Diyam

Episode Twenty Nine: The Broken Heart

by @mamanmaama

Inna ta saka na zagaya na gaishe da mutanen gidan, kuma kowa naje sai ta yi comment akan girman da nayi, ni kuma sam banga wani girma da nayi ba na dai san cewa kirjina ya kara cika amma bayan shi ban kara komai ba. Ina dawowa dakin Inna na tarar an aiko min da abinci kala kala daga gurin Hajiya Babba, Inna tace "da yake surukar ta tazo shine ta aiko mata da abinci, amma mu yaushe rabon da muga kwano daga dakinta" ni dai bance komai ba na fara bubbuda flasks ina zaben abinda zanci, na samu wani farfesun kaji na ja gefe na fara ci. Ina cikin ci Hajiya Yalwati ta shigo, ta kalli lodin abincin tace "hmmm. Ana cewa babu kudi bayan kudin suna can a inda aka ajiye su" Inna tayi dariya tace "ke kam ba kya rabo da bakar magana". A dakin Inna na wuni, sai da yamma ta tura ni inje in gaida Alhaji, kuma in shiga gidan Kawu Isa suma in gaishe su. Sai a lokacin na fahimci cewa ashe Alhaji Babba bashi da lafiya yana kwance. Ina dawowa sai ga sako dafa Hajiya Babba wai inje an gyara min daki a gurinta inje in sauka a can. Naki zuwa nace ace mata na gode amma a gurin Inna zan zauna, sai nayi sa'a kuma Innar bata matsamin in tafi din ba. Da daddare Inna take gaya min cewa gobe ne zata fita daga takaba, ashe shine dalilin da yasa aka dauko ni. Sai na tambayeta "Mama zata zo goben?" Inna tace "inajin zata zo, wani abun ne?" Nace "dama wata tambaya nake so inyi mata" ta zauna a kusa dani tace "tambayar me fa?" Sai na fara jujjuya hannuna ina feeling uncomfortable, ni ban saba irin wannan maganar da Inna ba dama Ummah ce da sauki. Sai data sake tambayata sannan nace "so na ke inji, wai dama in mutum yayi aure sai ya daina period? Dama matan aure basayi?" Sai ta tashi ta bude wardrobe kamar mai dauko wani abu, ta jingina kanta da kofar tace "yaushe rabon da kiyi?" Nace "tun kafin.....tun kafin biki" tace "wata uku kenan ko?" Na ce "eh" tace "matan aure sunayi Diyam, sai dai in matar aure tana da ciki ne bata yi" naji kaina ya kulle nace "ciki?" Sai kawai ta juyo tana kallo na, na dan yi shiru ina tunanin kalmar ciki sai kuma lokaci daya naji tamkar an ciro zuciyata an buga ta da kasa ta tarwatse. Nayi saurin rike kirjina na zamo daga kan gadon na fado kasa, a hankali na fara kiran innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Inna ta taho da sauri ta rike ni tana kokarin daga ni amma na dunkule a guri daya danji nake yi tamkar idan na mike zuciyata zata fado daga kirjina. Amma hawaye yaki zuwa idona, kalmar ciki ce kawai take yawo a kaina, wai ciki nake dashi ni Diyam kuma cikin ma wai na Saghir wannan wacce irin jarabawa ce, wannan wacce irin rayuwa ce. Har yanzu banyi accepting Saghir a matsayin miji na ba ballantana kuma in karbe shi a matsayin uban yayana. Inna ta rike ni tana cewa "haba Diyam, menene hakan kuma daga maganar ciki? Ciki ai kyautar Allah ne in aka same shi murna ya kamata ayi a kuma godewa Allah" sai na kifa kaina a jikinta ina j an numfashi da kyar. Na rufe ido na ina tunano fuskar Sadauki. Wannan cikin tamkar yayi sealing aurena da Saghir ne, tamkar ya tabbatar da rabuwa ta da Sadauki kenan. Ranar yadda naga rana haka naga dare. Ina jin ko lokacin da aka daura min aure da Saghir ban shiga irin wannan tashin hankalin ba. Sai bayan nayi Sallar asuba sannan nayi bacci dan haka har mutane suka fara zuwa yiwa Inna gaisuwa da kuma taya ta murnar fita daga takaba ban tashi ba, daga baya ma dana farka sai na yi kwanciya ta har saida naji muryar Mama sannan na tashi na gaisheta. Ta bini da kallo kamar mai accessing dina, wannan yasa na koma na kwanta na lulluba dan ji nake yi kamar duk wanda ya ganni yana iya hango cikin jikina. Ina kwance Mama ta shigo tace "Diyam taso ki raka ni unguwa" da sauri na mike ina straightening hijab dina dan ba karamin gajiya nayi da gidan da duk mutanen da ke cikinsa ba. Muna fita muka shiga motar da tazo da ita, Mukhtar yana ja muka tafi sai na gan mu munzo wani asibiti, naji gabana ya fadi ina tuna ranar da aka kaini asibiti naga gawar Baffa, ranar da rayuwata ta tarwatse. Na tambayeta "Mama waye bashi da lafiya?" Tace "ba kowa, ke na kawo ki ga likita" sai na sunkuyar da kaina a raina ina cewa Inna ta gaya mata kenan. Da yake asibitin kudi ne dan haka muna zuwa aka dauki jini na for a confirmation test, mu ka zauna jira sai kuma aka kira mu dakin likita, muka shiga suka gaisa da Mama sannan nima na gaishe shi ya dauko result din yana kallona yace "Halima Usman Kollere?" Na gyada masa kai, yace "how old are you?" Nace "14" sai naji kalmar 14 din tana burning a kirjina. Ya girgiza kai yana kallon Mama yace "how comes? Yarki ce?" Ta gyada kai tace "yar yaya tace, mahaifinta ya rasu shine yan uwansa suka aurar da ita ga dansu" ya girgiza kai yana kallona sannan yace "well, she is pregnant. Zamuyi scanning dai muga wata nawa ne sannan muga in ya shiga yadda ya kamata, za kuma mu duba lafiyar mahaifarta in zata iya daukar nauyin cikin" nayi sauri dago kai ina kallon doctor din, da rawar murya nace "doctor please ka cire cikin nan bana so" Mama tace "kul Diyam, kar in sake jin kince ba kyason abinda yake cikin ki. Allah ne fa ya baki ajjiya, ba naki bane ba na Allah ne kuma shi kadai zai karbi kayansa a lokacin da yake ganin ya dace". Muka je na kwanta akan gado Mama tana rike da hannuna da yake rawa saboda tsoro. Doctor ya zuba min wani abu mai sanyi a mara ta sannan ya fara goga wata roba akai yana kallon screen din gabansa, can sai naji yace "wow wow." Ya juyo yana kallon Mama yace "we are having twins here". Bayan an gama scanning din mun koma mun zauna yace "gaskiyar magana yarinyar nan tayi kankanta, bayan rashin shekaru gashi kuma tana da kankantar jiki, she can carry the pregnancy but I strongly suggest that kar a barta tayi labor, musamman tunda she is carrying multiple a shawarce da ta kai around 36 weeks ku kawo ta a cire babies din saboda lafiyar ta" Mama ta gyada kai da sauri tace "insha Allah doctor hakan za'ayi" ya tura mu mukayi sauran tests sannan ya rubuta mana drugs ya sallame mu. Hankalina idan yayi dubu to duk ya tashi, dan tunda doctor yace twins ne bankara magana ba dan in nayi ma inajin muryar ba zata fita ba. Wato ba daya ba, ƴaƴan Saghir guda biyu ne a cikina. Har muka zo gida bance komai ba ina dai jin Mama tana tayi min bayanai da yadda zan kula da kaina da abincin da ya dace in ke ci, ni dai na jingina kaina da kofar mota kawai na rufe idona. Muna packing su Salma suna fitowa ita da Aysha zasu tafi gidajen su, bana son magana dan haka ko kallon su banyi ba nazo zan wuce ta kusa dasu Salma tace "oh su Diyam manya, kamar ba itace nan take ta koke koke ba wai bata son auren hamma amma gata nan harda ciki. Ni ko zan so inga yadda akayi cikin nan". Sai suka kyalkyale da dariya. Har na taka step zan shiga palo sai na tsaya ina juya kai, it is hardly a gaya min magana inyi shiru and this is not going to be the first time. Na juya na sha gabanta nace "yes bana son yayanki kuma har duniya ta nade ba zan so shi ba ko da kuwa zan haifa masa duk mutanen da suke duniyar nan. Ni ma kuma zan so ace kinga yadda akayi wannan cikin dan a lokacin ne zaki tabbatar cewa yayanku is nothing but a monster, a big for nothing monster". Mama tazo da sauri ta jani muka wuce, amma naji dadi a raina. Mu da muka zo da niyyar kwana biyu sai da mukayi sati. A cikin satin na fahimci abubuwa da yawa, na farko shine arzikin Alhaji Babba ya ragu sosai, dan naji ana cewa yanzu shagunan sa na kantin kwari ne kadai suke functioning. Abu na biyu Inna tana cikin damuwa game da negligence da take fuskanta a gidan, babu wanda yake daukan abinsa ya bata dan zumunci sai dai idan ta roka, hatta sabulun wanka da wanki sai ta roƙa za'a bata. Da safiyar ranar da zamu tafi Inna ta dauko wasu kudi ta bude hannu na ta saka min, nace "kudin menene wannan?" Tace "kudin sadakin kine" na kalli kudin ina jujjuya su sannan nace "me zanyi dasu?" Sai tayi murmushi tace "ki sayi wani abu dasu, duk abinda kike so" a hankali nace "ni babu abinda nake so Inna, ni yanzu babu abinda nake tunanin zai saka ni farin ciki, Sadauki shine farin cik i na kuma a yanzu bana jin zan kuma ganinsa har abada". Sai na bude hannunta na saka mata kudin nace "ki karbi wannan kudin Inna dan Allah ki dauki Asma'u ku bar gidan nan. Ki koma gida ki samo masu rabon gado su fitar wa da Ummah gadon ta a gidan mu ki damka a hannun yaya Ladi ko Sadauki. Misali in aka fitar masu da dakunan Ummah sai su fitar da kofa daban. Dakunan ki kuma zaki iya saka yan haya a ciki ke kuma sai ki zauna a dakunan Baffa. Kinga kudin hayar zaki iya wani abu dashi sannan kuma zaki samu security yafi ki zauna ke kadai. Kudin nan kuma dubu hamsin sai ki kama sana'a dasu, idan ba zasu isa ba sai ki siyar da kayan dakin ki ko na dakin Baffa ki kara. A yanzu abinda zai sani farin ciki Inna shine in gan ku a farin ciki". Sai naga hawaye yana fita daga idonta, tayi sauri ta goge tace "Diyam. Ni a tunani na abinda nayi miki shine dai dai, amma na rasa me yasa na kasa jin farin ciki a zuciya ta" sai ta dawo min da kudin hannuna tace "bazan karbi sadakin ki ba Diyam. Ki ajiye su, wata rana zasu yi miki amfani" nace "to Inna zaki tafi din?" Nan ma sai ta girgiza kai tace "ba zaki gane ba Diyam". Sai nayi shiru ina kallonta, sai nayi realizing wani abu, ba wai gidan Alhaji Babba ne bata son bari ba but she is not strong enough to stand on her own, tana bukatar shoulder da zata jingina da ita. Na tuna cewa a kauye aka haife ta a can kuma ta girma ba tare da tayi karatun boko ba, sannan aka aura mata Baffa ya taho da ita Kano ya ajiye ta a gida. Tunda na taso ban taba ganin Inna da ƙawa ba, babu wanda ta sani sai Mama da Aunty Fatima sune kawayenta, in dai Inna ta fita unguwa to in ba gidan su ba to gidan Alhaji Babba ko kawu Isa, gaba daya rayuwarta tana revolving ne around them. Wannan ne ya kara banbanta ta da Ummah tunda ita Ummah tayi karatu a hannun Alhaji Bukar dan haka ta waye sosai tayi kawaye, sannan kuma ga auren da tayi duk da bansan yanayin gidan auren nata ba amma na fahimci ya kara buda mata idonta dan wani abun in tayi zaka yi mamakin cewa tashin kauye ce. Wannan yasa yanzu it will be hard for Inna ta tsaya da kafafuwanta, ko kuma tayi challenging Alhaji Babba. Maybe nan gaba. A ranar da muka koma gida ni da Uwani sai naji gidan yayi min wani iri, kuma nasan hakan yana da dangantaka da sanin da nayi cewa ina da ciki, twins, cikin Saghir. Naje dakina can wani lungu na saka kuɗin sadakin da Inna ta bani dan har a raina bana jin zan iya amfani da kuɗin dan a ganina in nayi amfani da su kamar nayi accepting auren Saghir ne. Da dare sai na bude balcony din da yake hade da palon sama. Na tsaya na lunshe idona ina jin dadin iskar da take kadawa, na bude idona naga sky ta cika da stars ga wata ya zama full. A hankali nace "Sadauki where are you?" Sai na tuno abinda ya taba fadamin "You Are The Only Star In My Sky" na shafa marata ina tunanin babies din da suke ciki amma sam banji wata soyayya tasu a raina ba. I can give anything to have them taken away from me. Da Sadauki na shirya haihuwa, dashi na shirya rayuwar aure. Da Sadauki nayi wannan plan din, dashi na shirya zanyi rayuwar aure har in samu ciki har in haifa mana ya'ya. Mace mukayi fatan zamu samu daga farko sai mu saka mata Subay'a sunan yar tsana ta, daga nan sai mu haifi namiji mu saka masa sunan Baffa mu kira shi da Junior.......... Na rufe ido na "Ya Allah take my life please, ya Allah end my suffering please" Sai na rike railers din gurin na durkusa ina kuka a hankali. The first tears da nayi shading tun first night dina a gidan.