8
*BAYAN AURE*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 8.
Sarac Stars R Pen...✍️
Tabbas yasan na Zinatu ne saboda ɗazun ya gani a lokacin da suke romancing juna ta zage zip ɗin doguwar rigarta, har ta zame hannu sai suka ji ana kwaɗa sallama daga ƙofar shigowa falon office ɗin, shi ne yayi sauri ya saketa ya saita kanshi kafin ya fito yayi magana da wanda ya shigo, to a lokacin ne Zinatu ta samu damar data cire birezia da pant ta saka a jaka, dan ko bayan daya sallami mutumin bai koma cikin office ɗin ba sai ya zauna a Cushing yana kwala mata kira akan ta fito nan, saboda yana tsoron ya koma ta riƙeshi da salonta har su kai ga aikata ɓarna kuma nan babu tsaro, sai ya sauke numfashi yana duban Hafsat tare da nuna ta da yatsa ya ce cikin haɗe gira.
To sai me idan na ta ne, aurenmu zan maida, ko kina ganin ban isa ba.
Haba wace ni, ai ka isa har kayi yawa, kuma nima zanfi so ka dawo da ita akan wannan gantalin da kuke yi a titi kuna zubar da mutunci...
Bata rufe baki ba Saminu ya yunƙuro yazo inda take tsaye sai dai taji saukar mari a kuncinta, kuma a dai-dai lokacin Bilal da ƙannensa suka fito daga ɗakinsu sun gama sauya kaya, sai suka yi cirko-cirko suna kallonsu dama duk sun ji hayaniyar da suka fara, Bilal da ya zo wuya yace cikin kumburo baki.
Abba me Mama tayi maka.? Haba! Haba mari fa.
Ubanka tayi min, ko zaka rama mata ne.?
Saminu ya faɗa a harzuke yana nuna shi da yatsa, Bilal yaja da baya ya tsaya a shagiɗe yana cewa.
Ni bazan rama mata ba amma dai ka daina dukanta, in baka sonta mu muna sonta...
Ni, ni Bilal kake faɗawa haka.? lallai ba shakka ka girma.
Saminu ya faɗa yana girgiza kai cike da mamakinsa, sai ya shiga kitchen da sauri ya ɗauko muciya ya fito yayo kan Bilal, shi kuma yana ganin haka sai ya ari na kare ya ruga ƙofar gida yana ƙunƙuni, Saminu ya bishi ya tsaya yana kallon Bilal da yake kumbura baki irin na 'yan daba.
Dan ubanka zan gyara maka zama, idan kuma Uwarka ce take gaya maka kayi min rashin kunya to duk zan haɗa ku naci kaza kazanta ubanku, ɗan iskan yaro lalatacce.
Ban haifa ɗan iska ba kuma ba zan taɓa haifan lalatacce ba.
Hafsa ta faɗa cikin kaushi murya, Saminu ya dawo cikin gidan ya tsaya yana kallota yana girgiza kai.
Gabaɗaya zaku san ni kuka yi wa haka, mutanen banza kawai.
Ya ƙare maganar yana jefar da muciyar a kasa sai ya juya ya fita waje kamar zai tashi sama, Hafsa ta buɗe murya tace.
An dai naɗe tabarma kunya da hauka.
Bai juyo ba bai kuma tanka mata ba ya wuce, tana jin tashin motarsa ya figa a guje wanda tasan ran maza ya ɓaci, sai dai ko ɗar bata ji ba dan in da sabo ta saba da halinsa.
Bilal kuwa masallaci ya wuce bai jira Ƙannensa ba, kuma har a zuciyarsa babu danasanin abunda yayi domin ya gaji da cin kashin da mahaifinsu ke yi wa mahaifiyarsu, tun bai yi wayo yasan kan duniya ba yake ganin wannan badaƙalar har kawo yanzu daya fahimci yanayin zamansu, kuma yaji daɗi daya mayar masa da magana, zai gane cewar yanzu ba da bane ya yi girman da zai shigarwa mahaifiyarsa faɗa musamman yadda ya bawa Zinatu lasisin da ta wulaƙanta masa uwa, to lokaci yayi da zai haɗasu su duka ya nuna musu shi ɗan halak ne. Bai yarda ya dawo gidan ba sai da aka yi sallar isha'i, domin mama ta saba masa duk runtsin ya dawo gida akan lokaci bata yarda da yawon dare ba ko hira da abokai na rashin tarbiyya. Tunda daga ƙofar gida ya gane Abbansu bai dawo ba, dan haka sai ya shiga cikin gida da sallama, ƙannensa da suke zaune a tsakar gida suna cin abinci suka amsa, sai ya wuce ɗakinsu dan ya rage kayan jikinsa, ya cire riga yabar sibgilet yana shirin cire dogon wandonsa sai ga mamansu ta ɗaga labule tana cewa.
Yanzu Bilal ka kyauta kenan da abunda kayi.? to daga yau sai yau karka ƙara saka mini baki in muna faɗa da Abbanku, babu ruwanka dan ba irin wannan tarbiyyar na baku ba, ba zan taɓa yarda na zuba ido naga ka raina shi ba domin da Uba ake ado duk lalacewarsa kuwa, kuma ka tabbatar in ya dawo anjima kazo ka bashi haƙuri, in ba haka ba zanyi mugun saɓa maka.
Tana kaiwa nan ta saki labulen ta wuce, Bilal ya dunkule hannu ya naushi iska ransa yana yi masa suya, ji yayi ya ƙara tsanar Abbansu, amma saboda ya faranta wa Mamansu dole zai sauke fushinsa yayi abunda tace dan duk duniya bashi da kamarta, daya gama ya zura jallabiya ya fito zuwa kitchen ya ɗauki abincinsa yazo inda su Yazeed suke ya zauna ya fara ci.
Ƙarfe goma da rabi, a wannan lokacin ne Saminu ya dawo gida, ya samu falon a buɗe amma da duhu sai ya saka haske wayarsa ya shiga ciki ya kunna wutar falon, yanayin shurun da yaji ya nuna alamun duk sunyi bacci, sai kawai ya rufe ƙofar ya nufi ɗankinsa ya yi shirin bacci ya kwanta dan baya buƙatar yin wanka saboda yayi a gidan wata budurwarsa, tsohuwar mace ce ta nace masa tana sonsa, kuma sai ya biye mata saboda akwai kuɗi a hannunta tana kashe masa a wajen girka masa abinci masu kyau, kuma shima yana biya mata nata buƙatar, da farko taso suyi aure amma ya nuna mata ba yanzu ba shi ne ta ɓullo masa da ya riƙa rage mata zafi, sai kuma ya yarda dan ya ci banza. A gidanta ya yi komai hatta abinci sai da ya cika tumbinsa kafin ya dawo gida. Bayan ya kwanta sai ya lalubi number ɗin Zinatu ya kira ta, ba jima ta ta ɗaga suka fara hira cikin nishaɗi tamkar a wani waje yake ba cikin gidansa ba, Hafsa taji dawowarsa amma sai ta jira ko zai zo ɗakinta yayi mata magana ta kawo masa abinci, amma sai taji shuru, kawai sai ta miƙe ta mayar da hular data zame mata a kanta, ta kunna hasken wayarta ta fito riƙe da shi zuwa ɗankinsa, sai dai tun kafin ta shiga ta ji dariyarsa yana magana da alama waya yake yi, tayi kasaƙe tana saurare sai taji yana cewa.
Ai in dai kin yarda a satin nan sai a mayar da aurenmu, in ya so nan da sati biyu saiki tare bayan na gama yi miki gyaran ɗaki, kinsan so nake na haɗe miki ɗaki ukun nan da suke jera na haɗa da sauran filin da ke baya yadda zaki samu falo mai girma da bayi a cikin ɗaki ɗaya.
Sai taji yayi shuru da alama yana sauraren magana ne, sai ya cigaba da cewa.
In dai kin yarda a sati biyu zanyi wannan gyaran domin akwai kuɗi a ƙasa karki ji komai a shirye nake, kin san ɗazu fa ba ƙaramin tada mini da hankali kika yi ba, kin tafi kin barni da tsantsar kewarki.
Ya ƙare maganar yana dariya sai yayi shuru yana saurare, Hafsa daga nan ta juya zuwa ɗaki dan ba zata jure ci gaba da jin hirarsu ba, takaici, kunci da baƙin ciki ya gama gasa mata zuciya har wani tururin zafi take ji, ba kuma na kishinsa ba sai na cewar yana da kuɗi amma yaƙi biyawa Bilal kuɗin da zai shiga poly, Kuma yace mata ƙiri-ƙiri ba shi da kuɗi, kenan ya mayar da ita sakarya wawuya bata san inda ke yi mata ciwo ba, saboda ta ɗauke masa hidimar makarantar yara ya miƙe ƙafa yana zuba sharafin iskanci da matan a waje, ko da yake idan tace ba zata biya musu ba sai lallai shi ne zai biya, to haka zasu jubge a gida ba arabi ba boko ko a jikinsa, shiyasa ta dage da neman kuɗi dan babu wani gata da iyaye zasu bawa 'ya'yansu sama da ilimin zamani dana addini tare da koya musu sana'a, shiyasa bata yi ƙasa a guiwa ba ta jajirce dan goben 'ya'yanta, ta tabbatar tana yin zubin da zata yi kyakkyawar kwasa ne a nan gaba, yanzu haka ta saka Bilal yana koyon aikin gyaran mota, Yazeed kuma yana zuwa shagon koyon ɗinki dake nan saman layinsu, Abdallah ne ta bari sai nan gaba in ya ƙara tasawa ta saka shi a koyon wani sana'ar. Haka ta shiga ɗaki ta zauna a gefen gado jikinta a sanyaye kamar an watsawa kaza gishiri, ta gama gane cewar Saminu ba zai taɓa canjawa ba domin mugu ne shi na bugawa a jarida, tabbas haƙurin data yi a da ba zata iya kwatanta rabinsa a yanzu ba, domin ta riga ta ƙuna bata tsoron ƙauri, a yanzu zata so ma ya dawo da Zinatu taga uwar sabadan ɗin da za a kwasa, dan ta tabbatar zata huta daga damuwarsa saboda zai tattara ya koma gurin amarya ne har sai ya ƙarar mata da duk wani tanadin data yi wa kanta, ita kuma ta samun damar da zata tattara duka natsuwarta gurin sana'arta da kula da Tarbiyyar yaranta.
Allah kana gani nayi haƙuri da Saminu kuma ina kan yi, ka shiga cikin lamarina dana 'ya'yana ka bani mafita.
Ta ce a fili tare da mayar da hawayen da yake ƙoƙarin zubo mata, a zuwa yanzu ta daina ɓata lokacinta wajen yi wa Saminu addu'ar shiriya domin babu alamar zai gyara rayuwarsa, shiyasa tafi mayar da addu'ar ta akanta da yaranta tare da niman mafita, domin ta gaji da wannan zaman wanda haƙurinta yana gab da ƙarewa. Haka ta kwanta ta ɓata lokaci cikin tunani, ba zato sai ga Saminu ya turo ƙofa ya shigo, sai ta rufe ido kamar mai bacci dan tun ɗazu baccin ne bai zo ba saboda tunanin data yi zurfi aciki, a hankali ya ƙaraso gurinta dan kar ya tada Samira, sai ya zauna a gefenta ya fara shafa ƙirjinta, da sauri ta bige masa hannu ta tashi ta zauna tana dubansa cikin duhun ɗakin fuska a haɗe.
Lafiya.?
Ban gane lafiya ba, kema kinsan me nake nufi, kinga ki tashi muje ɗakina dan kar mu tayar da Samira.
Yayi maganar cikin ƙasa da murya kamar ba shi ba, bata ce komai ba ta yunƙura ta sauka dan zata fi samun sakewa ta mayar masa da abunda zuciyarta ta guntsa, sai ya miƙe yayi gaba itama tabi bayansa zuwa ɗankinsa, ya samu gefen gado ya zauna yana dubanta da ta coge a ƙofar ɗaki rungume da hannunta.
Ki ƙaraso mana kin tsaya.
Saminu ina ganin zai fi ka je wajen wacce ta gama tayar maka da hankali, sai ta kwantar maka da kwarnafin abunda kake ji.
Me kike nufi.?
Saboda bazan sake amincewa da kai ba har sai kaje anyi maka gwajin jini na tabbatar da lafiyarka.
Ta ƙare maganar cikin ƙanƙance ido, Saminu daya kaɗu da maganarta sai ya miƙe tsaye kamar wanda aka tsikara, mamakinta ya cika masa zuciya domin Hafsa bata taɓa yi masa gardama ba a shimfiɗa duk kuwa da saɓanin da suka samu zata bashi haɗin kai.
Hafsa zargina kike yi.?
Ya wuce zargi domin Zinatu ta tabbatar mini da irin alaƙar dake tsakaninku, a cire maganar tsohuwar matarka ce ita, yanzu tana jerin Zawarawa ne, kuma Allah kaɗai yasan irin mutanen da take mu'amala da su, sannan ga cutuka na zamani da yawa suna yawo waɗanda ake kwasa a jikin mutanen banza, dan haka wlh Saminu ka kawo ni gaɓar da bazan taɓa iya jure baka haɗin kai ba domin lafiyata a yanzu yafi min komai.
Ta ƙare maganar tana juyawa da nufin fita daga ɗakin, sai ya daka mata tsawa.
Karki kuskura ki fita daga ɗakin nan bamu gama magana ba, sannan kina nufin ni ina da cutar HIV ne ko me.?
Ba haka nake nufi ba amma bincike shi ne zai tabbatar da akwai ko babu, domin yau na tabbatar da maganar mutane da kullum suke kawo mini zancenka an ganka kana yawo da mata a motarka, kuma saƙon da Zinatu ta aiko dashi ɗazun ya gama fayyace mini komai da komai. Idan kana son haɗin kaina muje asibiti likita ya tabbatar mini da lafiyar ka sannan.
Tana gama faɗar haka ta juya ta fice daga ɗakin da sauri, Saminu ya shiga kwala mata kira da ƙarfi amma tayi masa banza ta shige ɗaki tare da sake key ta rufe.
Rahma ce.