the history
by @surayyahms
*TALES OF THE WAZEERIS🦋* Arewabook@surayyahms
#Royal hate-love
#Forbidden bloodline
#Obsession
#royal politics
#Sisters love hate
Bismillah rahmanir raheem.
2 The history.
akaro na farko da uwar jini maqboola hanim ta ji tsananin baqin ciki da tsoro mai yawa ya turkuneƙeta tare da tsaga mata kahon zuciya atake.,.
domin makiyansu ba wasu bane face wani bangare na jininsu da bayine suka haifesu wanda tay kokarin shafesu a doron qasa gabaki daya sbd ta tsaftace jinin ahalinta.
ahalin bayi guda daya da yarage musu kenan agarin zamkora da tariga takashe iyayen su da 'ya'yansu maza da yawan gaske ta kuma shafe tarihin duk wani shaida mekyau akansu sbd sune suka tsaya mata kmr qashin kifi a wuyarta,..
wannan yarjejeniyar haÉ—in aure da su zai zama wani babban abin kunya da kuma qasqanci a cikin tarihin rayuwarta dan ta tsani haÉ—a jininta dana bayi koda kuwa daga tsatson ta suka fito.....
saidai kuma ahalinta na wazeeris sune mata abinda tafi so a duniya fiye da rayuwarta ko kadan tasan bazata iya xuba idanu harsu shafe abanza ba
cikin runtse idanuwa da budewa taƙafe ƙafafunta a ƙasa ahnkli tace ma ruhin “xan aikata..zan amince da yarjejiyar haɗin aure guda daya tal daga jini na domin ahalina su rayu suyi tsawon rai Amma kaba ni wani alama da zai saka maqiya na su amince da haka dan bazan iya roqonsu ba..
kai tsaye ruhin ya ce “Kawo agogon sarauta da ke hannunki, dan lokaci shi ne ke nuna rayuwa da mutuwa. Idan kinje ki ba su sako, nikuma zan saka cuta me tsanani ta juya kan duk wanda ya kawo miki gardama. idan kika gama kulla yarjejeniyar dakanki tabbas kece da babban nasara.
ranta a bala'in dagule taja numfashi batace komi ba tamiƙa masa agogon ahnkli ruhin ya ɗauka. can sai ga haske mai ƙarfi yafito daga bagarun dutsen ya shiga jikin agogon, ya miqa mata ta karba ta tashi tsaye ta fito daga haikalin hannunta ɗaya riqe da fitilarra daya riqe da agogon ta kama hanyar ficewa daga jejin zuciyarta cike da tunanin yadda komi xai auku...
kowani tarihi yana farawa ne da mutum daya, dan haka ahalin wazeeris su suka fara kafa tarihin su anan tharim vale wanda sabida tsawon rai da mahaukacin madaran dukiya da Allah ya basu yasa suka kakƙabe babban waje agarin zazzau suka kafa garinsu na tharim vale...
suna daya kawai suke amsawa a zuriarsu wato shine wazeeris
ahalin waziri tharim vale sune suka fara kafa tutar mulki, ilimi, daqarun yaqi, dukiya, kaka da kankani har zuwa zamani...
ahali ne da Allah ya bawa tsananin tsawon rai, lafiya da kaifin basira, wanda tsawon ransu ya basu cikkken dama har suka iya dora hannunsu akan dumbin ma'adanai, yankoki, snn suna da cikakken ilimika na ɗa can can da ba'a san dasu ba wanda ya hada da sirrikan tsafi, ilimin taurari da kuma ƙarfin dakarun yaqi da tsaro.
hakan ne ya basu tabbatacen dama suka zama sune kadai suke cikakken ikon É—aura manyan sarakuna a kowani kusurwa na yankuna daban daban
sun mamaye manyan kafafen tarihi da sarauta kamar Dala, daura, zazzau, biram, baushe, maru...
snn kowani masaurata suna da yankunan su da wani rabin jininsu koda mutum daya ne daga zuriarsu ke mulka.
daga yankin dala suna da ahalin zamkora babban garinsu ne na jinin sarauta inda suke aje duk wani jinin su ko jinin wani sarki da baiwa ce ta haifesa shiyasa ake masa lakabi da masarautar bayi.
daga yankin daura suna da masauratar maru garin dake dauke da koguna da bakaken jeji na aljanu inda suke tsafi da duk wani abunda ya shafi surkulle da ido baiya iya gani.
daga masarautar baushe suna da garin nabutu city of story tellers masu aje musu labarukan tarihi mutane masu ilimi da kaifin basira ,daga can yankin biram suna da garin talashir wato mazaunun malamai kama daga na addini har na zamani....haka har yankin maruwa inda suke yankunan da ake jinya, noma, kiwo, da sauransu.
yankinsu na tharim vale ne kadai suka ajeshi a yankin zazzau, acan karshen gari shekara da shekaru suna saka ido akan komi dake gudanawa a kowani tsibirin yankuna da masauratu...
ahalin wazeeriz vale suna da ƙakkarfan garkuwa na sojojin yaqi, da murdaddun dabaru wanda ya dada sakawa koda ace babu ikon tsafi atattare dasu sudin ababen tsoro ne duba da tsananin karfin tsaro, ancient ilimi, narkakken dukiya, da kuma makaman yaqi da suke balain ji dashi zamani izuwa zamani..
tsawon zamanai da suka shude pure ahalin wazeeris basu hawa kan kujerar sarauta suyi mulki saidai sune suke da ikon zaɓa tare da dora sarki akowani babban masarauta dake karkashi yankin su na tharim vale da suka kafa.
har aka zo zamanin addinin musulunci mai girma kakan kakansu na karshe wanda zamaninsa bai dogara da tsafi sosai ba ya auro wata yar uwarsa uwarjini maqboola hanim.
itace mace na farko ajinin zuriarsu saidai tun tana karama wata rikitattacyar matsafiya ce maisuna fattu vale ta raineta, bayan mutuwar fattu da addinin musulunci yazo kowa ya karɓa, amma maqboola hanim bata wani ƙarba ba sabida gani take kamar tsafi wani babban jigonsu ne na al'ada da sirri dan haka bazata iya zubar dashi ba dan acikinsa ta taso
azamanin da suke iko daga ita sai mai girma wazeeri vale suke sha'aninsu, da wani dan uwansa imamu wazeeri data mugun tsaña sabida uwa kawai suka hada da ahalin wazeeris amma uban imamu bawa ne daga jininsu na yankin zamkora.
duk da ilimin addinin musulunci ya shige jinin mai girma wazeeri vale alkcin kuma yana kaunar step brother dinsa imamu amma haka maqboola hanim ta farraka tsakaninsu acewarta jinin ahalin wazeeris tsaftaccciya ce baxasu hada jini da jinin bayinsu ba.
wanda inda anbiye mata ma da tuni ta hallaka imamu ya zamto zuriar su babu wani digon jinin bayi aciki.
sautin ƙawakkiyar sarqaqin kafafunta kakeji acikin jejin yadda take tsaga duhun hanyar da fitilarta tana tuna tarihi can baya..
yadda jinkirin haihuwa yasaka batasamu yara da wuri ba, tsawon lkcin nan da suke zaune a agidansu na tharim vale, uwarjini maqboola hanim tay tsafi kala kala danta hana dan uwan mijinta imamu shima samun haihuwa sabida karma jinin bayi ya cigaba da yaduwa a zuriarsu musmn da itadin alkcin bata haihu da mijinta shugaba wazeeri vale ba tukuna.
ranar kwasam sai imamu yaje ziyara a yankin zamkora garin bayi asalin tsatson mahaifinsa..
inda ubansa yay zama a matsayin bawa wa ahalin wazeeris, tarihi yamemeta kansa imamu yay auren sirri da wata amintacciyar baiwarsa ana ce mata uwar jini jalilah.. wanda da ikon Allah atarawar farko baiwa jalilah ta samu cikinsa.
cikin jalila na boye a yankin zamkora har watansa uku sunakan renonsa, can can kafin nan maqboola hanim tasamu labarin cikin, saidai lkcin kuma bazata iyayin komi ba sbd Allah ya riga ya bata nata cikin itama data jima tana nema ...
acikin tsananin baqin ciki da tashin hankli na sanin cewa imamu data tsana zai kara haifo musu jinin wata kaskantarcyar baiwa acikin zuriarsu daga yankin zamkora take kwana take tashi
dan tunda tasamu labarin uwar jini jalilah zuciyarta ya zamto babu haske aciki face duhu da baqin ciki me tsanani.
dakqyar da wahala maqboola ta bari har baiwa jalila ta haifo wa imamu dansu kwalli daya me suna salim wazeeri ...
haifar É—a namiji da imamu yay da baiwarsa jalilah yakara hatsala ta, dan ta hakuntasu yasaka tay amfani da tsafi tasaka musu ciwo me tsanani inda tay amfani da wannan daman ta gurbata kunnuwan al'ummarsu akace uwarjini jalilah ce ta gurbata musu jinin zuriarsu.
lkcin wazeeri na kwance shima akan gadon ciwon da itace tadora masa ciwo, snn ta zamana tana da da cikakakken iko a lkcin na rubuta dokoki masu tsauri ta shafe imamu da jalila da dansu salim zuwa masarautar zamkora na dindindin snn ta saka jan biro acikin kundin tarihin rayuwarsu cewa kanin mijinta imamu da ahalinsa bazasu sake tako kafafunsu cikin gidansu na tharim vale ba, bazasu sake amsa sunan ahalin wazeeris ba. sann bazasu sake alaqanta kansu da ahalin tharim vale ba har abada.
tana korarsu agarin tharim vale kuwa ta yaye ma mijinta wazeeri ciwonsa wanda yasaka shima yafara aminta da batun cewa tabbas tarayyar dan uwansa imamu da baiwa jalilah shiya gurbata musu jini
daga nan gaba me tsanani yaginu atsakanin yan uwan jini..
rayuwa ahnkli tashude maqboola haneem ta ci kyakkwan nasarar farraka alaqa dake tsakanin mijinta wazeeri da dan uwansa imamu.
rashin fahimta, riƙo, tsana, da kiyayya mai karfi ya ginu a tsakaninsu.
imamu yahau dokin zuciya ya dawo yana amsa sunan asalin tsatson ubansa wato zamkora.
tun bayan haihuwar dansa salim maqboola hanim bata sake ɓari an sake haifar wani ɗa namiji daga yankin zamkora ba, ko sun haifa zata kashe shi ta yaqi ko ta tsafi ahaka saida ta kashewa imamu yaransa maza guda goma casss, dan babban burinta shine ta shafe jinin bayi daga ahalin wazeeris gabaki daya
babban É—an imamu wato salim ya zama shugaban yankin zamkora bayan maqboola taci nasarar kashe babansa imamu da tsafi...
babban É—anta khaleefa kuma yazama shine ayanxu yake shugabantar tharim vale dake mijinta wazeeeri vale shima ya rasu bayan ta haifa masa yara guda uku bayan khaleefa(Imran, zafar da ummu salma) ya rage ita dasu ke da ikon dora sarakuna na tsawon lokaci.
babban danta khaleefa yakai shekara 47 yana shugaba da matarsa nana hafsa ya haifi dansa abdallah shima da matarsa hajarat sakeena da babban dansu shamsan wazeeri da kuma ya mace Rihanna wazeeri wacce ta zamo yar autarsu..
salim dan imamu da maqboola hanim tariga ta dora masa ciwon mutuwa me tsanani shima bayan ta kashe masa yaransaaza guda goma daqyar ta bari ya haifi dansa kwalli daya rayayye wato murad zamkora da matarsa hajiya amani noorain wacce duk ta haifi É—a namiji itama sai ya mutu, karshe y'ay'a mata ta haifa rayayyu, Arisha zamkora da kuma ushna zamkora kafin nan mahaifarta ya lalace gabaki daya.
ya zamana acan ahalin zamkora bayan murad da Allah yariga yace shi rayayye ne, uwarjini maqboola bata kara bari sun haifi da namiji ba kwata kwata dan jira take ciwo ya gama nakasa salim din ya mutu ta dorawa murad din shima ciwon mutuwa ya mutu shikenn taci nasarar shafe tarihinsu tunda yara mata kawai guda biyun nan ta kyalesu dashi..
tsananin kiyayya da gaba maizafi yacigaba da wanzuwa acikin wannan ahalin.
wanda akasari uwar jini maqboola hanim itace kekara hura wutar wannan tsana da gaba tana dada hassashi zamani izuwa zamani face saida yanxu da ruhin tsafinta ya nemi ta wanke hannunta daga tarin jinin kashe kashe datayi na zuriar ahalin imamu ta hanyar kulla wani kkkarfan alaqar aure tsakanin jininta dana ahalin zamkora koda sau daya ne sabida kar zunubinta ya jawo annoba me tsanani akansu gabaki daya.
tana takawa ahnkli Haikalin ya yi shiru sosai, acikin nazari take tahowa tsawon lokaci bata numfasa ba.
Sai can ta daga kai a hankali Idanun ta suka koma ja kamar wuta...
cikin ranta tace “Idan jinin Zamkora ne kadai zai ceci rayuwar ahalin Wazeeri toh sai na kwace duk wani qarfi da ikonsu a tafin hannu na ko da kuwa duniya zata ƙone ne....
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata
AREWABOOKS
@SURAYYAHMS
WATTAPAD @SURAYYAHMS
WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED
#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025