9
*BAYAN AURE*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Page 9.
Sarac Stars R Pen...✍️
Saminu yayi matuƙar mamakin Hafsa, bai zaci tana da wayo irin haka ba, har gobe kallon yarinya yake yi mata 'yar shekara sha bakwai da ya aura, ba zai mance yadda yake juya ta son ransa ba, sai abunda yake so take yi, tana gudun ɓacin ransa, sannan idan ta ɓata masa rai kamar ta kwanta ya takata wajen bayar da haƙuri, amma yau ita ce a gabansa take cewa sai yayi gwajin jini kafin zai raɓeta, ga dukkan alamu akwai waɗanda suka buɗe mata ido suke zugata, dan Hafsan da ya sani ba zata iya irin wanɗanan tunanin wa kanta ba, idan kuwa yayi bincike ya tabbatar da haka to tabbas rayukan kowa sai ya ɓaci, kuma a yanzu ba zai barta ba dole sai ya ɗauki mataki akanta ta yadda zata gane cewar Saminun da yana nan kawai sanyi ne yayi, haka ya kwanta yana saƙe-saƙe tare da cizon leɓe ransa a dagule, da kyar bacci ya ɗauke shi.
Da safe, wajen takwas da kwata Hafsa ta yakice baccin da ya kwashe ta tun bayan asubahi data idar da sallah ta koma, dan ita ma jiya sai bacci ɓarawo ne ya ɗauketa saboda takaicin Saminu daya cika ta. Bayan ta falo ta samu yaran sun gyara shi tsaf sunyi shara da mopping, sai ta fito tsakar gida, nan ma sun yi shara ga Yazeed yana wanke-wanke, Bilal kuma ta ji motsinsa a bayin tsakar gida yana wankewa, ta saki murmushin jin daɗin yadda kowa ya kama aikinsa ba tare da sun yi faɗan da suka saba ba, haka ta koyar da yaranta aikin gida duk da su maza ne kuma a hankali sun iya komai, abunda ya shafi shara mopping wanke-wanke hatta girki tana nuna musu wani abun, musamman in zata fita anguwa ta kan ce suyi mata jajjage ko yanka ganye kafin ta dawo. Abdallah da yake riƙe da Al-Qur'ani yana biya karatun hadda shi ne ya fara ganinta, sai ya saki murmushi.
Mama sannu da fitowa ina kwana.?
Lafiya lau Abdallah, karatun ake ta yi.?
Eh ina karanta wanda zan bada ne yau, kuma wlh tun ɗazu nake yi amma yaƙi zama.
Ya ƙare maganar kamar zai fasa kuka, tayi murmushi tana cewa.
A haka zaka cigaba da tisawa zai zauna In Sha Allah. Amma bari yayanku yazo sai kuyi karatun tare.
Ya gyaɗa mata kai yana cewa to kafin ta wuce kitchen ta samu har sun ɗaura ruwa a kan gas, sai ga Yazeed yazo ya gaisheta, ta amsa sai ya koma ya cigaba da aikinsa, ba jimawa Bilal ya zo shima ya gaisheta ta amsa kafin yace.
Ni ne na ɗaura ruwan ban san me za a yi ba, shiyasa ban saka lipton a ciki ba.
Ai ina ganin koko zamu dama sai kaje ka siyo mana fanke da ƙosai, naga lokaci ya ƙure ai da mun yi ƙosai anan gida.
Mama muyi kawai a gida ni zan wanke miki waken yanzu shape-shape.
Tace to sai ta wuce store ta ɗibo wake ta bashi, ya amsa sai suka ji Yazeed yana gaishe da babansu, wanda ya fito cikin shirin fita yana gyara mazaunin hular dake kansa sai ƙamshi yake fitarwa, da alama da ruwan sanyi yayi wanka bai jira mai zafi ba dan tun jiya ma basu haɗu da Hafsah ba sai yanzu, ko gaisuwar data saba binsa ɗankinsa tayi masa yau bata je ba. A lokacin suka fito daga kitchen gabaɗaya Bilal ya miƙa masa gaisuwa yana risinawa.
Ina kwana Abba, kayi haƙuri da abunda nayi jiya.
Hmmm haƙuri ko.? To ka jira ni tukuna.
Abban ya faɗa yana ƙara shan ƙamshi, Hafsa ta ce.
Abbansu ina kwana an tashi lafiya.?
Riƙe gaisuwarki kema ba yanzu zanyi lokacin ki ba.
Yana gama faɗar haka ya yi hanyar waje ya fita, Bilal ya wuce ya fito da turmi ya fara aikin surfe wake, Hafsa kuma ta koma kitchen ta dama koko dan ruwan ya tausa, ta duba robar sugar taga ya ƙare sai ta kwalawa Abdallah kira, da yazo tace masa ya ɗauki ɗari biyar a jakarta ya siyo gwangwanin sugar ya kawo su saka a kunu, yace to ya wuce.
Bayan kamar minti talatin har Bilal ya gama surfe wake an bawa Samira ta tafi niƙa, sai ga Abbansu ya dawo tare da wasu samari manya su uku 'yan ƙato da gora, ya shiga kwalawa Bilal kira wanda yake ɗakin Mamansu yana gyara mata gado, ya fito da sauri wanda a lokacin Hafsa ta fito daga kitchen sai duk suka yi turus suna kallonsu, Abba ya kalli ɗaya daga cikin samarin da suka shigo ya nuna masa Bilal.
Kun gan shi nan so yake ya zama ɗan iska ya gagare ni, ƙila ya fara bin 'yan shaye-shaye ne bamu sani ba, ku tafi da shi ku lallasa min shi kamar fulawar biredi.
In Sha Allah ba zan haifi ɗan iska ba, yanzu Abban Bilal abunda ka zaɓa kenan.? Madadin ka hukunta yaron nan a gida, ai bai fi ƙarfinka ba.
Karki sake ki saka mini baki a hidimar yarana, domin na fiki iko da shi, sannan idan bai fi ƙarfina ba taya zai yi mini rashin kunya a matsayina na ubansa, ai ya ɗauko hanyar lalacewa dole ne na daidaita masa tunaninsa ta yadda ba zai kuma kallon idona ya yi mini iskanci ba, sannan ƙannensa ma zasu kiyaye ni idan akwai mai niyyar yin hakan. Wlh ban haifi ɗan da zai gagare ni ba, ku tafi da shi kuyi aikin dana saka ku.
Ya ƙare maganarsa ga 'yan ƙato da gora, sai suka yi kan Bilal da ya tsuguna a ƙasa yana rokan Abbansu akan yayi haƙuri ba zai sake ba, amma haka yayi kunnen uwar shegu da shi suka kamashi yana turjewa suka fita da shi zuwa office ɗinsu dake can kan babban layi. Hafsa ranta ya ɓaci sosai amma sai taƙi cewa komai dan ba tada abun faɗa, tasan Saminu ya yi hakan ne danya ƙuntata mata ya rama abunda tayi masa jiya, saboda yasan tana mugun son 'ya'yanta, ta juya da niyyar komawa kitchen amma Saminu ya dakatar da ita da cewa.
Ki shirya ki tafi gidanku sai na nimeki. Kuma ki bar min yarana zasu iya kula da kansu.
Dama bada su nazo gidan ba, kuma bana tunanin zan tafi ba tare da hujjar tafiyata ba.
Haka kika ce.?
Ya faɗa a harzuƙe, bata tanka masa ba ta wuce zuwa kitchen ta cigaba da aikin ta, sai yayi kwafa yana kaɗa kai ya fita daga gidan.
****
Laila.
Cikin sassarfa ta haura sama wasu hawaye suna gudana a kuncinta, har wani duhu-duhu take gani saboda ɓacin rai, ta shiga ɗaki ta ɗauki wayarta ta goge hawayenta ta fara kai komo, can kuma sai ta tsaya ta shiga tunanin wacece zata kira ta faɗa mata matsalarta, sai dai kuma duk ƙawayenta babu wacce tasan mijinta ya ƙara aure sai aminiyarta wacce suke rufe sirrin juna mai suna Fadila kuma ita a yanzu bata ƙasar ba lalle in ta kirata ta same ta ba, sauran kuma ta ƙi faɗa musu ne kar suyi mata dariya saboda yadda take yawan cika baki akan Hafiz, sai ta sauke ajiyar zuciya ta yanke shawarar kiran ƙanwarta Zahida, a wannan gabar itace wacce take iya raba matsalarta da ita ta rarrasheta, ko da ta kira ta bugu biyu ta daga bata bari tace wani abu ba tace.
Zahida wlh Hafiz zai kashe ni, wai kin san cewa yayi kwana zai yi a ɗakin yarinyar nan fa, yana gaya min yana da feelings akanta shiyasa ma ya aure ta.
To anty Laila karya kike so yayi miki.? Ai ko da ace yace miki ba ya sonta bai kamata ki yarda da shi ba, domin tunda kika ga ya zage ya kashe kuɗi a auren nan to yana da interess akai, dan haka haƙuri za kiyi ki bishi a yadda yake so tunda kika ga yaƙi yarda da abunda ke kika so, a hankali zaki saba komai zai wuce.
Sai Laila ta fashe da sabon kuka da shassheƙa, Zahida ta cigaba ta bata haƙuri, Laila ta tsagaita kukan ta share hawaye tace.
OK shi kenan a wannan karan ya yi nasara akai na, nasan tunda har yayi min musu to ba zai fasa abunda yayi niyya ba, amma kuma ina da nawa sharuɗɗan da wlh dole ya yarda, in yaƙi kuma zan haƙura da zama da shi.
Ta faɗa cikin ƙarfafawa kanta guiwa, Zahira ta ɗan ware ido kamar tana gabanta ta ce.
Me za kiyi anty.? nifa wlh na gaji da wannan maganar auren Hafiz ɗin, ki yi haƙuri mana tunda tun farko ke ce kika amince masa yayi.
Shi kenan zan daure kamar yadda kowa ke faɗa, zan jure na gani ko zan iya, amma tabbas akwai wa'adin zaman yarinyar nan a gidana, zuwa yanzu zan iya aje aikina na fara Business dan na samu kan Hafiz.
Hmmm daga baya kenan ko anty, to Allah yasa zaki iya, ya kamata ki daina damun kanki tunda an riga an ɗaura, sannan duk abunda kike so Hafiz yana yi miki, wlh ni har fata nake yi na samu mijin da zai riƙa yi mini biyayya kamarsa, dan haka ki yi haƙuri dan zaki fi kowa amfanuwa da auren. Ni zan kwanta sai da safe.
Bata jira me zata ce ba ta kashe wayar dan har ga Allah ta fara gundura da halin yayarta da zafin kishin da bai da amfani, tun farko ya kamata ta ɗauki matakin da ba za a yi auren ba amma sai da ta bari yayi zata zo tana tayar musu da hankali, sai ta ja tsaki ta gyara kwanciyar ta. Laila kuwa galala tayi cike da mamakin Zahida, ko da yake laifinta da take faɗa mata komai, kuma a yanzu zata nuna mata zata iya komai ita kaɗai ba tare da niman shawararta ba, duk da ita ce abokiyar shawararta dan ba tada wacce zata yi maganar hankalinta kwance kamar Zahida, saboda anty Saudat haushin ta take ji da ta yarda Hafiz ya ƙara aure, momy kuma cewa take yi ba ruwanta tunda taji ta gani zata zauna da shi a haka, ta koma ta zauna a gefen gado waya a hannunta ta rasa wani tunani zata yi sai tayi kwafa tana cewa.
Namiji munafuki, da farko ya nuna min nice kawai zan amfana da auren amma lokaci guda ya zama tamkar hawainiya, saboda bai da kunya yake faɗa mini wai yana da feedings akan wannan kucakar yarinyar, hmmm zanyi maganinka.
Ta ƙare maganar cikin jan tsaki kafin ta hau gado ta kwanta tare da rufe ido tana cizon lebenta, bata taɓa zaton irin son da Hafiz yake yi mata zai iya kallon wata mace har ta bashi sha'awa ba, sobada ya nuna mata so irin wanda baki ba zai iya misaltashi ba, shi yasa itama ta mutu akansa ta ce sai shi, ta tsallake duk samarin ta masu lumbar susa, a gida sun nuna mata ba tsaranta bane tace ita zata mayar da shi ya zama dai-dai ita, ta bashi zuciyar ta gabaɗaya da tunanin ba zai taɓa cutar da ita ba, ta yarda da shi fiye da tunani amma lokaci ɗaya ya karya mata zuciya ya nuna mata alkawarin namiji a iya lebensa yake tsayawa baya kaiwa cikin baki balle yaje gurbin zuciya, akan mace basu da kunya basa kuma iya ɓoye kwaɗayinsu a fili, yanzu ya nuna mata ita ba tada wani amfani tunda ya gama da ita dole yayi ɗokin Amarya, shiyasa ya rufe ido har yake gaya mata maganar da ransa yayi masa, zata rama, tabbas zata jashi a ƙasa ta yadda nan gaba ko mace aka bashi kyauta ba zai amsa ba, akwai lokacin da zai san tana da amfani domin tana da babban makami wato kuɗi, kuma babansu ya na da shi sannan ya basu damar suyi wadaƙa da dukiyarsa dan nasu ne. Haka ta dinga ayyana abubuwa a cikin ranta wanda kusan babu alkhairin da yake saƙa mata sai sharri, a haka bacci mara daɗi ya ɗauke ta.
....
Washe gari.
Hamida.
A jiya ta tabbatar da aure yaƙin mata ne domin Hafiz ya biya mata wani sabon karatun da bata taɓa jin irinsa ba, wanda kwakwalwarta ta kasa juriyar riƙe bitar haddarsa, ta sha wuya, ya kuma samu yadda yake so dan bai taɓa zaton sai sameta da budurcinta ba duba da wasu 'yan matan sun gama yasar da mutuncinsa a waje, musamman ita da tayi yawon talla ya jinjina mata kwarai ya kuma yaba mata da ƙoƙarin data yi na riƙe mutuncinta bayan cuɗeɗeniya da ta yi da maza a titi, yadda ya samu gamsuwa ko a kan Laila bai samu haka ba a darensu na farko, domin Hamida ta nuna masa juriya da dauriya saɓanin Laila da ta dinga yi masa raki da kukan shagwaɓa haka ya ƙare daren cikin rarrashi. Sai da yayi wanka ya tsana kafin ya tafi masallaci sallar asuba, kuma koda ya dawo ɗankinsa dake sama ya wuce ya kwanta. Ita kuma Hamida ta samu ya haɗa mata ruwa ta gasa jiki ta kuma yi wanka, dama bata kawo zai riritata ba kamar yadda wasu suke rubutawa a labaren littafin Hausa ba, tasan a al'adar malam bahaushe babu irin wannan a rayuwarsu, sai kaɗan daga ciki da boko ya hudasu suka yi koyi da turawa, sannan ma sai so ya kai so Namiji ke ɓata lokacinsa wajen bawa mace irin wannan kulawar, sannan ita bata kai kanta da nisa ba tasan yanada matar data fita dan haka ba lallai ya shagala wajen kulawa da ita ba, ita Tama ji daɗi da ya barta ta yi wa kanta komai dan Inna Jamila ta karanta mata yadda zata kula da kanta, kuma data yi yadda ta faɗa ba ƙaramin ƙarfi da kuzari taji ba. Ta fito ta zura doguwar riga mara nauyi daga cikin kayan akwatinta da aka ciro aka jera mata a wardrobe, ta saka hijab ta gabatar da sallah, bayan ta idar sai ta kwanta ba jimawa bacci ya ɗauke ta.
Rahma ce