1
by @surayyahms
*TALES OF THE WAZEERIS🦋* Arewabook@surayyahms
#Royal hate-love
#Forbidden bloodline
#Obsession
#royal politics
#Sisters love hate
Bismillah rahmanir raheem.
MULKI amanah ce...
SARAUTA hidima ce....
kujerar mulki tana bukatar JINI...
jinin cikakken magajin mulki da jinin baiwa ne kadai zasu haifo wa tsaftacciyar ahalin magaji.....
lokaci yayi da ahalin WAZEERIS VALE zasu zauna akan KUJERAR MULKI, amma hakan bazaiyu ba face sai sun hada JINI da ahalin babban MAQIYANSU wato ahalin sarki MURAD ZAMKORA,tsananin tsana me shirin haifar da wata ZAZZAFAR SOYAYYA!!!.
1:
Tun zamanin da babu addini, babu shari’a, babu tsarki. ahalin wazeeris tharim vale sune kadai cikakkun legitimate king makers a shahariyar yankin Tharim Vale, ahalin dabasa zama akan karagar mulki amma kuma sune suke da qarfin ikon yanke duk wani hukunci tare da dora sarkin da ya dace akan kujeran mulki a masauratu na tsawon shekarun da suka ga dama tare da saukeshi a lkcin da suka ga dama,..
suna da cikakken iko tare da karfin hukunci na zantar da duk wasu dokoki masu tsanani ko tsauri, sune suke zantar da Al'ada, snn su kawo tsaron jini ga ko wani ahalin sarauta, tare da kare ƙima da darajar duk wani babban masarauta dake karkashin yankinsu na Tharim Vale, snn akwai kakkarfar amincewa da yarda na cewa jinin zuriarsu tsaftacciyace.
Tharim Vale
(old zazzau)
5:30pm
Baqar jeji ne me duhun gaske irin wanda daga ka taka kafarka cikinsa sai kaji tsiƙar jikinka na tashi, wanda ko kudi aka baka wnn lkcin bazakace karfe 5:30 na yamma bane tsabar duhunsa da kalar siffar sa na abun tsoro...
fala falan korayen ganyen manyan bishiyoyi da suke tsaye tamkar gidajen sama sun saka wajen yay liiff har sai sun kada ake ganin hasken rana sosai, baka jin motsin komi face kukan tsuntsaye da dabbobi tare da dedekun bayi da manoma da suke cikin gonayensu adede wnn lkcin kowa yana saur sauri domin shirin komawa gida dan ba'a kasancewa cikin jejin tharim vale muddin magrib ya karato
ƙarfe biyar na yamma na cikawa iskar jejin ta tsaya cakk lokacin da wata ginanniyar mata take ratsa doguwar hanyar shigowa cikin jejin da katon fitila a hannunta wanda hatta iskar dake wajen baida ikon motsi ayayinda take tahowa ahnkli...
tsuntsaye da dabbobin jejin suka yi shiru kmr an danna musu pause, tana tahowa ahnkli ahnkli cikin wani irin dakakken nitsuwa me ƙaifi tareda sanyi me tafe da kamemmen jinin kasaita dake kwaranya ajininta a izzance.
matar ɓaka ce, gata da tsayi doguwa ce sosai kamar isha, saidai bazaka iya hango asalin cikakken siffar fuskarta ba sabida wani irin baƙar yadin fatar dabban jeji me kaurin gaske da aka saba yimata alkyabban sarauta dashi baki kirin dogo sosai yanaja har kasa...
gajiyayyun bayi da manoman tharim vale suna hangota kowa ya xubda abunda yakeyi daga hannunsa ya dago a gaggauce da tsananin rawan jiki da tsoro.
Ahankali kowannansu yafara aje aikinda yakeyi yana ra6ewa gefen ciyawa tareda sunkuyar da kai qasa sbd sautin tahowar "uwarjini" kasaitacciya queen mother of the wazeeris, ' maqboola hanim wazeeri.
Wanda sautin sarkan kafa na zinarin dake qafarta shine yake sanarda isowarta ko tahowartar tundaga nesa wanda tunda ta tashi arayuwarta ta taso tana shugabantar ahalin wazeeris tasaba duk inda take takawa sautin sarqoqinta ke sanarda tahowarta har izuwa yanxu data manyanta sbd dukiya, izza, tsafi, da ƙarfin iko da mulki dake yawo a cikin jininta.
ganinta ajejin adede wann lokaci kusan abu ne mai masifar tsoratarwa da kaÉ—a hanji dan izuwa yanzu kusan kowa yaji labarin irin halin tsananin ciwon da babban danta khaleefa wazeeri dake kan kujerarsu na tharim vale yake ciki..
Tana qarasowa hanyar
ta tsaya cakk gaban wani dattijo tare da É—ansa duk dama babu wanda yake da darajar daga idonsa sama ya kalleta tadora jajayen ruwan idonta dake cike da damuwa akan É—an mutumin nan harna tsawon mintuna can snn ta kalle mahaifinsa da murdadden murya ahnkli cikin izza tace" wannan yaron ba alheri bane agareka zai girma ya dawo muku bala'i da annoba gobe kafin asuba yayi kayi marmaza ka jefashi a rijiyan bayan gari ya koma daga inda ya fito..
...bata jira cewarsa ba cikin dauke kai ta ƙara gaba ayayinda karar sarqar kafartan ne kawai yake motsi jikin kowa yana rawa kar kar harsaida ta kusa kure layin bayin snn ta tsaya agaban wani jigataccen bawan Allah da matarsa da suka bala'in jimawa da yin aure amma basu samu haihuwa ba, da gefen idonta ta juyo takalle matar mutumin da jikinta yake wani irin tsananin rawa rawa dan sunsan irin ƙarfin tsafin maqboola hanim bata taɓa furta wani magana da bai zama gaskiya ba,.
matar kamr zata tsaki fitsari ajikinta ta dauke numfashinta cakkk jin maqboola hanim din batace komi ba ta miƙa doguwar hannunta mai kama da majici tafara shafa saman shafafen cikin matar tafara wani irin magana da cikin tamkar da ɗa aciki, cikin rashin fahimta mata da miji suke kallonta can snn ta kallesu tace "ina magana da abunda yake cikinki ne..
kai akasa da rawar murya matar tace amma ranki shi dade shekarunmu 22 kenan yau munakan neman haihuwa bamu samu ba.kanta na kasa ta sanar da maqboola hanim cikin girmamawa cewa bata taɓa daukar ciki ba..
karamin sace ajiyan zuciya maqboola hanim din tay snn tace "kina da tsohon ciki ynxu haka saidai idonki bazai iya nuna miki shi ba. yaro yay rarrafe daga cikin kasa ya shiga cikinki kuma har nayi magana dashi, xaki haifeshi lafiya..
tana furta hakan takalle mijin ahnkli cikin kauda kai tace saiku shirya haihuwar abunda zaizo ya kashe ku dan shidin rayayye ne..ku kuma matattu...
daga haka suma ta wucesu cikin kasaitaccen takunta metafe da jinin mulki da izza tabarsu acikin yanayin razana da tsananin tashin hankali sun rungume juna jikinsu na rawa tareda jiyo sautin karar sarkan kafarta akunnuwansu ayayinda ta kutsa kai cikin duhun jejin batare da alamar tsoro ba.
Har ta wuce cikin jejin babu wani mahaluki wanda ya iya kara saƙin numfashinsa bare kuma yay motsi bakajin komi a dokar jejin face takunta mai ɗauke da kawaƙƙiyar abin ƙafa na jinin sarauta masu sauti mai ban tsoro....
Daga ita sai dan fitilarta me disasshen haske ta isa bakin wani tsohuwar haikali a cikin dutse mai girma da fadi a tsakiyar dajin
snn ta shiga ciki, tana kaiwa ciki gaban wann tsauni ta durkusa kasa bisa gwiwoyinta a gaban babban bagaru nawani dutse mai kama da siffar mutum mai girma, wanda ke da ido masu haske awarwaron zinari dake hannunta tafara karka dawa a hankali cikin kulawa tamkar tana busawa wnn dutsin ne rai ta tsuguna can ƙasa hannunta a kan ƙafafunta snn ta ɗaga kai tace da murya mai ƙarfin tsiya amma cike da damuwa hannunta na rawa rawa tace
“Ya Mai Warkarwa, ruhin da ke mulkin lokaci da rayuwa, ji nin ɗana yana shanyewa a gado. cutar da yake fama dashi yasaka jinin jkinsa ya bushe, zuciyarsa tana bugawa a hankali ko ruwa ba ya iya sha. Ka gaya mini gaskiya, Shin zai rayu ko zai mutu? Inaso, in ji gaskiya, domin ni ce ke zaɓar sarakuna, amma yanzu ina neman cikakken taimako domin sanin makomar ɗa na da kuma jikoki na....
tana kammala furta hakan daji ya yi shiru na É—an lokaci..
can sai ga wata murya mai zurfi, kamar iska mai yawo a cikin ruhin dutsen tana fitowa daga bagaru da wani irin yasashhiyar sanyin iska me niimatacen sanyi wanda inbakada nitsuwa ajikinka zaka iya bingirewa da wani irin bacci da baka shirya masa ba...
ahnkli muryan yake cewa “ranki ya dade..uwarjini, haƙika kece ke da iko akan mulki da sihiri na zuriar tharim vale, amma kisani lokaci bashida iko a garemu duka, ɗanki shugaba khaleefa zai mutu...hakama jikokin ki maza, da yayansu maza, zamani izuwa zamani. face har sai anbi sharadin gyara.
jin amsar daya bata yasaka atake taji wani abu me tsananin zafi ya tsaya mata a kirji amma kuma ko kaÉ—an bata nuna alamar girgiza a fili ba...
cikin hadiyar zuciya ahnkli ta nutsa kai can ƙasa muryanta dake cike da baqin cikin jn wann batun kai tsaye tahaɗe ranta da wani irin jarumta tace “mene ne sharadin...
mai warkarwa Ka faÉ—a mini, koma menene zan bi shi dan ahali na su rayu..jinin wazeeri tharim vale ba jinin da zai gushe bane..har abada!!
cikin katseta Ruhin ya ce “Cutar da ke cikin ɗanki bata daga jikinsa, tana daga kuskurenki ne. wani laifin jini dakike aikata wa na rashin adalci da farraka zumunci a tsakanin ahalin wazeeri da ahalin zamkora.
Domin kuci gaba da rayuwa gabaki dayan ku, dole ne a haÉ—a wani tsaftacciyar yarjejeniya ko bakance da zai jawo ahada aure da jinin ahalin zamkora.
kisani suma jinin wazeeris ne wanda kika koresu a tharim vale shekaru dayawa, wanda kika kashe mahaifinsu imamu, kika shafesu acikin babin ahalin wazeeri vale da kuma kujerar iko. dolene Sai kun haɗa jini a aure. yaya ko yayan jikokin ki suzama daya a gidan sarauta, sannan nan ne jinin ki zai rayu. Wnnan ne kawai miki sharadi kuma tabbatacen tsira da magani. Idan ba haka ba, kowa daga ahalinki zai mutu a gaban idonki, kuma ikonki zai ƙare tare da rushewar tarihi me girma....SURAYYAHMS
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata
AREWAPEN
@SURAYYAHMS
TIKTOK:SURAYYAHMS
WATTPAD @SURAYYAHMS
WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED
#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025