zulai ta ce "haba ƙanwata kefa da hannunki kika ɗauko kayan kika bani. Ni nawa kaiwane amman bai kamata kiga laifina ba".
Hajjiya Ummah hankali a tashe yake sai gumi take fitarwa tace "to zama bai kamamu ba, ki wuce wajen Gundala kice ansami matsala ya dakatar da aikin"
Hajjiya zulai ta san halin Gundala kuma ta san zuwa yanzu ya kammala aikinsa. Amman dan hankalin aminiyarta ta ya kwanta tace "to Hajjiya yanzu ma zan wuce wajensa.
Tana barin masarauta ta wuce sabgar gabanta dan ta san muddin tajewa boka Gundala da wannan batun to ba Hajjiya ba hatta ita sai sun fuskanci fushinsa.
Kuma yau shekaru 35 suna fama da bin bokaye kuma duk da haka sun kashe rayuka a wannan masarautar kusan mutum 20. Amman har yanzu burinsu bai cika ba kuma ba abin da suka tsinana har zuwa yanzu sai albishir na ƙarya aminiyar ta take masu.
************************
*FADAR SARKI AMADU*
Hayaniya ce ka tashi a fada anyi² Maleek yayi shuru yaƙi wai shi sam sai yarima MAHEER ya fito masa da kayansa ko kuma ayi wacce za ayi.
Mahaifinsu yace "kai Maleek ka shiga hankalinka kuma ka nemi waje ka zauna".
"Ido yayi jajir dama yasha yayi tatil sai huci yake. Ya zauna kamar yadda mahaifinsa ya umurce shi.
Sarki Amadu yace "yarima MAHEER yi min bayani mai ya faru?"
MAHEER ya kwashi duk yadda abin ya faru ya sanar wa da mahaifinsu.
Mai martaba yayi ajiyar zuciya yana kallon ɗansa maleek ko yaushe zai yi hankali. Ya jima da fahimtar irin zaman da ake yi a wannan masarautar kuma yana gab da yanke hukunci kawai dai yabar abin a ransa zuwa wani lokaci.
Yace "Maleek to kaji abin da ɗan'uwanka ya faɗa dan haka kai ne mai laifi da kayan ke hukunci ba tare da kayi bincike ba.
Cikin maye yace "a hab dama na san haka zata faru, tun muna yara shine baya laifi ni kuma saboda an tsaneni sai a daura min laifin"
MAHEER yayi murmushin taƙaici, da ba abin da ya fi tsana irin wannan mummunar aƙidan da Maleek da mahaifinyar su saka a ransu.
Isowan waleed mai gugane yasa aka yi shuru dan yasanar da yadda akayi kayan Maleek da aka gansu a ɗakin yarima MAHEER.
Walid cikin girmamawa ya ce "muna neman afuwa a yafe mana, kuskurenmu ne ɗan wajena na aiko saboda ina da uzuri shine yakawo kuma sai da nace ya kai ɗakin yallaɓai Maleek amman ya sha'afa yakai dakin yarima Maheer"
Wani wawan ashar Maleek yayi cikin muryan maye ya ce "da yake kai uzurin ka ya fi nawa dole ka aiko ɗanka, eh saboda ni ba yarima bane to da ga yau ka daina aiki a wannan masarautar.
Maimartaba ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Maleek tashi ka tafi kuma waleed zai ci gaba da aikinsa, ni nake da hurumin yanke hukunci"
Ya tafi yana laye kamar zai faɗi ƙasa yayi waje, shima MAHEER ya mik'e yayi waje.
************************
*GIRLS BOARDING SCHOOL (G B S)*
Muna tafe muna ƴar firan mu ni da Shareefa ɗiyar Principal na yadda zamu zana jarabawar ƙarshe ta gama makaranta dan yanzu mun kai ss3.
"Tace ƙawata ban baki labari ba, wancen satin bakin yi zazzaɓi ba har Abbana ya aikeni a madadinki to ina zuwa wannan haɗaɗɗen shop din, ina cikin siyayya aka fara sanarwa wai kowa yayi waje ga Yarima zai yi siyayya, niko da mamakina nace to sabon salo. Mu kayi waje sai ga wani haɗaɗɗen gaye yana taku da izza dajin mulki yawuce ciki yayi siyayyar sai da ya fito, aka barmu muka shiga. Inji shareefa.
"Kai kuka yadda niko ba yarima ba ko sarkine yazo siyayya sai na kammala duk abinda nake yi zan fita akan me za ace wai ayi waje, aiko da a ranan ina wajen zaku yi kallo. Inji Deeje.
Shareefa tace "tab ina zaki iya da wannan Yarima akwai wacce tayi gardama cewa yayi a ɗaukar masa ita ko ina aka kaita sai Allah"
Nayi wani salle na dire nace "ita taso, sun isa mulki haukane ke dai bari. Wacce rana yake zuwa siyayyar tasa?"
Shareefa tace "ance yawanci ƙarshen mako"
Nace "Allah ya nuna mana dama akwai siyayyar da mom tace zan yi mata"
************************
*MASARAUTAN sarki Amadu*
_Bayan kwanaki uku_ _da boka Gundala ya bayar_.
Wani wawan mari sarki yayi wa ɗansa maleek da ya gama sauraron yarinyar da take zaune a gabansa bayan ta gama sanar masa abin da ya kawota.
_*BIRNI*_
*MASARAUTAN sarki Amadu*
Hajjiya Ummah da Aminiyarta a gaban boka Gundala, su naso ya juya tsafin kan MAHEER amman ina boka Gundala ya ce aikin gama ya gama kuma dole ne su rungumi ƙaddararsu dan shi aiki ɗaya yake yi kuma nan da kwana uku za su ga abinda zai faru.
Sannan ya umurce su da su bar masa waje, aishi ba laifinsa bane, sai da ya ce Hajjiya Zulai ta kalli cikin ƙwarya dan tabbar da wanda yake ciki kuma taƙi hakan tace duk abinda yayi daidai ne.
Suna barin wajen boka faɗa ta ɓarke tsakanin aminai dan kuwa Hajjiya Ummah cewa ta yi da sanin Hajjiya Zulai hakan ta faru. Dan haka mai rabasu yau sai Allah.
Hajjiya Zulai tasan halin kawar ta, zata iya kashe ta a tsakiyar daji kuma ta tafi ba tare da wani farga ba ba. Kawai ta ari na kare ta ruga aguje.
Haka Hajjiya Ummah ta dawo gida jiki ba kwari, ta kasa tsaye ta kasa zaune.
Tasa danta agaba wai dan kar yafita balle yayiwa wata ciki.
Ita bata san aikin gama yari ga da ya gama.
Ɗanta tuni ya dirka wa Hauwa kulu ciki ana kiranta da kulu duniya dama sun jima suna sharholiyarsu.
Kuma kulu cewa tayi sai ta kai cikin gidansu kowa ya sani.
Har sau biyu yake aikowa akashe ta amman tana tsira tazo faɗar mai martabar kai saye ta sanar dashi.
_Bayan kwanaki uku_ _da boka gundala ya bayar_
Wani wawan mari sarki yayi wa dansa maleek, bayan yagama sauraron yarinyar da take zaune a gabansa bayan ta gama zayyana masa abinda yafaru sakaninta da Malik.
Mahaifiyar malik ce ta ce maimartaba adai bi a hankali dan gano asalin abinda ya faru kasan ɗan Adam da sharri yanzu haka ƙarya ne.
Maimartaba yace "wannan bai shafe ki ba, hukunci a hannun fada yake kuma kowa ya san dokokin wannan Masarautar".
Hukunci shine duk wanda yake cikin wannan masarautar kuma yayi wa wata ciki to dolene yabar ta na har abada.
Wannan hukuncin ba ƙaramin gigita Hajjiya ummah da ɗanta yayi ba. Ba don basu sani bane a'a kawai ba su yi tunanin za a zartar akan su ba nan kusa.
Bata taɓa shiga da na sani ba irin wannan karon, tayi na dama iya barnan da ta aikata sa tsawon shekaru 35 tana cin galaba akan mutane amman wannan karon sharrinta ya koma kanta.
Ta fara tuna irin abubuwan da ta shuka abaya na rashin imani da tausayi ta ɗauki ran mutane bil adadi dan burinta ya cika amman kash ƙudirinta bai cika ba kuma da alamu ba zata taɓa yin nasara ba.
Aka tattara ɗanta da kuma duk abin da yaza ma mallakinsa aka masa rakiya yabar masarautar kuma har abada ba zai sake dawowa ba.
Hajjiya Ummah kuka wiwi kamar ƙaramar yarinya.
Ma'aikatanta dama haushinta suke ji cewa ma suke" Ashe babu daɗi.
Ta dawo ɗaki ta fara ƙaramin hauka da alamu abinda ta tshuka zata fara girɓa.
Ta fara tuna asalin labarin Abin da ya faru a cen baya tun farkon kafuwar wannan masarautan.
To be continue
************************
*GIRLS BOARDING SCHOOL (G B S* )
Bayan la'asar na fito zan je siyayya wa matar Principal namu, na saka doguwar riga maroon color nayi Rolling da gyellen, da wata ƴar jakata da takalmina mai dan tudu.
Shareefa tace wow ƙawata kin gan ki kuwa wannan ai sai ki zubar da maza ƙasa.
Nayi murmushi nace "bar fasamin kai ƙawata.
Tace "da gaske nake"
Nace "godiya nake"
Na fito na hau ɗan sahu. Ya kai ni har bakin SHOP ɗin, aiko makil yake da mutane danko babban shop ne kuma mafi yawanci attajirai ke zuwa siyayya.
Na shigo na fara siyayya, saura min kaɗan na kammala naji anfara sanarwa ga Yarima MAHEER ya iso kowa ya dakatar da duk wani abin da a keyi, sai bayan Yarima MAHEER ya kammala nasa siyayyar.
Mutane ko sai sauri suke suna ficewa wasu harda jefar da abubuwan dake hannun su.
Ni kam ko ɗar banyi ba ballantana na masa na bar wajen.
Takun sa yake cikin izza da mulki, da ji da kai da kuma wanda kudi ya jiƙashi, yana wani ɗaga kai yana kallon kayan wajen kamar wanda ba saya zayyi ba.
Tsaki naja kuma shine ya dawo da ganinsa kaina.
Guard nashi cikin rawar jiki yazo inda nake yace
"Hala dai baki ji sanarwan da akai yi ba?.
Na juyo nace "gaskiya ban jiba ina ga sai an dauko microphone kila naji"
Yarima tsab yaji abin da nace, yayi wani murmushin mugunta ya tako inda nake yace "kina nufin zaki ja da nine?"
Na juyo a karon farko mu kayi 4eyes da shi naji ƙirjina ya ba da ras, amma na dake shima ni ya tsaya kallo, why he feels like ya taba ganin wannan face din a baya, sai dai kuma ya kasa tunawa.
Na ce "ku kuka sani ni dai siyayya nazo yi dan haka kowa yayi abin da ya kawo shi"
Na juya naci gaba da ɗaukan duk abin da akace na sayo.
Guard ɗin sa ya ɗaga hannun sa zai mareni na waro masa daradaran idanuwa na nace "kul, kana marina akan Oganka zan rama akan meye? saboda nace ba zan fitaba".
MAHEER abin ya bashi mamaki shida mace ko kallon ƙwayar idonunsa bata iyayi amman ace yau an sami wata tana cewa zata maresa, kut.
Yace "zaki san dani kike yi kuma sai kin duka har ƙasa kin bani hakuri a kan na kyaleki"
Na ce "duk tsananin hukuncin da zaka min ba zai wuce ka maidani masarautar ku a matsayin baiwa ba dan nasan baka isa ka kasheni ba".
"Tsayama tukunnah, ba ta kamarka mulki ba to anyi mutanen da su kayi mulki fiye da naka, yau ina suke?, sannan in takamarka dukiya ne, to anyi waɗanda suka ninƙa naka dukiyar yau ina suke?, in kuma taurin kai da ji da kai ne shima anyi waɗanda sun ninƙa naka. Yau ina suke sun bar duniya don haka kai ma za ayi ka ka wuce kamar ma ba ayi ka ba"
"Abin farin ciki ne ace talakawa suna alfarhari da shugabannin su ba wai su tsanesu ko su dinga guje musu ba"
Yanzu jibi, ka fitar da wasu waje su jira har sai ka kammala duk wani abin da zaka yi, batare da kasan a wane hali suke ciki ba ko sun fika buƙatar siyayya dan ciyar dana ƙasa dasu"
Jikin MAHEER yayi sanyi ya kasa furta ko da kalma ɗaya, tabbas yau ya haɗu da daidan sa, to wacece wannan yarinyar zai so jin tarihinta.
Juya wa yayi ya fito waje tsayawa yayi yana kollon mutanen da suke waje suna jiran fitowansa su shiga don biya wa kansu bukatu.
Ya wuce wajen motarsa. Su kuma suka shiga ciki dan yin siyayya.
Kalaman yarinyar ne yake masa yawo a ƙwanyarsa da kuma dara daran idanuwanta da ɗan karamin bakinta, yadda take motsa shi tana gaggasa masa maganganu da take yi babu ko shakka ko tsoro a tare da ita.
Dukar motar yayi ya cewa guard nasa, su shiga su fito mishi da yarinyar su kai masa ita REST HOUSE nasa ya basu minti 5.
Comments and share fisabilillah