08
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
*08*
Asabar.
*8:30am*
Washegari ta kama asabar ɗin karshen mako ne, tun ƙarfe takwas da rabi na safe Alhaji Sheriff ya kira Habib da umarnin ya zo gida yanzu-yanzu yana son ganin shi, yana barci ne ma ya tashe shi haka nan yana tura baki da ƙunƙuni ko wanka bai tsaya yi ba ya sauya kaya ya fita.
A tunanin shi ma ko ya kira shi daga can su wuce gidan su Ummu Salma ne, sai kuma ya ji akasin haka. Domin ɗaki Baffan na shi ya saka shi yana ta yi masa faɗa da jan kunne.
"An juma za mu haɗu acan gidan su iyalin naka. Habibu kai da kanka ka zo ka same ni cikin girma da arziƙi, ka ce kun daidaita da wannan yarinya mu je a nema maka auran ta, ga shi iyayenta masu mutumci da dattako ne. Ba za ka dawo daga baya ka kunyata kanka sannan mu ma iyayenka ka kunya tamu ba, don Allah in mun je ka ba ma iyayenta haƙuri maganar ciki kuma tunda har ka ɗiga shi to sai dai ka yi haƙuri bayan ya fito duniya daga baya in har kun gama daidaitawa da matarka to wannan ruwan ku ne, ku tsayar da haihuwa har na tsawon shekarun da kuke so ba ruwan mu a aciki. Amma yanzu maganar zubar da ciki ka janye ta Habibu."
Shuru kawai ya yi yana sauraran shi, amma ba ya jin zai iya aikata abin da ya ke so bai shirya ba. Ko ma ya shirya to ba da Ummu ba amma sanin ko ya zauna yana yi ma Baffan na shi bayani ba zai gane ba shi ya sa kawai ya yi musu shuru, sai dai maganar zubar da ciki ba gudu ba ja da baya.
"To Abba in sha Allahu"
Haka Habib ya faɗa ba wai domin ya saduda ba yana nan akan bakan shi.
"Allah ya yi maka albarka."
Ya amsa da amin kansa na ƙasa.
"Abba ko za ka shirya ne sai mu je daga nan?
Habib ya tambaya nan take ya ce masa aa ya koma gida ya ɗau matarsa su haɗu acan ƙarfe goma ne kar su makara. Habib ba haka ya so ba domin shi ba ya ƙaunar ma Ummu Salma ta sake zama a kusa da shi, yadda ba ya son ta haka ya tsani ya gan ta a kusa da shi amma saboda kar ya yi masa gaddama a yanzu anan gaba ya ƙi yi masa amfanin da yake so shi ya sa ya amsa masa da to.
Yana fita daga gidan ƙanin mahaifin na sa, ya shiga mota ya bar anguwa yana hanya ya ɗau waya ya lalubo lambar wayar Ummu Salma da tuni ya daɗe da blooking ɗin ta shi ya sa ko ta kira shi ba ta samun shi, wayar tana ta ringing gabda za ta yanke ta ɗauka murya a cunkushe ta yi masa sallama da mamaki a muryanta na dalilin me ya sa Habib ya kira ta kuma yau?
"Kar ki fita ki jira ni gani nan zuwa."
Haka kawai ya faɗa lokaci ɗaya ya yanke kiran yana mai sakin tsaki shi kaɗai, ba domin yana da wata manufa anan gaba ba, da ba wanda ya isa ya saka shi zuwa gidan su Ummu shi fa ya daɗe da gamawa da ita, sai dai in ya yi gaddama nan gaba ƙwaɓarsa za ta iya yin ruwa shi ya sa yake bi a hankali a yanzu.
***
Kiran da Habib ya yi mata a waya ya ɗaure mata kai. Yaushe rabon da ya kira ta a waya har ta manta. Da man tana ɗan share falon ne ganin ya yi ƙura ta ɗan jima ba ta share ba tana fama da kanta ta ji ana kiran wayarta a ciki tana zuwa ta ga shi ne, tunda ya ce ta jira shi gabanta ya yanke ya faɗi ta kasa sukuni domin ba ta san da abin da zai zo da shi ba.
A haka ta gama sharan ta yi wanka tana cikin shiryawa ya shigo gidan bai neme ta ba ya shiga ciki sama da mintina talatin ya fito sannan tana jin ya sake fita amma bai neme ta ba, tana zaune gefen gado ta yi tagumi ya sake kiran ta a waya.
"Malama ki fito ina waje"
Haka ya faɗa a fusace kamar zai kai mata duka ta cikin wayar, jikin ta a sanyaye ta ɗau hijabin da ta fito da shi dogo jalbab, ta zura lokaci ɗaya tana rataya baƙar jakarta haka ma takalmin kafanta ma baƙi ne keys ɗin gidan ta ɗauka sannan ta fita ta kulle ƙofar baya cikin haraban gidan a can wajen get ta gan shi yana jiran ta a cikin mota.
Tana zuwa ta buɗe ta shiga a sanyaye ko kafin ta gama ma rufe ƙofar motar ya fizgi motar a guje sai da ta firgita.
Kallon shi ta yi ya haɗe fuskar nan kamar hadari, da sauri da kauda kanta saboda hawaye sun kawo mata sai ta yi saurin shanye su.
"Ina kwana."
Ta faɗa muryan ta a sanyaye, yau da ta ga Habib sai ta ji ba za ta iya ɗaukan kaddaran rasa shi ba, tana son shi kuma tana son ta ƙarishe sauran rayuwanta da shi har abada.
Da ta gaishe shi da farko bai amsa ba sai ta sake gaishe shi nan ma sai ya yi mata banza kamar bai san tana ma cikin motar ba, ita kuma tana ce sai ta gaishe shi ya amsa.
"Ina kwana Noori?
Ta sake faɗa cikin marairaicewa.
Wani kallo ya yi mata na tsana da takaici ita wai ba ta da zuciya ne haka ya faɗa a cikin zuciyarsa? Duk yadda ya ke share ta da nuna mata ba ta da wani muhimmanci a rayuwarsa bai sa har yanzu ta fahimci da gaske yake yi ba, watakila sai ya sake nuna mata matsayinta sosai wataƙila a lokacin za ta fi gane matsayin ta.
Kallon da ya yi mata ne ya sa ta kama bakinta ta yi shuru, har suka isa gidan su dake anguwan Zone 3, da suka iso ta ga bai fito daga motar ba ya dai yi parking a bakin get ɗin su, itama ganin bai fito ba sai ta zauna shi kuma ya ɗauko wayarsa yana dubawa shuru ya ji ba ta fita daga motar ba sai ya juya yana mata wani kallo cikin mamakin ta.
"Sai na ce ki fita za ki fita?
Ya faɗa yana ware mata idanuwanta da sauri Ummu Salma ta buɗe motar ta fita tana kallon shi, kauda kansa ya yi lokaci fuskar nan kamar bai taɓa dariya ba. Jikinta a sanyaye ta taka ta nufi get ɗin su, ta tura ta shiga ciki amma sai da ta tsaya a haraba ta daidaita kanta sannan ta shiga cikin gidan. Ammah da Baffa tare da Baffa Umaru suna cikin ɗakin Baffa suna ta hira can ta nufa ta shiga da sallama ta duka a gaban su tana gaishe shi.
"Auta kin iso?
Baffa ya faɗa, sai ta gyaɗa masa kai, ba su daɗe da gama karyawa ba tunda ga kayan karyawan nan a gaban su Ammah ba ta ɗauke ba. Sannan tun wajen tara na safe Baffa Umaru ya iso Jimeta.
"Sannu Ummu Salama."
Baffa Umaru ya faɗa yana kallon ta ganin yadda ta ɗan rame, yana shigowa Jimeta
Harkokinsa sosai kuma yana zuwa gidan ɗan'uwan na shi, kuma duk abin da ya danganci yaran Baffa na ba shi girman shi yana saka shi a ciki.
Kan Ummu na ƙasa ta amsa ta kasa mgana, Ammah ta kalle ta ta gefen ido kafin ta ce" Ke kaɗai kika zo? Ina shi Habibun?
"Yana waje."
"Bai shigo ba kuma?
In ji Ammah sai ta gyaɗa kanta kafin ta ce" Zai shigo daga baya."
Ammah ba ta sake magana ba ta miƙe ta kwashi farantin kwanukan da su Baffa suka yi amfani da shi ta fita zuwa kitchen.
Baffa Umaru ya sake tambayan Ummu Salma abin da ke faruwa ta sake warware mishi kamar yadda ta warware ma Baffa a farkon maganar.
"Wannan ai ba mgana ba ne, shi ma bai taki gaskiya ba."
Ya faɗa cikin ɓacin rai Baffa na gefe ya kaɗa kai kafin ya ce" Kuma tunda har an samu cikin maganar a zubar da shi ai bai ma taso ba."
"Sosai, bari Baban na shi ya ƙariso a zauna zan faɗa masa ba mu yadda da wannan tsarin ba."
Ita dai kanta na ƙasa ba ta yi magana ba ganin sun faɗa wata hiran ya sa Baffa ya ce ta je wajen Ammah kafin waliyin Habib ya iso, sai ta tashi a sanyaye ta koma ɗakin Ammah ta isketa tana shara, ta yi saurin ijiye jaka za ta karɓa da sauri Amma ta ce" Ke bar shi, ba ki jin daɗi je ki kwanta ki huta"
Fir Ammah ta ƙi sakar mata sharan dole ta haƙura ta koma ta zauna a saman kujera ta yi tagumi.
"Kin ci wani abu kafin ki fito?
Sai ta girgiza ma Ammah kai amma ba ta yi magana ba.
"Akwai kunun gyaɗa da kosai za ki ci?
Da sauri ta ce" Zan sha Ammah."
Saboda tana son ƙosai ta daɗe ma ba ta ci ba kunun ɠyaɗan ma tana son shi har ƙamshin ɠyaɗan take ji yanzu a hancin ta.
Ammah da kanta ta ajiye sharan da take yi ta je Kitchen ta zubo ma Ummu kunun sannan ta zuɓo mata ƙosan a wani faranti, ta kawo mata har ɗaki aiko ta zauna ta shan kunun tana cin ƙosan har wani lumshe idanuwanta take yi saboda da daɗi addu'a take yi a cikin zuciyarta Allah ya sa kar ta yi amai, Ammah na ta kallonta ta gefen ido. Tana sake tausaya ma rayuwar Ummu ta sake ramewa bisa ranar da ta zo har a cikin zuciyarta ta ke jin tausayin Autar nata kuma tun da ta ji wannan lamarin ba ta sake barci tun daga dare har safe ba, addua'a take yi ba dare ba rana, tana roƙon Ubangiji da kar ya kaddara ma Ummu zawarci da kaddaran aure, domin kaddaran tana da nauyi Ummu Salma ta yi ƙanƙanta da fuskanta hakan.
Allah ya taimaki Ummu har ta gama shan kunun ta da ƙosai ba ta ji amai ba Ammah kuma ta gama sharan ta ta shiga wanka kafin ta fito har Alhaji Sheriff ya iso ashe shi Habib ya jira daga waje su Baffa suka fito sai suka shigo da su, ba daɗewa sai ga Hamma Abdullahi, Ummu ba ta ji wani fargaban zuwan shi ba tunda shi ɗan ba ruwan mu ne ɗakin Ammah ya leƙo duk da sun daɗe ba su haɗu ba, ko a fuska bai yi mamakin ganin ba, ballatana ya fahimci tana cikin wani hali.
"Ina kwana Hamma"
Ummu ta faɗa tana gyara zamanta kallonta ya yi kafin ya ce" Aa Ummu ke ce?
Sai ta gyaɗa mata kai.
Gaisawa suka yi sannan ya tambayi Amma sai ta ce tana wanka ficewa ya yi duk da ya yi mamakin ganin Ummu da mijinta tare da ƙanin mahaifinsa ya san da matsala amma bai tsaya tambayan matsalan ba, mgana ya zo su yi da Baffa amma ganin sa da ɓaki ya sa kawai ya bar gidan, ƙarin mamakin shi ganin har da Baffa Umaru ya ta so daga Mubi lamarin ya girmama a cikin zuciyarsa dai ya yi fatan koma mene ne Allah ya daidaita.
Kafin Amma ta fito wanka Baffa da kansa ya leƙo falon Ammah ya kira Ummu, hijabin ta sanya sannan ta bi bayan Baffa zuwa cikin ɗakin sa. Kan ta a ƙasa ta shiga cikin ɗakin a gefen su Baffa daga hannun dama ta zauna a saman cafet sannan ta ɗan ɗago kanta tana gaishe da Alhaji Sheriff wanda ke zaune shima a ƙasan cafet gefen shi kuma Habib ne ƙansa na ƙasa kamar na gari.
"Lafiya lau, kina lafiya dai ko?
Alhaji Sheriff ya faɗa bayan Ummu ta gaishe shi.
Kanta na ƙasa ta amsa da lafiya lau.
Bayan buɗe taro da addu'a, da Baffa Umaru ya yi sai ya maimaita abin da Baffa ya kira shi ya sanar da shi kan matsalan da ke faruwa tsakanin Ummu da Habib.
"Tabbas haka ka kira ni ka faɗa mini nima, nima na kira shi na yi masa mgana. Saboda ma a samu daidaito shi ya sa na ce gwara mu haɗa su gabaɗaya."
Alhaji Sheriff ya faɗa Baffa Umaru ya amsa da haka ne Baffa dai na gefe bai saka baki ba, Habib kuma kansa na ƙasa bai ɗago ba sai yanzu ya fahimci Ummu ta ɓoye ma iyayenta wasu abubuwan. Sai da ya murmusa lalle ta yi kuskure wataƙila da ta sanar da su duka abin da ke faruwa da sun sauƙaƙa mata wasu abubuwan da suke jiran ta anan gaba.
"Yanzu maganar zubar da ciki ba ta, na yi masa faɗa sosai kuma ya yi mini alƙawarin in sha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba"
Alhaji Sheriff ya sake faɗa cikin taushin murya, Ummu ya sake kallo kafin ya cigaba da cewa" Ki yi haƙuri kin ji ko?
Sai ta gyaɗa kanta hawaye na kece mata ta saka gefen hijabin ta share da sauri.
"To Alhamdulillah mun ji daɗin da aka samu masalaha cikin lokaci. Kai Habibu abin da ka yi ba ka yi daidai ba tunda har cikin nan ya shiga ba ku ɗau wani mataki daga farko ba, to sai dai ka yi hakuri Ummu Salama ta haihu, daga baya in kuka zauna kuka samu fahimtan juna za ku iya bari sai a lokacin da kuka sake shiryawa ku sake haihuwa wannan tsarin ku ne, ba ruwan mu a ciki amma mganar a zubar da ciki bai yi daidai ba kuskure ne mu kuma a matsayin mu na iyayen ku ba za mu bari ku kauce ma hanya ba shi ya sa muka shiga ciki domin mu samar muku da masalaha kuma Alhamdulillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu."
Habib ya yi shuru yana sauraran Baffa Umaru har ya gama jawabinsa.
Baffa da ba zai yi mgana ba Baffa Umaru ya ce ya ɗan tofa wani abu mana.
"Ni ba ni da wani abin da zan ce duk abin da zan faɗa kun gama faɗa sai dai ba zan fasa tunsar da su abubuwa guda uku zuwa huɗu ba."
Habib ya kalla sannan ya kira sunan shi.
"Habibu."
Sai da ya ɗago kansa sannan ya amsa da Naam Ummu ma ya juya ya kira sunan ta.
"Auta."
"Naam Baffa."
"Ku sani aure ibada ne, kuma shi da man ibada sai an ɗaure za a samu riba, dukkan ku saboda kun aminta da juna kuke zaune a inuwa ɗaya na aure. To ina so ku sani sai kun yi hakuri kun girmama junan ku , sannan za ku samu fahimtar juna. Ku sani ibadar da kuke yi sakamakon ku na wajen ubangijin ku, saboda haka in kuka yi wani abu saɓanin umarninsa ma duk yana sama yana kallon ku. Daga karshe ina mai sanar da ku da cewa ku ji tsoron Allah. Ku zaauna lafiya ku girmama zamantakewarku Allah ya yi muku albarka ya sake kaɗe fitina a tsakanin ku."
Gabaɗaya su Baffa suka amsa da Amin, Ummu ma ta amsa a cikin zuciyarta Habib ne bai amsa ba domin kalaman Baffa sun shiga ne sun kuma fita, domin gani yake yi kamar ba su da amfani a wajen shi, bai so ya yi magana ba sai da Alhaji Sheriff ya ɗan zungure shi sannan ya ɗan yi gyaran murya yana faɗin.
"Ku yi haƙuri Baffa in sha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba."
Habib ya fada yana ɗan cije baki, Baffa ya ɗan jinjina kai kafin ya ce" Na ji daɗin haka. Ubangiji ya zaunar da ku lafiya."
Zaman bai wani ɗau lokaci ba tunda an samu matsaya, Baffa ya ce Ummu ta tashi ta bi mijinta ta koma gidan ta, tun da dalilin da ya kawo su an samu masalaha, Ammah ba ta fito ba kuma Habib bai neme ya shiga ya gaishe ta ba suma su Baffa ba su buƙaci haka ba, Ummu kaɗai ta shiga ta yi ma Ammah sallama.
"Ki kula da kanki kin ji ko?
Sai ta gyaɗa ma Amma kai kafin ta ce" In sha Allahu Ammah"
Daga nan suka yi sallama har ƙofar gida su Baffa suka raka su, Alhaji Sheriff ya shiga motarsa shi ya fara tafiya sannan su daga baya, har sun shiga mota Baffa ya ƙwanƙwasa ma Habib gilashin mota ta bangaren sa, bayan ya zuge gilashin Baffa ya kalle shi lokaci ɗaya yana kallon Ummu kafin ya kira sunan shi.
"Habibu"
Ya amsa ƙansa na ƙasa amma a cikin zuciyarsa faɗi ya ke yi an fa dame ni
"Kai ne da kanka ka zo ka ce kana son Auta na kuma ba ka ita cikin yaƙinin cewa za ka iya riƙe mini ita amana. Ko ba haka ba?
"Haka ne"
"To ina so ka sani amanarta da na baka tun ranar da ta tashi a ƙarƙashin ikona na ke so ka sake tunawa. Habibu kar ka saka na ji na sare bisa yaƙinina akan ka, don Allah ka riƙe mini Ummu bisa amana da gaskiya."
Baffa ya ƙarishe faɗa cikin magiya, Habib ya kalle shi yana masa mirmishin yaudara da bai kai zucci ba kafin ya ce" In sha Allahu Baffa"
Baffa ya ji daɗi har ya miƙa masa hannu suka sake musabaha yana ɗaga musu hannu suka bar ƙofar gidan Baffa Umaru yana gefe kamar an kira shi a waya ne yana ta mgana.
Suna fita daga kwanar anguwan Habib ya kalli Ummu kafin ya ce" Me ya sa kika ɓoye ma iyayenki gaskiyan manufata a kan aurana da ke?
Ummu ta ɗago tana kallon shi cikin mamaki murna take yi na ganin komai ya daidai ta tsakanin ta da Habib amma kalamsa sai suka ruguza murnan ta da saka ranta.
"Me ya sa ba ki faɗa musu cewa bana son ki ba sannan kin rufe musu ba auran soyayya na yi da ke ba, auren shaa'awa ne. Me ya sa ba ki sanar da su gaskiyan mganar ba?
Ya sake jefo mata tambayoyi, kanta na ƙasa tana wasa da gefen hijabinta ta ce" Saboda ina tunanin ba gaskiya ka faɗa ba, kana dai fadin haka ne saboda na ƙi bi umarnin ka na zubar da cikin jikina."
Habib ya kece da wata dariya kafin ya ce," Har yanzu ke a tunanin ki wasa na ke yi dake Ummu Salma?
Lalle ko ba ki da hankali na kuma yadda ke ɗin shashasha ce."
Ya fada har yana buga sitiyarin mota, Ummu ta kalle shi idanuwanta da hawaye kafin ta ce" Ka kirani da kowani suna ban damu ba. In dai har zan cigaba da zama a ƙarkashin ka, sannan zan tsira da cikin jikina na yarda ka kirani da kowa ni suna har wanda ma ya fi shashasha"
Kallon ba ki da hankali yake yi mata ita kuma kawai sai ta kece masa da kuka.
"Habib ka san ina son ka? Kai ma kana sona me ya ka sauya! Ni ce fa Ummu salman ka?
Ta ƙarishe faɗa cikin kuka, sai ya sake yin dariya kafin ya ce" Lalle ba ki da hankali."
Haka kawai ya ke faɗa lokaci ɗaya yana kallonta kuma yana dariyan haushi da takaici.
"Na ji ba ni da hankali in dai akan ka ne Habib. Na ji ka ma ce na haukace duk na yarda da haka amma don Allah ka saurara mini haka nan na azabatu don Allah Noori."
Yadda take marairaicewa ne ya sake tunzura shi, a fusace ya daka mata tsawa.
"Wallahi bana son ki, bana sha'awan sake wani sauran zama a tsakanina da ke."
ƙasaƙe Ummu ta yi tana kallon shi hawaye na kece mata wasu na zuba wasu na sake tunkuɗowa.
Gefen titi Habib ya gangara ya kashe motan ya gyara zama yana sake kallon Ummu tana kuka kamar ran ta zai fita.
"Ko zuwa gidanku da kike ganin na yi kina jin daɗin watakila na sauka daga kan kudiri na ne, to gwara ki daina murna ki dawo cikin hayyacin ki, sannan ki sake buɗe kunnuwan ki da kyau ki saurare ni."
Ya faɗa yana karkaɗa kunnunsa guda ɗaya sannan ya cigaba da faɗin" Na bi umarnin Abba ne saboda shima nan gaba zai yi mini wani amfani saboda ke kuma ba zan ɓata gobe na ba, amma wallahi tallahi ban sauka daga kan kudirina ba. Bana son ki sannan ba na son cikin dake jikin ki, sai dai ina so ki sani daga yau ba zan sake matsa miki akan zubar da ciki ba da kanki za ki yi nadamar taurin kan da kika yi mini. Ke ba ki ga komai ba yanzu ne za a fara wasan Ummu Salama."
Ya ƙarishe faɗa yana yi mata wani irin kallo har yana kashe mata ido ɗaya.
"Ka san da haka me ya sa ka amsa ma Baffa da cewa za ka riƙe ni bisa Amanar da ya ba ka?
Ta tambaye shi cikin kuka, ƴar dariya ya yi kafin ya ce" Ummu in kin koma gida ya kamata ki koma makaranta ki yi karatu mai zurfi wataƙila zuwa lokacin za ki fahimci komai."
Kallon ban gane maka ba ta yi masa sai ya girgiza kai lokaci ɗaya ya ta da motar suka fara tafiya.
"Har sai na faɗa miki maganganun babanki da na yayansa ne ma ko ƙaninsa duk sun shiga ne sun fita? Sai na faɗa miki ni da man ban karɓi amanarki tun farko ba, abin da ya sa na aure ki jikin ki, kuma sadaki na biya sannan more komai, ai amanar kenan bayan na gama amfana dake zan mayar masa dake gidansa."
Ummu ta yi ƙuru tana kallon Habib, hawaye suna kwaranya a saman kumatun ta.
"Don Allah kar ka rabu da ni Habib.'
Ta faɗa cikin matsanancin kuka.
"Kar ki damu da sauran lokaci ai ba ki gama yin nadama ba. Sai na tabbatar da kin yi nadaman taurin kan da kika yi mini sannan zan ba ki sakamakonki ki ƙara gaba. Wataƙila a lokacin za ki ji kin tsane ni har ki fahimci da gaske na ke yi wannan manufar tawa da gaske na ke yi a kan ki."
"Habib kar ka lalata mini rayuwata don Allah"
Ummu Salma ta faɗa tana ji kamar ranta zai fita daga gangan jikin ta.
"Ni kuma in ban yi haka ba tawa rayuwarce za ta lalace ki gane mana. Ni tawa rayuwar ban ma fara ba ke kuma tunda kin fara taki ki bari kawai na ƙarisa lalatata gabaɗaya kowa ma ya huta."
Ya ƙarishe faɗa har yana shafa kumatun ta, kuka kawai Ummu Salma take yi kamar za ta shiɗe mai fitar da sauti. Habib na ta dariyan nishaɗi daga ƙarshe ma sai ya ƙure wakar Auta waziri na Autar mata ba ya son jin kukan ta, tana damun shi har suka isa gida ba ta daina kuka ba ta ɗauka yana ajiye ta sai juya amma ina tana saka ƙafa a bedroom ɗin ta yana shigowa tun da ta ga ya tura ƙofa yana nufota ta san manufarsa.
"Tunda ka ce ba ka sona to jikina ya haramta a gare ka Habib."
Ta faɗa lokaci ɗaya tana kuka samnan ta ƙamƙame jikinta da hannayen ta.
"Allah? To ai saboda jikin na ki na aure ki, kin ga kenan ba ki isa ki hana ni more abin da na biya sadaki saboda shi ba."
Yana gama faɗin haka ya tura ta , ta faɗa saman gado ya bi ta ya danne da ƙarfin tsiya yake so ya haye mata ta fara mutsu mutsun hana shi cimma burin shi a zafafe ya kifa mata maruka biyu a saman fuskarta.
"Saboda jikin ki na aure ki, saboda haka in kika kuskura kika sake saka mini hannu sai na yi miki illah."
Ummu-Salma ta ji kamar duniyar ta tsaya mata cak, tana mai kallon Habib da idanuwanta masu zubar da ƙwalla, ko motsin kirki ba ta ƙara yi ba har Habib ya raba ta da kayan jikinta ya biya buƙatan shi son ran shi ya tashi ya bar ta nan, hawaye ne masu zafi suke zubo mata ta gefe da gefen fuskarta. A cikin zuciyarta take jin wani irin zafi zafin da ba ta taɓa jin irin shi ba tun da Amma ta kawo ta duniya, ta yi kuka ta yi kuka kukan nadama da baƙin ciki sannan a karon farko ta ji ta fara tsanar Habib, tunda har ya iya kai hannun shi jikinta sannan ya haiƙe mata ba da son ran ta ba, ta daina faɗa da shi ne domin a yadda ya zuciya zai iya yi mata illa ita da abin da ke cikin ta, ta fi awa biyu tana kwance tana kuka ta kasa tashi sai da ta ji ana ta sallar azahar a masallatan kusa sannan ta iya jan kafafunta zuwa tiolet ta tsarkake jikinta sannan ta yo wanka da alwala azaune ta iya yin salla har kuma ta gama ba ta daina hawaye ba. Fuskarta ta yi jajir in da Habib ya mare ta har da tashin hannayensa zuciyarta ta yi duhu tana mata suya haka ta yini a cikin wannan halin bai kuma hana Habib dawowa gare ta da daddare ba, ba ta sake ƙoƙarin hana shi ba ta bar shi ya yi duk abin da ya ga dama da ita ya tsallake ta ya barta tana fama da suyan zuciya da hawayen bakin ciki da tausayin kanta. Domin ba ta isa ta hana shi abin da ya aura sabo da shi ba.
Tun daga ranar zaman su ya sake juya teburi. Hatta kayan abinci kaf Habib ya kwashe su a gidan nan ma'ana ta dinga ci da kanta, store ɗin ta bai bar ko ƙwayan abinci ba sai abin da ba a rasa ba da kuma ta gani ba ta yi mgana ba domin ita ta riga ta gama aminta da duka kalaman Habib, da gaske ba ya son ta sannan saboda jikinta ya aure ta kuma tana bashi yana cigaba da mora. Duk lokacin da ya ji bukatarta zai zo gare ta ita kuma za ta kwanta ta buɗe masa har ya yi ya gama abin da zai yi ya tashi ba zai yi mata mgana ba itama ba za ta yi masa ba, tun in yana yi tana kuka har ta samu nauyin zuciya ta daina kuka sai dai idanuwanta na kallon rufin sama tana mai jin suya a cikin zuciyarta. Ta ɓoye ma kowa halin da ta ke ciki har Baffa Umaru sai da ya kirata ta ce masa komai ya daidai ta, ta riga ta gama sarewa da rayuwarta, gwara ta zauna a duk wani tsanani daga Habib kar ta yadda ya sake ta saboda in ya sake ta a yanzu ya gama cutar da ita. Duk wani abu da mace za ta yi taƙama da shi Habib ya ɗauke da ga wajen ta, ba ta da komai sai rai kawai sannan ba za ta koma gida ta bar ma su Baffa abin faɗe a anguwa da dangi ba gwara ta cigaba da zama a yadda Ubangiji ya zaɓa mata rayuwa. Za ta zauna da Habib ta ba shi abin da yake so matukar zai barta ta cigaba da zama da auran shi a kanta
Ko da yaushe Ammah za ta kirata tana tambayanta yadda take sai ta ce suna lafiya haka ma Baffa, har Hamma Abdulrrahman sai da ya kirata yana mata jan ido da cewa Baffa ya faɗa masa an samu masalaha yana ta jan ta mganar cewa in Habib bai daina maganar zubar da ciki ba kar ta ɓoye masa ta faɗa masa shi zai tsaya mata, amma ta ce komai lafiya bayan sum gama waya ta yi ta kuka, da ma a ce za ta iya da ta faɗa masa komai amma ba za ta iya ba suna zaman su lafiya ba za ta zama silan matsala da damuwa ga iyayenta da ƴanuwanta ba. Tun tana jin Habib a ranta har ta daina jin sa kwata-kwata ya tozarta ta ya ci mutumcin ta, ta koma sai ta fita ta siyo dan abin da za ta ci kuɗaɗe ne a hannunta sama da dubu ɗari amma sai da suka ƙare a wajen ciyar da kanta da zuwa asibiti, tunda ta sake komawa cikin ta har ya shiga wattani uku sannan ga shi likita ya ce jininta ya yi ƙasa tana ɓukatar cin ganyayyaki saboda inganta lafiyanta da abin da ke cikin ta, ba saboda kanta ba saboda gudun jinin dake tare da ita, shi take so domin duk halin da ta faɗa saboda kare shi da ta yi ne shi ya sa nan duniya babu abin da take so da ƙoƙarin karewa sai cikin jikinta. Kuma a haka dare na yi Habib zai zo ya biya buƙatar shi da ita ko a jikinsa. Tabbas saboda jikinta ya aure ta, kuma yana moran abin shi son ran shi, Ummu ta gama sakawa a ranta jikin ta ne kuma da man Habib ya kusa kai sa zuwa ga expearing date ɗin shi, gwara ta bar masa komai ya ƙarisa shi tundaa shi ya fara.
Baɗɗo ba ta nan ta tafi gidan kakanin ta a Mubi, Shamsiya kuma ta kwana biyu ba ta ji ta ba, ba ta kiran kowa wanda ya kira ta kuma ta yi masa ƙaryan tana lafiya. Mami ma ta kirata tana ba ta haƙurin cewa ba za su samu zuwa jimeta ba za su je Paris ita da megidanta da yara sai dai in sun dawo ko ita kaɗai za ta zo ta duba su. Sai ta ji daɗin haka domin ba za ta so wani na ta ya zo ya ganta a cikin wannan halin ba, kuma ta tabbata in Mami da diro Jimeta sai ta zo gidan ta kamar yadda ta saba abu ɗaya take yi da ke saka ta farinciki kallon girke-girke a wayanta sai ko salla da karatun Qur'ani amma Allah kaɗai ya san girman nauyin da ke cikin zuciyarta ita kaɗai ta san abin da ke muƙurƙusanta a cikin zuciyarta ƙarfin imani ne kawai ke riƙe da ita.
****
Shafewar sama da kwanaki arba'in Ummu Salma na cikin wannan halin rayuwan Ammah ta kira ta a waya ta shaida mata zuwan Hamma Jibo tare da matarsa da yara. Sai ta yi saurin ce ma Amma za ta zo ta gaishe su, a lokacin ma ba ta da ko sisi ballanta ta yi kuɗin abin hawa, duk kuɗaɗen dake cikin acct ɗin ta ta gama kashe su a hidimar kanta.
jiya ma waken da take dafawa ta haɗa da allaiyahu ya ƙare, kuma tun jiyan ba ta ci komai ba sai ruwan zafi kawai take sha cikinta na ɗagowa. Farkon cikin ne take laulayi ba ta iya cin abinci yanzu kuma da ta ɗan samu sauƙi tana ci ko da za ta yi amai haka likita ya ce saboda abin da ke cikin ta. Ba ta da kuɗi ta kuma rasa yadda za ta yi Allah ya dube ta a washegari Hamma Mustapha ya tura mata 10k kamar ya saka ta a aljannah haka ta ji ta kira shi tana yi masa godiya kamar za ta yi masa sujjuda.
Kuɗin sun zo mata a lokacin da take cikin matukar buƙatar su shi ya sa gari na wayewa ta shirya ta tafi kasuwa. Sai ta kwana uku ba ta sa Habib a idanuwanta ba wata rana ma ba ya kwana a gidan sai ranar da yake da buƙarar ta to tana ganin shi, shi ya sa game da fita neman abin da za ta ci da lafiyanta, in za ta fita za ta ce Allah kana gani na fita da izinin ka domin lafiyata da abin da ke cikina, sai ta saka kafarta ta fita to haka ta yi ranar ta je kasuwa ta kaso dubu takwas sauran ta dawo dasu domin ta yi na abun hawa zuwa gida gobe. Abin da ba ta sani ba tana fita ba daɗewa motar Hamma Jibo ɗauke da Matarsa Nauwara da yara suka shiga haraban gidan su, suka iske ƙofar bangarenta a rufe kuma Hamman na ta kiran wayan ta, tana ringing amma ba ta ɗagawa.
Megadi ya tambaya shi ya ba su tabbacin ta fita amma yana tunanin ba za ta daɗe ba sai Nauwara ta ce su zauna a mota su jira ta. Haka ko aka yi suna cikin mota suna hira Ummu Salma ta shigo gidan tana tafiya kamar za ta faɗi hijabi ne a jikinta amma duk wanda ya santa in dai ya ganta sai ya firgita da raman da ta yi sannan ta ɗan yi duhu hasken ta ya ragu, hannunta ɗauke da ledojin da ta auno shinkafa da fulawa sai wake da manja sai kayan ganye tun da yanzu ta daina cin mangyaɗa saboda ta fahimci in dai ta ci abincin mangyaɗa to ba za ta kwana lafiya ba bayan amai ta yi ta fama da tashin zuciya.
Ko kaɗan ba ta ma lura da motar dake bakin bangarenta ba, har ta nufi ƙofarta ta sauke kayan hannunta tana neman maƙulli a cikin jakar ta sai ji ta yi an kira ta kuma da sunan da aka kirata yan gidan su ne kawai ke kiranta da sunan sannan kuma ta jiyo murya kamar ta Hamma Mustapha.
"Auta."
Da sauri ta juya ba Hamma Mustapha ba ne, Hamma Jibo ne mamaki ya kamata sai da daburce.
"Hamma."
Ta faɗa cikin sauri nan da nan idanuwanta suka kawo ruwa da ta gan shi sai ta ji kamar ta warke da duka matsalolinta. Hamma Jibo ya kalli Nauwara itama ta kalle shi amma ba su yi mgana ba ya fara takawa zuwa ga Ummu sai ya ga ta kwaso gudu zuwa gare shi, ko da take gida in ya zo tana murna da ganinsa har ta zo ta riƙe mishi hannu amma ba ta taɓa faɗawa jikinsa irin na yau ba sannan lokaci ɗaya ta kece masa da kukan da ya ɗaga masa hankali.
"Hamma."
Ummu-Salma take faɗa cikin muryan kuka rike ta ya yi a zuciyarsa yana jin wani iri, me ya samu Ummu ne duk ta rame ta lalace haka?
Ɗago kanta ya yi lokaci ɗaya yana share mata hawaye da tafukan hannayen sa
"Ya isa haka Auta. Ya isa haka."
Ya ke faɗa yana sake share mata wasu hawayen da suka kwaranyo.
Nauwara na gefe ita da su Saudat duk jikinta ya yi sanyi yaran ma sun raɓe a jikinta suna kallon Babansu da Annin su, duk da yara ne amma suma sun ji wani iri fuskar su ta yi ɗif alamun damuwa.
"Me ya same ki Auta? Ko kin yi ciwo ne?
Ya faɗa yana kallon ta, sai ta basar da tambayan tana sakin shi wajen Nauwara ta nufa tana gaishe ta.
"Adda Nauwara ina shirin zuwa na gaishe ku ne fa."
"To ai duk ɗaya ne mu ba ga shi mun zo ba."
Ta ba ta amsa suna gaisawa ta jawo Saudat jikinta tana yi mata fillaanci sai ta ba ta amsa itama da fillancin amma ta haɗa da turanci. Ummu ta yi dariya ta ba ta hannu suka tafa lokaci ɗaya tana faɗin.
"Lalle za ku shirya da Amma yanzu."
Suka yi dariya gabaɗayan su Ammi na gefe ta yi karaf ta ce itama ta yi iya fillanci Ummu ta ce ta yi mata ta ji, bayan ta tambaye ta ina su Isma'il? ganin ba ta gansu ba da yaren fillanci sai kawai Ammi ta ma yar mata da amsar tambayanta da turanci.
Da cewa suna gidan wajen Ammah.
"Ke kam Ammi za ki ko shirya da takwaran na ki kuwa ?
Ammi ta tura baki tana rantsuwan ta iya, Saudat na cewa ba ta iya ba sai kawai Ammi ta fara kuka sai da Ummu ta rumgumeta tana lallashinta. Hamma Jibo ne ya ce a waje za su cigaba da tsayuwa sannan Ummu ta tuna da suna waje ne da sauri ta wuce gaba suka bi bayan ta, tana can ƙokarin neman maƙulli Hamma Jibo ya duƙa ya kwaso mata ledojin da ta ajiye a ƙasa.
"Auta Kasuwa kika je ne?
Ya faɗa lokaci ɗaya yana duba ledojin hannunsa
"E Hamma."
Ta faɗa lokacin da ta ɗauko key din tana ƙoƙarin buɗe ɗakin, shi ko jikinsa ne ya yi sanyi har sake leƙa ledojin ya yi ganin abubuwan dake ciki, sai ya sake ɗagowa yana kallon Ummu lokacin da ta buɗe ɗakin tana cewa su shigo, kallon matarsa ya yi itama ta kalle shi domin tana kusa da shi ne ta ga ƙulle ƙullen su manjan da ke ciki da shinkafa da wake da in an haɗa duka ba su wuce tiya ba.
Sai da suka shiga falon suka zauna ita kuma ta kwashi kayanta zuwa kitchen sannan ta kawo musu ruwan a jug na famfo ne da ta siya, Hamma Jibo ya sake shan mamaki a ran shi sai yana tunanin ko dai mijin Ummu ya samu matsala ne a wajen aiki?
Nauwara ma tunanin da take yi a cikin ranta kenan amma ba ta furta ba.
"Anni ni swanwater na ke so na sha ba wannan ba"
Cewar Saudat. Da ya ke da Annni ƴa'ƴan yayyenta suke kiranta a matsayinta na ƙaramar uwa a gare su.
Ammi na jin haka itama ta ce" Anni ni kuma hollandian zan sha."
Ta faɗa da harshen turanci, Ummu ta kasa mgana ta yi wani wiƙi-wiƙi da idanuwana duk Hamma na lura da ita.
"To yanzu dai ba ni dashi ku fara shan wannan sai na fita na siyo muku."
Ummu ta faɗa cikin yaƙe da dariya.
"Haba. Ƙyale su Auta rigima ce"
"Adda ki bari na fita ko megadi na ba ma saƙo ya siya musu."
Hamma Jibo ne ya saka baki ya ce Aa, yaran ma ya yi musu jan ido ya ce su ɗau ruwa su sha in ba za su sha ba su bar shi, dole suka ɗauka suka sha kaɗan Hamma ma ya sha shi da Nauwara, miƙewa ta yi tana faɗin me za su ci ta dafa musu?
Da sauri Hamma Jibo ya ce" Sai da suka ci abinci muka fito fa, Auta ki yi zaman ki kawai."
"Dad ni egg zan ci "
Ammi ta faɗa kamar za ta yi kuka wannan karon Nauwara ce ta balla mata harara kafin ta ce" Ba shi kike taso kika bari a gidan Ammah ba? Zan zane ki fa"
Ta faɗa mata cikin harshen turanci lokaci ɗaya tana hararanta Ummu duk ta zama wata iri sai yaƙe take yi amma da ka ganta tana cikin damuwa.
"Auta taho nan ki zauna kusa da ni."
Ya faɗa mata yana mai nuna mata kusa dashi jikinta a sanyaye ta zo ta zauna kusa da shi kanta a ƙasa.
"Auta me ke faruwa ne?
Ya tambaya yana kallon ta, sai ta ɗago tana kallon shi cikin yaƙe kafin ta ce" Me ka gani Hamma? Lafiya ta lau na yi ta zazzaɓi kwana biyu ne "
"Haka Ammah ta ce sannu?
Nauwara ta faɗa tana kallon ta, Amma ta faɗa mata Ummu na da ciki shi ke ɗan ba ta wahala wataƙila shi ya sa duk ta rame.
Hamma Jibo ya yi shuru yana kallonta ya kasa magana.
"Hamma ba fa komai Allah."
Ummu ta sake faɗa tana faɗaɗa mirmishinta wanda ba ta san bai boye damuwarta ba.
"Megidan na ki ba shi da aiki ne yanzu?
Cikin mamaki ta ce" Yana aiki me ka gani Hamma?
"Na ga kin siyo abinci Auta."
Ya faɗa kai tsaye yana kallon ta cikin nazarin ta. Sai ta kasa mgana, kanta na ƙasa amma hawaye take yi ganin haka ya sa Hamma Jibo ya ce Nauwara ta kwashi yaran su shiga ciki zai yi magana da Ummu Salma. Da sauri ta bi umarnin sa ta kwashi yaran suka shiga bedroom ɗin Ummu suka zauna.
"Auta ki faɗa mini abin da ke faruwa ni fa ɗan'uwan ki ne, zan yi komai domin ganin kin yi farinciki."
Kalamansa sake sake ruguza rauninta ta sake fashe masa da kuka, kanta ya dafa yana ɗan bubbugawa alamun lallashi, sai da ta yi kukan ta ya ishe ta sannan ta warware masa komai amma shima ta ɓoye masa abubuwa da yawa kamar yadda ta ɓoye ma su Baffa, sai dai ta bayyana masa ita ke ciyar da kanta tunda har ya gannin ma idanuwansa ƙarya ba na ta ba ne. Har da haɗa sun da aka yi waje ɗaya kamar an samu masalaha duk ta sanar da shi.
Hamma jibo ya ji wani abu ya kama shi na tausayin ƙanwarsa da jin haushin Habib cikin faɗa ya ce" Kuma kike zaune yunwa za ta kashe ki Ummu ga su Baffa a kusa?
Tana kuka ta ce" Hamma ina son aurena sannan ina son iyayena ba na so na saka su cikin damuwa."
"Ai cutar da kanki da kike yi shi ne zai saka su a damuwa Auta."
Ya faɗa yana kallon ta, tana hawaye ta ce" Ka yi hakuri Hamma."
Kanta ya jawo a saman kafaɗanta yana lallashin ta.
"Ya nuna ba ya jin maganar na gaba da shi tunda an masa mgana ya nuna ya ji amma bai ji ba, sakarai ne shi? Ta ina aka taɓa haka? Kawai sai ya ce sai kin zubar da ciki saboda ba shi da tunani?
Ya cigaba da faɗa Ummu na ta kuka tana faɗin Hamma ka yi haƙuri.
"Ya zama dole su Baffa su sake sanin halin da ake ciki."
Ya faɗa yana sakin ta lokaci ɗaya yana ƙokarin ɗauko wayarsa.
"In ba haka ba wata rana zaki mutu ba a sani ba, kin ga yadda kika rame? Kuma kina da juna biyu in wani abu ya same ki fa?
Da sauri Ummu ta sauko ƙasa ta duƙa tana faɗin" Don Allah Hamma ka yi haƙuri, kar ka sanar ma da su Baffa ba na so hankulansu ya sake tashi."
Tsayawa ya yi yana kallon ta cikin mamakin ta.
"Hamma ina son na tsira da aurena ba abin da ya rage mini a yanzu. Don Allah kar ka bari su Baffa su san abin da ke faruwa."
Ya rasa yadda zai yi da ita ganin tana ta kuka shi ya sa sai ya mayar da wayar shi aljihu yana faɗin" To na ji ya isa."
Ya saka hannu ya ɗago ta yana share mata hawaye miƙewa ya yi yana ce mata bari ya je ya dawo.
"Hamma."
"Zan dawo yanzu."
Yana gama faɗin haka ya fice, nan ta zauna tana kuka Nauwara ta fito ta same ta, tana kuka ba ta tambayi ba'asi ba ta zauna tana ta lallashinta Ammi ta yi barci Saudat ne idanuwanta biyu da ya ke akwai wutar nepa sai Nauwara ta kunna mata cartoon zaman shuru suka yi Ummu ta daina kukan amma ba ta daina ajiyar zuciya ba.
Ba daɗewa sai ga Hamma Jibo ya dawo Allah sarki ɗan'uwa. Kayan abinci ne ya siyo mata mai yawa kuma shi ya dinga ɗauka yana shiga mata da shi cikin store, Ummu ta yi hawaye ta yi kuka tana yi masa godiya ba abin da bai siya mata ba har kayan tea sannan ya tura mata 100k ya ce ta riƙe a hannunta. Ba su daɗe ba ya ce su tashi su tafi da alƙawarin zai faɗa ma Baffa halin da take ciki amma ba zai bari a kashe mata aure ba, sai dai za a sake kiran Habibu a ji dalilin shi na yi mata horan yunwa.
*Janafty*