7
*BAYAN AURE*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 7.
Sarac Stars R Pen...✍️
Ƙarfe tara dai-dai ƙarar alerm ɗin agogon bango dake babban falo ya buga, wanda shi ne ya saka Hamida ɗaukar wayarta ta duba dan tabbatarwa, zuwa lokacin yunwa ya gama tsinka mata 'ya'yan hanjinta dan tun tana yin game a wayarta har sai da ta gaji, haka ta fara tunanin ko ta fito ta samawa kanta abunda zata ci ne, sai dai kuma tana tsoron kar su dawo su sameta a kitchen, dama ɗazun taje ta ɗauko ruwa tasha harta shagala da kallon kayan alatum da ke kitchen ɗin, da kuma ta fito kamar ta zauna a falo ta kunna TV, amma a matsayinta baƙuwa kuma amarya bai dace a sameta a falon ba, shiyasa ta koma ɗaki ta kwanta ta rufe ido tana tunanin da ko an turketa ba zata ce akan me take yinsa ba, domin kwakwalwarta ta ƙi bata haɗin kai saboda bata iya gane komai dan yunwa. Ƙarar hon data ji a gate shi ne ya saka ta tashi zaune ta yi kasaƙe dan ta tabbatar a gidan ne ake yi ko a maƙota, sai kuma taji buɗe gate da shigowar mota, sai ta koma ta kwanta tana mai lumshe ido zuciyarta cike da farin ciki amma bana dawowar Hafiz take yi ba sai na murnar zata samun abunda zata ci. Hafiz bayan ya daidaita parking ya fito, Laila da take gefensa a zaune taƙi fitowa sai da ya zagayo ya buɗe mata kafin ta fito tana murmushi, sai tayi gaba shi kuma ya buɗe mazaunin baya yaran suka fito ya ɗauki ledan siyayyar da suka yi yabi bayansu suka shiga falo, komai yana nan yadda suka barshi amma kuma ƙamshin falon ya sauya ba kamar yadda yake ba, Hafiz ya wuce dinning ya aje ledojin, Laila da yara suka haura sama dan su shirya su sauko su ci abinci, a lokacin Hafiz ya wuce ɗakin Hamida ya kwankwasa, daga bisani ya murɗa handle ya shiga, ya sameta a kwance kamar tana bacci sai ya yi gyaran murya.
Hamida! Hamida ba dai bacci kika yi ba.
Na'am, baccin ya soma ɗaukata amma shigowar motarka na farka.
Hamida ta bashi amsa a lokacin data tashi zaune.
Ok bani wasu mintuna zan watsa ruwa ina zuwa.
To tace masa sai ya juya ya fita tabi bayansa da kallo, wato tun ɗazu yana tare da matarsa yaje ɗaukosu ita ya barta tana zaman jiransa, anya zai iya yi mata adalci ma kuwa a yadda taga yana kafa-kafa da Laila, matar da ta ɓata musu daren farkonsu itace yake yiwa wannan kulawa kamar bata aikata laifin komai ba, sai ta girgiza kai cike da takaici dan abun ya ɓata mata rai kuma kishinta ya motsa, amma haka zata daure ta yi haƙuri dan ganin ta bisu yadda suke so, ta haka ne kaɗai zata gane halin kowa. Hafiz daya fita ya hau sama zuwa ɗakinsa yayi wanka sannan ya fito ya shirya cikin doguwar riga Jallabiya cream color ya fesa turare ya fito falo, nan ya samu Laila itama ta shirya cikin kayan bacci riga da wando masu sulɓi kuma kanta ba hula sai sumar ta data ɗaure da rebom wanda yasha ƙarin attach, Hafiz ya sakar mata murmushi itama ta mayar masa.
Kin yi kyau kamar Laila 'yar shekara sha takwas.
Au, yanzu 'yar shekara nawa ce?
Kin fini sani.
Ya faɗa yana yin hanyar fita daga falon, sai ta biyo bayansa tana murmushi, tana son Hafiz ya yabeta domin ta san zallar gaskiyarsa yake faɗa, hakan ke ƙarawa kanta girma ganin har gobe tana kan zarafinta, sam bata tsufa kuma kyawuta yana nan. Da suka sauko ƙasa ya shiga kitchen da kansa ya ɗauko plate da faranti da cup, yazo ya zubawa Hamida shinkafa fried rice sannan ya ɗaura a saman tiren, ya saka ledan kaza guda ɗaya a gefen tiren da drink da ruwan gora da wannan cup ɗin ya dubi Laila.
Bari na sallami Hamida na zo mu ci.
Haba mana Man, kawo ni na kai mata, ai wannan aiki na ne, kaga daga nan sai mu gaisa.
Ta faɗi maganar cikin murmushi amma a cikin ranta bata so ne ta barshi yaje ga Hamida saboda bata son abunda zai sashi kusanci da ita, Hafiz kuwa hakanan zuciyarsa taƙi aminta da maganarta, dan gani yake yi kamar in taje zata aikata wani abu ne da zata dagula masa lissafi, sai ya tsura mata ido alamar bai yarda da ita ba, Laila ta saki murmushi.
Beb ya kake mini irin wannan kallon.? ka yarda dani, Allah komai ya wuce na karɓi Hamida, kuma da gaske ina so na gaisa da ita.
Shi kenan, ni dai ina tuna miki karki yi abunda zai zubar miki da mutunci, kuma Hamida tana da sauƙin kai zaki ji daɗin zama da ita.
Ya ƙare maganar yana miƙa mata tire ɗin, wannan murmushin dake kan fuskarta ta ƙara faɗaɗashi wanda yake da ma'anoni da yawa, ta saka hannu ta amsa ba tare da ta kuma yin magana ba, sai ta nufi ɗakin Hamida tayi sallama, daga ciki Hamida, ta amsa sai Laila ta yi amfani da ɗaya hannunta ta buɗe ƙofar ta shiga, a tsaye taga Hamida tana kallon ƙofar, sai suka tsaya suna kallon-kallo, ko ba a fadawa Hamida ba wannan ita ce Laila, domin yadda 'yan uwanta suka faɗa mata kamanninta zahiri hakane, kuma har tafi yadda take lissafata a zuciyarta kyau, sai taji ƙafafunta suna niman gaza ɗaukarta saboda rawar da jikinta ke yi, sai dai murmushin da ta gani a kan fuskar Laila shi ne ya sanyaya mata jiki wanda yasa ta mayar mata da martanin murmushin tace cikin sauri.
Ina yini.
Haba mana Hamida ai nice da gaisuwa tunda ni ce na zo na same ki, ina yi miki sannu da zuwa gidanmu, da fatan kina cikin ƙoshin lafiya.
Lafiya lau.
Hamida ta faɗa a gajarce, sai Laila ta ƙaraso ta aje tire ɗin a kan bedside drower ta juya ta tsaya a gaban Hamida dan har lokacin a tsaye take, sai Laila ta dafa kafaɗarta.
Kiyi haƙuri da yadda abubuwa suka kasance jiya, sannan ina fatan zaki ɗauke ni a matsayin 'yar uwa, ƙawa abokiyar shawara, ga ni ga yarana ga kuma mijina, Allah yasa zaki zauna damu da amana.
In Sha Allah Anty.
Hamida ta samu kanta da faɗar haka cikin sanyin murya ta sunne kai ƙasa saboda mamaki da tsoron da ya cikata.
Nagode, ga abinci nan sai da safe ko.
Allah ya kaimu, nima nagode.
Cewar Hamida sai Laila ta saki ƙafaɗarta ta yi hanyar fita ta buɗe ƙofar ta fita, kana ta tsaya tana hura iska mai ɗumi daga bakinta, domin ba ƙaramin jarumta tayi ba da ta tsaya tayi magana da ƙazamar yarinyar da bata kai ace ta haɗa miji da ita ba, Hafiz ne daga gurin dinning ya juyo ya ɗaga mata hannu.
Hey beb yane.? Ƙaraso mana.
Sai ta zo da sauri tana murmushin yaƙe harta ƙaraso ta tsaya ta ja kujera ta zauna, ko kafin ta fito ya gama haɗa dinning ɗin har ya zubawa yara nasu abincin sun fara ci, ita kawai yake jira, bai ce mata komai ba kamar yadda itama bata ce masa ba suka fara cin abinci a natse, sai Khalil ya miƙe yana cewa.
Naƙoshi, bacci, zan je na kwanta.
OK boy ka tabbatar ka yi brush kasa kayan bacci.
Gyaɗa mata kai yayi ya wuce, ba jimawa Afrah itama ta miƙe tace.
Mom, dad good night.
OK baby.
Cewar Laila, Hafiz yace.
Ki tabbatar kin yi a addu'a kafin ki kwanta.
OK Dadee.
Afrah ta faɗa da ɗan ƙarfi tana haurawa sama da gudu, Laila itama ta aje tsokali ta ɗauki tissue tana goge baki ta kalli Hafiz tana cewa.
Nima na gama bari na je na kimtsa sai ka shigo ko.
Ina ganin sai dai muyi sallama anan dan a ɗakin Hamida zan kwana, sai nace sai da safe ko.
Ya ƙare maganar yana kai loman abinci a bakinsa, sheƙeƙe Laila ta tsaya tana kallonsa har sai da ya tsargu ya mayar da kallonsa gareta yana waro ido.
Lafiya.?
Ban gane zaka kwana a ɗakin Hamida ba, ban yi zaton akwai wannan tsarin a cikin zamanku ba.
Haba Laila, karki kawo mana rikici a daren nan, dama kina zaton zan aureta na zuba mata ido ne.? Ai haƙƙinta ne na bata lokacina kamar yadda kema zan baki.
Ya faɗa yana kurɓan ruwa, Laila ta haɗiye wani miyau tana ƙara ƙanƙance idonta akansa.
Yanzu kana nufin zaka haɗa jiki da ƙazamar yarinyar nan.? Hafiz babu haka a cikin wannan tsarin, saboda ka aureta ne ba domin haka ba.
Ta ƙare maganar cikin hucin ɓacin rai tare da miƙewa ta ja kujera ta mayar da shi yadda yake ta tsaya tana jiran amsarsa, Hafiz ya cigaba da cin abincisa yayi kamar bata gurin sai yaji tace.
Kamin shuru, me kake nufi.?
Lailaaa! bana tunanin tun farko munyi dake ba zan tara da Hamida ba, dan baya cikin sharuɗɗan da kika gindaya mini, kuma koda akwai shi a ciki to bazan amince ba, saboda bazan yi asarar kuɗina ba wajen aurota na zuba mata ido haka kurum dan saboda naki buƙatar, ni ina da feelings akanta shiyasa ma na aureta.
Ohhh hakane.?
Ta faɗa tana ja da baya cikin ɗaga hannunta duka biyun, Hafiz ya ɗage gira tare da kafaɗa.
Hakane domin zan mori halak ɗin da Allah ya azurtani da shi, zan iya yi miki komai Laila amma banda wannan, kuma maganar nan ya isa haka.
Yana gama faɗar haka ya miƙe ya fara haɗa kayan abincin ya kwashi wasu ya wuce dasu kitchen, tana tsaye har ya je ya dawo ya kwashe sauran ya kai, ya ɗauko towel ɗin kitchen ya goge dinning ɗin ya mayar, kafin ya ɗauki wayoyinsa guda biyu da keyn mota ya juya zuwa ɗakin Hamida tare da cewa Laila sai da safe wacce take ƙame a gurin kamar gunki.
....
Hamida.
Bata iya aje numfashinta ba sai bayan da Laila ta fita daga ɗakin kafin ta sauke shi da nauyi, sai ta koma gefen gado ta zauna tana kallon ƙofar, ganin komai take yi ya faru kamar a mafarki, abu ne da bata taɓa zaton zai zo a haka cikin sauƙi ba, matar data rusa tarewarta a ɗakinta jiya kuma ita ce yau ta kawo mata abinci har da magana mai daɗi.
To me take nufi.? Anya babu wata a ƙasa kuwa. Domin ruwa baya tsami banza fa.
Wani sashi na zuciyarta ya ambaci haka, sai ta kuma sauke ajiyar zuciya, amma matar data kafa mata tarihi akan ranar farkon zuwanta gidan miji ta ƙare da kwana a gidan surukai, tayi komai ba tare da an nuna mata ɓacin rai ba taci bulus, shi ne zata zo mata da sauƙin kai, to anya ko maganar data ji Suhaima tana faɗan cewar da gangan ta rufe gidan ba gaskiya bane, domin matar data kasance a gabanta yanzu bata yi kama da wacce zata aikata haka ba, ko da yake ma gashi ta nuna mata lafiyar yaron ƙalau tunda bata kawo mata maganar a matsayin uzurin abunda ya faru jiya ba, tabbas ta aikata! Amma kuma haɗuwarsu yau ya goge mata hadda ta shiga kokwanto kamar da akwai manufa, idan kuma hakane meyasa zata nima ta zauna lafiya da ita, haka lamarin ya riƙa juya mata kwakwalwa ta rasa a wani muhalli zata aje lamarin Laila, ta ɗaure mata kai tamau ta kuma yi mata dabaibayin da ba zata iya ɓullewa ba balle har tunanin ta hakaikaito mata inda Laila ta dosa. Ganin tunanin ba zai kaita ko'ina ba sai kawai ta sauke tagumin data yi ta matsa kusa da abincin ta buɗe plate ɗin da aka rufe, sai ta ja numfashi ta sauke ta ƙara baza hanci ta shaƙi ƙamshin abincin sosai, nan take yunwar da take ji ya taso mata, ta ɗauki tiren ta aza akan cinyarta ta soma aika abincin nan zuwa cikinta tare da kurɓar drink da ruwa, sai da ta kusa tada abincin kafin ta bar saura ta buɗe ledan kazar, guda ɗaya ce amma an yanyanka, ta soma ci tana lumshe ido, sai da taci kusan rabi kafin ta ƙulle sauran akan da safe zata karya da shi, sai ta aje tire ɗin abincin ta miƙe ta gyara zaman mayafinta ta ɗauki tire ɗin ta nufi ƙofa dan ta mayar kitchen, tana shirin buɗewa taji taku kamar na Hafiz yana kusanto ɗakinta, sai ta koma da sauri ta aje tiren a inda yake ta zaune tana jan mayafinta dan ya rufe mata fuska. Hafiz ne ya shigo da sallama ta amsa kafin ya zauna gefen gado ya tambaye ta taci abincin, tace ta ci, sai ya fara janta da hira wanda duk rabi na hirar aurensu ne na daga ɗaurin aure zuwa walimar da ya yi da abokansa.
******
Hafsah.
Ƙarfe shida da mintuna na yamma yaranta suka dawo daga islamiyya Bilal ya taso ƙeyarsu, dama Yazeed, Abdallah da Samira hadda suke zuwa Asabar da Lahadi na ƙarfe daya zuwa uku da rabi, daga nan sai su yi sallah a makaranta su shiga islamiyya, sai kuma shida na yamma in an tashe su su dawo gida, shi Bilal yaƙi yin haddar, kuma babu irin mitar da Hafsa bata yi ba amma yace kwakwalwarsa bata ja ba zai iya ba, haka ta haƙura bata matsa masa ba ta dage masa da zuwa islamiyya ya samu ya yi sauka, tana iya ƙoƙarinta akan yaran tunda Saminu kusan ya sakar mata ragamar gidan ne, ko laifi suka yi ta faɗa masa baya wani ɗaukar mataki, sai yace idan ita tayi musu hukunci ya wadatar shi ba lallai sai yayi ba.
Sannu da gida Mama, ina yini.
Yaran suka haɗa baki wajen gaisheta, Hafsah ta amsa fuska sake sai ta miƙe ta naɗe tabarma ta bawa Samira tace ta kai mata ɗaki sannan ta cire uniform ta zo tayi alwalar sallar magriba, tace to, sai ta nufi kitchen dan ta ɗumama shinkafa wanda da sun dawo daga masallaci zasu ci, nan taji ƙarar ƙugin tsayuwar mota a ƙofar gida wanda ta tabbatar na Saminu ne, kawai sai ta tsaya taga shigowarsa, ba jimawa sai gashi ya faɗo gidan da sallama, ta amsa kana tayi masa sannu da zuwa, ya amsa sai ta wuce kitchen shi kuma ya wuce zuwa cikin falo yana cewa cikin ɗaga murya.
Ki juye mini ruwan wanka ki kawo min sauri nake zan ƙara fita.
Aiko ban dafa ba saboda ban san zaka shigo yanzu ba.
To uban me ya saka ba za a dafa a ajiye ba duk lokacin dana dawo na yi amfani da shi, ko ke ce kike siyan gas ɗin, bana son iskanci fa.
Kayi haƙuri bari na ɗaura yanzu.
Ta faɗa cikin ɗaga murya itama, sai yace cikin tsawa.
Ki bar shi bana so.
Ya ƙare maganar yana shigewa ɗankinsa, ko da ya shiga turus yayi lokacin da idonsa ya sauka aka saƙon Zinatu a tsakiyar gadonsa, da sauri ya juya ya fito tsakar gida yana cewa.
Hafsa waɗancan kayan me suke yi a kan gadona.? yaushe na zama sa'anki da zaki riƙa yi mini ƙazanta a ɗaki.
Ba nawa bane, saƙon Zinatu ne data aiko maka, shi ne na aje maka su anan yadda zaka gansu da kyau.
Ta ƙare maganar tana fitowa daga kitchen ta tsaya suna kallon juna, nan take Saminu ya diririce dan sai yanzu ya gane tabbas na Zinatu ne saboda ya gane kalar birezian data saka ɗazun.
Rahma Ce.