BAYAN AURE

6

by @rahmakabir13

*BAYAN AURE*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 6.

Sarac Stars R Pen...✍️

Bayan ta idar da sallah ta fito ta koma kitshen dan ɗaura sanwar miyar albasa wanda Abba zai ci abinci da shi dan tasan ba ya son shinkafa da mai da yaji, kuma shi suka ci da rana ta dafashi har dare, duk da ranta a ɓace yake bata fasa yi masa miyar ba, dan kyautata masa kamar wajibi ne saboda ibada take yi, kuma tana kwaɗayin samun ladan, duk abinda yake aikatawa wannan tsakaninsa ne da Allah, sannan ba zata biye wa dokin zuciyata ba wajen kin kyautata masa dan kawai yana cin amanar ta, gwara ta fita hakkin aure wata rana sai labari. Tana zaune a kujerar tsuguno ta haɗa miyar bata tashi ba har ta kammala ta sauke, sai ta fito ta ɗauko tabarma ta shimɗa a tsakar gidan ta zauna, kana ta kunna data ta shiga WhatsApp dan ganin saƙonni, bayan sun gama shigowa sai ta ga baƙuwar number an bar masa saƙo, ta buɗe ta shiga karantawa.

Uwargida kenan, da fatan kin ga saƙo na ɗazun, ina so na tabbatar miki cewar har yau ban fita daga rayuwar Saminu ba kuma babu rana, sannan idan ɗakina ba a share yake ba to ki sa yara su share dan ina nan dawowa Hafsu sha wuyar Saminu.

Ta karanta ta ƙara ranta yana suya musamman sunan data kira ta da shi shawuyar Saminu, kuma a zahiri gaskiya ta faɗa, ta cancanci wannan sunan domin babu irin taskun da bata gani ba a gurin Saminu, haƙuri da juriya shi ne ya kawo su tsayin wannan lokacin, dan shekarar su sha tara da aure yaransu huɗu, Bilal shi ne babba ɗan shekara sha takwas ya kammala secondary yana jiran shiga jami'a, sai Yazeed ɗan shekara sha uku yana js 2, sannan Abdallah ɗan shekara 9 shi kuma yana primary 4 Sannan autarta Samira 'yar shekara biyar tana primary 1, a yanzu addu'a take Allah yasa haihuwarta ta tafi kenan duk da implant take sawa na shekara uku, in tayi expire a cire a sake saka mata wani, domin yin hakan ya zama kamar dole ne a gurinta, dan Saminu kwata-kwata baya son haihuwa, cewa yayi waɗanda suka haifa sun isa, shiyasa ba zata taɓa mance wata rana ba da ta kira shi a waya akan ya siyo mata kayan marmari tana so ta sha saboda bakinta babu daɗi, sai buɗar bakinsa ya ce. 

Kar dai ki faɗa mini ciki ne dake, to wlh baki isa ba, ina ce mun gama magana dake akan ba zaki sake haihuwa ba, me kika ɗauke ni.? shashasha ban san me nake yi ba ko, to kisan yadda zaki da shi amma ba dai a gidana zaki haife shi ba. 

Bai jira me zata ce ba ya kashe wayar, wanda a lokaci wasu zafafan hawaye suka sauka a kuncinta saboda baƙin cikin faɗan da yayi mata a cikin mutane dan tana jin maganar abokansa a kusa da shi, me ya ɗauke ta.? wawuya bata san ciwon kanta ba, tun bayan aurensu Saminu ya tabbatar mata da shi ba ɗan halak bane saboda sabbin halayyen daya tsuro mata dasu wanda bata taɓa zatonsa da shi ba, amma haka ta jure ta yi haƙuri har kawo yanzu wanda haihuwar ma ƙiri-ƙiri ya nuna baya so da ita. Sai ta sauke numfashi tana mai yin murmushin takaici, to meye ne a halinsa wanda bata sani ba dan ya cigaba da hulɗa da Zinatu, ai abu ne mai sauƙi a gurinsa, tun shi in dai mace ce jinsa yake kamar Ayu, kowace karabiti budurwarsa ce sai dai in bata yi masa ba, a yanzu tafi ƙarfin shekara rabon da ta shiga motarsa, amma kusan kullun sai ya ɗauki mace a motar ya kaita anguwa ko ya kaita ya kashe mata kuɗi a super market, ita ko bata kai wannan matsayin ba dan duk mitar da zata yi masa akan ya kaita anguwa ko wani gurin ƙiri-ƙiri zai ce yana da uzuri, haka mutane zasu zo su faɗa masa sun ga Saminu da mace a mota sun fita, to dan haka duk wani iskanci da Zinatu zata yi mata wuri ta samu, shiyasa ba tada lokacin ɓatawa akanta dan takaici kawai zata ƙara mata kawai. Bayan ta gama karanta saƙon sai ta fita ba tare da ta bata amsa ba ta yi blocking ɗinta, ranta kuma ya cigaba da zafi dan sosai taji zafin kalamanta, babu wanda ya ja mata zubewar mutunci sai Saminu, da bai bada fuska ba babu wata mace da zata takata a dalilinsa, sai ta sauke ajiyar zuciya ta cigaba da duba saƙon mutane ciki harda waɗanda suka yi oder, bayan ta gama dasu sai ta shiga group ɗin littafin KOMAI YAYI FARKO na Rahma Kabir labarin Farida da Umar, sosai littafin ke yi mata daɗi saboda rayuwar aurenta yaso yayi kama da wannan, duk da ita gaskiya Saminu ya tsare mata ci da sha bata da matsalar abinci yana wadatasu sosai har ta girka ta bawa wasu, amma in tana so taci mai daɗi dole sai ta saka kuɗinta, kuma abunda ya shafi rashin lafiyarta dana yara sai ya ga dama zai yi, batun makarantarsu kuwa kusan itace take biyan school fees ɗinsu boko da islamiyya, wani lokacin sai ya ga dama yayi cikon kuɗi in ya kakare mata, shiyasa ga Bilal nan ya gama karatun secondary yana buƙatar cigaba amma ba hali saboda har yau bata gama haɗa kuɗin registration ɗinsa ba gashi an kusa rufe wa, tayi wa Saminu magana amma yace bai da shi sai ya samu, shiyasa ta dage da amsar oder ɗin mutane dan ta samu ta haɗa kuɗin hannunta da adashen da zata amsa ƙarshen satin nan sai ta bashi yaje ya biya a nan kadpoly ya fara zuwa. A fannin sutura kuma sai salla-salla yake yi wa yara shima baifi kala ɗaya ba sai dai ta ƙara yi musu da kuɗinta, ita kuma dama bata cikin lissafinsa, dan rabonsa daya ɗinka mata kaya ta manta, kamar ma tun kayan akwatinta daya yi mata, ita ce suturarta da duk wani buƙatunta, haihuwar ta huɗu bai taɓa yi mata ɗinkin fitar suna ba ita take nimowa ta yi wa kanta, na yaro kuwa yana siya guda ɗaya a saka masa, wasu kayan haihuwar ma baya siya sai dai ita ta nima, ba zata mance haihuwar Yazeed ba saboda rashin wadatar kaya dan yaƙi siya, yace ta yi amfani dana Bilal wanda suka yi masa kaɗan, ƙarshe 'yan uwanta ne suka yi mata kwalimar kayan Yaransu na jarirai da suka yi musu kaɗan suka kawo mata, a lokacin bata sana'ar komai  shiyasa tasha baƙar wahala har sai da ya zama fita yana niman gagararta saboda ba tada kayan fita kunya, duk sun koɗe an gama sanin ta dasu, ga Bilal ya fara zuwa makaranta amma kuɗin school fees ya gagara biya, idan ta kai maganar wajen iyayenta kullun sai dai su bata haƙuri.

A watarana data je gida babanta ya bata dubu goma yace ta fara ƙulle-kullen kayan miya a gida, idan Allah yasa mata albarka sai taga jarin yayi ƙarfi tana yi wa kanta hidima, to da wannan kuɗin ta fara sayar da manja, mangyaɗa, daddawa da kukar miya, kanwa da su maggi, Kuma Allah ya duba lamarinta ta fara samun alkhairi da wannan sana'ar, daga nan sai Saminu ya fara tsiran sakar mata cefanen gidan, tare da siyan sabulun wanka da wanki, ganin zai karyata rannan daya cire kayansa ya shiga wanka ta lalube shi ta kwashe duka kuɗin ciki ta fita zuwa maƙota ta bada ajiya, ko da ya tashi fita daya laluba yaga ba kuɗin ya fara tuhumar ta, babu ja tace ita ta ɗauka a madadin bashin data tara masa na cefane da yake bar mata da siyan sabulu, nan ya fara kumfar baki tana mayar masa ya zageta ta rama sai ya rufe ta da duka, da Allah ya bata sa'a ta rarumi kwalbar coke ta maka masa, Allah ya tsare kwalbar bata fashe ba, to wannan rikicin da suka yi sai da ya koreta gida da cikin Abdallah a jikinta, da kyar dai aka sulhunta ta dawo sai kuma ya shiga hankalinsa ya fara cefane yana siyan sabulu ya bar mata sana'ar ta, saboda mahaifiyarsa sosai ta yi masa faɗa har da barazar in ya rabu da Hafsa yayi asara kuma babu ita babu shi, shiyasa ya gyara dan zaman ya daidaita. A haka zaman nasu ya miƙa har ta haifi Abdallah, to anan ne Allah ya ƙara bunƙasa samun Saminu saboda ya rabu da uban gidansa da suke harkar dillancin gidage, dama sana'arsa kenan dillancin gida da fili ko nimarwa mutane haya, ya zama ogan kansa ya buɗe shago babba da office ƙarami a ciki, ya zuba manyan kujeru a falo, ciki kuma ya zuba kayan office dan ganawa da mutane, a wani ɓangare kuma yana ta gina musu sabon gida dan inda suke ciki haya suke yi, bayan ya kammala gini shi ne suka tare, gida ne babba akwai babban falo da ɗaki biyu a ciki da bayi a kowanne, ɗaya nata ɗaya nashi, sai kuma ɗaki huɗu falle-falle a tsakar gida inda yace yayi wa yara ne ko wanne da nashi in sun girma tunda maza ne su uku, sai ɗaya ɗakin yace su barshi a matsayin na baƙi, sai ƙaton kitchen a tsakar gida da aka saka masa kitchen cabinets na zamani, sai ƙaramin store a ciki da suke zuba abinci. Haka suka fara rayuwa mai daɗi daga ita sai yaranta, sai dai basu wuce wata takwas a gidan ba Saminu ya ƙara aure, ya auri Zinatu kuma a lolacin yana sane da Hafsa tayi masa maganar hutun makaranta ya ƙare ya biyawa yara kuɗin makaranta amma ya yi mata kunnen uwar shegu, ashe ya tattara kuɗinsa ya ƙara aure, Zinatu bata tare a gidan ba haya ya kamata mata, amma tun sadda ya aureta ya daina kwana a gidan sai dai kullun safe zai zo gidan ya gansu ya bata kuɗin cefane. A haka aka shafe wata biyu bai kalleta a matsayin matarsa ba, a wannan lokacin babu irin halin da bata shiga ba dan har depression sai da ya kamata, ita kaɗai ta dinga surutu ga yawan kuka idanunta har ƙanƙacewa suka yi, yaranta tun basu fahimci abunda ke faruwa ba har suka gane, musamman Bilal da shi ne mai wayo a lokacin yana da shekara sha biyu, data gaji da wannan rashin adalcin da Saminu yake yi mata sai ta je gurin Mahaifiyarsa ta faɗa mata halin da suke ciki, tayi mata faɗa akan meyasa bata zo tun satin farko daya ƙi kwana ta faɗa mata ba, tunda bazawara ya aureta kwana uku ne musulunci ya bata, amma ace wata biyu ba miji ita dutse ce, nan Umma ta bata haƙuri tace zata yi masa magana. To a ranar da daddare sai ga Saminu ya shigo yayi kicin-kicin da fuska, wanda hakan ya tabbatar mata da saƙonta ya isa gare shi, ya kalleta a wulaƙance yace. 

Hafsa banda jaraba shekararmu sha uku da aure meye ne baki samu ba a jikina, yanzu fa yaranki uku, amma dan na ƙara aure ba zaki iya yi mini uzuri ba na ɗan lokaci na saba da Zinatu, shi ne zaki haɗa ni da mahaifiyata, to bari ki ji baki isa ki hanani abunda nayi niyya ba wata biyar na yi wa Zinatu alƙawari zata ci amarci dan haka ki jira, idan kuma jarabar taki ce ta motsa idan nazo da safe sai ki faɗa na sauke miki. 

Ba wata biyar ba ka yi shekara ma ka gani in zan mutu, wani dare ne jemage bai gani ba ai sai dai daren mutuwarsa, kaje kai da Allah dan ba zan yafe cutarwar da kake yi mini ba, a madadin yadda ka samu buɗi nima na huta amma sai ka jajibo aure duk da haka ban ɗaga maka hankali ba nayi haƙuri, amma kuma sai sabon wulaƙanci ya taso, ka nuna bani da darajar da zaka yi mini bayanin zaka kwashe watanni da matarka, sai dai na jika shiru sannan kace ba zanyi magana ba, tun bayan aurenmu Saminu kake ƙunsa mini baƙin cikin dana yi dana sanin aurenka, amma duk da haka nayi haƙuri har kawo yanzu sai dai baka sauya ba.

Ta ƙare maganar cikin kuka, Saminu yaja tsaki. 

Hafsa idan kin gaji da zama dani ga hanya nan ban ɗaure miki ƙafa ba, in banda rashin godiyar Allah meye ne bana yi miki.? Na wadata ku da abinci, wata ma rayuwar da kike ciki take sha'awa amma bata samu ba, to ni dai na faɗa miki zaki iya tafiya, kin san ni sauya mace a gurina kamar na cire hula ne na sake wata, Allah ya rufa mini asiri babu wata shegiya da zata tona mini. 

Ni dai ba shegiya bace kuma Allah ya isa haƙƙina daka danne. 

Ni kike gayawa haka.?

Ya faɗi maganar yana nuna kansa tare da ƙarasa shigowa cikin ɗakin, sai ya kai mata mari yana mai cigaba da kumfar baki da gargaɗi, yaraf Hafsa ta zauna a Cushing tana dafe da kuncinta tare da tsiyayar hawaye, haka ya gama bambaminsa ya fita. 

Hmmm Hafsat ta sauke numfashi akan tunawa da kaɗan daga rayuwar bayan aurensu da Saminu, ta ɗaga kai sama tare da shanye kukan daya zo mata, tace cikin sanyi murya. 

Alhamdulillahi ala kullu halin. 

Sai ta cigaba da duba wayar tasoma karanta littafin komai yayi farko saboda ta tura kuɗinta aka saka ta a paid group, sosai take jin tausayi Farida musamman labarin da aka ce da gaske ya faru, haka ta soma karanta page ɗin jiya da bata karanta ba, karatun ne ya ɗauke mata hankali daga tunanin damuwar da take ciki har ta ɓata lokaci.

****

Hamida.

Sai yamma lis 'yan uwanta suka tafi bayan sun gyara gidan yayi tsaf har da turaren tsinke suka kunna cikin waɗanda suka zo mata dashi, sun jira Laila ta dawo su danƙa mata amanar Hamida kamar yadda ake yi na al'ada, amma shuru bata dawo ba, haka suka gaji da jira suka wuce akan Inna Jamila da gogo Larai zasu dawo bayan kwana biyu su ga Laila. Haka suka bar Hamida ita kaɗai cike da tsoro dan gabaɗaya ta jita a takure, lallai mutum Rahma ne dan sai taji dama 'yan uwata sun jira sai mutanen gidan sun dawo kafin su tafi, ganin ba sarki sai Allah yasa ta rufe kanta a ɗaki ta kwanta a gado tana karanta wasiƙar jaki, tunanin abubuwan da suka faru tsakanin jiya da yau take yi, bata yi mamakin Hafiz ba na rufe abunda Laila tayi da zancen rashin lafiyar yaronsa, ko ita ce a matsayinsa abunda zata aikata kenan dan a samu masalaha ba tare da afkuwar wata matsala ba, dan ta tabbatar da danginta sun san me ya faru to ba za a kwashe ta daɗin rai ba, musamman Inna Jamila ba tada sauƙi tana da faɗa irin Mamansu musamman akan gaskiyarsu, to a mutu daga liman har na'ibi.

Hamida tun tana zuba ido bayan sallar magriba taga Hafiz ya dawo amma shuru har zuwa bayan sallar Isha'i, ga yunwa tana nuƙurƙusarta ga shi a yinin ranar bai kirata ba, ita sai taga kamar ya sauya mata akan kafin aurensu, dan a rana suna waya sama da sau uku, ita kuma a yanzu bai ma dace ta kira shi ba dan yafi kowa sanin yana ajiye da baƙuwa a gidansa, gwara ta zuba ido taga iya gudun ruwansa, ta haka ne zata gane a wane matsayi take a cikin gidansa. 

*Yanzu ne labari zai fara, domin daga shafin farko zuwa yau tamkar shimfiɗa ne. A ɓangare guda kuma ga labarin Uwargida Hafsah wanda rayuwar da take yi a gidanta shi ne da yawan wasu mata suke fuskanta a gidan aurensu a zahiri, dan haka ku saka labarin BAYAN AURE a matsayin na gaske domin zallar abunda ke faruwa ne. Kafin aure mace ai 'yarlele ce, amma BAYAN AURE sai abunda ta gani a ɗakinta, domin komai sauya wa yake yi akan tayi dace ko akasinsa.*

Rahma ce.