Chapter 16
by @khairatup01
ADNAN(The Artist)
Na
Ummulkhair S Panisau
(Khairatup)
Vote@arewabookkhiratup01
@Wattpadkhairi_muhd
Free page 16
Mami dai ɗaki ta shige ba tare da ta tsaya dogon zance ba wanka ta fara yi sannan ta ɗan kwanta bata wani jima a kwance ba kuma ta tashi ta saka wata riga mara nauyi ta saka hula ta fita falon. Ko ina fes Lamrat ta gyara mata shi sai ƙamshi falon yake yi. Ta kalli su Bilkisu na sakan biyu ta ɗauke kai ta zagaya tace "Sannun ku, na bar ku ko? Gajiya nayi na ɗan kwanta fatan kun ci abinci?"
Mimi tace "Mami ba mu ci ba."
Mami ta miƙe da kanta ta shiga kitchen ta samu Lamrat a kwance a ƙasan tiles bacci ya ɗauke ta. Hannu ta sa ta ɗan dafa kafaɗarta tace "Lamrat, ke Lamrat tashi daga ƙasan nan tashi."
Lamrat da bacci ya soma mata daɗi ta dinga magagi tana murza idanuwanta kamar wata ƙanƙanuwar yarinya.
"Mami...kin fito?"
"Tashi daga nan me yasa za ki zo ki kwanta a nan a ƙasa cikin sanyi ba ga ɗaki can ba?"
"Yi haƙuri Mami baccin ne ya zo ya ɗauke ni a nan."
"Amma yaya aka yi baki bawa baƙi abinci ba?"
"Mami ban iya irin abincin ku na yan gayu masu kuɗi ba shi yasa."
Mami taji kamar ta make mata baki sai kuma tace "Dalla tashi kina mace baki iya abinci ba ko meye?"
"Lah Mami na iya mana na iya awara da ina siyarwa ma na iya wainar fulawa na iya wake da shinkafa na iya tuwon masara miyar kalkalashi."
"Shi ne za ki ce ba ki iya abinci ba? Duk wannan ba abinci bane?"
Lamrat tayi shiru. Mami ta ɗan yi gajeren tsaki ta juya tace da ita "Wanko tukunya ki zo muyi girkin tare daga yau in kika ga ina girki kina zuwa kina tayani a haka za ki koya."
"Tom Mami." Duk yadda Mami ta ce haka tayi tana girkin tana miƙa mata abubuwa har aka gama lafiyayyiyar jellof ɗin taliya da ta ji busashen kifi da kayan veggies sai ƙamshi kitchen ɗin ya ke.
Tare suka fitar da komai kan dinning Mami ta ajiye flask ɗin ta juya tace "To ku taso ku ci abinci ya kamalla."
Sum-sum suka miƙe suka nufi dinning ɗin suka zauna suna ma Mami Sannu. Mami na murmushi ta dau plate ta zubawa Lamrat tace ta zauna ta ci da Bilkisu da Mimi suka kalli junansu suka kalli Mami sannan suka kalli Lamrat da ke jan kujera tana neman zama.. Mimi dai ta kasa jurewa tace "Ke! Kar ki sake ki zauna kusa damu."
Lamrat tace "Me yasa me na maku?"
"Baki san yar aiki bata da hurumin zama a kusa da masu gida ba?"
"Ai Mami tace ni yar ta ce ba yar aiki ba."
Mimi zata kuma magana Mami tace da ita "Ya isa shi kenan zata tashi." Ta kalli Lamrat tace mata "koma falo ki zauna. Kin gyara ɗakin Adnan amma ko?"
"Eh na gyara tun da safe."
"To ya yi."
Ta koma Falo ita da Mami suna cin abincin suna kallo.
Bilkisu ta kalli Mimi tace "Ke wai wanann ɗin wacce ce?"
"Baki ji ba mai aikin Mamin ce kin san Mami akwai iyayi ita ma sai kin yi maganin ta."
"Gaskiya na ga tana da rainin wayo Mamin."
"Ba kaɗan ba fa ta iya munafurci da iyayi."
"Ba zan lamunci iskanci ba kam Wallahi."
"Na goyi da bayan ki kam."
"Amma kina ganin zamu daidaita da Adnan kuwa ? Na ga yana da zafin kai da kiliya yadda na ji labarin sa ai ya wuce nan."
"Wallahi dai tsakani da Allah yana da wulaƙanci baki ji labarin kwanaki an kusan kashe shi ba?"
"Na ji fa."
"Taurin kai gare shi kamar jinjirin jaki."
Bilkisu tayi dariya ƙasa-ƙasa sannan ta kurɓi lemo.
"Allah da gaske fa ba shi da kirki baki ga yadda yake ma Mama rashin kunya ba."
"Maman ma bai bari ba?"
"Wallahi kuwa."
Lallai kice babban kai ne."
"Sosai ma.."
"Zan yi maganinsa kam ai zai shigo hannuna ba kyale shi zan ba dama."
"A'a kar ki raga mar ki matse shi a hannun ki sannan ne zaku zauna lafiya da juna."
"Ai babu wai mutuniyata."
Jim kaɗan motar Adnan ta shigo cikin farfajiyar gidan ya yi fakin ya fito ba tare da ya kula kowa ba ya shige ciki hannunsa da karan sigari sai kuma ya tuna daidai lokacin da ya sa ƙafarsa ta dama cikin falon Mami. Ya koma da baya ya jefar da sigarin a bayan tukwanen fulawowi ya saka mint a bakinsa ya shiga ciki da sallama.
"Assalamu alaikum."
Mami ta juya da fara'a ta amsa masa sallamar "Wa'alaikum Salam! Sannu da dawowa."
"Mami na gaji." Ya faɗa yana zama kan one seater da ke kallon Mami kafin yace wani abu kuma sai ga Ishaq ya fito cikin shiga ta fita ya kalle shi ya kalli agogon hannunsa yace "Ina zaka kuma kai?"
"Yaya ba nisa zan yi ba zamu ɗan yi hangout da abokanai na ne suna can suna jirana ba zan daɗe ba zan dawo."
Zai ce wani abu Mami ta girgiza masa kai ta juya ta kalli Ishaq tace "Kar ka daɗe don Allah."
"In sha Allahu Mamita." Ya faɗa tare da rungumeta ta ɓari ɗaya ya kuma tafa da yayan na shi ya fice. Da Kallo Adnan ya bi shi jikinsa a sanyayye yana son ya hana shi fita bai san dalili ba amma baya so ya fitan.
Lamrat ce ta fito cikin kauɗi da karaɗi tace "Mami na gama komai zan tafi."
Ya juya ya zabga mata harara ya yi tsaki ya miƙe ya hau sama suka bi shi da kallo.
Bilkisu bata san Adnan ya haɗu ba sai yanzu ɗan zaman da ya yi sai da ta ji ta gama sa'a a duniya sai ta ji ta fi kowa ba wai don dukiyar kawai take son shi ba ita fa ya gama sace mata ruhi da gangar jiki gabaɗaya. Sai dai halin ko in kulan da ya nuna mata ya sanyaya mata guiwa ta kuwa kalli Lamrat ta maka mata harara a tunaninta ita ce silar komai da ace bata zo da hauka ba ƙila ya kula ta ganin dai ba ta ita yake ba ya sa ta tashi tace "Mami zamu koma sai da safe."
Mami tace "A'a ba ku gaisa da Babana ba."
"Mami dare ya yi zamu koma watarana zamu dawo in sha Allah!"
"To shi kenan jira ni." Ta kwalla kiran Lamrat. Lamrat ta fito da sauri ta tsugunna tace "Gani Mami."
" Shiga ɗaki za ki ga wata leda ki ɗauko min ita akan gado."
"To Mami." Ta faɗa ta juya ta shiga ciki ta ɗauko ledar ta kawo mata.
"Ga shi Mami."
"Yauwa na gode."
Ta miƙawa Bilkisu ledar tana murmushi tace "Ga shi ayi kwalliya."
Bilkisu ta sunkuyar da kai ta ƙi amsa sai Mimi ce ta amsa tana godiya suka fita. Mami ta bi bayansu da kallo kawai ta juya ta kalli sama ta kalli ƙofar ɗakin Adnan ta haura saman. Kan ta shiga ciki wayar ta tayi ƙara tana dubawa ta ga Abdul ne.
"Mami yau na samu network."
"Gaisuwar kenan yayansu?"
"Afuwa Mami Barka da dare fatan na same ku lafiya?"
"Lafiya lau, Alhamdu Lillahi yaya kake?"
"Lafiya lau Mami sai Kewar gida da fama da marasa ji."
"Allah Ya baku nasara ,Ya kiyaye ku."
"Amin Ya Allah Mami."
"Mami yaya Adnan?"
"Yana nan lafiya lau."
"Ya yanayin na shi yanzu fatan ya sauya yanayin shi ya daina biyewa wannan mutanen?"
"Hmm! Ga shi nan dai akwai sauyi fiye da baya gaskiya. Ina fatan ya bar su gaba ɗaya."
"In sha Allah Mami zai bari. Ya batun auren?"
"Huh! Yanzun nan ma na raka yarinyar na rakata ko kallon ta bai yi ba fa."
"Wai zuwa tayi Mami." Ya faɗa yana dariya.
Mami tace "Ta zo fa wai gaishe ni."
"To is she okay? Ta yi miki ke?"
"Ba laifi. Ko bata min ba ka sani Daddyn ku ba zai bar maganar ba sai anyi ban san hayaniya ya aure ta in ya so sai ya auri wadda yake so a gaba."
"Allah Ya tabbatar da alheri."
"Amin."
"Zan koma ana jirana na samu chance ne nace bari na kira ki."
"To Allah Ya bada sa'a."
"Amin Mami."
Suka ajiye waya.
*
Bayan Mami ta idar da sallar asuba ta gama azkhar ɗin ta. Tashi tayi ta fita don ta ɗora ruwan tea saboda yara tuna yara da tayi ya sa ta tuna fa Ishaq ya fita kuma har tayi bacci bata ji shigowar sa ba,haka ya saka ta isa bakin ɗakinsa ta buga amma ba amsa sai ta koma ko ya tafi Masallaci har ta gama haɗa break da komai ta kuma komawa don gari ya yi haske sosai kusan takwas saura ma.
Ta kuma buga ɗakin amma ba a buɗe ba.
Sai kuma hankalinta ya tashi Ishaq baya haka baya fita ya dawo bai neme ta ba ko da kuwa tayi bacci ne zai tashe ta yace "Mami na dawo." Saman Adnan ta haura ta yi knocking bai buɗe ba sai kawai ta buɗe ta shiga da sallama a bakin ta.
Yana kwance a gado lulluɓe cikin bargo ɗakin ba haske sosai sai na rana da ke shigowa ta kunna fitilar ɗakin sai wurin ya yi wani tar ya haske. Ta sa hannu ta ja bargon na shi tace "Babana tashi."
Adnan ya ɗan yamutsa fuska ya juya ta sa hannu ta kuma dukan bayansa ya tashi yana murza ido haɗe da miƙa.
"Mami."
"Babana tashi muje ka buɗe ɗakin Ishaq ban gan shi ba ya ƙi buɗe ɗakin."
Sai a lokacin ya wartsake yace "Ban gane ba yana ina?" Ya faɗa yana saukowa daga kan gadon daga shi sai gajeren wando ya ma riga Mami fita daga ɗakin.
Bibiyu ya haɗa ya sauka daga kan benen coriidor ɗin da zata sada shi da ɗakin Ishaq ya shiga ya soma bugawa amma bai buɗe ba..
"Bai buɗe ba ko?"
"Mami anya ya dawo kuwa?"
"Ban sani ba muje waje."
Ba motarsa a gun. Ya isa gun masu guard yace "Kai Ishaq ya dawo jiya?"
"A'a Yallaɓai bai dawo ba gaskiya ban gan shi ba hasalima babu wanda ya zo."
Adnan ya cakumi wuyansa yace "Amma ka kasa zuwa ka faɗa?"
Mami ta kwace hannunsa tace "Adnan....cika shi ba wannan zaka yi ba zuwa zaka yi mu nemo Ishaq ɗauki wayar ka call him."
Suka kuma komawa ciki sama ya haura da sauri ya lalubo wayarsa ya dinga kiran layinsa amma bai ɗaga ba.
"Yaya?"
"Na kira shi amma bai ɗaga ba."
"Sake kira baya kin ɗaga waya."
Ya sake kira sau biyu amma ba a ɗaga ba ya saki tsaki a jere sau uku ya yi kamar zai yi wulli da wayar.
"Ya aka yi ne?"
"Tana ringing amma ba a ɗagawa Mami."
Shiru ya lulluɓe ɗakin. Adnan ya haɗiyi miyau yana jin wani irin abu mai nauyi a ƙirjinsa. Ba ya son ya rayawa kan sa komai tun jiya da Ishaq zai fita ya dinga jin babu daɗi a ransa bai san dalili ba. Yana ji a jikinsa akwai abinda ba daidai bane ba wani abu mai nauyi ya tsaya masa a ƙirjinsa.
Mami tace "Ko yana cikin hayaniya ne?"
Sai dai ita da kanta ta san ta faɗa ne amma ba haka bane.Hawaye suka zubo mata hankalin Mami ya tashi sosai tana jin kamar Ishaq ba lafiya ba be saba ba fita ya kwana a waje ko ya ƙi ɗaga wayarsa...
"Adnan zuciyata tana gaya min Ishaq ba lafiya ba...." Kalmomin suka tsaya mata a maƙogwaron ta ba ta so ta ƙarasa ragowar.
Shiru har azahar babu Ishaq har Lamrat ta zo ta gama ayyukan da zata yi ta lura babu lafiya a gidan sam sai dai ba ta da hurumin tambaya.
Mami ta miƙe zumɓur ɗankwalinta a hannu ta ce "Kai tashi Adnan tashi ka je ka nemo min Ishaq ba zan iya zama haka ba! Je ka nemo shi!"
Adnan bai musa ba ya ɗauki mulkin motar sa zuciyarsa na bugawa kamar zata fashe. Ya shiga mota ya fice daga gidan.
A mota ya kira layin Sahib bugu biyu ya ɗauka.
"Sahib ka taimaka ka nemo min last location ɗin Ishaq."
"To amma ,me ya faru?"
"Ka duba min dai tukunna zan gaya maka."
"Ka san bana gari amma bari na kira wani abokina duk da an hana akwai risk but zamu gwada."
"Na gode."
Ya kashe wayar ya sake kiran Ishaq wannan karon wayar a kashe take gabaɗaya.
Ya daki sitiyarin motar da ƙarfi ya yi tsaki kamar yayi tsuntsu haka ya dinga ji da ya gaji ya faka motar gefe bai taɓa jin kan shi helpless ba sai yau duk wani tunani da hange ya kasa ya sa kai ya kwanta kawai so yake ya yi kuka amma ya kasa, wani abu ya mai tsaye a maƙogwaronsa Adam apple ɗinsa sai sama da ƙasa yake yi.
Wayar shi ta soma ƙara da sauri ya ɗauka nan ya ga Sahib ne ya gaya mai adireshin ba tare da ya ba shi amsa ba ya ja mota ya yi gaba ya ajiye wayar gudu yake yi kamar zai tashi sama. Yana zuwa gun ya ji babu hayaniya, babu kiɗa, ba mutane ana ta tattara kaya ana gyara wurin.
Wani ya gani ya isa gaban shi ya nuna masa hoton Ishaq a waya.
"Ka ga wannan yaron don Allah?"
Ya kalli hoton ya girgiza masa kai kawai ya ɗaga kai zai yi magana sai ya ga Adnan tuni ya rikice ya soma murmushi kamar zai rungume shi yace "The Blaze ashe ina da rabon ganin ka a duniya Innallillhi wayyo Allah ya...."
Blaze ya juya ya sake yin wani wurin duk wanda ya tambaya bai ga Ishaq ba hakan ya sake ɗaga masa hankali.
Yana fita ya isa gun security ya nuna masa hoton ya ce "Tabbas na ga wannan yaron da wasu mutane sun shiga wata baƙar mota."
Wani sanyi ya ratsa jikinsa.
Zai fita wani security a ɗan ɗarare ya matsa kusa da Adnan ya ce "Yallaɓai." Haɗe da jujuyawa yana kallon ko Inan. Adnan yace "Ya aka yi?"
"Wanda kake nima na san me ya same shi."
Adnan ya ƙara girman idanuwan shi yace "Ka sani? Me ya faru?"
"Yallaɓai jiya dadddare wani matashi ya fito bayan wasu maza hudu majiya ƙarfi cikin shiga mai duhu suka zo a wata mota baƙa fuskokinsu a rufe suka zagaye shi jim kaɗan daga fitowar sa."
"Waɗanne mutane ne haka?"
"Ban san su ba hasalima ban ga fuskokin su ba."
Adnan ya ji ƙafafuwansa sun mai sanyi idanunsa sun sauya kala. Ya sani wanann ba ƙaramin abu bane kuma ba abin wasa bane wanann wani babban abu ne wanda dole sai ya yi taka tsan-tsan. Mutumin ya Kuma cewa "Yallaɓai wanann wayar ma daga jikin shi ta faɗo."
Adnan ya karɓi wayar ƙaramar waya ce keypad ba babbar bace ya zura cikin akwati ya shiga mota ya tafi.Ikon Allah ne kawai ya kai shi gida lafiya.
Yana isa ko fitowa bai gama yi ba Mami ta iso da Lamrat a bayan ta ita ma jiƙanta a sanyayye ba wai ta ma saba da Ishaq ɗin bane kawai yanayin da Mami ta shiga ne yake ɗaga mata hankali.
"An same shi? Ko yana cikin motar? Kai Ishaq daina wahalar dani haka fito daga cikin motar nan yau sai na zane ka...."
Adnan ya buɗe baki da ƙyar yace "Mami ba a ga Ishaq ba."
Dam ta ji zuciyarta ta buga.Ƙafafunta suka gaza ɗaukar ƙafar ta tayi gefe ta faɗi ƙasa a bazata.
"Ishaq! Ishaq! Ishaq! Ɗina ina ka shiga ka zo kana ɗagawa Mamin ka hankali kai ne fa Aura ta..."
Adnan ya kasa jura ya juyar da kan sa gefe yana jin zuciyarsa na ƙuna. Wayar sa tayi ƙara ya kasa ɗauka lamba ce bai san ta ba kuma be san me kiran ba Muryar Mami ya ji tana cewa "Ka ɗaga mana."
"Hello."
Daga can aka yi shiru.
Sai da ya kuma cewa Hello tukunna aka fashe da dariya zuwa yanzu na san bugun zuciyar ka ya sauya fiye da yadda ya dace ya buga haka nake so wannan zai zame maka izina ya kuma nuna maka ƙarfin ikona akwai saƙo yana jiran ka wataƙila ma da na kashe wayar zaka samu daddaɗan labarin da zai hana ka mantawar da Nigeria har abada." Bai iya cewa komai ba amma yana jin wani iri wayar dai aka kuma kira wanann karon ma bai san lambar ba sai dai ya zaɓi ya ɗaga saboda bai sani ba ko wayar na da alaƙa da ɗan'uwan sa ne.
Yana sa wa a kunne aka ce "Inspector Kamal Jamal ke magana shin ina magana da Adnan Muhamamd ne?"
"Shi ne." Ya faɗa yana huci.
"Kai ne ɗan uwan Ishaq?"
"Eh....ni...ne...ina yake? Me ya faru?"
Ya ɗan jinkirta kaɗan irin jinkirin nan mai tsawo ,maifirgitarwa sannan yace masa
"Ku zo ofishin yan sanda."
Numfashin sa ya ƙarasa karyewa a hankali a iya fatar leɓɓensa yace "Wanne ofishin?"
"Lagos State Command." Daganan ya kashe wayar gaba ɗaya.
Adnan ya tsaya cak kamar an dasa shi a gun wayar a hannunsa yana rawa. A hankali ya kalli Mami dake zaune a ƙasa tana kuka tana kallonsa "Me suka ce?"
Ya buɗe baki don yi mata bayani kuma sai ya ji ya rasa kalmomin faɗa sun mai tsaye a ciki sun kasa fitowa duk yadda ya bawa zuciyar sa umarnin fito da kalmomin ya kasa saboda cikin zuciyar sa ya riga da ya fahimci cewa wannan al'amarin ya wuce iya ɓacewa kawai, akwai wani sirri,akwai wani abu mai duhu, kuma Ishaq na cikin haɗari mai girma.